Haɓo shi ne zubar jini daga ƙwayar halittar tissues a cikin hancin mutum. Wannan lamari ne na kowa kuma ba a cika damuwa ba. Haɓo zubar jini ne daga hanci, wanda aka sani a likitance da epistaxis. Haɓo ya zama ruwan dare saboda matsayin hanci da kuma yawan jijiyoyin jini. Yawancin ba su da tsanani, amma wani lokacin zubar da jini zai iya haifar da wani yanayi mai tsanani, kamar cutar sankarar ɓargo.
Hanci cike yake da magudanan jini, shi ya sa ko da ƙananan raunin da ake fuskanta na iya sa hanci ya zubar da jini. Haka nan zubar jini na iya faruwa ba tare da fitowa waje ba. Waɗansu na iya fitowa nan take amma galibi suna haifar da abubuwan da ba a gani ba.
Misali, mucous membrane, wani ɓawo ne ko tantani wanda yake kare tissues na cikin hanci, idan ya bushe zai iya murjewa ko ya tarwatse, idan haka ta faru to yakan janyo zubar jini.
Haka nan kuma jini na iya zuba daga hancin mutane masu amfani ƙwayar maganin anticoagulants da waɗanda suke da cutar zubar da jinin. Anticoagulants, wasu kwayoyin maganin jini ne kamar aspirin.
Nau’ikan haɓo
Haɓo nau’i biyu ne akwai anterior (na ciki) da kuma posterior (na waje).
Haɓo nau’in anterior
A nau’in haɓo anterior, jinin na fitowa ne daga bangon da ke tsakanin kofofin hancin biyu. Wannan ɓangare na hanci yana ɗauke da jijiyoyin jini da yawa. Wannan nau’in haɓo shi ne mafi yawan nau’in zubar jini daga hanci.
Haɓo nau’in posterior
Shi kuwa posterior, zubar jinin ya samo asali ne daga bayan saman hanci. Wannan yanki na kogon hanci yana ɗauke da rassan artery (jijiyoyin jini) da ke ba da jini ga hanci. Rushewar wadannan jijiyoyin yana haifar da zubar jini mai nauyi wanda zai iya canjawa tare da lokutan rashin zubar jini kwata-kwata.
Abubuwan da ke janyo haɓo
Dalilan gama gari na zubar jinin hanci sun haɗa da:
• Rauni kai tsaye
Dukan fuska ko bugewa na iya lalata murfin hancin mutum, wanda hakan zai iya haifar da zubar jini.
• Jirkita hanci
Yawaita ƙwaƙula ko face hanci da ƙarfi na iya sa murfinsa ya fitar da jini.
• Shigar baƙin abubuwa
Shigar wasu nau’ikan halittu ko abubuwa a cikin kogon hanci na iya dagula nama da hanyoyin jini, har su kai ga haddasa yin haɓo.
• Shigar iska mai ƙarfi
Canje-canje na yanayi da ƙarfin iska na iya haifar da taɓuwar hanyoyin jinin hanci. Wadannan canje-canje na iya haifar da zubar jini.
• Kumburi
Kumburi saboda cututtuka, kamar sinusitis, na iya lalata hanyoyin jini a cikin hanci su haifar da yin haɓo.
• Ƙarancin danshi
Yanayin da ake da ƙarancin danshi, sakamakon yanayin gari hakan na iya haifar da tsagewar tissues a cikin hanci. Wannan kuma yana iya haifar da zubar jini.
• Cutar hanta
Cutar hanta na iya zama silar yin haɓo sakamakon toshewar jini, har kuma ta haifar da zubar da jini akai-akai ko mai tsanani.
• Magunguna
Yin amfani da magungunan kashe jini ko magungunan hana kumburin ƙwayar cuta wanda ba na steroidal ba, na iya haifar da zubar jini. Magungunan steroid na hanci na iya bushe murfin hanci, hakan kan ƙara haɗarin faruwar haɓo.
• Magungunan da suka saɓa wa ka’ida
Yin amfani da hodar iblis ko wasu magungunan da ake shaƙa ta hanci na iya dagula tantanin hanci tare da haifar da zubar jini.
• Maganin Radiation da chemotherapy
Chemotherapy na iya rage yawan adadin platelet a cikin jini. Wannan yana sa haɓo ya zo da wahala, kuma ya zama kodayaushe.
