Ƙasar Peru, wadda sunanta na hukuma yake Republic of Peru, wato Jamhuriyar Peru, tana ɗaya daga cikin ƙasashen da ke nahiyar Kudancin Amurka. Ƙasar tana da babban matsayi a tarihin nahiyar, musamman saboda tsofaffin daulolin da suka wanzu a cikinta kafin zuwan Turawa. Babban birnin Peru shi ne Lima, wanda yake ɗaya daga cikin manyan birane da cibiyoyin tattalin arziki da siyasa a ƙasar.
Peru ta shahara saboda kasancewarta tsohuwar cibiyar daular Inca, wadda ta kasance ɗaya daga cikin manyan yankuna a tarihin nahiyar Amurka. Haka kuma, ƙasar tana da muhimman wuraren tarihi kamar Machu Picchu, wanda ya zama ɗaya daga cikin shahararrun wuraren tarihi da yawon buɗe ido a duniya. Baya ga tarihin da take da shi, Peru ƙasa ce mai yalwar albarkatun ƙasa, al’adu daban-daban da kyawawan wuraren da suka haɗa da tsaunukan Andes, dazukan Amazon da gaɓar tekun Pacific. Harshen Sifaniyanci shi ne harshen da aka fi amfani da shi, tare da wasu harsunan asali kamar Quechua da Aymara.
A yau, Peru tana taka muhimmiyar rawa a fannin tattalin arziki, noma, haƙar ma’adanai, yawon buɗe ido da hulɗar ƙasashen duniya. Ƙasar tana da yawan jama’a sama da miliyan 30, kuma tana ci gaba da fuskantar sauye-sauye a fannonin siyasa, tattalin arziki da zamantakewa.
Tarihin kafuwar Peru
Tarihin ƙasar Peru ya samo asali ne tun dubban shekaru kafin zuwan turawa a nahiyar kudancin Amurka. Yankin da a yau ake kira Peru ya kasance gida ga tsofaffin al’ummomi daban-daban waɗanda suka bunƙasa a fannonin noma, gine-gine, fasaha da tsarin zamantakewa.
Ɗaya daga cikin tsofaffin cigaban da aka samu a yankin ita ce Caral Civilization, wadda ta bunƙasa kusan shekaru 5,000 da suka gabata. Daga baya, Chavín, Nazca, Moche da Chimú suka bunƙasa a yankin.
A kusan ƙarni na 13, Inca ta cigaba da bunƙasa zuwa yankin Cusco. A ƙarƙashin jagorancin sarakunanta, musamman Pachacuti a ƙarni na 15, daular ta faɗaɗa zuwa yankuna masu yawa na Kudancin Amurka, inda ta kafa tsarin mulki, hanyoyin sufuri da tsarin tattalin arziki mai ƙarfi. Daular Inca ta kasance ɗaya daga cikin manyan daulolin nahiyar Amurka kafin zuwan Turawa.
A shekarar 1532, wani mai binciken ƙasar Spain mai suna Francisco Pizarro ya jagoranci sojojin Spain zuwa yankin. A wannan lokacin, daular Inca tana fama da rikicin cikin gida tsakanin ƴan’uwa Atahualpa da Huáscar. Mutanen Spain sun kama sarki Atahualpa a Cajamarca, sannan suka kashe shi a shekarar 1533. Wannan lamari ya taimaka wajen durƙusar da daular Inca, duk da cewa turjiya daga wasu ƴan asalin yankin ta ci gaba har zuwa shekarar 1572.
Bayan mamayar Spain, an kafa mulkin mallaka a yankin, inda aka samar da Viceroyalty of Peru a shekarar 1542. Birnin Lima, wanda Francisco Pizarro ya kafa a shekarar 1535, ya zama cibiyar mulkin Spain a yankin Kudancin Amurka na tsawon lokaci. A wannan zamani, an riƙa fitar da zinariya da azurfa daga yankin zuwa Spain.
A ƙarni na 19, ƙungiyoyin neman ƴancin kai suka fara samun ƙarfi a yankin Latin Amurka. A ranar 28 ga Yuli, 1821, José de San Martín ya ayyana ƴancin kan Peru daga ƙasar Spain. Sai dai yaƙin samun cikakken ƴanci ya ci gaba har zuwa watan Disamba na shekarar 1824, lokacin da sojojin masu neman ƴanci suka samu nasara a yaƙin Ayacucho ƙarƙashin jagorancin Antonio José de Sucre.
Daga nan ne Peru ta fara tafiyar da mulkin jamhuriya mai zaman kanta. Duk da haka, ƙasar ta fuskanci sauye-sauyen shugabanci, rikice-rikicen siyasa da yaƙe-yaƙe a lokuta daban-daban.
Yanayin ƙasa da muhalli
Kamar yadda ya gabata, ƙasar Peru tana a yankin nahiyar yammacin kudancin Amurka , inda take fuskantar Tekun Pacific a gefen yammacinta. Tana da iyaka da ƙasar Ecuador da Colombia a arewa, Brazil a gabas, Bolivia a kudu maso gabas, sannan Chile a kudu. A yammacin ƙasar kuma akwai Tekun Pacific.
Peru tana da faɗin fili kusan murabba’in kilomita 1,285,216, wanda hakan ya sanya ta cikin manyan ƙasashe uku mafi faɗi a kudancin Amurka, tare da Brazil da Argentina. Babban birninta shi ne Lima, wanda yake a yankin gabar tekun Pacific.
Har ila yau, Peru tana da manyan yankuna uku da aka rarraba ta fannin yanayin ƙasa, daga cikin yankunan akwai:
Yankin gaɓar teku
Wannan yanki yana gefen yammacin ƙasar, inda yake da tsawon bakin teku mai kusan kilomita 3,080. Yawancin yankin yana da yanayin hamada da ƙarancin ruwan sama, sai dai wasu kwarurruka da koguna suna samar da wuraren noma. Babban birnin Lima yana cikin wannan yanki, wanda kuma yake ɗaya daga cikin wuraren da jama’a suka fi yawa a ƙasar.
Yankin tsaunuka
Wannan yanki ya ƙunshi jerin manyan tsaunukan Andes, waɗanda suka ratsa tsakiyar ƙasar daga arewa zuwa kudu. Yankin yana da tsaunuka masu tsayi, kwarurruka da filaye masu tudu. A nan ne ake samun tsaunin Huascarán, wanda shi ne mafi tsayi a Peru, mai tsayin kusan mita 6,746. Yankin yana da muhimmanci wajen noma da samar da ma’adanai.
Yankin dazukan amazon
Wannan shi ne yanki mafi faɗi a Peru, wanda ya mamaye babban ɓangaren gabashin ƙasar. Yana cikin dajin Amazon, inda ake samun manyan koguna, bishiyoyi masu yawa da nau’o’in dabbobi da tsirrai daban-daban. Yankin yana da yanayin zafi da yawan ruwan sama, kuma yana taka rawa wajen kiyaye muhalli da samar da albarkatun gandun daji.

Ta ɓangaren yanayin ruwa da koguna kuwa, Peru tana da manyan koguna da tabkuna. Daga cikin manyan kogunanta akwai kogin Amazon, wanda tushensa yake a tsaunukan Andes na Peru. Haka kuma, ƙasar tana da kaso a tafkin Titicaca tare da ƙasar Bolivia. Wannan tafki yana daga cikin manyan tafkuna mafi tsayi a duniya da ake iya zirga-zirgar jiragen ruwa a cikinsu.
A fannin sauyin yanayi kuwa, saboda bambancin yanayin ƙasar, Peru tana da yanayin damina da zafi a yankin Amazon, ƙarancin ruwan sama a gaɓar teku, sannan yanayin sanyi a tsaunukan Andes. Wannan bambanci yana shafar rayuwar jama’a, noma, yawon buɗe ido da sauran harkokin tattalin arziki. Gaba ɗaya, yanayin ƙasar Peru yana da matuƙar bambanci, tun daga hamadar gaɓar teku zuwa manyan tsaunuka da dazukan Amazon. Wannan ya sanya ƙasar ta kasance ɗaya daga cikin wuraren da suka fi samun yalwar halittun muhalli a kudancin Amurka.
Al’umma da harshe
Al’ummomi
Ƙasar Peru tana daga cikin ƙasashen kudancin Amurka masu yawan jama’a da bambancin al’adu da asalin al’umma. Mutanen ƙasar sun samo asali ne daga tsofaffin al’ummomin yankin, musamman mutanen Inca da sauran ƙabilun asali, tare da zuriyar turawa, Afirka da kuma wasu al’ummomin da suka yi ƙaura daga sassa daban-daban na duniya.
