Harry Potter yana cikin jerin littatafaiĀ guda bakwai da marubuciyar Birtaniya J. K. Rowling ta rubuta. Littafin na daga cikin littatafan da suka fi shahara a duniya, musamman a tsakanin yara da matasa. A lokacin da marubuciyar ta rubuta littafi na farko, Harry Potter and the Philosopher’s Stone, sai da ta turawa kamfanonin ta’alifi har guda 12 amma duk suka Ęi karÉar littafin, daga Ęarshe dai kamfanin Bloomsbury suka karÉa suka buga, ya kuma ya fito cikin sa’a tare da samun gagarumar nasara.
Tun daga lokacin da littafi na farko, Harry Potter and the Philosopher’s Stone, ya fita a ranarĀ 26 ga watan Yuni 1997, litattafan suka samu shahara da karÉuwa sosai a wurin masu karatu da manazarta gabaÉaya.

Zuwa watan Fabarairun 2023, an siyar da jimillar kwafi na litattafan guda dubu Éari shida a duniya. Hakan ya sa littafin ya zama mafi samun ciniki a duniya bakiÉaya. An fassara litattafan zuwa harsuna 85 na duniya.
Bayanin littafin a takaice
Sunan littafi: Harry Potter
Marubuciya: J. K. Rowling
Tsara bango: Thomas Taylor, Cliff Wright, Giles Greenfield & Jason Cockcroft
Ęasa:Ā Burtaniya
Harshe: Turanci
MaÉaba’a;Ā Bloomsbury
Kwanan watan Éab’i: 26 ga Yuni 1997
Sabuntawa: 21 ga Yuli, 2007
Rabe-rabe: Bugun hannu, na sauraro da e-book
Yawan littattafai
Ga jerangiyar litattafan da shekarun da suka fita tare da lambobinsu na Éab’i:
1. Harry Potter And The Philosopher’s Stone (1997)
- Hardcover: ISBN 0-7475-3269-8
- Paperback: ISBN 0-7475-3270-1
2. Harry Potter And The Chamber of Secrets (1998)
- Hardcover: ISBN 0-7475-3848-8
- Paperback: ISBN 0-7475-3849-6
3. Harry Potter And The Prisoner of Azkaban (1999)
- Hardcover: ISBN 0-7475-4215-9
- Paperback: ISBN 0-7475-4216-7
4. HarryĀ Potter And The Goblet of Fire (2000)
- Hardcover: ISBN 0-7475-4624-6
- Paperback: ISBN 0-7475-4625-4
5. Harry Potter And The Order of the Phoenix (2003)
- Hardcover: ISBN 0-7475-5595-8
- Paperback: ISBN 0-7475-5596-6
6. Harry Potter And The Half-Blood Prince (2005)
- Hardcover: ISBN 0-7475-6979-9
- Paperback: ISBN 0-7475-6980-2
7. Harry Potter And The Deathly Hallows (2007)
- Hardcover: ISBN 0-7475-9108-8
- Paperback: ISBN 0-7475-9109-6
TaĘaitaccen bayanin abin da kowane littafi ya Ęunsa
1. Harry potter And The Philosopher’s Stone
Ā (Sorcerer’s Stone a Amurka): Harry ya gano haĘiĘa bin matsayinsa na matsafi tare da fara zuwa makarantar Hogwarts domin koyon tsafi.
2. Harry Potter And The Chamber of Secrets
Harry tare da abokansa sun gano wani Éoyayyen babban Éaki a makarantar Hogwarts mai Éauke da halittu masu haÉari.
3. Harry Potter And The Prisoner of Azkaban
Harry ya gano cewa wani fursuna mai suna Sirius Black, ya gudo daga magarĘama kuma shi ne ya ci amanar iyayensa har ya ja aka kashe su, yanzu kuma yana so ya kashe Harry.
4. Harry Potter And The Goblet of Fire
Wutar tsafi ta bayyana sunan Harry a matsayin Éaya daga cikin waÉanda za su fafata a gasar makarantun matsafa.
5. Harry Potter And The Order of the Phoenix
Harry ya kafa tawaga mai suna Dumbledore’s Army domin tunkarar baĘaĘen matsafa sakamakon dawowar Voldemort.
6. Harry Potter And The Half-Blood Prince
Harry ya koyi abubuwa masu yawa game da Voldemort da tarihinsa da kuma shi kansa yayin da ya fara girma.
