Magana Jari Ce, yaro ba da kuɗi a faɗa maka. Wannan shi ne ma’anar wannan zancen. Littafin Magana Jari Ce, littafi ne da ya ƙunshi gajerun labarai kala-kala kuma masu cike da hikima da basira tare da yin hannunka mai sanda a kan al’amuran rayuwar malam Bahaushe. Littafin ya yi nutso sosai kan matsaloli da kuma mafitarsu, ta fuskar zamantakewa, addini da kuma al’ada.
Magana Jari Ce, yana cikin littattafai guda uku da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta a cikin wata shida na zamansa a Zariya, a shekarar 1936. Dalilin zaɓo shi kuwa ya rubuta waɗannan littattafai shi ne ya shiga wata gasa ta rubutun littafi a shekarar 1933 ya kuma ci nasara da littafinsa na farko ‘Ruwan Bagaja’.
Kamar yadda Rupert East ya bayyana, littafin labari ne wanda aka rubuta da harshen Hausa, littafin ana ɗaukar shi ɗaya daga cikin littafi mafi girma da aka taɓa rubutawa a cikin Harshen Hausa a duk faɗin Arewacin Najeriya, littafin a hukumance an amince da shi a matsayin littafin adabi a makarantun sakandare na Najeriya don darussan Hausa da kuma tsara manhajar ilimi.
Bayanin kowane kashi
Magana Jari Ce littafi ne da ba a gajiya da karanta shi. Wani abu mai armashi shi ne; gabaɗaya littatafan a shekara ɗaya mawallafin ya rubuta su, shekarar 1937. Domin ya samu kammala su ne cikin wata shida. Sai dai bambance-bambance da aka samu na shekarar sabuntawa. Littafin Magana Jari Ce ya kasu zuwa gida uku kamar haka;
1. Magana Jari Ce littafi na ɗaya
An fara rubuta littafin Magana Jari Ce littafi na ɗaya a shekarar 1937, an sake bugawa sau 17 a shekarar 1954 zuwa 1985. An yi masa gyara na farko a shekarar 1993,1997, da kuma 1998. An shirya shi karkashin kamfanin littatafai na Nijeriya ta arewa lambar gidan waya 412 a kamfanin gaskiya dake garin Zariya. Lambar tantancewa wato IBS 978-169-057-7. Haƙƙin mallaka kuma Zariya 1945.
Yawan shafuka da labarai
Littafi na ɗaya yana da adadin shafuka ɗari da goma sha shida (116), kuma ƙunshi labarai guda ashirin da tara (29) ga wasu kaɗan daga ciki:
- Labarin Wani Bororo Da Ɗan Zaki
- Banza Ta Kori Hofi
- Sauna Kira Mana Shashasha, Idan Ka Ga Sakarai Ku Taho Tare
- Labarin Waɗansu Abokai Su Uku
- Idan Ajali Ya Yi Kira Ko Babu Ciwo Sai An Je
- Labarin Annabi Sulaimanu
- Ba Wahalalle Sai Mai Kwaɗayai
- Saurin Fushi Shi Ke Kawo Danasani
- Sauri Ya Haifi Nawa
- Labarin Shaihu Ɗanfodiyo
2. Magana Jari Ce littafi na biyu
An fara rubuta littafin Magana Jari Ce littafi na biyu a shekarar 1937, an sake bugawa sau 17 daga 1954-1985. An sake sabunta shi a 1993-1999. An shirya shi a kamfanin littatafai na Najeriya ta arewa a garin Zariya. Lambar gidan waya 412 a kamfanin gaskiya dake jihar Zariya. Lambar tantancewa wato IBS 978-169-058. Haƙƙin mallaka kuma Zariya 1945.
Yawan shafuka da labarai
Littafi na biyu yana da shafuka ɗari da tamanin da huɗu (184)ya kuma ƙunshi labarai gajeru har guda (32) masu hannunka mai sanda, ga kaɗan daga cikin labaran kamar haka:
- Labarin Kalala Da Kalalatu
- Yaro Tsaya Matsayinka Kada Zancen ‘Yan duniya Ya Ruɗeka
- Labarin Sarki Noma Da ‘Ya’yansa
- Da Muguwar Rawa…
- Labarin Wani Makaho
- Anƙi Cin Biri An Ci Dila
- Labarin Ɗan Sarkin Noma Na Fari
- Jarrabawar Da Aka Yi Wa Ɗan Sarkin Noma
- Gamuwar Ƙosau da Jimrau da Nomau
- Labarin Waɗansu Maɗinka Uku
3. Magana Jari ce littafi na uku
Shi ma an rubuta littafi shi a shekarar 1937, an sake bugawa shekarau 1954.1955, 1959, 1964, 1966, 1968, 1970, 1972, 1974, 1975, 1976, da kuma 1977. An shirya shi a kamfanin littatafai na Najeriya ta arewa a garin Zariya. Haƙƙin mallaka NNPC 1970.