Ta fuskar yawan jama’a, bisa ga sakamakon ƙidayar jama’a ta shekarar 2025 da hukumar ƙididdiga ta ƙasar Peru (INEI) ta fitar a shekarar 2026, yawan jama’ar ƙasar ya kai mutum 34,157,732. Wannan ya sanya Peru a matsayi ƙasa ta huɗu a yawan jama’a a kudancin Amurka, bayan Brazil, Colombia da Argentina.
Harsuna
Harshen Sifaniyanci shi ne harshen da aka fi amfani da shi a Peru, musamman a harkokin gwamnati, ilimi, kasuwanci da sadarwar yau da kullum. Baya ga Sifaniyanci, ƙasar tana da wasu harsunan asali masu muhimmanci, ciki har da Quechua, wanda harshe ne da ya shahara tun zamanin daular Inca. Da kuma Aymara, shima harshe ne da ake amfani da shi musamman a yankunan kudancin tsaunukan Andes. Sai Asháninka, yana daga cikin harsunan al’ummomin asalin yankin Amazon. Da kuma Shipibo-Konibo, wanda harshen wata al’umma ne da ke zaune a yankin dajin Amazon.
Gwamnatin Peru tana amincewa da harsunan asali a matsayin wani muhimmin ɓangare na al’adun ƙasar. Akwai harsunan asali 48 da ake magana da su a ƙasar, waɗanda suka haɗa da na yankin Andes da na Amazon.
Gaba ɗaya, bambancin al’umma, ƙabilu da harsuna ya sanya Peru ta kasance ƙasa mai ɗimbin al’adu da tarihi.
Addini da al’adu
Ƙasar Peru tana da bambancin addinai da al’adu waɗanda suka samo asali daga tsofaffin al’ummomin kudancin Amurka, musamman daular Inca, tare da tasirin zuwan turawan Spain a ƙarni na 16. Wannan haɗuwar tarihi ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da tsarin addini da al’adun mutanen ƙasar a yau.
Addinai
Addinin Kiristanci ne addinin da ya fi yaɗuwa a ƙasar Peru, musamman ma addinin Katolika. Wannan ya samo asali ne daga lokacin da Mutanen Spain suka mamaye yankin tare da yaɗa addinin Kiristanci.
Bisa ga ƙidayar jama’a ta shekarar 2017 da hukumar ƙididdiga ta Ƙasa (INEI) ta gudanar, kashi 76 na mutanen ƙasar masu shekaru 12 zuwa sama mabiya Katolika ne, yayin da kashi 14.1 suke bin addinin Furotesta. Kashi 4.8 suna bin wasu addinai, ciki har da Yahudanci, Musulunci da addinin Buddha, yayin da kashi 5.1 suka bayyana cewa ba su bin wani addini.
Haka kuma, akwai wasu al’ummomin asali da suke kiyaye tsofaffin aƙidun gargajiya waɗanda suka danganci girmama kakanni da alaƙar ɗan Adam da yanayi. A wasu yankuna, ana samun haɗuwar wasu al’adun gargajiya da bukukuwan Kiristanci.
Al’adu
Al’adun Peru sun ƙunshi abubuwa da dama waɗanda suka haɗa da al’adun Inca, sauran tsofaffin al’ummomin yankin, da tasirin al’adun Spain, Afirka da Asiya.
Ta fuskar Abinci, Peru tana da shahararrun nau’o’in abinci da suka bambanta daga yankin gaɓar teku zuwa tsaunukan Andes da dazukan Amazon. Daga cikin shahararrun abincinsu akwai Ceviche, wanda ake haɗawa da kifi, ruwan lemun tsami, albasa da kayan ƙamshi. Haka kuma, suna da abinci irin su Lomo Saltado da Cuy.
A fannin kiɗa da rawa kuwa, suna da matuƙar muhimmanci a al’adun mutanen Peru. Suna amfani da kayan kiɗa na gargajiya kamar Quena, Siku da Charango. Daga cikin shahararrun raye-rayensu akwai Marinera da Huayno.
A bukukuwan gargajiya, ɗaya daga cikin shahararrun bukukuwan ƙasar shi ne Inti Raymi, wanda ake gudanarwa a birnin Cusco domin tunawa da bikin Rana na tsohuwar daular Inca. Wannan biki yana nuna muhimmancin rana a tsarin rayuwa da aƙidun tsoffin mutanen Inca.
Tufafi da Sana’o’in Gargajiya, A yankunan tsaunukan Andes, wasu al’ummomi suna amfani da tufafin gargajiya masu launuka daban-daban, waɗanda ake ƙawatawa da zane-zane. Haka kuma, ƙasar ta shahara wajen saƙa, yin tukwane, sassaka da sauran sana’o’in hannu.
Tsarin mulki
Ƙasar Peru tana amfani da tsarin mulkin Jamhuriyar Dimokuraɗiyya, inda jama’a suke da damar zaɓen shugabanninsu ta hanyar zaɓe. Tsarin mulkinta ya dogara ne da kundin tsarin mulkin shekarar 1993, wanda ya tanadi yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati da sauran hukumomin ƙasa.
Peru ƙasa ce mai tsarin shugaban ƙasa, inda shugaban ƙasa yake zama shugaban ƙasa kuma shugaban gwamnati a lokaci guda. Ana zaɓen shugaban ƙasa ne ta hanyar zaɓen jama’a kai tsaye na wa’adin shekaru biyar, kuma kundin tsarin mulki bai ba shi damar yin tazarce nan take ba.
Sannan tsarin mulkin Peru ya kasu zuwa manyan rassa uku da suka haɗa da:
Ɓangaren zartarwa
Wannan shi ne ɓangaren da ke kula da aiwatar da dokoki da gudanar da harkokin yau da kullum na gwamnati. Shugaban ƙasa ne yake jagorantar wannan ɓangare, tare da taimakon Firayim Minista da majalisar ministoci. Shugaban ƙasa yana da alhakin kula da tsaron ƙasa, hulɗar ƙasashen waje, aiwatar da manufofin gwamnati da tabbatar da bin kundin tsarin mulki.
Ɓangaren Majalisa
Majalisar dokokin Peru ita ce cibiyar samar da dokoki da sa ido kan ayyukan gwamnati. A shekarar 2026, ƙasar ta koma tsarin majalisa mai gida biyu wato Bicameral Legislature, bayan gyaran kundin tsarin mulkin da aka yi a shekarar 2024. Sabon tsarin ya ƙunshi Majalisar Dattawa Mai mambobi 60. Da Majalisar Wakilai Mai mambobi 130. Ayyukansu sun haɗa da ƙirƙira da amincewa da dokoki, duba kasafin kuɗin ƙasa da sa ido kan ayyukan gwamnati.
Bangaren Shari’a
Wannan ɓangare ne mai alhakin gudanar da shari’a da tabbatar da adalci a ƙasar. Babbar Kotun Ƙasa tana daga cikin manyan hukumomin shari’a, tare da Kotun Tsarin Mulki
Aikin wannan ɓangare shi ne fassara dokoki, sauraron ƙararraki da tabbatar da cewa ana gudanar da shari’a bisa tanadin kundin tsarin mulki.
A fannin zaɓe kuwa, ana gudanar da babban zaɓen ƙasa duk bayan shekaru biyar domin zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisa. Idan babu ɗan takarar shugaban ƙasa da ya samu rinjayen ƙuri’un da ake buƙata a zagayen farko, ana gudanar da zagaye na biyu tsakanin manyan ƴan takara biyu. Haka kuma, dokar ƙasar ta tanadi cewa zaɓe wajibi ne ga ƴan ƙasa masu shekaru 18 zuwa 70, sai dai waɗanda doka ta keɓe.
A tarihin sauyin tsarin mulki, Peru ta samu sauye-sauye da dama a tsarin mulkinta tun bayan samun ƴancin kai a shekarar 1821. Ƙasar ta yi amfani da kundin tsarin mulki daban-daban a lokuta daban-daban, kafin kafa tsarin da kundin tsarin mulkin shekarar 1993 ya tanada.