7. Harry Potter And The Deathly Hallows
Harry, Ron, da Hermione sun Éauki niyyar yin wata tafiya mai hatsarin gaske domin samun lagun Voldemort domin samun nasara.
KarÉuwa
Labarin Harry Potter ya samu karÉuwa sosai a duniya. KarÉuwarsa da shahararsa ya sa aka fassara shi zuwa harsuna 85. Faruwar hakan ya sa marubuciya J. K. Rowling ta zamo marubuciyar da aka fi fassara litattafanta a duniya. Daga cikin harsunan da aka fassara litattafan akwai Koriyanci, Armaniyanci Yukraniyanci, Larabci, Hindi, Urdanci, Bengaliyanci, Walshanci Bulgariyanci Afirkanci, Latbiyanci da dai sauransu.Ā Gaba Éaya litattafan guda bakwai an siyar da kwafinsu sama da guda miliyan Éari shida. Sannan wannan gagarumar nasara ta sa marubuciyar littafin da zama marubuciya ta farko da ta taÉa zama biloniya a duniya.

Litattafan Harry Potter sun samu karÉuwa a wajen yara da matasa fiye da kowane irin littafi, hakan ya sa littafin ya zamo sananne a sama da Ęasashe 200, kuma dukkan litattafan sun samu nasara a harkar kasuwancinsu. A bisa wannan karÉuwa da suka yi ne ma har ta kai ga an juya labaran zuwa fim, inda aka Éauki labarin kowane littafi a matsayin fim Éaya, face Harry Potter And The Deathly Hollows wanda aka raba shi gida biyu, kuma duka fina-finan sun samu karÉuwa sosai, jimillar kudin da fina-finan suka kawo a harkar kasuwancinsu ya kai dala biliyan bakwai da Éigo bakwai. Bayan shekaru kuma sai kamfanin HBO suka sanar da cewa za su shirya wani sabon shiri mai dogon zango a kan labarin Harry Potter. Akwai kuma wasannin wayoyin hannu da na kwamfuta da aka ĘirĘiro duk saboda karÉuwar Harry Potter.
Yabawa
Masana da kuma masu sharhi sun yaba wa littafin sosai, musamman ta fannin abubuwa kamar haka:
- Fikirar marubuciyar wurin iya ĘirĘiro duniya guda mai faÉi irin haka.
- Taurarin labari masu shiga rai waÉanda mai karatu ke iya alaĘantuwa da su.
- TaÉo abubuwa masu muhimmanci irin su abota, soyayya tare da nuna bambanci tsakanin adalci da zalunci.
- Ā Salon rubutu, barkwanci da kuma iya bayyana lokutan annashuwa da kuma na baĘinciki.
- Tsara labari mai ma’ana tare da jan hankalin mai karatu wanda ke cike da abubuwan mamaki.
Kyautuka da lambobin yabo
Marubuciya J. K. Rowling ta samu lambobin yabo masu tarin yawa a sakamakon labarin Harry Potter. Daga cikin lambobin yabon da ta samu a kwai: National Book Award, Hugo Award, da kuma Order of the British Empire award.
Litattafan Harry Potter sun samu lambobin yabo masu yawan gaske tun bayan fitowarsu, ga wasu daga ciki:
- Platinum Award daga Whitaker Gold
- Whitbread children’s book of the year award (1999)
- WHSmith book of the year (2006)
- Hugo Award for Best Novel 2001, Harry Potter and the Goblet of Fire
Baya ga waÉannan kamfanonin jaridu da mujallu, da laburare tare da sauran kafofin yaÉa labarai da na ilimi da dama sun karrama litattafan Harry Potter da lambobin yabo tare da rubuta muĘalolin yabo a kan wannan littafi.
Babbar nasarar da littafin ya samu fiye da kowane shi ne farfaÉo da son karatu a tsakanin yara da matasa, tare da samun mabiya masu Éumbin yawa
Manazarta
Harry Potter (n.d.).Ā Ā Official Harry Potter Encyclopedia.
Wikipedia contributors. (2024, August 20). Harry Potter.
Wiki, C. T. H. P. (n.d.). Harry Potter (book series). Harry Potter Wiki.
SharuÉÉan Editoci
Duk maĘalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na Ęwararru. Kuma kowace maĘala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maĘalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.








