Skip to content

Gudawa

Gudawa na nufin samun sauyi ko yanayin sako-sako ko bahaya mai ruwa. Tana faruwa sosai a tsakanin yara da manya, kuma yawanci takan tafi da kanta a cikin ‘yan kwanaki. Idan ba ta tsaya ba ko kuma idan ana fuskantar wasu alamomi kamar zazzabi ko gudawar mai jini, sai a tuntuɓi likita ko masu ba da magani. Gudawa na canja yanayin bahaya zuwa ruwa-ruwa kuma akai-akai.

Yawancin lokuta na gudawa ba ta buƙatar gwaji ko magani.

Gudawa ita kadai ba cuta bace amma alamace da take nuna cewa wani abu yana tafiya ba dai-dai ba a jikin dan’adam. Gudawa ita ce mutum ya samu sauyin bahaya kamar karuwar yawansa (sau hudu ko fiye) a rana, canjin yanayinsa ba kamar yadda mutum ya saba yi ba. Bugu da kari, yana da matukar muhimmanci a gane cewa yara ƙanana musamman na goye sun fi manya nesa ba kusa ba shiga cikin haɗarin kamuwa da gudawa, kuma yara sukan galafaita sosai fiye da manya a duk lokacin da suka yi gudawa musamman ma idan aka yi rashin dace ta zo da amai.

Wasu lokuta gudawa alama ce ta wani yanayi mai tsanani. Tana iya sa wa mutum ya rasa ruwa mai yawaba jiki wato (dehydration) ko kuma ta hana mutum samun isasshen sinadarin abinci mai gina jiki. Yana da mahimmanci a san abin da za a nema yayin gudawa da kuma lokacin da za a ga ma’aikacin kiwon lafiya da kuma tsawon lokacin da take ɗauka kafin ta tsaya.

Nau’ikan gudawa

Gudawa tana da sunaye daban-daban dangane da tsawon lokacin da take ɗauka:

• Gudawa mai tsanani

Gudawa mai tsanani ita ce mai sauya bahaya cikin sauri ta zama kamar ruwa, takan kai tsawon kwana ɗaya zuwa biyu. Ita ce mafi yawan nau’in gudawa kuma yawanci tana tafiya ba tare da magani ba.

• Gudawa mai ci gaba

Irin wannan gudawa tana ƙaruwa ne bayan farawa, tana ɗaukar kimanin makonni biyu zuwa huɗu kafin ta tsaya.

• Matsananciyar gudawa

Matsananciyar gudawa tana ɗaukar sama da makonni huɗu ko ta zo tana tafiya akai-akai na tsawon lokaci. Irin wannan gudawa da ke dadewa na iya nuna wani yanayi mai tsanani wanda ke tilasta ziyartar maaikacin lafiya.

Waɗanda ke kamuwa da gudawa

Gudawa yanayin bahaya ne mai ban mamaki, wanda ke shafar mutane a kowane zamani. Yawancin manya suna kamuwa da gudawa sau ɗaya a shekara, yayin da yara sukan kamu da shi sau biyu a shekara.

Abubuwan da ke haifar da gudawa

Babban abin da ke haifar da gudawa shi ne kwayar cutar da ke cutar da hanji  (gastroenteritis). Wasu suna kiran ƙwayar cutar da ‘stomach flu’ murar ciki. Baya ga wannan kuma gudawa na iya afkuwa bisa dalilai da yawa.

Cututtuka

Kwayoyin cuta (virus, bacteria da parasites) duk suna iya janyo cututtukan da ke haifar da gudawa. Mafi yawan sanadin gudawa a jikin manya shi ne ‘norovirus’ mai haifar da gastroenteritis. Rotavirus  shi ne mafi yawan sanadin cutar gudawa mai saurin gaske a jikin yara.

Abinci mai guba

Ana iya cin guba mai cutarwa da ƙwayoyin cuta daga gurɓataccen abinci ko abin sha. Da zarar sun kasance a cikin hanji, ƙwayoyin cuta na iya haifar da gudawa.