Tattalin arziki
Ƙasar Peru tana da tattalin arzikin da ya dogara da fannoni daban-daban. Tana daga cikin ƙasashen kudancin Amurka masu bada gudummawa wajen samarwa da fitar da albarkatun ƙasa zuwa kasuwannin duniya.
A shekarar 2025, tattalin arzikin Peru ya samu ci gaban kusan kashi 3.4, yayin da jimillar GDP ɗinta ta kai kusan dala biliyan 334.85 na Amurka, bisa bayanan Bankin Duniya.
Manyan ginshiƙan tattalin arzikin Peru sun haɗa da:
Haƙar ma’adanai
Haƙar ma’adanai na sahun farko a cikin manyan hanyoyin samun kuɗaɗen shiga a Peru. Ƙasar tana da arzikin tagulla (Copper), zinariya, azurfa, zinc da gubar ƙarfe . Peru tana daga cikin manyan ƙasashen duniya wajen samar da waɗannan ma’adanai, musamman tagulla da azurfa. Ana fitar da su zuwa ƙasashe daban-daban, musamman China da Amurka, inda suke taimakawa wajen samun kuɗaɗen shiga daga cinikayyar ƙasashen waje.
Noma
Noma na taka muhimmiyar rawa wajen tattalin arzikin ƙasar da samar da ayyukan yi. Ana noma amfanin gona iri-iri kamar dankali, masara, shinkafa, kofi, inabi, avocado, bishiyar asparagus da blueberries. Peru tana daga cikin ƙasashen da suka yi fice wajen fitar da wasu kayan amfanin gona zuwa kasuwannin duniya. Yankunan gaɓar teku da kwarurukan tsaunukan Andes suna bada gudummawa wajen gudanar da harkokin noma.
Kamun kifi
Kasantuwar Peru tana da tsayin bakin teku a Tekun Pacific, kamun kifi ya zama wani muhimmin ɓangare na tattalin arzikinta. Ƙasar tana samar da nau’o’in kifaye da sauran halittun ruwa, musamman anchovy, wanda ake amfani da shi wajen samar da garin kifi da man kifi. Ana kuma fitar da kayan kamun kifi zuwa wasu ƙasashe, wanda ke taimakawa wajen samar da ayyukan yi da kuɗaɗen shiga.
Masana’antu
Peru tana da masana’antun sarrafa abinci, masaƙu, tufafi, kayayyakin ƙarfe, sinadarai da kayayyakin kamun kifi. Waɗannan masana’antu suna taimakawa wajen sarrafa albarkatun da ake samu a cikin gida zuwa kayayyakin da ake amfani da su a ƙasar da kuma waɗanda ake fitarwa zuwa ƙasashen waje.
Yawon buɗe ido
Yawon buɗe ido yana daga cikin muhimman hanyoyin samun kuɗaɗen shiga a Peru. Ƙasar tana da wuraren tarihi da kyawawan abubuwan jan hankali, musamman tsohon birnin Machu Picchu, birnin Cusco, tsaunukan Andes da dazukan Amazon. Masu yawon buɗe ido daga sassa daban-daban na duniya suna ziyartar ƙasar domin ganin wuraren tarihi, koyon al’adun gargajiya da jin daɗin kyawawan yanayinta.
Kasuwanci da huldar ƙasashen waje
Peru tana gudanar da harkokin kasuwanci da ƙasashe da dama, ciki har da China, Amurka da ƙasashen Tarayyar Turai. Manyan kayayyakin da take fitarwa sun haɗa da tagulla, zinariya, azurfa, kifi da kayan amfanin gona. Haka kuma, ƙasar tana cikin ƙungiyoyin hulɗar tattalin arziki na duniya kamar APEC da Pacific Alliance.
Muhimmancin Peru a duniya
Ƙasar Peru tana da muhimmiyar rawar takawa a duniya ta fuskar tattalin arziki, tarihi, al’adu, yawon buɗe ido da albarkatun muhalli. Kasancewarta ɗaya daga cikin ƙasashen da suka kasance cibiya mai daɗaɗɗen tarihi, tare da yalwar albarkatun ƙasa, ya ba ta matsayi na musamman a tsakanin ƙasashen duniya.
Ta fuskar tattalin arzikin duniya, Peru tana daga cikin manyan ƙasashen duniya wajen samar da ma’adanai. Kamar yadda ya gabata, tana da arzikin tagulla, zinariya, azurfa, zinc da tin. Bisa rahoton U.S. Geological Survey na shekarar 2024, Peru tana cikin manyan ƙasashen duniya wajen samar da azurfa da zinc, sannan tana matsayi na uku wajen samar da tagulla. Waɗannan ma’adanai suna da muhimmanci ga masana’antun lantarki, gine-gine da fasahar zamani.
A ɓangaren muhalli da halittu kuwa, Peru tana daga cikin ƙasashen duniya masu yalwar halittu da muhallin halitta. Wani babban ɓangare na dajin Amazon yana cikin ƙasar, inda ake samun nau’o’in tsirrai da dabbobi masu yawa. Dazukan ƙasar suna taimakawa wajen daidaita yanayin duniya, kiyaye halittu da kuma kare albarkatun ruwa. Haka kuma, yankin Andes yana da bada gudummawa wajen samar da ruwan koguna da ke taimaka wa al’ummomin yankin.
A fagen yawon buɗe ido, Peru tana daga cikin ƙasashen da suka shahara wajen yawon buɗe ido saboda wuraren tarihi da kyawawan yanayinta. Machu Picchu, Cusco, tafkin Titicaca da dazukan Amazon suna jawo hankalin masu yawon buɗe ido daga sassa daban-daban na duniya. Yawon buɗe ido yana taimakawa wajen samar da ayyukan yi, bunƙasa kasuwanci da kuma yaɗa al’adun mutanen Peru zuwa sauran duniya.

Har ila yau, abincin Peru ya samu karɓuwa a duniya saboda haɗuwar dabarun girki na tsofaffin al’ummomin yankin da tasirin al’adun Spain, Afirka da Asiya. Abinci irin su Ceviche da Lomo Saltado sun zama sanannu a ƙasashe daban-daban.
A wajen alaƙar Peru da ƙasashen duniya, Peru tana shiga cikin ƙungiyoyin haɗin gwiwar tattalin arziki da siyasa na duniya, ciki har da Majalisar Ɗinkin Duniya, Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO), APEC da Pacific Alliance.Ta hanyar waɗannan ƙungiyoyi, ƙasar tana hulɗa da sauran ƙasashe wajen kasuwanci, ilimi, tsaro, muhalli da ci gaban tattalin arziki.
Matsaloli da ƙalubale
Duk da arzikin ƙasa, albarkatun ma’adinai, kyawawan wuraren tarihi da ci gaban tattalin arzikin da ƙasar Peru ta samu, ta wata fuskar kuma tana fuskantar matsaloli daban-daban waɗanda suke shafar ci gabanta da rayuwar al’ummarta. Waɗannan ƙalubale sun haɗa da:
Rikicin siyasa
Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen Peru shi ne rashin daidaiton siyasa da sauye-sauyen shugabanci akai-akai. A cikin ƴan shekarun baya-bayan nan, ƙasar ta fuskanci sauye-sauyen shugabannin ƙasa, rikice-rikice tsakanin shugaban ƙasa da majalisa, da kuma rashin cikakken amincewar jama’a ga wasu hukumomin gwamnati. Wannan yanayi yana kawo tsaiko wajen aiwatar da manufofin gwamnati da wasu muhimman sauye-sauyen da ake buƙata domin ci gaban ƙasa.
Talauci
Duk da arzikin da Peru take da shi, har yanzu akwai al’ummomi da dama da suke fuskantar talauci da ƙarancin abubuwan more rayuwa. Bambancin tattalin arziki tsakanin mazauna birane da mutanen karkara yana daga cikin manyan matsalolin ƙasar. Wasu yankunan karkara, musamman na tsaunukan Andes da dazukan Amazon, suna fuskantar ƙarancin hanyoyin sufuri, cibiyoyin lafiya, makarantu da sauran muhimman ayyukan gwamnati.
Rashin ayyukan yi
Peru tana fuskantar matsalar rashin isassun ayyukan yi na tsari. Rahoton OECD na shekarar 2025 ya nuna cewa sama da kashi 70 na ma’aikatan ƙasar suna cikin ayyukan yi na ba bisa ƙa’ida ba. Irin waɗannan ayyukan ba sa ba ma’aikata cikakkiyar kariya ta dokokin aiki, inshorar lafiya da sauran hakkokin ma’aikata. Wannan kuma yana rage kuɗaɗen harajin da gwamnati ke samu.
