Harshe tsoka ce a cikin baki. An lulluɓe shi da tantanin ɗanɗano, yana da launin ruwan hoda da ake kira da mucosa. Akwai dubban sunadarai da ƙwayoyin halittar ɗanɗano da suka rufe saman harshe. Sinadaran ɗanɗano dai tarin ƙwayoyin halitta ne (cells) masu kama da jijiyoyi waɗanda ke haɗuwa da jijiyoyi masu saduwa da kwakwalwa.
Harshe na daga cikin gaɓɓan jiki, wadda ya ƙunshi tsokoki da dama da tantanai masu yawa. Harshe yana da launin ruwan hoda, yana ba da gudunmawa wajen lasawa da ɗanɗanawa da yin numfashi da taunawa da haɗiya har ma da yin magana. Tantanin papillae da ke kan harshe ya ƙunshi tantanai (tissues) masu laushi. Akwai jijiyoyi da yawa a jikin harshe waɗanda ke taimakawa wajen isar da saƙon ɗanɗano ga ƙwaƙwalwa.
Harshen yana maƙale a baki a jikin wata tsoka mai tauri. Igiyar da ke riƙe da gaban harshe ana kiran ta frenum. A bayan baki, an ƙarfafi harshe da wani ƙashi mai suna hyoid. Harshe yana da mahimmanci wajen taunawa da hadiye abinci kuma da yin magana. Abubuwan da ke ɗauke da ɗanɗano guda huɗu ne; su ne zaƙi da tsami da ɗaci da gishiri. Harshe yana da jijiyoyi da yawa waɗanda ke taimakawa wajen ganowa da aika saƙon ɗanɗano zuwa ga ƙwaƙwalwa. Saboda haka, duk sassan harshe na iya gano waɗannan abubuwan ɗanɗano guda huɗu.
Har ila za a iya fahimtar harshe a matsayin wani tsari na tsoka mai motsi wanda yake cikin ƙasan bakunan mafi yawan dabbobin da ake kira vertebrates (wato, masu ƙashin baya) waɗanda ke ɗauke da ƙananan gland masu ayyuka na musamman wajen sha da haɗiyar abinci da kuma cikin mutane a matsayin ɓangaren magana.
Ayyukan harshe
Harshe tarin tsokoki ne da tantanin da ake kira mucous membrane wanda ke da mahimmanci don jin ɗanɗano. Harshe yana da wasu muhimman ayyuka masu yawa da suka haɗa da:
Tauna da haɗiya
Harshe yana taimakawa wajen taunawa da haɗiye abinci ta hanyar motsa abinci a cikin baki da matsar da shi ga haƙora don narkewa yadda ya kamata.
Ɗanɗano
Harshe yana taimakawa wajen gano abin da zai zama mai lafiya kuma mai daɗi a wajen ci ko sha, tare da jin daɗin ɗanɗano kamar yadda tantanin ɗanɗano yake ganowa. Sinadaran ɗanɗano na asali sun haɗa da zaƙi, gishiri, tsami da ɗaci.
Tsaftar baki
Harshe na iya taimakawa wajen tsaftace baki ta hanyar hana abinci ɗaukar dogon lokaci a baki da kuma jikin haƙora.
Magana
Harshe muhimmin ɓangare ne na yin magana. Harshe yana ba da damar tsara kalmomi da kuma furta su (magana). Wannan ya dogara da tsokoki waɗanda ke canja siffa da yanayi na harshe a lokacin yin magana. Rashin aikin harshe na iya haifar da mummunar matsalar magana.
Kariya
Harshe na iya taimakawa wajen ganowa da daƙile abubuwan da ba su da daɗi wanda kan iya haɗawa da guba. Idan an taba bayan harshe, za a iya samun ƙaƙƙarfar tsoka ta maƙogwaro, wacce kan rufe maƙogwaron.
Taimaka wa haɗiya
Harshe yana taimakawa wajen haɗiyar magunguna cikin hanzari. Wasu magunguna ƙwayoyi ko ɗigo da ake amfani da su a ƙarƙashin harshe suna saurin narkewa kuma su shiga cikin jijiyoyi. Sulingual nitroglycerin, alal misali, ana amfani da shi don faɗaɗa tasoshin jini lokacin da ciwon ƙirji mai tsanani ya faru.
