Bolivia ƙasa ce mai cin gashin kanta da ke tsakiyar nahiyar kudancin Amurka. Ƙasar tana da iyaka da ƙasashe biyar da suka haɗa da Brazil a arewa da gabas, Paraguay a kudu maso gabas, Argentina a kudu, Chile a kudu maso yamma, da Peru a arewa maso yamma. Bolivia ba ta da gaɓar teku, duk da cewa a tarihi ta taɓa mallakar yankin bakin tekun Pacific kafin ta rasa shi sakamakon yaƙin Pacific a ƙarni na 19.
Babban abin burgewa game da Bolivia shi ne bambancin yanayin ƙasarta, wanda ya haɗa da manyan tsaunukan Andes, babban filin Altiplano, dazuzzukan Amazon da kuma filayen ƙasa masu zafi. Haka kuma, ƙasar tana da albarkatun ƙasa masu yawa, musamman lithium, tin, iskar gas da azurfa.
Bolivia tana da tsarin mulkin jamhuriyya, kuma tana da manyan birane biyu masu muhimmanci ta fuskar mulki, La Paz, cibiyar gudanarwar gwamnati, da Sucre, babban birnin kundin tsarin mulki.
Tarihin kafuwar Bolivia
Tarihin kafuwar Bolivia ya samo asali ne tun kafin zuwan turawan Spain a nahiyar kudancin Amurka. Yankin da a yau ake kira Bolivia ya kasance gida ga wasu tsofaffin al’ummomi da dauloli daban-daban, waɗanda suka bunƙasa manyan hanyoyin cigaba a yankin.
Ɗaya daga cikin fitattun hanyoyin cigaba na farko a yankin ita ce Tiwanaku, wadda ta bunƙasa a yankin da ke kusa da tafkin Titicaca. Masana tarihi sun danganta wannan da gagarumin ci gaban gine-gine, noma, fasahar sarrafa duwatsu da tsarin zamantakewa. Daga baya, al’ummar Inca ta faɗaɗa ikonta zuwa babban ɓangaren yankin Bolivia na yanzu, inda ta haɗa shi cikin babbar daular Inca.
A farkon ƙarni na 16 ne, turawan Spain suka fara mamaye yankunan da ke ƙarƙashin daular Inca. A kusan shekarar 1535, sojojin Spain suka mamaye yankin da daga baya ya zama Bolivia. Daga nan yankin ya shiga ƙarƙashin ikon daular mulkin mallakar Spain. A lokacin mulkin mallaka, ana kiran yankin da sunaye kamar Upper Peru da Charcas.

Daga cikin muhimman abubuwan da suka jawo hankalin turawan Spain zuwa yankin shi ne yawan ma’adinan azurfa. Birnin Potosí ya zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin haƙar azurfa a duniya, musamman bayan gano ma’adinan Cerro Rico a shekarar 1545. Arzikin azurfar yankin ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin daular Spain.
Yayin da mulkin mallakar Spain ke ci gaba kuma, rashin adalci, tilasta wa ƴan asalin ƙasar aiki da nauyin haraji sun haifar da ƙiyayya da turjiya a tsakanin al’umma. A ranar 25 ga watan Mayu, 1809, wani gagarumin yunƙurin tawaye ya faru a birnin Chuquisaca wanda a yau ake kira Sucre. Wannan tawaye yana daga cikin hanyoyin farkon motsin neman ƴancin kai a yankin Latin Amurka.
Haka kuma, a ranar 16 ga Yuli, 1809, an sake samun wani gagarumin yunƙurin juyin juya hali a birnin La Paz, wanda Pedro Domingo Murillo ya kasance cikin manyan jagororinsa. Duk da cewa hukumomin Spain sun murƙushe waɗannan yunƙuri, amma dai sun taimaka wajen ƙarfafa gwagwarmayar samun ƴancin kai.