Cin hanci da rashawa
Cin hanci da rashawa yana daga cikin manyan matsalolin da suke kawo cikas ga ci gaban Peru. Zarge-zargen cin hanci da suka shafi wasu jami’an gwamnati da shugabannin siyasa sun raunana amincewar jama’a ga hukumomin ƙasar. Haka kuma, wannan matsala tana iya kawo cikas ga gudanar da ayyukan raya ƙasa, amfani da kuɗaɗen gwamnati da jawo hankalin masu zuba jari.
Matsalar tsaro
A wasu yankunan Peru, ana fuskantar matsalolin fashi da makami, safarar miyagun ƙwayoyi, ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka da sauran matsalolin tsaro. Haka kuma, haɓakar ayyukan ƙungiyoyin masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba tana da alaƙa da wasu nau’o’in laifuffuka da tashin hankali. Waɗannan matsaloli suna shafar zaman lafiyar al’umma da harkokin kasuwanci.
Lalacewar muhalli da sare dazukan Amazon
Peru tana fuskantar matsalar sare bishiyoyi, lalacewar dazukan Amazon, gurɓacewar ruwa da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba. Wasu ayyukan hakar zinariya ba bisa ƙa’ida ba suna haifar da gurɓacewar ƙasa da ruwa, musamman saboda amfani da sinadaran da ke cutar da muhalli. Haka kuma, sare bishiyoyi domin noma da sauran ayyukan tattalin arziki yana barazana ga namun daji da tsirrai.
Sauyin yanayi da bala’o’i
Saboda yanayin ƙasarta, Peru tana fuskantar barazanar sauyin yanayi, ambaliyar ruwa, zaizayar ƙasa, fari da narkewar dusar ƙanƙara a tsaunukan Andes. Waɗannan matsaloli suna iya shafar noma, samar da ruwa, gidaje da hanyoyin sufuri. Haka kuma, al’ummomin da ke zaune a yankunan da ke fama da bala’o’in halitta suna cikin haɗarin rasa muhallansu da hanyoyin samun abin rayuwa.
Matsalolin ilimi da kiwon lafiya
A wasu yankunan Peru, har yanzu ana fuskantar ƙarancin makarantu masu inganci, kayan koyarwa da ƙwararrun malamai. Haka kuma, wasu yankunan karkara suna da ƙarancin cibiyoyin lafiya da ma’aikatan jinya. Bambancin samun damar ilimi da kiwon lafiya tsakanin birane da karkara yana daga cikin abubuwan da ke ƙara faɗaɗa rashin daidaiton rayuwa tsakanin al’ummomin ƙasar.
Jerin shugabannin Peru daga farko
Tun bayan ayyana samun ‘yancin kan Peru daga hannun Spain a ranar 28 ga Yuli, 1821, ƙasar ta samu shugabanni da dama waɗanda suka jagoranci mulkinta a lokuta daban-daban. Tarihin shugabancin ƙasar ya ƙunshi zaɓaɓɓun shugabanni, shugabannin riƙon ƙwarya, shugabannin mulkin soja da waɗanda suka karɓi mulki ta hanyar juyin mulki. A wasu lokuta kuma, an samu sauye-sauyen shugabanci cikin ɗan gajeren lokaci sakamakon rikice-rikicen siyasa da yaƙe-yaƙe.
Shugabannin farkon Jamhuriyar Peru (1821–1845)
- José de San Martín (1821–1822)
José de San Martín shi ne jagoran rundunar ‘yancin kai da ta taimaka wajen ‘yantar da Peru daga mulkin mallakar Spain. Ya ayyana ‘yancin kan ƙasar a ranar 28 ga Yuli, 1821, sannan ya jagoranci gwamnatin wucin gadi da mukamin Protector of Peru. Babbar gudunmawarsa ita ce kafa tubalin mulkin ƙasar mai zaman kanta da shirya sauyin da ya kai ga kafa jamhuriya.
- José de la Mar (1822–1823)
José de la Mar ya kasance shugaban majalisar gudanarwar gwamnati da aka kafa bayan tafiyar San Martín. Ya jagoranci wannan majalisa tare da Manuel Salazar y Baquíjano da Felipe Antonio Alvarado. Gwamnatinsu ta yi ƙoƙarin tafiyar da ƙasar a lokacin da ake ci gaba da yaƙin neman ‘yancin kai da kafa sababbin hukumomin gwamnati.
- José de la Riva Agüero (1823)
José de la Riva Agüero shi ne shugaban farko da aka ba wa mukamin shugaban ƙasar Peru a hukumance. Ya karɓi mulki a watan Fabrairu, 1823, a lokacin da ake fama da yaƙi da Spain da rikicin siyasa. Gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin ƙarfafa rundunar sojojin ƙasar, amma rashin jituwa da majalisar dokoki ya haddasa rikicin shugabanci.
- José Bernardo de Tagle (1823–1824)
José Bernardo de Tagle, wanda aka fi sani da Marqués de Torre Tagle, ya jagoranci Peru bayan rikicin da ya shafi gwamnatin Riva Agüero. Ya taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da gwamnati a lokacin da ake fafatawa da rundunar Spain. Sai dai rikice-rikicen siyasa da na soja sun raunana gwamnatinsa, musamman bayan zuwan Simón Bolívar.
- Simón Bolívar (1824–1826)
Simón Bolívar ya jagoranci gwagwarmayar tabbatar da ‘yancin kan Peru, tare da taimakon manyan shugabannin soja ciki har da Antonio José de Sucre. Nasarar rundunar ‘yancin kai a Yaƙin Junín da Ayacucho a shekarar 1824 ta taka muhimmiyar rawa wajen kawo ƙarshen mulkin Spain a Kudancin Amurka. Bolívar ya kuma taimaka wajen tsara tsarin mulkin ƙasar, kafin ya bar Peru a shekarar 1826.
- Andrés de Santa Cruz (1826–1827)
Andrés de Santa Cruz ya jagoranci gwamnatin Peru a matsayin shugaban majalisar gudanarwa bayan tafiyar Bolívar. Ya yi ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiyar siyasa da ci gaba da tafiyar da hukumomin gwamnati a lokacin da ake sauya tsarin mulkin ƙasar.
- Manuel Salazar y Baquíjano (1827)
Manuel Salazar y Baquíjano ya jagoranci gwamnatin ƙasar na ɗan lokaci a lokacin sauyin shugabanci bayan tafiyar Santa Cruz. Ya kasance ɗaya daga cikin manyan jami’an gwamnati da suka taimaka wajen tafiyar da harkokin ƙasa a farkon zamanin jamhuriya.
- José de La Mar (1827–1829)
José de La Mar ya zama shugaban ƙasar bayan majalisa ta zaɓe shi a shekarar 1827. Ya yi ƙoƙarin ƙarfafa tsarin jamhuriya da hukumomin gwamnati. A lokacin mulkinsa, Peru ta shiga yaƙi da Gran Colombia, wanda ya haifar da matsalolin siyasa da soja. Daga ƙarshe aka hambarar da shi a shekarar 1829.
- Antonio Gutiérrez de la Fuente (1829)
Antonio Gutiérrez de la Fuente ya karɓi ragamar shugabanci na ɗan lokaci bayan hambarar da José de La Mar. Ya jagoranci gwamnati a lokacin rikicin siyasa da ya kai ga hawa karagar mulki na Agustín Gamarra.
- Agustín Gamarra (1829–1833)
Agustín Gamarra ya kasance ɗaya daga cikin fitattun shugabannin soja da siyasa a farkon tarihin Peru. Ya yi ƙoƙarin ƙarfafa ikon gwamnatin tsakiya da tabbatar da zaman lafiyar ƙasa. Sai dai mulkinsa ya fuskanci rikice-rikicen siyasa da na soja, musamman saɓani tsakanin ƙungiyoyin da ke neman rinjayar gwamnatin ƙasar.
- Antonio Gutiérrez de la Fuente (1830–1831)
Ya sake jagorantar harkokin gwamnati a matsayin mataimakin shugaban ƙasa mai riƙon ragamar mulki yayin da Agustín Gamarra ba ya gudanar da wasu ayyukan shugabanci kai tsaye. Wannan lokaci ya kasance cikin jerin sauye-sauyen shugabanci da aka samu a farkon jamhuriyar.