Sauran abubuwan da ke haifar da zubar jini
A wasu lokuta, yanayin rashin lafiya da ƙananan abubuwan da ba a saba gani ba na iya haifar da zubar da jini. Waɗannan sun haɗa da:
- Yanayin da ke shafar hanyoyin jini, kamar hemorrhagic telangiectasia
- Tiyatar hanci
- Ƙarancin calcium
- Cututtukan jini, kamar hemophilia da cutar sankarar bargo
- Wasu cutukan
Alamomin haɓo
Babban alamar haɓo ita ce jinin da ke fitowa daga hanci. Wannan zubar jini na iya bambanta ta fuskar tsanani, kuma yana iya fitowa daga hanci ɗaya ko duka biyun. Haɓo na baya shi ne ya fi haifar da zubar jini a cikin kofofin hanci biyu.
Idan haɓo ya faru yayin da mutum yake kwance, yawanci zai ji wani abu kamar ruwa a bayan maƙogwaro kafin jinin ya fito daga hanci.
Magance haɓo a gida
Yawancin haɓo ba a cika gaggawar kai mutum ga likita ba, mutanen da ke tare da mutum na iya yi masa magani a gida.
- Matakin farko na maganin gida shi ne a dakatar da zubar jini.
- A zaunar da mutum a danne sassa masu laushi na hanci da ƙarfi, ya yi numfashi ta baki.
- Ya jingina kai tare daga shi sama don hana jini zubowa cikin sinuses da makogwaro, wanda zai iya haifar da shakar jinim.
- A zauna a miƙe, wannan yana rage hawan jini kuma yana rage yawan zubar jini.
- Idan zubar jini ya ci gaba fiye da mintuna 20, to kulawar likita ta zama dole.
Magance haɓo a asibiti
A yayin da zubar jinin haɓo ta ƙi tsayawa da dabarun gida, za a dangana da mutum zuwa asibiti. Likita zai yi ƙoƙarin dakatar da zubar jini a matsayin matakin farko na aiki. Haka nan za a iya duba hawan jini da bugun jini na mutum.
Idan ana tunanin an samu karaya a hanci ko fuska, za a iya daukar hoton X-ray kafin ba da shawarar zaɓin magani mai dacewa.
Yanayin zubar jinin da kuma dalilinsa su ne kan ba da damar sanin wane irin magani za a ɗora mutum a kai. Wasu daga cikin hanyoyin magance haɓo a likitance sun haɗa da:
• Nasal packing
Likita na iya saka ribbon gauge ko soso na hanci na musamman a cikin kogon hanci don gano tushen da jinin ke fita.
• Cautery
A wannan hanya, ƙwararren likita yana toshewa ko ƙona wani yanki na rufin hanci don rufe hanyoyin da jinin ke zuba.
• Embolization
A wannan hanya kuma, likitan fiɗa zai saka wasu abubuwa a cikin magudanan jini ko jijiyoyin jini don toshe kwararar jini. Wannan zai dakatar da duk wani zubar jini daga hanci. Sai dai ba kasafai likitoci kan ba da shawarar yin aiki da wannan hanyar ba.
• Septal surgery
Idan karkacewar septum tana haifar da zubar jini akai-akai, likita na iya daidaita shi yayin tiyata.
• Ligation
Wannan aikin tiyata ne da ya ƙunshi ɗaure ƙarshen hanyoyin jini da aka gano ko jijiyoyin jini da ke haifar da haɓo. Kwararrun likitocin yawanci suna amfani da wannan tiyata idan wasu magunguna ba su yi aiki ba. Kaso 5 zuwa 10 cikin ɗari ne na nau’in haɓon bayan hanci ke buƙatar ligation.
Riga-kafi
Akwai abubuwa da yawa da mutum zai iya yi don hana kamuwa da haɓo, kamar:
- Nisantar jan hanci
- Guje wa fyace hanci da karfi ko akai-akai
- Guje wa yin aiki mai tsanani
- Nisantar abubuwan shaƙa masu rikitarwa
- Buɗe baki lokacin yin atishawa
Tabbatar wa rufin hanci damshi zai iya taimakawa wajen hana yin haɓo. Misali, yin amfani da nasal saline sprays and humidifiers a lokacin bazara ko yanayin rani, na iya taimaka wa wasu mutanen.
Manazarta
Higuera, V. (2023, December 21). What causes nosebleeds and how to treat them. Healthline.
Mayo Clinic. (2024, May 25).Nosebleeds: First aid Mayo Clinic.