Skip to content

Karamin hanji

Hanji bututu ne na tsoka wanda ya tashi daga sashen ƙasa na ƙarshen ciki zuwa dubura, ƙaramin sashen hanyar narkewar abinci. Abinci da abubuwan da suke narkewa suna ratsa cikin hanji, wanda ya kasu kashi biyu, akwai; ƙaramin hanji da babban hanji.

Ƙaramin hanji wani bangare ne da ke sashen na’urar narkewar da abinci. Ya ƙunshi wani ɓangare na doguwar hanyar da abinci ke ɗauka a jiki, wanda ake kira sashin gastrointestinal (GI). Lokacin da abinci ya fita daga ciki, yana shiga cikin ƙaramin hanji. Ƙaramin hanji yana haɗuwa da babban hanji. Hanji ne ke da alhakin ruguza abinci, da zuƙar abubuwan da ke cikinsa da kuma tura tarkacen da ke ciki zuwa waje. Ƙaramin hanji shi ne mafi tsawo na sashin GI, kuma shi ne inda yawancin aikin narkewar abinci ke faruwa.

Hoton hanji a cikin ɗan’adam – Daga Andullah195. A shafin Pixabay.

Bangarorin ƙaramin hanji

Ƙaramin hanji yana da sashin farko da sashe na tsakiya da kuma sashin ƙarshe, kamar yadda ya zo a kafar Cleveland Clinic. Kodayake babu rarrabuwa tsakanin sassan, a haɗe suke, amma suna da siffofi daban-daban da rawar da suke takawa.

• Duodenum

Duodenum shi ne ɓangare na farko na ƙaramin hanji wanda ciki ke ciyarwa a ciki. Gajere ne guntu bai da tsayi, yana saukowa, kimanin inci 10 ne tsayinsa. Yana kewayawa a kusa da pancreas da siffar “C” kafin ya haɗu da sauran hanjin da aka naɗe.

• Jejunum

Ragowar ƙaramin hanji yana kwance a cikin gaɓoɓi masu yawa a cikin kogon ciki na ƙasa. Sashinsa na tsakiya, wanda ake kira jejunum, bai kai rabin-rabin wannan tsayin da ya rage ba. Jejunum yana da alaƙa da jijiyoyin jini da yawa, waɗanda ke ba shi launin ja mai zurfi.

• Ileum

Ileum shi ne sashi na ƙarshe kuma mafi tsayi na ƙaramin hanji. A nan bangon ƙaramin hanji ya fara ɓata, kuma yana raguwa, har jini ma yana raguwa. Abinci yana daɗewa sosai a wannan sashe, inda yawancin ruwa da abubuwan gina jiki ke shiga jiki.

Aikin ƙaramin hanji

Karamin hanji nan ne inda mafi akasarin aikin narkewar abinci ke faruwa, a cewar Kenhub, abinci na ɗaukar lokaci sosai a cikin ƙaramin hanji. Daga cikin ayyukan ƙaramin hanji akwai:

  • Yana ruguza abinci cikin tsari
  • Yana zuƙar sinadaran gina jiki
  • Yana tace ruwa
  • Yana tura abinci zuwa gastrointestinal tract.

Ayyukan sassan ƙaramin hanji

• Duodenum

Wannan sashe na taimakawa wajen ruguza abinci, ƙaramin hanji yana karɓar ruwan abinci narkakke daga wasu gaɓoɓin da ke aikin narka abincin, waɗanda suka haɗa da hanta da gallbladder da pancreas. Wasu hanyoyi daga waɗannan gabobin suna shiga cikin duodenum. Hormone gland a cikin duodenum suna ankarar da waɗannan gaɓoɓin su saki sinadarai a lokacin da abinci ya shiga ciki.

• Jejunum

Bayan narkewar sinadarai a cikin duodenum, abinci yana isa zuwa cikin jejunum, inda aikin tsoka na narka abinci ke farawa. Jijiya a jikin hanji tana haifar da tsoka mai murƙushe abinci gaba da baya, su haɗa shi da narkakken ruwan abinci.

• Mucosa

Bangon jikin ƙaramin hanji an lulluɓe shi da ƙaƙƙarfar fata da ake kira da mucosa da gland mai yawa waɗanda duka suke kebance. A cikin jejunum da ileum, mucosa tana ɓoye ƙananan ƙwayoyin enzymes masu narkarwa da suke ɗaukar sinadaran gina jiki daga abinci. Kowane sashe an tsara shi don ɗaukar nau’ikan sinadaran gina jiki daban-daban, da kuma ruwa.

Mucosa mai kauri tana da sunadarai da yawa wanda sararin samanta ya kai ninki 100 na saman fatar jiki. Wannan shi ne dalilin da ya sa kashi 95% na carbohydrates da furotin da ake ci suke shiga cikin ƙaramin hanji. Haka nan tana zuƙar kusan kashi 90% na ruwan da yake samuwa yayin narkewar abinci. Sauran za ana zuƙar su ne a cikin babban hanji.