- Andrés Reyes y Buitrón (1831)
Andrés Reyes y Buitrón ya jagoranci gwamnati na ɗan lokaci a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa, bisa tsarin maye gurbin shugabanci. Lokacinsa ya kasance cikin ƙoƙarin tabbatar da ci gaban harkokin gwamnati a lokacin da ake fama da rashin daidaiton siyasa.
- Manuel Tellería Vicuña (1832)
Manuel Tellería Vicuña ya riƙe ragamar shugabanci na ɗan lokaci a shekarar 1832 a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa. Wannan na daga cikin lokutan da shugabanci ke sauyawa tsakanin jami’an gwamnati sakamakon rashin zaman lafiyar siyasa.
- José Braulio del Campo Redondo (1833)
José Braulio del Campo Redondo ya jagoranci gwamnatin ƙasar na ɗan lokaci a shekarar 1833, a matsayin mataimakin shugaban majalisar gudanarwa. Ya kasance cikin jami’an da suka taimaka wajen tafiyar da gwamnati kafin kafa sabon shugabanci.
- Luis José de Orbegoso (1833–1835)
Luis José de Orbegoso ya zama shugaban ƙasar a shekarar 1833. Gwamnatinsa ta fuskanci saɓani tsakanin ƙungiyoyin siyasa da manyan hafsoshin soja. Wannan rikici ya taimaka wajen haifar da gwagwarmayar da ta kai ga kafa ƙawancen Peru da Bolivia.
- Felipe Santiago Salaverry (1835–1836)
Felipe Santiago Salaverry ya karɓi mulki ta hanyar juyin mulkin soja a shekarar 1835. Ya yi ƙoƙarin kafa gwamnati mai ƙarfi, amma ya fuskanci rundunonin Andrés de Santa Cruz waɗanda suka goyi bayan gwamnatin Orbegoso. Daga ƙarshe aka kama shi aka kashe shi a shekarar 1836.
- Andrés de Santa Cruz (1836–1839)
Andrés de Santa Cruz ya jagoranci kafa ƙawancen Peru da Bolivia, wanda aka sani da Peru-Bolivian Confederation. Manufarsa ita ce haɗa ƙasashen biyu domin samar da haɗin gwiwar siyasa da tattalin arziki. Sai dai ƙawancen ya fuskanci adawa daga wasu ƙungiyoyin Peru da ƙasashen waje, wanda ya kai ga rushewarsa a shekarar 1839.
- Agustín Gamarra (1839–1841)
Gamarra ya sake zama shugaban Peru bayan rushewar ƙawancen Peru da Bolivia. A mulkinsa na biyu, ya yi ƙoƙarin sake gina tsarin jamhuriya da ƙarfafa ikon gwamnatin tsakiya. Ya mutu a shekarar 1841 yayin da yake jagorantar rundunar sojojin Peru a yaƙi da Bolivia.
- Manuel Menéndez (1841–1842; 1844–1845)
Manuel Menéndez ya jagoranci Peru a matsayin shugaban riƙon ƙwarya bayan mutuwar Agustín Gamarra. Ya yi ƙoƙarin tabbatar da ci gaban mulkin doka a lokacin rikice-rikicen siyasa da na soja. Ya sake komawa shugabanci a shekarar 1844, inda ya taimaka wajen shirya hanyar komawa ga gwamnatin tsarin mulki.
- Francisco de Vidal (1842–1843)
Francisco de Vidal ya jagoranci ƙasar a lokacin rikice-rikicen siyasa da suka biyo bayan mutuwar Gamarra. Ya kasance ɗaya daga cikin shugabannin soja da suka shiga fafutukar tabbatar da sabon tsarin shugabanci a ƙasar.
- Domingo Nieto (1843)
Domingo Nieto ya taka muhimmiyar rawa a gwagwarmayar da aka yi da gwamnatin mulkin soja ta Manuel Ignacio de Vivanco. Ya jagoranci rundunonin da suka yi adawa da gwamnatin Vivanco, tare da taimakawa wajen dawo da tsarin mulkin doka. Ya rasu a shekarar 1844 kafin kammala wannan sauyin siyasa.
- Manuel Ignacio de Vivanco (1843–1844)
Manuel Ignacio de Vivanco ya karɓi mulki ta hanyar juyin mulkin soja, inda ya kafa gwamnatin da ya kira Supreme Directory. Gwamnatinsa ta fuskanci adawa daga manyan shugabannin soja da ƙungiyoyin siyasa, musamman rundunonin da Domingo Nieto da Ramón Castilla suka jagoranta.
- Domingo Elías (1844)
Domingo Elías ya jagoranci wani ɓangare na gwamnatin Peru a shekarar 1844, musamman a yankin arewacin ƙasar, a lokacin da ake fama da rikicin mulkin Vivanco. Gudunmawarsa ta kasance cikin ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin da dawo da zaman lafiyar siyasa.
- Justo Figuerola (1844)
Justo Figuerola ya riƙe shugabancin majalisar gudanarwa na ɗan lokaci a watan Agustan 1844, bayan sauye-sauyen da suka biyo bayan faɗuwar gwamnatin Vivanco. Mulkinsa ya kasance cikin jerin gwamnatocin riƙon ƙwarya da suka taimaka wajen dawo da tsarin mulkin doka.
- Ramón Castilla (1845–1851)
Ramón Castilla ya hau karagar mulki a shekarar 1845, inda ya zama ɗaya daga cikin shugabannin da suka fi taka rawa wajen gina Peru ta zamani. Ya ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar ta hanyar amfani da kuɗaɗen shiga daga takin guano. A lokacin mulkinsa na biyu, ya soke bautar da mutane a shekarar 1854, sannan ya kawo ƙarshen harajin da ake ɗora wa wasu al’ummomin asali. Ya kuma inganta hanyoyin sufuri, sadarwa da rundunar sojojin ruwa.
Shugabannin Peru a Ƙarni na Sha Tara (1851–1899)
- José Rufino Echenique (1851–1855)
José Rufino Echenique ya zama shugaban ƙasa bayan Ramón Castilla. Gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin inganta tattalin arziki da samar da kuɗaɗen raya ƙasa. Sai dai ta fuskanci zarge-zargen almundahana da rashin gaskiya wajen biyan basussukan gwamnati, lamarin da ya haddasa babban rikicin siyasa. Daga ƙarshe aka hambarar da shi bayan yaƙin basasar da Ramón Castilla ya jagoranta.
- Ramón Castilla (1855–1862)
Castilla ya sake komawa shugabanci bayan nasarar da ya samu a yaƙin basasa. A wannan wa’adi ya ci gaba da sauye-sauyen zamantakewa da tattalin arziki, tare da ƙarfafa rundunar sojojin ƙasar da inganta harkokin sufuri. A shekarar 1860, an amince da sabon kundin tsarin mulki wanda ya zama muhimmin ginshiƙi a tarihin siyasar Peru.
- Miguel de San Román (1862–1863)
Miguel de San Román ya zama shugaban ƙasa a shekarar 1862, amma bai daɗe a kan karagar mulki ba saboda rasuwarsa a shekarar 1863. A lokacin mulkinsa an aiwatar da sauye-sauye a tsarin kuɗin ƙasar, ciki har da ƙarfafa amfani da kuɗin Sol.
- Pedro Diez Canseco (1863)
Pedro Diez Canseco ya karɓi shugabancin ƙasa a matsayin mataimakin shugaban ƙasa bayan rasuwar Miguel de San Román. Ya jagoranci gwamnati na ɗan lokaci kafin Juan Antonio Pezet ya karɓi shugabancin ƙasar bisa tsarin mulki.

- Juan Antonio Pezet (1863–1865)
Juan Antonio Pezet ya jagoranci ƙasar a lokacin rikicin diflomasiyya da Spain, wanda ya samo asali daga takaddamar da ta shafi tsoma bakin Spain a harkokin Peru. Gwamnatinsa ta fuskanci matsin lamba daga sojoji da jama’a kan yadda take tafiyar da rikicin. Daga ƙarshe aka hambarar da shi a shekarar 1865.
- Mariano Ignacio Prado (1865–1868)
Mariano Ignacio Prado ya karɓi mulki bayan hambarar da Pezet. Ya jagoranci ƙawancen Peru, Chile, Bolivia da Ecuador wajen fuskantar mamayar Spain a Kudancin Amurka. A lokacin mulkinsa, rundunar ƙasashen ƙawancen ta samu gagarumar nasara a Yaƙin Callao a shekarar 1866, wanda ya taimaka wajen kawo ƙarshen barazanar Spain a yankin.