Gwagwarmayar samun ƴancin kai kuma ta ɗauki kusan shekaru 16, inda aka yi yaƙe-yaƙe da dama tsakanin sojojin Spain da masu neman ƴancin kai. A shekarar 1824, sojojin masu neman ƴancin kai ƙarƙashin jagorancin Antonio José de Sucre sun taka muhimmiyar rawa wajen karya ƙarfin sojojin Spain a Yaƙin Ayacucho na ƙasar Peru. Bayan wannan nasara, gwagwarmayar samun ƴancin kai a Upper Peru ta samu sabon ƙarfi. A ranar 9 ga Fabrairu, 1825, Sucre ya bayar da umarnin gudanar da babban taron wakilan yankin domin yanke shawarar makomar siyasar Upper Peru. Bayan shafe shekaru ana gwagwarmaya, a ranar 6 ga Agusta, 1825, wakilan yankin Upper Peru suka ayyana kafa sabuwar ƙasa mai cin gashin kanta.
A lokacin taron, an tattauna hanyoyi daban-daban na makomar yankin, ciki har da haɗewa da Argentina, komawa ƙarƙashin Peru ko kafa ƙasa mai zaman kanta. A ƙarshe, wakilan suka zaɓi kafa ƙasa mai cin gashin kanta, wadda aka sanya wa suna Bolivia, domin girmama fitaccen jagoran gwagwarmayar ƴancin kai na kudancin Amurka, Simón Bolívar.
Sabuwar ƙasar ta fara rayuwa a matsayin jamhuriya mai cin gashin kanta, yayin da Antonio José de Sucre ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa hukumomin gwamnati na farko.
A shekarar 1826, an amince da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar, wanda Simón Bolívar ya taimaka wajen tsara shi.
Yanayin ƙasa da muhalli
Kamar yadda ya gabata, ƙasar Bolivia tana tsakiyar nahiyar kudancin Amurka, inda take da faɗin fili kimanin murabba’in kilomita 1,098,581. Tana daga cikin manyan ƙasashen nahiyar ta fuskar faɗin ƙasa. Sannan ta ƙara samun matsayi na musamman a nahiyar kasantuwar tana da yankuna masu tsaunuka, manyan filaye masu tudu, sai dazuzzukan da suke yawan samun ruwan sama da kuma filayen ƙasa masu faɗi.
Bolivia ƙasa ce da ba ta da mashigar ruwa zuwa teku wato Landlocked Country. Wannan na nufin cewa ba ta da iyakar bakin teku da kowace teku ko babban ruwan teku. Tana da iyaka da ƙasashe biyar da suka hada da Brazil a arewa da gabas, Paraguay a kudu maso gabas, Argentina a kudu, Chile a kudu maso yamma, da Peru a arewa maso yamma.
Har ila yau, yanayin ƙasar Bolivia ya kasu zuwa manyan yankuna uku, waɗanda suka bambanta sosai ta fuskar tsawo, yanayin ƙasa da kuma tsarin halittu, daga ciki akwai:
Yankin tsaunukan Andes (Andean Region)
Wannan yanki yana yammacin ƙasar, inda manyan tsaunukan Andes suka ratsa ta cikinsa. Yankin ya ƙunshi manyan tsaunuka, kwarurruka da kuma babban filin tudu da ake kira Altiplano.
Altiplano wani babban fili ne da yake tsakanin jerin tsaunukan Andes guda biyu. Yana da tsawo sosai, inda wasu sassan sa suka kai kusan mita 3,800 zuwa 4,000. Yanayinsa yakan kasance mai sanyi da bushewa, musamman a wasu lokutan shekara.
A wannan yanki ne kuma ake samun wani ɓangare na tafkin Titicaca, wanda Bolivia ke tarayya da Peru. Tafkin yana daga cikin manyan tafkunan da ke yankin Andes, kuma yana taka muhimmiyar rawa ga rayuwar al’ummomin da ke kewaye da shi.
Yankin tsaunukan ƙasa da kwaruruka (Sub-Andean Region)
Wannan yanki yana tsakanin manyan tsaunukan Andes da filayen ƙasa na gabashin Bolivia. Ya ƙunshi kwarurruka, tsaunuka masu matsakaicin tsawo da kuma yankin Yungas, wanda ya shahara da dazuzzukan da ke da ɗimbin ciyayi.
Yankin Yungas yana da yanayi mai ɗumi da danshi, saboda haka yana taka muhimmiyar rawa wajen noma. Ana noma kayayyaki daban-daban kamar kofi, ƴaƴan itatuwa da sauran amfanin gona.
Yankin filayen ƙasa
Wannan yanki ya mamaye babban ɓangaren gabashi da arewacin Bolivia. Ya ƙunshi filayen dazuzzukan Amazon, filaye masu ciyayi da suke da faɗi da kuma yankunan Chaco a kudu maso gabashin ƙasar.
