Skip to content

Lagwada

Lagwada, cuta ce mai saurin yaɗuwa ta hanyar ƙwayar cutar varicella zoster (VZV). Tana haifar da ƙaiƙayi, kurji mai kumburi. Yawancin mutane suna warkewa a cikin makonni 1-2, amma wasu suna wuce wannan lokaci. A tsakanin mutanen da ba a yi musu allurar ba, tana da saurin yaduwa. Kodayake cutar ba cuta ce mai barazana ga rayuwa ba, amma wani lokaci tana iya haifar da babbar matsala.

Lagwada ta fi kama ƙananan yara musamman waɗanda ba a yi musu allurar riga-kafi ba.

Cutar tana ɗaukar kusan kwanaki 4 zuwa 7 kafin bayyanar da alamomi. Ga yawancin mutane, kamuwa da cutar sau ɗaya yana zama riga-kafi na tsawon rayuwa. Mutum na iya kamuwa da cutar lagwada fiye da sau ɗaya, amma ba a saba ganin haka ba.

Matakai uku na cutar lagwada

Matakan guda uku na cutar lagwada yawanci suna nuni ne ga yadda ƙurajen ke bayyana:

  • Mataki na farko: Bayyanar ƙuraje kuma yawanci jajaye, wannan na iya ɗaukar kwanaki kaɗan.
  • Mataki na biyu: Shi ne matakin da ƙurajen za su cika da ruwa. Kumburin zai ƙaru har ya kai ga fashewa bayan kamar kwana ɗaya zuwa biyu.
  • Mataki na uku: Wannan shi ne lokacin da kumburin ya sace bayan ruwan ƙurjin ya fita. Wannan matakin kuma yana ɗaukar kwanaki kaɗan.

Kodayake ƙurajen sukan wuce matakai uku, ana iya ganin kowane irin kumbura a lokaci guda. Wannan yana nuna cewa wasu ƙurajen na iya tasowa yayin da wasu ke motsewa. Gabaɗaya ƙurajen na iya ɗaukar kusan kwanaki goma.

Yawancin wuraren da lagwada ke farawa

Mafi yawan lokuta ana fara kamuwa da cutar lagwada a fuska da gangar jiki, kamar kirji da baya. Daga nan, sai tana yaɗuwa zuwa ga sauran sassan jiki har zuwa yatsun hannu da yatsun kafa.

Alamomin cutar lagwada

Alama bayyananniya ta lagwada ita ce ƙurji wanda ke haifar da ƙaiƙayi da kumburi mai cike da ruwa wanda a ƙarshe yake zama tabo. Kurjin na iya fara bayyana a kan ƙirji da baya da fuska, kafin ya bazu zuwa ga sauran sassan jikin. Mutumin da ke da lagwada na iya samun kumburin ƙuraje har guda 500 a jikinsa. Yawancin lokaci tana ɗaukar kusan mako guda ga dukkan ƙurajen su kumbura.

Wasu mutanen da aka yiwa allurar riga-kafi daga cutar lagwada tun suna yara, suna iya kamuwa da cutar bayan sun girma. Sai dai yawanci suna samun alamomi masu sauƙi. Alamomin cutar lagwada suna da sauƙin bayyana. Ma’aikatan lafiya sau da yawa suna iya duba fatar yara kuma su fahimci idan suna da yiyuwar kamuwa da cutar lagwada. Alamomin cutar yawanci suna faruwa da:

  • Zazzaɓi sama-sama
  • Jin gajiya da kasala
  • Ciwon kai
  • Ciwon ciki wanda ke sa ba za a iya ci abinci ba.
  • Ƙurajen fata masu tsananin ƙaiƙayi

Yaran da aka yi wa alurar riga kafin cutar yawanci suna samun kariya daga kamuwa da cutar. Amma maganin ba shi da tasiri dari bisa dari, kuma wasu yara za su iya kamuwa da cutar duk da allurar riga-kafin.

Abin da ke haifar da cutar lagwada

Kwayar cuta tana alaƙa da karanta. Kwayoyin cutar suna yaɗuwa lokacin da mai cutar ya ba wa wani mutum ko dai ta hanyar ruwan da kan fito ta jiki kamar feshin tari da atishawa da sauran su, ko taba ƙurajen.