Numfashi
Daga cikin ayyukan da harshe ke yi akwai ba da damar yin numfashi yayin barci. Idan harshe ya koma baya sosai a cikin makogwaro, mai yiwuwa ne hakan ta faru lokacin yin numfashin ta baki, hakan na yana iya haifar da matsaloli ciki har da munshari da barci marar daɗi.
Yanayin siffar harshe
Harshen ɗan’adam yana da tsayin kusan inci 3.3 a bakin maza da inci 3.1 a bakin mata. Harshe ya kasu kashi uku:
- Tsini (tip)
- Gangar jiki (body)
- Tushen (Base)
Harshe yana da bangarori biyu, akwai bangaren gaba da na baya. Ɓangaren gaba shi ne wanda ya haɗa da tushen da aka haɗe zuwa kasan ramin baki. Yayin da ɓangaren baya shi ne wanda ya haɗa da tushe da ke samar da tantanin ventral na oropharynx. Haka nan kuma harshe ya ƙunshi abubuwa guda uku:
• Epithelium
Epithelium ya ƙunshi tantanin papillae da tantanin ɗanɗano wato buds. Tantanin ɗanɗano suna da yawa, suna taimakawa wajen tantance ɗanɗano. An lullube wadannan tantanai da wata tsoka da ake kira epithelial squamous.
Ƙwayoyin halittar dandano suna taimakawa wajen fahimtar dandano, wanda ke samuwa ta hanyar haɗuwar abin da aka ci da yawu.
• Muscles
Tsokokin harshe na son rai ne kuma suna ƙunshe da filayen tsoka da ke giciye.
• Glands
Harshen ya ƙunshi ƙanana ƙwayoyin halitta (cells) waɗanda ake kira da glands, suna da yawa sosai a jikin harshe. Waɗannan glands sun kasu kashi uku:
- Mucous Glands
- Serous Glands
- Lymph Nodes
Bangaren ɗanɗano na harshe
Ana iya gano ɗanɗano huɗu da aka sani ta hanyar tantanin ɗanɗano wato buds ko ƙwayoyin halittar ɗanɗanon masu karɓar sakonni. Waɗannan ɗanɗano su ne:
- Zaƙi: Ana samar da dandano mai daɗi ta hanyar carbohydrates kamar sucrose da fructose, da kuma kayan zaki na wucin gadi kamar aspartame da saccharin.
- Gishiri: Ana samun ɗanɗanon gishiri ta hanyar gishiri mai ɗauke da ions sodium, irin su sodium chloride gishirin tebur da sodium bicarbonate baking soda. Gishiri mai ɗauke da potassium, lithium, da sauran sinadaran alkaline su ma suna samar da ɗanɗano mai gishiri.
- Tsami: Ana samun ɗanɗanon tsami ta hanyar sinadaran acidic, kamar vinegar da citric acid ana samunsa a cikin lemo.
- Ɗaci: Ana samar da ɗanɗano mai ɗaci ta nau’ikan sinadarai masu ɗaci.
Matsalolin harshe
Matsalolin harshe na bayyana ta alamomi iri-iri, kama daga ciwo zuwa canje-canje a launi da yanayi, waɗanda kan faru sakamakon dalilai daban-daban. Lafiyayyan harshe yana da launin ruwan hoda, kuma an rufe shi da tantanin papillae. Canje-canjen launi da ƙwayoyin halitta (cells) na iya zama alamar rashin lafiya. Waɗannan dalilai na da alamomi daban-daban, za su iya kasancewa:
- Ciwo
- Zafi
- Kumburi
- Ciwon ciki
- Canjin launi, kama daga fari zuwa baki.
Matsalolin motsin harshe
- Rashin dandano
- Dalilan matsalolin harshe
Akwai dalilai iri-iri na bayyanar cututtukan harshe gama-gari. Yawancin matsalolin ba su da tsanani, kuma ana iya magance su cikin sauri.
A wasu lokutan, harshe marar launi ko mai raɗaɗi na iya nuna yanayi mai tsanani, a dalilin rashi bitamin ko cutar AIDS ko kansar baki. Saboda wannan dalili, yana da matukar mahimmanci a nemi shawarar likita idan an ga wata matsala dangane da harshe.
Ciwon harshe
Abubuwa da yawa na iya haifar da ciwon harshe mai raɗaɗi, za su iya haɗawa da:
- Tashin hankali: Cizon harshe da kan faru ba tsammani ko ƙonewa da wani abu mai zafi kamar abinci ko abin sha, zai iya haddasa wa harshe yin ciwo har sai ƙunar ta warke.