Yankin Amazon yana da yawan ruwan sama, dazuzzuka masu yawa da nau’o’in halittu daban-daban. A gefe guda kuma, yankin Chaco yana da yanayi mai zafi da bushewa, musamman a wasu lokutan shekara.
Ta wani ɓangare kuma, Bolivia tana daga cikin yankuna masu manyan tsaunuka a kudancin Amurka. Mafi tsayin dutse a ƙasar shi ne Nevado Sajama, wanda tsayinsa ya kai kimanin mita 6,542. Wannan dutse yana cikin yankin Oruro, kusa da iyakar Chile.
Sauran fitattun tsaunukan sun haɗa da Illimani, Illampu da Huayna Potosí. Waɗannan tsaunuka suna cikin jerin tsaunukan Andes, kuma wasu daga cikinsu suna da dusar ƙanƙara a samansu saboda tsananin sanyi da tsayinsu.
Har ila yau, Bolivia tana da manyan tafkuna da koguna waɗanda suke taka rawa wajen samar da ruwa, noma, sufuri da kuma rayuwar halittu.
Daga cikin mafi shahara akwai Lake Titicaca, wanda yake kan iyakar Bolivia da Peru. Yana daga cikin manyan tafkunan da ke yankin Andes, kuma ana ɗaukarsa a matsayin tafki mafi girma a Kudancin Amurka ta fuskar yawan ruwan da yake ɗauke da shi.
Akwai kuma tafkin Poopó, wanda yake a yankin Altiplano. Sai dai wannan tafki yana fuskantar matsalolin raguwar ruwa da bushewa sakamakon sauyin yanayi da sauran matsalolin muhalli.
Manyan kogunan ƙasar sun haɗa da Mamoré, Beni, Madre de Dios da Pilcomayo. Wasu daga cikin waɗannan koguna suna cikin tsarin kogunan Amazon, yayin da wasu suke cikin tsarin kogin La Plata.
Ta fuskar yanayi kuma, Bolivia tana da yanayin sararin samaniya iri-iri saboda bambancin tsayin wurarenta. Duk da cewa tana cikin yankin da ke da wurare masu zafi, sai dai ba dukkan ƙasar ce take da zafi iri ɗaya ba.
A yankunan tsaunukan Andes da Altiplano, yanayi yakan kasance mai sanyi, kuma wasu wurare suna fuskantar tsananin sanyi da dusar ƙanƙara. A yankunan kwaruruka kuwa, yanayi yakan kasance mai ɗumi, yayin da yankunan gabas da Amazon ke da yanayin zafi da danshi.
A yankin Chaco kuwa, yanayi yakan kasance mai zafi da ƙarancin ruwan sama idan aka kwatanta da dazuzzukan Amazon. Wannan bambancin yanayi yana da alaƙa da tsayin ƙasa, yanayin tsaunuka, iskar da ke shigowa daga yankunan zafi da kuma tasirin ruwan sama.
Al’umma da harshe
Bolivia tana daga cikin ƙasashen Kudancin Amurka da suka shahara da bambancin al’ummomi, harsuna da al’adun gargajiya. Al’ummar ƙasar ta ƙunshi mutane masu asali daban-daban, waɗanda suka haɗa da ƴan asalin nahiyar Kudancin Amurka, mutanen da ke da gaurayen asalin turawa da ƴan asalin nahiyar, da kuma al’ummomin da zuriyarsu ta samo asali daga Afirka da Turai.
Al’ummomi
Babban ɓangare na tarihin zamantakewar Bolivia yana da alaƙa da al’ummomin waɗanda suka zauna a yankin tun kafin zuwan Turawan Spain. Waɗannan al’ummomi suna da nasu harsuna, al’adu, tsarin shugabanci, hanyoyin noma da kuma tsarin rayuwa.
Daga cikin manyan al’ummomin asalin Bolivia akwai Quechua da Aymara. Al’ummar Quechua tana da alaƙa da aInca, wadda ta taɓa mamaye manyan yankuna na tsaunukan Andes. Harshen Quechua ya bazu a ƙasashe da dama na Kudancin Amurka, musamman Peru, Bolivia da Ecuador.