Wasu magunguna

Akwai gudawa da ke zuwa sakamako ta’ammali da wasu magunguna. Misali, magungunan riga-kafi suna kashe ƙwayoyin bakteriya masu cutarwa waɗanda ke sa rashin lafiya, amma suna iya lalata wadanda suke taimakon garkuwar jiki. Rashin isassun ƙwayoyin bakteriya masu kyau na iya haifar da gudawa. Har ila yau, cutar gudawa sakamako ne na wasu sinadaran anacids da magnesium da wasu magungunan kansa.

Abincin mai wahalar narkewa

Waɗanda ba sa iya sarrafa sinadarin lactose, wani nau’in sukari ne, suna iya kamuwa da gudawa saboda jikinsu zai yi ta ƙoƙarin narkar da sinadarin. Wasu mutanen suna fama da matsalar narkewar fructose, wani nau’in sukari da ake samu a cikin zuma da ‘ya’yan itatuwa. Cutar celiac na iya haifar da gudawa saboda jiki na fuskantar matsalar sarrafa sinadarin gluten, wani nau’in furotin ne a cikin alkama.

Cututtukan da ke shafar hanji

Gudawa alama ce ta gama-gari ta yanayin da ke haifar da kumburi a cikin hanji. Cutar Crohn, ulcerative colitis da ciwon hanji (IBS) duk na iya haifar da gudawa. Damuwa da tunani na iya rura wutar alamomin gudawar idan ana fama da cutuka kamar IBS.

Yanayin da hanji ke ciki

Mutane da yawa suna fama da gudawa bayan aikin tiyata a hanjinsu. Yana iya ɗaukar ɗan lokaci kafin sashin narkewar abinci ya zuƙi abubuwan gina jiki daga abincin da ake ci, kuma ya haifar da ƙaƙƙarfar bahaya.

Alamomin gudawa mai sauƙi

Babban alamar gudawa ita ce yin bahaya mai ruwa-ruwa. Sauran alamomin na yau da kullun sun haɗa da:

  • Ciwon ciki.
  • Tsananin buƙatar yin bahaya akai-akai.
  • Gurbacewar ciki.

Waɗannan alamomin yawanci ba sa buƙatar ziyartar asibiti, musamman idan ba su wuce ‘yan kwanaki ba.

Alamomin gudawa mai tsanani

Matsalolin gudawa mai tsanani na iya nuna alamar buƙatar tallafin likitoci, kamar kamuwa da cuta mai tsanani, wanda ba za a iya waraka ba ba tare kulawar likita ba. Idan gudawa ta haɗa da waɗannan alamomin da ke tafe sai a tuntuɓi likita;

  • Zazzaɓi
  • Tsanani ciwo
  • Yin amai
  • Jini ko majina a cikin bahaya
  • Raguwar nauyi wannan na iya zama alamar cewa jiki ba ya samun isassun sinadaran gina jiki.

Ƙarin alamomin gudawa

Ana iya fuskantar ƙarin wasu alamomin da ke da alaƙa da gudawa ciki har da rashin ruwa a jiki ko kuma;

  • Ciwon kai
  • Bushewar fata
  • Yanayin damuwa da rudani
  • Tsananin tashin zuciya da amai
  • Ciwon kai sama-sama da juwa
  • Gajiya wacce hutawa ba ta magance ta
  • Fitsari mai duhu, kaɗan ko ma rashin  fitsarin
  • Yin amfani da nafkin guda shida a rana (ga jarirai)
  • Rashin danshi a matse-matsin yara na tsawon awanni takwas
  • Rashin hawaye lokacin kuka (ga jarirai da yara)

Matsalolin gudawa

Rashin ruwa yana daya daga cikin manyan matsalolin gudawa. Wannan na da tasiri musamman a tsakanin jama’a masu rauni (jarira da manya’yan shekaru 65 da tsofaffi da kuma mutanen da ke da raunin garkuwar jiki). Idan ba a yi magani ba, rashin ruwa na iya haifar da gazawar ƙoda, bugun jini, bugun zuciya ko ma mutuwa gabaɗaya.