Yawan shafuka da labarai
Littafi na uku yana adadin shafuka ɗari biyu da sittin da tara, sannan ya ƙunshi labarai masu fadakarwa da kuma jan hankali har guda (23) ga kaɗan daga cikinsu:
- Kowa Ya Dogara Ga Allah Ya Isar Masa
- Ɗan Hakkin Da Ka Raina Shi Ne Yake Tsone Maka Idanu
- Alheri Danƙo Ne Ba Ya Faɗuwa Ƙasa Banza
- Rama Cuta Ga Macuci Ibada Ne
- Labarin Sarki Jatau
- Sa’a Ta Fi Manyan Kaya
- Hassada Ga Mai Rabo Taki Ce
- Munafurci Dodo
- Wanda Ke Wulaƙanta Jama’a Zai Ga Iyakarsa
Dalilin/jigon rubutua littafin
Babbar manufar rubuta littafin Magana Jari Ce shi ne saboda wata gasa, sai dai kuma littafin na ɗauke da jigogi masu girma kuma kala-kala masu cike da armashi tare nuni kan lamuran rayuwa. Ga misalan wasu daga cikin jigogin da littafan suka ƙunsa:
- Soyayya
- Yaudara
- Amana
- Talauci
- Cin amana
- Sarauta
- Hikima
- Yarda da ƙaddara
- Imani
- Yaƙini
Ra’ayoyin makaranta littattafan
• Farfesa Abdallah Uba Adamu
“Littafin magana jari ce ya yi zarra wajen sarrafa labari da kuma nuna aƙidar Malam Bahaushe. Shi ne kaɗai littafin Hausa da aka fassara zuwa harsunan Larabci da kuma Portuguese. Ko muna so, ko ba ma so littafin shi ne ya fito da martaba da rayuwar Bahaushe a cikin labari.”
• Malama Maijiddah Muhammad Musa.
“Magana Jari Ce hikayoyi ne masu matuƙar amfani ko kuma darasi cikin hikima domin al’umma su gane, su gyara idan kana da wani abu da ya yi daidai da halinka. Wato dai hannunka mai sanda.”
• Muhammad
“Magana Jari Ce shi ne littafin da na karanta da har zuwa yau ban ga wanda ya kama ƙafarsa ba a gajerun labarai masu cike da ma’ana. Magana Jari Ce, hikaya ce ko labari da aka ƙirƙiro mai cike da fasaha da zalaƙa wajen ba da darasi da labarai masu sa nishaɗi da kuma isar da saƙo.”
• Muttaƙa A. Hassan
“Idan na tuna a littafin an ba wa tsuntsu (Aku) gadin ɗan sarki, kuma ya yi amfani da hikima ya dinga saƙa labarun da suka hana shi fita har sarki ya dawo; sai in ce ban taɓa karanta littafin Hausa da aka tara hikima kamarsa ba.”
Taƙaitaccen tarihin marubucin
An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam a shekarar 1911 a cikin garin Kagara lokacin tana cikin lardin Kwantagora, yanzu kuwa tana Jihar Neja. Ya yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a makarantar Midil ta Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta littafin sa na ‘Ruwan Bagaji’. Ganin ƙwazonsa wajen ƙirƙirar labari mai ma’ana ya sa Dr. R. M. East shugaban Offishin ta’alifi na Zariya ya roƙi a ba da shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce-rubuce a Zariya.
Bayan ya koma Katsina aka bi shi da roƙon ya ƙara rubuta wasu littattafan. A can ya rubuta ‘Karamin Sani Ƙuƙumi’ cikin 1937. A cikin shekara 1938 sai Gwamnan Kaduna ta roƙi a dawo da Imam Zariya a koya masa aikin edita ya zama editan jaridar farko ta Arewa. Shi ne ma ya raɗa mata suna ‘Gaskiya Ta Fi Kwabo’ aka fara bugawa a watan Janairu na shekara 1939.
Wani mashahurin littafi kuma da ya rubuta shi ne ‘tarihin Annabi da na Halifofi’ wanda aka fara buga shi a shekara 1957 lokacin nan yana shugaban hukumar ɗaukar ma’aikata ta Nijeriya ta Arewa. Alhaji Dr. Abubakar Imam ya rasu yana da shekara 70 a duniya ranar Juma’a 19 ga watan Yuni 1981.
Manazarta
BBC News Hausa. (2017, September 10). Littafin Magana Jari ne ya fito da martabar Bahaushe – Farfesa Abdallah Uba. BBC Hausa News.
Google Books (n.d.).Magana jari ce littafi na farko Google Books.
Wikipedia contributors. (2024, July Magana Jari Ce Wikipedia.