Aymara kuwa wata babbar al’umma ce da tarihinta ya daɗe a yankin tsaunukan Andes da kewayen tafkin Titicaca. Wannan al’umma tana da nata harshe da al’adun gargajiya, waɗanda suka ci gaba da kasancewa wani muhimmin ɓangare na rayuwar Bolivia har zuwa yau.
Haka kuma, akwai al’ummar Guaraní, musamman a gabashi da kudu maso gabashin ƙasar. Suna da nasu harshe da al’adun gargajiya, kuma suna daga cikin al’ummomin asali da kundin tsarin mulkin Bolivia ya amince da su.
Baya ga waɗannan, akwai wasu al’ummomin asali da dama, waɗanda suka haɗa da Chiquitano, Mojeño, Uru, Weenhayek da sauran ƙananan al’ummomi.
Haka kuma, Bolivia tana da al’ummar Afro-Bolivian, wato mutanen da zuriyarsu ta samo asali daga Afirka. Tarihinsu yana da alaƙa da cinikin bayi da Turawan mulkin mallaka suka yi a nahiyar Kudancin Amurka. Wasu daga cikin zuriyarsu sun zauna a yankin Yungas, inda suke ci gaba da kiyaye wasu al’adun Afirka, musamman ta fuskar kiɗa da rawa.
Harsuna
Bolivia tana daga cikin ƙasashen da ke da yawan harsunan hukuma. Kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 2009 ya amince da harshen Spanish tare da harsunan al’ummomin asalin ƙasar a matsayin harsunan hukuma. Akwai harsunan asali guda 36 da kundin tsarin mulkin ƙasar ya amince da su, wanda hakan ya sa jimillar harsunan hukuma suka kai 37.
Harshen Spanish shi ne harshen da ya fi yaɗuwa a harkokin gwamnati, ilimi, kasuwanci da sadarwa a tsakanin al’ummomi daban-daban. Daga cikin manyan harsunan asali akwai Quechua, wanda miliyoyin mutane ke magana da shi a Bolivia da wasu ƙasashen makwabta. Harshe ne mai dogon tarihi, wanda ya taka muhimmiyar rawa a zamanin daular Inca.
Harshen Aymara ma yana daga cikin manyan harsunan ƙasar. Ana amfani da shi musamman a yankunan tsaunukan Andes, ciki har da sassan La Paz da kewayen tafkin Titicaca. Harshen Guaraní kuwa ya fi samun masu magana da shi a gabashi da kudu maso gabashin Bolivia. Yana taka rawa wajen adana tarihin al’ummar Guaraní da al’adunsu.
Sauran harsunan hukuma sun haɗa da Bésiro, Araona, Baure, Canichana, Cavineño, Chácobo, Chimán, Ese Ejja, Guarayu, Itonama, Leco, Maropa, Mosetén, Movima, Pacawara, Sirionó, Tacana, Tapiete, Toromona, Uru-Chipaya da Yuracaré, da sauransu.
Duk da amincewar waɗannan harsuna a matsayin na hukuma, ba dukkansu ne suke da yawan masu magana ba. Wasu daga cikinsu suna fuskantar barazanar bacewa saboda ƙarancin masu amfani da su, musamman matasa.
Addini da al’adu
Bolivia tana daga cikin ƙasashen Kudancin Amurka da ke da al’adu masu zurfin tarihi, waɗanda suka samo asali daga tsofaffin al’ummomin yankin. Rayuwar al’ummar ƙasar tana da alaƙa da al’adun gargajiya, bukukuwan addini, kiɗa, rawa, tufafi da sauran hanyoyin gudanar da rayuwar yau da kullum.
Addinai
Addinin Kiristanci shi ne addinin da ya fi yawan mabiya a Bolivia, musamman Cocin Katolika na Roman. Wannan addini ya samu gagarumin tasiri a ƙasar tun lokacin mulkin mallakar Spain, lokacin da mishanoni suka yaɗa koyarwar Kiristanci a tsakanin al’ummomin yankin.
A halin yanzu, akwai kuma mabiya ƙungiyoyin Furotesta, waɗanda suka haɗa da Evangelical, Pentecostal da Seventh-day Adventist. Waɗannan ƙungiyoyin sun samu karɓuwa a sassa daban-daban na ƙasar.