- Pedro Diez Canseco (1868)
Pedro Diez Canseco ya sake karɓar shugabancin ƙasa a shekarar 1868 bayan sauyin gwamnati. Ya jagoranci gwamnatin riƙon ƙwarya, inda ya kula da harkokin ƙasa har zuwa lokacin da aka miƙa mulki ga José Balta.
- José Balta (1868–1872)
José Balta ya mai da hankali kan bunƙasa ababen more rayuwa, musamman gine-ginen hanyoyin jirgin ƙasa da inganta hanyoyin sufuri. Gwamnatinsa ta ƙaddamar da manyan ayyukan gine-gine domin haɗa birane da yankunan da ke samar da albarkatun ƙasa. Sai dai ta fuskanci matsalolin kuɗi sakamakon yawan bashin da aka karɓa domin gudanar da waɗannan ayyuka.
- Tomás Gutiérrez (1872)
Tomás Gutiérrez ya jagoranci juyin mulkin soja a shekarar 1872 domin hana Manuel Pardo karɓar shugabancin ƙasa bayan zaɓensa. Mulkinsa bai daɗe ba saboda adawar jama’a da sojoji. Daga ƙarshe aka kashe shi a lokacin rikicin da ya biyo bayan juyin mulkin.
- Manuel Pardo (1872–1876)
Manuel Pardo shi ne shugaban farar hula na farko da aka zaɓa a tarihin Peru. Ya yi ƙoƙarin ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya, inganta ilimi da gyara harkokin kuɗin gwamnati. Ya kuma nemi rage dogaro da kuɗaɗen shiga daga takin guano, tare da bunƙasa tsarin siyasar farar hula a ƙasar.
- Mariano Ignacio Prado (1876–1879)
Prado ya sake zama shugaban ƙasa a shekarar 1876. A lokacin wannan wa’adi ne Peru ta shiga Yaƙin Pacific da Chile a shekarar 1879, bayan rikicin da ya shafi Bolivia da Chile da kuma yarjejeniyar ƙawancen Peru da Bolivia. Gwamnatinsa ta fuskanci manyan matsalolin soja da tattalin arziki. A lokacin yaƙin ya bar ƙasar zuwa Turai, lamarin da ya jawo masa suka sosai.
- Nicolás de Piérola (1879–1881)
Nicolás de Piérola ya karɓi mulki a lokacin Yaƙin Pacific bayan rikicin da ya biyo bayan tafiyar Mariano Ignacio Prado. Ya jagoranci Peru a lokacin da Chile ke samun nasarorin soja da mamaye wasu yankunan ƙasar, ciki har da Lima a shekarar 1881. Gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin tsara rundunar tsaro da ci gaba da yaƙin, amma matsin lambar soja ya raunana ikon gwamnati.
- Francisco García Calderón (1881)
Francisco García Calderón ya jagoranci gwamnatin Peru a lokacin mamayar Chile. Ya yi ƙoƙarin kare ‘yancin kan ƙasar da kuma kawo ƙarshen yaƙin ta hanyar tattaunawar diflomasiyya. Sai dai ya ƙi amincewa da wasu sharuɗɗan Chile da suka shafi miƙa yankunan Peru, lamarin da ya sa aka kama shi aka kai shi Chile.
- Lizardo Montero (1881–1883)
Lizardo Montero ya jagoranci gwamnatin Peru bayan kama García Calderón. Ya ci gaba da ƙoƙarin shirya rundunar sojojin ƙasar da kare sauran yankunan da ba su shiga hannun Chile ba. Gwamnatinsa ta fuskanci matsalolin gudanar da mulki saboda mamayar ƙasar da rashin cikakken ikon gwamnati.
- Miguel Iglesias (1883–1885)
Miguel Iglesias ya jagoranci gwamnatin Peru a lokacin ƙarshen Yaƙin Pacific. Ya amince da yarjejeniyar Ancón da Chile a shekarar 1883, wadda ta kawo ƙarshen yaƙin. Yarjejeniyar ta tanadi miƙa yankin Tarapacá ga Chile da kuma tsarin gudanar da ƙuri’ar jama’a kan makomar wasu yankuna. Sai dai wannan mataki ya haifar da saɓani da wasu shugabannin siyasa da soja a ƙasar.
- Andrés Avelino Cáceres (1886–1890)
Andrés Avelino Cáceres ya kasance fitaccen jagoran soja a lokacin Yaƙin Pacific, inda ya jagoranci gwagwarmayar adawa da sojojin Chile. Bayan ya zama shugaban ƙasa, ya yi ƙoƙarin sake gina tattalin arzikin Peru bayan asarar da ƙasar ta yi a yaƙin. Gwamnatinsa ta kuma fuskanci matsalolin basussukan ƙasa da sake fasalin harkokin kuɗi.
- Remigio Morales Bermúdez (1890–1894)
Remigio Morales Bermúdez ya jagoranci ƙasar a lokacin da ake ƙoƙarin dawo da zaman lafiyar siyasa da bunƙasa tattalin arziki bayan matsalolin da suka biyo bayan Yaƙin Pacific. Gwamnatinsa ta ci gaba da wasu ayyukan raya ƙasa, amma ya rasu a shekarar 1894 kafin kammala wa’adinsa.
- Justiniano Borgoño (1894)
Justiniano Borgoño ya karɓi shugabancin ƙasa bayan rasuwar Morales Bermúdez. Ya jagoranci gwamnatin riƙon ƙwarya, amma mulkinsa ya fuskanci suka saboda matakan siyasa da suka shafi shirya zaɓen shugaban ƙasa. Ya miƙa mulki ga Andrés Avelino Cáceres bayan zaɓen da aka gudanar a shekarar 1894.
- Andrés Avelino Cáceres (1894–1895)
Cáceres ya sake zama shugaban ƙasa a shekarar 1894, amma wannan wa’adi ya fuskanci babban adawa daga ƙungiyoyin siyasa da Nicolás de Piérola ke jagoranta. Bayan rikicin soja da ya biyo baya, ya yi murabus a shekarar 1895, lamarin da ya kawo ƙarshen wa’adinsa na biyu.
- Manuel Candamo (1895)
Manuel Candamo ya jagoranci gwamnatin riƙon ƙwarya a shekarar 1895, a lokacin sauyin shugabanci bayan ficewar Cáceres. Ya taka rawa wajen shirya hanyar da ta kai ga kafa gwamnatin Nicolás de Piérola.
- Nicolás de Piérola (1895–1899)
Nicolás de Piérola ya koma shugabanci bayan nasarar ƙungiyarsa a rikicin siyasa da ya kawo ƙarshen mulkin Cáceres. A wa’adinsa na biyu, ya yi ƙoƙarin sake gina tattalin arzikin Peru, gyara tsarin kuɗi da ƙarfafa hukumomin gwamnati. An kuma samu ci gaba a wasu fannonin sufuri da kasuwanci, wanda ya taimaka wajen dawo da zaman lafiyar tattalin arzikin ƙasar.
Shugabannin Peru a Ƙarni na Ashirin (1899–1999)
- Eduardo López de Romaña (1899–1903)
Eduardo López de Romaña ya jagoranci Peru a lokacin da ake samun sauye-sauyen tattalin arziki da bunƙasar masana’antu. Ya mayar da hankali kan noma, haƙar ma’adanai da inganta hanyoyin sufuri. A gwamnatinsa an kuma ƙarfafa ayyukan gine-gine da bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.
- Manuel Candamo (1903–1904)
Manuel Candamo ya zama shugaban ƙasa a shekarar 1903. Ya yi ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiyar siyasa da ci gaba da shirye-shiryen raya ƙasar da gwamnatocin baya suka fara. Sai dai ya rasu a shekarar 1904 kafin kammala wa’adinsa.
- Serapio Calderón (1904)
Serapio Calderón ya karɓi shugabancin ƙasa a matsayin riƙon ƙwarya bayan rasuwar Manuel Candamo. Ya jagoranci gwamnati har zuwa lokacin da aka gudanar da zaɓen da ya kai José Pardo y Barreda kan karagar mulki.
- José Pardo y Barreda (1904–1908)
José Pardo y Barreda ya mai da hankali kan bunƙasa ilimi, faɗaɗa makarantu da inganta ayyukan gwamnati. A lokacin mulkinsa an ƙarfafa tsarin ilimin jama’a, tare da gudanar da wasu sauye-sauye a harkokin zamantakewa da gudanar da mulki.