Yadda cutar lagwada ke yaɗuwa

Lagwada cuta ce mai saurin yaɗuwa da ƙwayar cuta ta varicella-zoster (VZV) ke yaɗawa. Ta fi yaɗuwa daga mutanen da ba a yi musu allurar riga-kafin cutar ba zuwa wasu da ba su taba kamuwa da cutar ba. Kusan kashi 90% na mutanen da ba su da ƙarfin garkuwar jiki kuma suke zaune da wanda ke da cutar za su iya kamuwa.

Yara na iya kamuwa da cutar lagwada a kowane lokaci. Bayan kamuwa da cutar, yaro na iya zama kamar yana da lafiya har tsawon makonni ɗaya zuwa uku kafin ya ji rashin lafiya. Yara za su iya yaɗa cutar daga kwana ɗaya zuwa biyu kafin su nuna alamun rashin lafiya har sai duk ƙurajen sun motse ko kuma sun bushe. Sauran hanyoyin da lagwada ke yaɗuwa sun haɗa da:

  • Cuɗanya da wanda ke da cutar
  • Shaƙar iska daga mai cutar da ke yin atishawa ko tari
  • Taɓa hawaye daga idanun yaron da ya kamu da cutar, ko majina ko yawu

Waɗanda ke cikin haɗarin kamuwa

Duk waɗanda ba su taɓa karɓar allurar riga-kafi ba kuma ba su taɓa kamuwa da cutar ba, to suna cikin haɗarin kamuwa. Haɗarin ya fi tsananta idan mutum ya kasance a kusa da yara ko aiki a makaranta ko wurin kula da yana. Cutar na iya haifar da cututtuka masu tsanani a jikin manya ‘yan sama da shekaru goma sha takwas.

Wasu mutanen da suka kamu da ciwon lagwada na iya samun alamomin cututtuka masu tsanani kuma suna iya zama mafi haɗari da rikitarwa. Kazalika  tana iya zama mai tsanani, har ma tana da haɗari ga rayuwa, musamman a lokacin ɗaukar ciki ga mata da jarirai da matasa da manya da mutanen da ke da raunin garkuwar jiki. Mutanen da ke da raunin garkuwar jiki suna da ƙarancin damar yaƙar ƙwayoyin cuta da cututtuka.

Waɗanda suka fi fuskantar matsala

Yara masu cikakkiyar lafiya waɗanda suka kamu da cutar lagwada ba sa fuskantar matsala mai tsanani. Fuskantar mummunan yanayin cutar lagwada na iya zama mafi haɗari ga:

  • Yaran da aka haifa da ga iyaye da ba su yi riga-kafi ba
  • Masu ciki waɗanda ba su taɓa yin cutar lagwada ba
  • Duk wanda ya wuce shekara 18
  • Mutanen da ke da raunin garkuwar jiki
  • Mutanen da ke da cutar kansa ko HIV
  • Mutanen da ke fuskantar chemotherapy.
  • Mutanen da aka yiwa gaɓoɓi

Ko cutar lagwada na kisa?

Abu ne mai matuƙar wuya samun rahotan mutuwa a sakamakon cutar lagwada. Yawancin mutane suna warkewa ba tare da wahala ba. A cikin waɗanda ke mutuwa dalilin cutar, yawancin mutane ne manya. A cikin shekarar 2022, an sami mutuwar mutane ƙasa da 30 daga cutar, a ƙasar Amurka, a rahotan da asibitoci 1,400 suka bayyana.

Riga-kafi

Kare kanka da maganin. Hanya mafi kyau don rigakafin cutar lagwada ita ce yin allurar riga-kafin cutar. Kowane mutum ciki har da yara da matasa da manya ya kamata su karɓi allurai 2 na riga-kafin cutar lagwada idan ba su taɓa kamuwa da cutar ba ko kuma ba a taɓa yi musu riga-kafi ba. Yawancin mutanen da suka yi riga-kafin ba sa kamuwa da cutar.

Alurar riga-kafi tana hana kusan dukkanin yanayin rashin lafiya mai tsanani. Tun lokacin da aka fara shirin riga-kafin cutar a Amurka, an samu raguwa sama da kashi 97 cikin 100 na kamuwa da ita.

Manazarta

Brazier, Y. (2023, November 13). What you need to know about chickenpox. Medical News Today.

Cleveland Clinic (2024, May 1) Chickenpox. Cleveland Clinic. 

About chickenpox. (2024, April 24). Chickenpox (Varicella).

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×