Baya ga Kiristanci, wasu al’ummomin asali suna ci gaba da bin tsofaffin al’adun ruhaniya da suka gada daga kakanninsu. Wasu daga cikinsu suna haɗa wasu al’adun gargajiyarsu da koyarwar Kiristanci, wannan ne ya haifar da wani salo na musamman na gudanar da bukukuwa da ibadodi.
Haka kuma, akwai ƙananan al’ummomin mabiya addinin Musulunci, Yahudanci da sauran addinai a ƙasar. Duk da ƙarancin yawansu idan aka kwatanta da mabiya Kiristanci, suna cikin al’ummomin da ke da ƴancin gudanar da addininsu.
Al’adu
Al’adun Bolivia sun ƙunshi haɗakar tsofaffin al’adun yankin Andes, al’adun da suka shigo daga Spain da kuma tasirin wasu al’ummomin da suka zauna a ƙasar a tsawon tarihi.
A wasu yankunan ƙasar, ana ci gaba da kiyaye tsofaffin al’adun da suka shafi girmama kakanni, yanayi da albarkatun ƙasa. Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ke cikin tunanin ruhaniya na wasu al’ummomin Andes shi ne Pachamama, wadda ke wakiltar Uwar Ƙasa wato Mother Earth. A al’adunsu, ana kallon ƙasa a matsayin tushen rayuwa, abinci da sauran albarkatun da ɗan Adam yake dogaro da su.
Wasu al’ummomi suna gudanar da bukukuwa da ibadodi na gargajiya domin nuna godiya ga ƙasa da neman albarka ga noma da sauran harkokin rayuwa. Waɗannan al’adu suna nuna irin alaƙar da ke tsakanin al’ummomin asali da muhalli.
Ɗaya daga cikin fitattun bukukuwan ƙasar shi ne Carnival of Oruro, wanda ake gudanarwa a birnin Oruro. Wannan biki ya shahara saboda manyan jerin masu rawa, kayan ado masu launuka daban-daban, kiɗa da kuma wasan kwaikwayon gargajiya. Daga cikin fitattun abubuwan da ake gabatarwa a lokacin bikin shi ne rawa mai suna Diablada, wadda masu rawa ke sanya manyan abin rufe fuska masu siffar shaidanu da tufafi na musamman. Wannan rawa tana da alaƙa da labaran addini da al’adun yankin Andes.
Wani bikin mai muhimmanci kuma shi ne Alasita Festival, wanda ake gudanarwa musamman a birnin La Paz. A wannan biki, mutane suna sayen ƙananan samfuran abubuwa kamar gidaje, motoci, kuɗi da takardun shaida. Waɗannan ƙananan abubuwa suna wakiltar buƙatu da burin da mutane suke fatan cimmawa a rayuwarsu. Bikin yana da alaƙa da al’adar Ekeko, wani mutum-mutumi da ke wakiltar wadata da yalwa a al’adun yankin.

Haka kuma, akwai Gran Poder Festival, wanda ake gudanarwa a La Paz. Wannan biki ya ƙunshi jerin masu rawa da mawaka, inda ake haɗa al’adun gargajiya da bukukuwan addinin Kiristanci.
Kiɗa da rawa
Kiɗa da rawa suna daga cikin muhimman ginshiƙan al’adun Bolivia. Ƙasar tana da nau’o’in kiɗa da rawa da suka samo asali daga tsofaffin al’ummomin Andes da kuma tasirin al’adun Turawa da Afirka.
Ɗaya daga cikin fitattun kayan kiɗan gargajiya shi ne Pan Flute, wanda ake kira Siku ko Zampoña. Wannan kayan kiɗa yana ƙunshe da bututun sarewa masu tsayi daban-daban, waɗanda ake busawa domin samar da sautuka masu daɗin ji. Haka kuma, ana amfani da kayan kiɗa irin su Charango, wani ƙaramin kayan kiɗa mai kama da guitar, da kuma Quena, wadda take daga cikin tsoffin kayan busa na yankin Andes.
A fannin rawa, Bolivia tana da shahararrun raye-raye irin su Diablada, Morenada da Caporales. Waɗannan raye-raye suna da nasu tarihin, kayan sawa da salon gabatarwa.
Abinci
Abincin gargajiya na Bolivia ya samo asali ne daga haɗakar amfanin gona na yankin Andes da kuma tasirin al’adun Spain.