- Augusto B. Leguía (1908–1912)
Augusto B. Leguía ya jagoranci ƙasar a wa’adinsa na farko, inda ya mayar da hankali kan bunkasa tattalin arziki da inganta ababen more rayuwa. Ya kuma ƙarfafa hulɗar Peru da ƙasashen waje, musamman a fannin kasuwanci da zuba jari.
- Guillermo Billinghurst (1912–1914)
Guillermo Billinghurst ya yi ƙoƙarin inganta rayuwar ma’aikata da samar da sauye-sauyen zamantakewa. Ya nuna goyon baya ga buƙatun ƙungiyoyin ma’aikata, amma rashin jituwa tsakaninsa da majalisa da manyan jami’an soja ya kai ga hambarar da shi a shekarar 1914.
- Óscar R. Benavides (1914–1915)
Óscar R. Benavides ya karɓi mulki bayan hambarar da Billinghurst. Ya jagoranci gwamnatin wucin gadi a lokacin da ake ƙoƙarin dawo da zaman lafiyar siyasa da shirya zaɓen sabon shugaban ƙasa.
- José Pardo y Barreda (1915–1919)
Pardo ya sake zama shugaban ƙasa a shekarar 1915. A wannan wa’adi ya ci gaba da ƙarfafa ilimi da ayyukan gwamnati. Sai dai ƙasar ta fuskanci matsalolin tattalin arziki da ƙungiyoyin ma’aikata, waɗanda suka ƙara tsananta saɓani tsakanin gwamnati da wasu ɓangarorin al’umma.
- Augusto B. Leguía (1919–1930)
Augusto B. Leguía ya sake karɓar mulki a shekarar 1919, inda ya kafa tsarin mulkin da aka fi sani da Oncenio de Leguía, wato mulkin shekaru goma sha ɗaya. Ya gudanar da manyan ayyukan gine-ginen hanyoyi, gine-ginen gwamnati da samar da ababen more rayuwa. A shekarar 1920 an kafa sabon kundin tsarin mulki, amma mulkinsa ya kasance mai tsauri, tare da takaita wasu ‘yancin siyasa. An hambarar da shi a shekarar 1930.
- Luis Miguel Sánchez Cerro (1930–1931)
Sánchez Cerro ya karɓi mulki bayan hambarar da gwamnatin Leguía. Ya jagoranci gwamnatin soja a lokacin da ƙasar ke fama da rikicin siyasa da matsalolin tattalin arziki. Daga baya ya sauka daga mulki, wanda ya buɗe hanyar kafa gwamnatin riƙon ƙwarya.
- David Samanez Ocampo (1931)
David Samanez Ocampo ya jagoranci gwamnatin riƙon ƙwarya a shekarar 1931. Babban aikinsa shi ne dawo da tsarin dimokuraɗiyya, tsara zaɓen shugaban ƙasa da tabbatar da gudanar da harkokin gwamnati cikin doka. Zaɓen da aka gudanar ya kai Sánchez Cerro ga shugabanci a karo na biyu.
- Luis Miguel Sánchez Cerro (1931–1933)
Sánchez Cerro ya koma shugabancin ƙasa bayan lashe zaɓen shekarar 1931. Gwamnatinsa ta fuskanci rikice-rikicen siyasa, tashe-tashen hankula da matsalolin tsaro. A shekarar 1933 aka amince da sabon kundin tsarin mulki. An kashe shi a ranar 30 ga Afrilu, 1933, yayin da yake kan karagar mulki.
- Óscar R. Benavides (1933–1939)
Óscar R. Benavides ya karɓi shugabancin ƙasa bayan kisan Sánchez Cerro. Ya mayar da hankali kan dawo da zaman lafiyar siyasa, bunƙasa tattalin arziki da sake ƙarfafa hukumomin gwamnati. A mulkinsa an gudanar da wasu ayyukan more rayuwa da gyare-gyaren hukumomi.
- Manuel Prado y Ugarteche (1939–1945)
Manuel Prado ya jagoranci Peru a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu. A shekarar 1941, ƙasar ta shiga yaƙi da Ecuador sakamakon takaddamar iyakoki. Gwamnatinsa ta kuma ƙarfafa hulɗar ƙasar da ƙasashen ƙawancen duniya da bunƙasa wasu fannonin tattalin arziki.
- José Luis Bustamante y Rivero (1945–1948)
José Luis Bustamante y Rivero ya jagoranci gwamnatin dimokuraɗiyya bayan lashe zaɓen shekarar 1945. Ya yi ƙoƙarin ƙarfafa bin doka, ‘yancin hukumomi da tsarin mulkin farar hula. Sai dai gwamnatinsa ta fuskanci matsalolin tattalin arziki da rikice-rikicen siyasa, waɗanda suka kai ga juyin mulkin soja a shekarar 1948.
- Manuel A. Odría (1948–1956)
Manuel A. Odría ya karɓi mulki ta hanyar juyin mulkin soja a shekarar 1948. Ya jagoranci gwamnatin soja kafin daga baya ya zama shugaban ƙasa ta hanyar zaɓen shekarar 1950. A mulkinsa an gudanar da ayyukan gine-ginen makarantu, asibitoci, hanyoyi da wasu manyan gine-ginen gwamnati. Duk da ayyukan raya ƙasa, gwamnatinsa ta takaita wasu ‘yancin siyasa.
- Manuel Prado y Ugarteche (1956–1962)
Prado ya sake zama shugaban ƙasa a shekarar 1956. A wannan wa’adi ya mayar da hankali kan bunƙasa tattalin arziki, inganta ilimi da ƙarfafa harkokin kasuwanci. Sai dai gwamnatinsa ta fuskanci rikice-rikicen siyasa da zarge-zargen maguɗin zaɓe, wanda ya kai ga juyin mulkin soja a shekarar 1962.
- Ricardo Pérez Godoy (1962–1963)
Ricardo Pérez Godoy ya jagoranci gwamnatin soja bayan hambarar da Manuel Prado. Babban aikin gwamnatinsa shi ne kula da harkokin ƙasa da shirya sabon zaɓen shugaban ƙasa. Sai dai daga baya aka cire shi daga shugabancin gwamnatin soja, inda Nicolás Lindley López ya maye gurbinsa.
- Nicolás Lindley López (1963)
Nicolás Lindley López ya jagoranci gwamnatin soja ta riƙon ƙwarya a shekarar 1963. Ya kula da shirya zaɓen da ya dawo da gwamnatin farar hula a ƙarƙashin Fernando Belaúnde Terry.
- Fernando Belaúnde Terry (1963–1968)
Fernando Belaúnde Terry ya jagoranci gwamnatin farar hula bayan nasarar zaɓensa. Ya mayar da hankali kan dimokuraɗiyya, samar da gidaje, gine-ginen hanyoyi da bunƙasa yankunan karkara. Sai dai takaddamar siyasa da matsalolin tattalin arziki sun raunana gwamnatinsa, har aka hambarar da shi ta hanyar juyin mulkin soja a shekarar 1968.
- Juan Velasco Alvarado (1968–1975)
Juan Velasco Alvarado ya karɓi mulki ta hanyar juyin mulkin soja. Babban sauyin da ya yi shi ne garambawul a fannin noma, inda aka ƙwace manyan gonaki aka mayar da su hannun ƙungiyoyin manoma. Ya kuma mayar da wasu muhimman masana’antu da albarkatun ƙasa ƙarƙashin ikon gwamnati, tare da aiwatar da sauye-sauyen zamantakewa da tattalin arziki.
- Francisco Morales Bermúdez (1975–1980)
Francisco Morales Bermúdez ya jagoranci gwamnatin soja bayan hambarar da Velasco Alvarado. Ya fuskanci matsalolin tattalin arziki da matsin lambar jama’a na komawa mulkin dimokuraɗiyya. Babban abin da ya cimma shi ne jagorantar tsarin sauyin mulki, wanda ya haɗa da kafa kundin tsarin mulkin shekarar 1979 da shirya zaɓen da ya dawo da gwamnatin farar hula.