• Ileum

A cikin ileum, ruguza abinci yana raguwa inda peristalsis ke karɓar aikin tare da tura lalataccen abinci a hankali zuwa babban hanji. Sashen ileocecal valve, ya raba ileum da babban hanji. Jijiya da hormones suna ankarar da valve ya buɗe don barin abinci ya wuce sannan ya rufe don kariya daga bakteriya masu cutarwa. Kwayoyin halitta na musamman suna tallafa wa ileum don samun kariya daga bakteriya.

Muhallin ƙaramin hanji a ciki

Ƙaramin hanji a ciki yake, cikin kogon ciki na ƙasa a ƙarƙashi ko kasan ciki. Babban hanji yana kewaye da shi.

Siffofin ƙaramin hanji

Ƙaramin hanji yana kama da bututu mai tsayi, ruwan hoda-hoda ko ja mai riɓi da yawa. Yana kama da faɗin ɗan-yatsa manuniya. Faɗinsa ne ya sa shi ya zama ƙarami fiye da babban hanji, ba tsayi ba.

Tsawon ƙaramin hanji

Karamin hanjin shi ne mafi tsayin sashe na gastrointestinal tract, tsayin kusan taku 22 ne. Har ila yau, rufinsa daga waje yana da fili mai faɗin gaske. Idan za a warware rufin zai iya kaiwa faɗin filin wasan tennis.

Cututtukan ƙaramin hanji

Akwai wasu abubuwa da ke haifar da cututtukan ƙaramin hanji kamar yadda HUB suka kawo;

  1. Karamin hanji yana zuƙar sinadaran gina jiki da ruwa daga abincin da aka ci. Idan wannan aiki ya samu tasgaro, to akwai yiyuwar samun ƙarancin abinci mai gina jiki, sannan za a iya kamuwa da gudawa.
  2. Motsin tsoka a cikin ƙaramin hanji yana taimakawa wajen ruguza abinci da sarrafa shi a jiki. Idan wannan motsin ya samu matsala, za a iya fuskantar rashin narkewar abinci da sauran matsaloli.
  3. Cututtuka iri-iri na iya haifar da kumburin ƙaramin hanji, wanda kan janyo ciwon ciki, tashin zuciya da amai.

Hanyoyin kula da hanji

Akwai hanyoyi da yawa da kuma dabaru da ake bi don kula da lafiyar hanji, sun haɗa da:

Cin kayan lambu

‘Ya’yan itacen da kayan marmari kamar kayan lambu da dukkan nau’in hatsi suna taimakawa wajen samar wa hanjin isasshen sinadarin fiber. Fiber yana taimakawa wajen ciyar da bakteriya masu amfani a cikin hanji, kuma yana taimakawa wajen cire ragowar abincin da bakteriya ba za su ci ba. Ƙarin sinadarin fiber yana ƙara sha’awar ruwa. Fiber da ruwa za su taimaka wajen ci gaba da motsin hanji akai-akai, wanda ke taimaka wa ƙaramin hanji ya ci gaba aiki yadda ya kamata.

Yawancin ‘ya’yan itatuwa da kayan marmari suna taimakawa wajen daidaita tsarin abincin mai yawan sinadarin acidic. Yawan sinadarin acid zai iya lalata ƙwayar halitta mai ba da kariya da ke cikin hanji.

Guje wa shan taba da magunguna

Sanannen abu ne cewa taba da barasa suna ƙara acid a ciki, wanda ke lalata rufin ƙwayar halitta mai ba da kariya.  Magunguna irin su aspirin da ibuprofen na rage zafi da raɗaɗi, na iya lalata rufin ciki. Idan an yi amfani da fiye da ɗaya daga cikin waɗannan magunguna lokaci ɗaya, hakan yana ta’azzara lalacewar rufin cikin. Yana da kyau kada a yi amfani da ɗaya daga cikin waɗannan sau da yawa, kuma a guji amfani da su a tare.

Abin da ke faruwa a cikin ciki zai iya rinjayar duodenum. Yawan sinadarin a ciki zai iya shiga cikin duodenum kuma ya fara lalata rufinsa. Rushewar rufin ciki kuma yana barin ciki ya zama mai saurin kamuwa da cututtukan bakteriya, kamar H. pylori, wanda kuma zai iya cutar da duodenum. Yawan amfani da magungunan rage zafi da raɗaɗi da kamuwa da cutar H. pylori  su ne manyan abubuwan da ke haifar da ulcer a ciki da duodenum.

Manazarta

Diseases of the small intestine, colon and rectum – Visceral Surgery division. (n.d.). HUG.

Professional, C. C. M. (2024c, June 21). Small intestine. Cleveland Clinic.

Small intestine. (2023, November 3). Kenhub.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×