Daga cikin muhimman kayan abincin ƙasar akwai dankali, masara, quinoa da wake. Waɗannan kayan abinci sun daɗe suna taka muhimmiyar rawa a rayuwar al’ummomin yankin, tun kafin zuwan Turawan Spain. Ɗaya daga cikin shahararrun abincin ƙasar shi ne Salteñas, wani irin cake ne da ake cika cikinsa da nama, kayan lambu da miya mai kauri. Ana cin sa musamman a matsayin abincin safe ko na tsakar rana.
Akwai kuma Silpancho, abinci ne da ya shahara a yankin Cochabamba, wanda ake haɗawa da shinkafa, dankali, nama da soyayyen ƙwai. Haka kuma, Anticuchos na daga cikin abincin da ake sayarwa a tituna. Ana yin sa da guntayen nama da ake tsirawa a sanduna sannan a gasa su.
Tufafin gargajiya
Tufafin gargajiya na Bolivia suna bambanta daga yanki zuwa wani, musamman tsakanin yankunan tsaunukan Andes da filayen gabashin ƙasar.
A yankunan Andes, wasu mata suna sanya tufafin gargajiya da ake kira Pollera, wanda yake kama da dogon siket mai yalwa. Sau da yawa ana haɗa shi da riguna, mayafi da kuma huluna na musamman.
Wasu matan Aymara da Quechua suna sanya hulunan gargajiya da aka fi sani da Bowler Hats, waɗanda suka zama sanannen ɓangare na suturar wasu al’ummomin yankin. Maza kuwa a wasu yankuna suna sanya tufafin ulu masu kauri domin kare jikinsu daga sanyin tsaunuka.
Tsarin mulki
Bolivia tana da tsarin mulkin dimokuraɗiyya, inda ikon gudanar da harkokin ƙasa yake bisa kundin tsarin mulki da dokokin ƙasar. Sunan hukuma na ƙasar shi ne Plurinational State of Bolivia. Wannan suna yana nuna amincewar ƙasar da kasancewar al’ummomi, ƙabilu, harsuna da al’adu daban-daban a ƙarƙashin ƙasa guda.
Bolivia tana amfani da tsarin jamhuriya mai ikon cin gashin kanta, inda al’umma take da ikon zaɓen shugabanninta ta hanyar zaɓe. Kundin tsarin mulkin ƙasar na yanzu ya fara aiki a ranar 7 ga Fabrairu, 2009, bayan amincewa da shi ta hanyar ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a a ranar 25 ga Janairu, 2009.
Ɗaya daga cikin siffofin tsarin mulkin Bolivia shi ne raba ikon gwamnati zuwa manyan sassa huɗu, waɗanda suka haɗa da bangaren zartarwa, majalisa, shari’a da kuma hukumar zaɓe. Kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadi cewa waɗannan hukumomi su kasance masu cin gashin kansu a aikinsu, tare da haɗin kai da juna wajen gudanar da ayyukan ƙasa.
Inda ɓangaren zartarwa shi ne ke da alhakin gudanar da harkokin gwamnatin ƙasa da aiwatar da dokoki da manufofin gwamnati. Shugaban ƙasa ne yake jagorantar wannan bangare, tare da mataimakinsa da ministocin gwamnati.
Ana zaɓen shugaban ƙasa da mataimakinsa ta hanyar zaɓen gama-gari na ƴan ƙasa. Shugaban ƙasa shi ne shugaban ƙasa kuma shugaban gwamnati, yayin da ministoci suke kula da ma’aikatun gwamnati daban-daban kamar harkokin waje, tsaro, kuɗi, ilimi da lafiya. Kundin tsarin mulkin ya tanadi wa’adin mulkin shugaban ƙasa na shekaru biyar, tare da damar sake tsayawa takara bisa ƙa’idojin kundin tsarin mulki da fassarar kotuna.
Bangaren majalisa kuma yana da alhakin ƙirƙira, tattaunawa, gyarawa da amincewa da dokokin da za su jagoranci ƙasar. Ana gudanar da wannan aiki ne ta wata hukuma mai suna Plurinational Legislative Assembly. Majalisar tana da ɓangarori biyu wato Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa.