- Fernando Belaúnde Terry (1980–1985)
Belaúnde ya sake zama shugaban ƙasa bayan dawowar tsarin dimokuraɗiyya. Ya ci gaba da ayyukan raya ƙasa, gine-ginen hanyoyi da samar da gidaje. Sai dai gwamnatinsa ta fuskanci matsalolin tattalin arziki da ƙaruwar ayyukan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, musamman Shining Path, wanda ya haifar da rashin tsaro a wasu yankuna.
- Alan García (1985–1990)
Alan García ya jagoranci ƙasar a lokacin da ake fama da manyan matsalolin tattalin arziki. A mulkinsa na farko, Peru ta fuskanci hauhawar farashi mai tsanani, raguwar darajar kuɗi da matsalolin biyan basussukan ƙasa. Haka kuma, ƙasar ta ci gaba da fuskantar matsalar ayyukan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
- Alberto Fujimori (1990–2000)
Alberto Fujimori ya yi mulkin Peru na tsawon shekaru goma. A lokacin mulkinsa an gudanar da manufofin sake fasalin tattalin arziki, waɗanda suka taimaka wajen rage hauhawar farashi da farfaɗo da wasu sassan tattalin arziki. Gwamnatinsa ta kuma samu nasarori wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya. Sai dai ta fuskanci manyan zarge-zargen take haƙƙin ɗan Adam, cin hanci da rashawa da tauye dimokuraɗiyya. A shekarar 1992 ya rushe majalisa tare da sake fasalin tsarin gwamnati, matakin da ya jawo suka daga ƙasashen duniya.
Shugabannin Peru a arni na Ashirin da ɗaya (2000–2026)
- Valentín Paniagua (2000–2001)
Valentín Paniagua ya jagoranci gwamnatin riƙon ƙwarya bayan ficewar Alberto Fujimori daga mulki a shekarar 2000. Babban aikinsa shi ne dawo da tsarin dimokuraɗiyya, ƙarfafa amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati da shirya zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2001.
- Alejandro Toledo (2001–2006)
Alejandro Toledo ya zama shugaban ƙasa bayan dawowar tsarin mulkin dimokuraɗiyya. A gwamnatinsa an samu ci gaban tattalin arziki, faɗaɗa shirye-shiryen rage talauci da ƙarfafa hulɗar kasuwanci da ƙasashen waje. Ya kuma ƙarfafa wasu shirye-shiryen ilimi da zamantakewa.
- Alan García (2006–2011)
Alan García ya koma shugabancin ƙasa a karo na biyu a shekarar 2006. A wannan wa’adi Peru ta samu bunƙasar tattalin arziki sakamakon ƙaruwar kasuwanci, zuba jari da fitar da ma’adanai zuwa ƙasashen waje. Gwamnatinsa ta kuma ƙarfafa yarjejeniyoyin kasuwanci da wasu ƙasashen duniya.
- Ollanta Humala (2011–2016)
Ollanta Humala ya mayar da hankali kan rage talauci, inganta rayuwar al’ummomin karkara da faɗaɗa shirye-shiryen taimakon jama’a. Gwamnatinsa ta kuma ci gaba da ayyukan more rayuwa da bunƙasa tattalin arziki, tare da aiwatar da shirye-shiryen rage bambancin rayuwa tsakanin masu hannu da shuni da talakawa.
- Pedro Pablo Kuczynski (2016–2018)
Pedro Pablo Kuczynski ya jagoranci Peru bayan lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2016. Ya mayar da hankali kan bunƙasa tattalin arziki, inganta harkokin zuba jari da gyaran ababen more rayuwa. Sai dai gwamnatinsa ta fuskanci rikicin siyasa da zarge-zargen da suka shafi cin hanci da rashawa, wanda ya kai ga murabus ɗinsa a watan Maris na 2018.
- Martín Vizcarra (2018–2020)
Martín Vizcarra ya zama shugaban ƙasa bayan murabus ɗin Kuczynski, bisa tsarin maye gurbin shugabanci. Ya mai da hankali kan yaƙi da cin hanci da rashawa da gyaran tsarin shari’a. A lokacin mulkinsa, ya jagoranci matakan yaƙi da annobar COVID-19, amma rikicin siyasa da majalisa ya kai ga tsige shi a watan Nuwamba na 2020.
- Manuel Merino (2020)
Manuel Merino ya zama shugaban ƙasa bayan majalisa ta tsige Martín Vizcarra. Sai dai mulkinsa ya ɗauki kwanaki biyar kacal, daga 10 zuwa 15 ga Nuwamba, 2020. Zanga-zangar jama’a da rikicin siyasa da suka biyo bayan hawansa mulki sun tilasta masa yin murabus.
- Francisco Sagasti (2020–2021)
Francisco Sagasti ya jagoranci gwamnatin riƙon ƙwarya bayan murabus ɗin Merino. Babban aikinsa shi ne dawo da zaman lafiyar siyasa, ƙarfafa hukumomin gwamnati da shirya zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2021. Gwamnatinsa ta kuma kula da fara shirin rigakafin COVID-19.
- Pedro Castillo (2021–2022)
Pedro Castillo malamin makaranta ne kafin shiga siyasa. Ya zama shugaban ƙasa bayan lashe zaɓen shekarar 2021. Ya yi ƙoƙarin mayar da hankali kan ilimi, rage bambancin tattalin arziki da inganta rayuwar mutanen karkara. Sai dai gwamnatinsa ta fuskanci rikice-rikicen siyasa, zarge-zargen cin hanci da rashin jituwa da majalisa. A ranar 7 ga Disamba, 2022, ya yi ƙoƙarin rusa majalisa da kafa gwamnatin gaggawa, amma matakin bai yi nasara ba, aka tsige shi tare da kama shi.
- Dina Boluarte (2022–2025)
Dina Boluarte ta zama shugabar ƙasa bayan tsige Pedro Castillo, bisa tsarin maye gurbin shugabanci. Ita ce mace ta farko da ta riƙe shugabancin Peru. Gwamnatinta ta fuskanci zanga-zanga, matsalolin tsaro, zarge-zargen take haƙƙin ɗan Adam da rikice-rikicen siyasa. A watan Oktoba na 2025, majalisa ta tsige ta bisa dalilan da suka shafi rashin iya gudanar da shugabanci.
- José Jerí (2025–2026)
José Jerí ya zama shugaban ƙasa a ranar 10 ga Oktoba, 2025, bayan tsige Dina Boluarte. Ya karɓi mulki bisa tsarin maye gurbin shugabanci, domin jagorantar gwamnatin wucin gadi har zuwa zaɓen sabon shugaban ƙasa. Ya mayar da hankali kan matsalolin tsaro da yaƙi da laifuffuka, amma ya fuskanci zarge-zargen da suka shafi alaƙar da wasu ‘yan kasuwa da kuma rashin bayyana wasu tarurruka. Majalisa ta cire shi daga shugabancin majalisa a ranar 17 ga Fabrairu, 2026, wanda ya kawo ƙarshen shugabancinsa na ƙasa.
- José María Balcázar (2026)
José María Balcázar ya karɓi shugabancin ƙasa a ranar 18 ga Fabrairu, 2026, bayan cire José Jerí. Ya kasance lauya, tsohon alƙali kuma ɗan majalisar dokoki. Ya jagoranci gwamnatin riƙon ƙwarya har zuwa 28 ga Yuli, 2026. Babban aikinsa shi ne kula da harkokin gwamnati, tabbatar da zaman lafiyar siyasa da shirya miƙa mulki ga sabon shugaban ƙasa bayan zaɓen shekarar 2026.
- Keiko Fujimori (2026–zuwa yanzu)
Keiko Sofía Fujimori Higuchi ita ce shugabar ƙasar Peru ta yanzu. Ta hau karagar mulki a ranar 28 ga Yuli, 2026, bayan lashe zaɓen shugaban ƙasa, domin wa’adin shekarar 2026–2031. Ita ce ‘yar tsohon shugaban ƙasa Alberto Fujimori kuma shugabar jam’iyyar siyasa ta Popular Force (Fuerza Popular). Manufofin da ta bayyana a farkon mulkinta sun haɗa da yaƙi da laifuffuka, inganta tsaro, farfaɗo da tattalin arziki, ƙarfafa ayyukan more rayuwa da shirya ƙasar domin fuskantar illolin sauyin yanayi.
Manazarta
Economic and political overview in Peru. (n.d.).
Peru. (2021, February 10). Geography.
Peru Overview: history, culture, wildlife & cuisine. (n.d.).
98 Most famous Peruvian Politicians | Pantheon. (n.d.).
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.