Gwaje-gwajen gudawa

Yawancin lokuta na gudawa ba ta buƙatar gwaji ko magani. A yanayin mai tsanani, likita zai yi gwaje-gwaje don gano dalilan gudawa. Likita na iya yin gwaje-gwaje kamar haka:

  • Gwajin jini don kawar da wasu matsalolin da ke haifar da gudawa.
  • Gwajin bahaya don bincika jini, cututtukan ƙwayoyin bakteriya da ƙwayoyin cuta.
  • Gwajin numfashi na hydrogen don bincika rashin matakin sinadarin lactose ko fructose.

Magungunan gudawa

Yawancin lokaci, za a iya kawar da gudawa a gida. Likita na iya ba da shawarar yin amfani da magunguna kamar:

  • Maganin riga-kafi ko antiparasitics. Waɗannan magungunan suna kashe ƙwayoyin bakteriya masu haifar da kamuwa da cuta.
  • Magungunan da ke kula da yanayi na yau da kullum. Magance yanayin da ke haifar da gudawa, kamar cutar ciwon hanji mai kumburi (IBD) da IBS, na iya taimakawa.
  • Probiotics. Probiotics suna shigar da ƙwayoyin bakteriya masu kyau a cikin hanji don magance gudawa.

Magance gudawa a gida

Sau da yawa ana iya kawar da gudawa mai tsanani ta hanyar sauye-sauyen da dabarun da za a iya yi a gida. Daga cikin hanyoyin da za a bi akwai;

  • Sha ruwa mai yawa da sauran abubuwa masu ruwa-ruwa. Waɗannan sun haɗa da ruwan ‘ya’yan itace da aka matse. Waɗannan abubuwan sha suna maye gurbin ruwan da ya ƙone da kuma sinadarin electrolytes da ake rasawa a yayin gudawa.
  • A zaɓi abincin da zai tabbatar da lafiyar jiki. Wasu abinci masu ƙarancin sinadarin fiber suna sa bahaya ta yi ƙarfi.
  • A guji abinci da abin sha da ke da iskar gas. A guji wake, kabeji, brussels sprouts, giya da abubuwan sha na sinadarin carbonate don daƙile ciwon ciki. Wasu lokuta, gudawa na iya haifar da matsalar lactose na ɗan lokaci.

Hanyoyin riga-kafin gudawa

Ba koyaushe za a iya daƙile gudawa ba, amma ana iya rage haɗarin kamuwa da ita saboda cututtuka ko gurɓataccen abinci. Ga wasu hanyoyin riga-kafin kamuwa da gudawa:

  • A lizimci tsafta kodayaushe, a wanke hannaye da sabulu da ruwa bayan shiga banɗaki ko yayin cin abinci da bayan an gama.
  • Allurar riga-kafin rotavirus na hana yaɗuwar ƙwayoyin rotavirus, sanadin gama-gari na gudawa. Alurar riga-kafin COVID-19 na iya rage haɗarin samun COVID da fuskantar alamomin COVID, akwai gudawa.
  • A ajiye abinci a daidai yanayin zafi, kuma a rika dafa dukkan abinci har sai sun kai ga yanayin da ake so. Kada a cin abinci ko abin sha da suka wuce kwanakin ƙarewar su.
  • Kada a sha ruwan da ba a kula da shi lokacin da ake tafiya. A guji ruwan famfo, kankara ko goge hakora da ruwan famfo.
  • A guji danye ko naman da ba a dafa shi ba (da shellfish), da danyen kayan marmari. ‘Ya’yan itacen marmari da ganyaye yawanci suna da amfani ga lafiya, amma ganyensu da ɓawo na iya ƙunsar gurɓatattun abubuwa waɗanda za su iya kawo rashin lafiya.

Manazarta

Cleveland Clinic. (2024, December 26). Diarrhea. Cleveland Clinic.

Healthdirect. (2024, October 31). Dehydration. Healthdirect.

Mayo Clinic. (2021b, October 14). Dehydration – Symptoms & causes.  Mayo Clinic.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×