Majalisar Wakilai a Bolivia tana da kujeru 130, yayin da Majalisar Dattawa take da kujeru 36. Wakilan majalisar suna wakiltar al’ummomi da yankuna daban-daban na ƙasar, kuma suna taka muhimmiyar rawa wajen tsara dokoki, amincewa da kasafin kuɗin gwamnati da kuma sa ido kan ayyukan bangaren zartarwa.
Bangaren shari’a yana da alhakin tabbatar da bin doka da oda, warware rikice-rikice da kare haƙƙin jama’a bisa tanadin kundin tsarin mulki.
Ɗaya daga cikin manyan hukumomin wannan bangare ita ce Supreme Tribunal of Justice, wadda ita ce babbar kotun shari’a ta ƙasa. Akwai kuma Plurinational Constitutional Court, wadda take da alhakin fassara kundin tsarin mulki da tabbatar da cewa dokoki da ayyukan hukumomin gwamnati sun yi daidai da shi.
Wani abin ban sha’awa a tsarin shari’ar Bolivia shi ne amincewar kundin tsarin mulki da tsarin shari’ar gargajiya na al’ummomin asali. Wannan yana ba wasu al’ummomin asali damar warware wasu rikice-rikicen da suka shafi rayuwarsu ta hanyar dokoki da al’adunsu, muddin hakan bai saɓa wa kundin tsarin mulki da dokokin ƙasa ba.
Tattalin arziki
Kamar yadda ya gabata, Bolivia tana daga cikin ƙasashen Kudancin Amurka da suka shahara wajen samar da ma’adinai, makamashi da kuma noma, daga cikin arzikin ƙasar akwai:
Haƙar ma’adinai na daga cikin tsofaffin ginshiƙan tattalin arzikin Bolivia. Ɗaya daga cikin wuraren da suka shahara wajen samar da ma’adinai shi ne birnin Potosí, wanda ya zama cibiyar haƙar azurfa tun ƙarni na 16.
Dutsen Cerro Rico, wanda yake a Potosí, ya shahara a tarihin tattalin arzikin duniya saboda yawan azurfar da ake haƙa daga cikinsa. A lokacin mulkin mallakar Spain, azurfar yankin ta kasance ɗaya daga cikin manyan hanyoyin samun arzikin daular Spain.
A zamanin yanzu, Bolivia tana ci gaba da samar da ma’adinai daban-daban. Daga cikin waɗanda suka fi shahara akwai azurfa, tin, zinc, zinariya, gubar ƙarfe da tungsten. Binciken yanayin ƙasa na Amurka a shekarar 2024, ya bayyana Bolivia na daga cikin manyan ƙasashen duniya wajen samar da azurfa, tin, zinc da wasu ma’adinai.
Sannan daga cikin albarkatun ƙasa da suka jawo hankalin duniya zuwa Bolivia shi ne Lithium. Wannan wani sinadari ne da ake amfani da shi wajen ƙera batirorin da ake amfani da su a wayoyin hannu, kwamfutoci, motocin lantarki da wasu na’urorin adana makamashi.
Bolivia tana da manyan albarkatun lithium a yankin Salar de Uyuni, wanda yake cikin sashen Potosí. Wannan yanki yana ɗauke da tarin ruwan gishiri a ƙarƙashin saman filin gishirin, wanda ke ƙunshe da lithium.
Har ila yau, Iskar gas na daga cikin muhimman kayayyakin da Bolivia ke samarwa da fitarwa zuwa ƙasashen waje. A shekarun baya, ƙasar ta samu kuɗaɗen shiga masu yawa daga sayar da iskar gas ga ƙasashe kamar Brazil da Argentina.
Haka kuma, Bolivia tana da matatun sarrafa man fetur da wasu cibiyoyin makamashi da ke taimakawa wajen biyan buƙatun cikin gida, duk da samar da iskar gas ɗin ya ragu a shekarun baya sakamakon raguwar yawan rijiyoyin da ke samar da iskar gas da kuma ƙarancin sabon bincike da zuba jari a wannan ɓangare.
Noma na daga cikin muhimman hanyoyin samun abinci da kuɗin shiga a Bolivia. Ƙasar tana da manyan filayen noma, musamman a gabashi da yankunan da ke da yanayin zafi da danshi.