- Shan taba: Yawan shan taba yana iya takura wa harshe har ya riƙa yin ciwo.
- Ciwon harshe: Wasu matan bayan gama al’ada suna fuskantar wannan ciwo, wanda ke sa harshen ya ji kamar an kona shi.
- Wasu matsalolin lafiya: Yanayin rashin lafiya, kamar ciwon sukari da anemia, na iya haddasa ciwon harshe a matsayin alamar ciwukan.
- Kamuwa da cuta: Wasu cututtukan da ke samuwa dalilin ƙwayoyin cuta (virus) ko bakteriya ko halittun fungal na iya haifar da ciwon harshe.
- Matsalolin hakori: Rashin kula da baki da kyau zai iya sa harshe ya yi zafi kuma ya canja launinsa zuwa fari ko rawaya ko baki. Idan haƙora ba su tsaftatu da kyau ba, za su iya haifar da ciwon baki da harshe.
- Glossopharyngeal neuralgia: Wannan wani yanayi ne da ba kasafai yake faruwa ba wanda ke shafar jijiya a wani ɓangare na harshe, kuma yana haifar da zafi mai tsanani ga harshe.
Kumburin harshe
Idan aka lura da kumburi a jikin harshe, to hakan na iya zama ta dalilai kamar haka:
Kansa
Mutane da yawa za su iya samun wannan ciwon a harshe a wani lokacin. Amma babu tabbataccen dalilin da ke kawo shi, yana iya tsananta sosai a lokacin da ake cikin damuwa.
Girman papillae
Idan ɗaya ko fiye daga cikin tantanan ɗanɗanon ya kumbura ko ya yi haushi, zai iya haifar da tudu ko kututture mai zafi a harshe.
Kansar baki
Yawancin ciwon daji na baki ba sa ciwo a matakin farko, don haka kar a ɗauka rashin jin zafi yana nufin babu wata matsala, lallai a nemi agajin likita.
Cutar syphilis
Wannan cuta ce da ake samu ta hanyar jima’i, tana iya haifar da raunuka da ake kira chancres wanda ke bayyana a saman harshe da sauran sassan baki da maƙogwaro. Suna farawa a matsayin ƙananan ƙuraje da launin ja, kuma suna girma su yi manyan, buɗaɗɗun raunukan sukan iya zama launin ja ko rawaya ko toka.
Herpes stomatitis
Kwayar cuta herpes na iya haifar da ciwon sanyi a harshe, amma ciwon sanyi yawanci yana shafar lebe ne.
Matsalar rashin ɗanɗano
Abubuwa da yawa na iya haifar da rashin ji ko tantance ɗanɗano wanda ake kira da ageusia, waɗannan sun haɗa da:
- CUTAR COVID 19
- Cutar sankara (sinusitis)
- Sanyin gama-gari
- Cutar mura
- Ciwon makogwaro (pharyngitis)
- Cututtukan salivary gland
- Ciwon dasashi
- Raunin kai ko kunne
Atrophic glossitis
Wannan wani yanayi ne da ke sa harshe ya rasa ƙwanƙolinsa kuma ya zama santsi. Wani lokaci, wannan yana faruwa saboda anemia, rashi bitamin B, ko rashin lafiya, kamuwa da cuta, rauni, ko rauni. Alamomin sun hada da:
- Ciwo, taushi, ko zafi
- Kumburi
- Launin ja sosai
- Matsalar magana, cin abinci, ko hadiyewa.
Gwajegwajen matsalolin harshe
Likita na iya ganowa da fadar abin da ke damun harshe ta hanyar kallo da nazarin harshen kawai. Yana yiwuwa kuma a buƙaci yin wasu gwaje-gwaje da na’urori. Likita na iya yin gwajin laryngoscopy, wani gwaji ne da ake yi don duba tushen harshe. Wannan wata hanya ce da likitoci suke amfani da wani ƙaramin madubi mai haske don duba cikin maƙogwaro.
Manazarta
Dental, S., & Dental, S. (2024, November 12). What is the function of the tongue? Sunrise Dental.
Merriam-Webster Dictionary “Tongue Definition & Meaning tongue. (2024). In Merriam-Webster”
Peters, B., MD. (2024, July 16). Tongue: anatomy, functions, and common disorders. Verywell Health.
Parker, H. (2024, May 13). Tongue problems. WebMD.