Waken soya na daga cikin muhimman kayayyakin da Bolivia take fitarwa zuwa kasuwannin ƙasashen waje. Ana kuma noma Brazil nuts, waɗanda ake samu daga bishiyoyin dazuzzukan Amazon, tare da wasu ƴaƴan itatuwa da kayan amfanin gona.
A ɓangaren kiwo kuwa, ana kiwon shanu, tumaki, awaki da sauran dabbobi. Ana samun manyan wuraren kiwon shanu musamman a yankunan gabashin ƙasar. Haka kuma, naman shanu na daga cikin kayayyakin da Bolivia take fitarwa zuwa wasu ƙasashe.
Ta ɓangaren masana’antu ma suna taka rawa wajen sarrafa albarkatun ƙasa da amfanin gonar Bolivia. Daga cikin masana’antun da ake da su akwai sarrafa abinci, sarrafa ma’adinai, ƙera kayayyakin masaƙu, siminti, kayayyakin ƙarfe da sarrafa man fetur.
Matsayin Bolivia a duniya
Ƙasar Bolivia tana da daraja a idon duniya ta fuskoki daban-daban da suka haɗa da:
Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka sanya Bolivia ta shahara a duniya shi ne yawan albarkatun Lithium da take da su. A cewar rahoton Asusun ba da lamuni na duniya (IMF) na shekarar 2025, Bolivia tana da kusan kashi 22 cikin 100 na albarkatun Lithium da aka gano a duniya. Wannan ya sanya ta cikin ƙasashen da za su iya taka muhimmiyar rawa wajen samar da wannan ma’adini a nan gaba.
Kamar yadda ya gabata, Bolivia tana daga cikin ƙasashen da ke da albarkatun ma’adinai da suka haɗa da azurfa, tin, zinc, zinariya, gubar ƙarfe da tungsten.
A cewar hukumar binciken ƙasa ta Amurka (USGS), a shekarar 2024 Bolivia ta kasance ƙasa ta huɗu a duniya wajen samar da azurfa, sannan ta kasance cikin manyan ƙasashen da ke samar da tin da zinc.
Waɗannan albarkatu suna taimaka wa tattalin arzikinta tare da samar da kayayyakin da masana’antun duniya ke buƙata.

Bolivia tana da albarkatun iskar gas da man fetur. Musamman iskar gas, wadda ta kasance ɗaya daga cikin manyan kayayyakin da ƙasar ke fitarwa zuwa kasuwannin ƙasashen waje.
Kasashen Kudancin Amurka, musamman Brazil da Argentina, sun kasance cikin manyan abokan hulɗarta ta fuskar cinikayyar makamashi.
Yayin da ƙasashe da dama ke ƙoƙarin rage amfani da makamashin da ke gurɓata muhalli, ana ƙara maida hankali kan motocin lantarki da makamashi mai tsafta.
A wannan fanni, Bolivia tana da muhimmanci saboda albarkatun Lithium da take da su. Wannan ma’adini yana da amfani wajen samar da batirorin da ake amfani da su wajen adana makamashi.
Bolivia tana da filayen noma masu albarka da yanayin ƙasa daban-daban da ke ba ta damar noman amfanin gona iri-iri. Daga cikin kayayyakin da take samarwa akwai waken soya, ƙwayar Brazil nut, nama da sauran kayan amfanin gona. Waɗannan kayayyaki suna shiga kasuwannin ƙasashen duniya, musamman a nahiyoyin Amurka, Turai da Asiya.
Bolivia tana da dazuzzukan wurare masu zafi, dazuzzukan busassun yankuna, koguna, tsaunuka da sauran wuraren da ke ɗauke da nau’ikan halittu masu yawa.
Wasu daga cikin yankunanta suna cikin tsarin muhallin Amazon, wanda yake da matuƙar muhimmanci wajen daidaita yanayin duniya da kuma kiyaye nau’ikan halittu. Saboda haka, Bolivia tana da rawar da za ta iya takawa wajen kare gandun daji, namun daji da albarkatun muhalli.
Duk da rashin samun damar shiga teku kai tsaye, Bolivia tana da iyaka da ƙasashe biyar: Brazil, Peru, Chile, Argentina da Paraguay. Wannan matsayi yana ba ta damar hulɗar kasuwanci da sauran ƙasashen Kudancin Amurka. Bayanan Hukumar Ciniki ta Duniya (WTO) sun nuna cewa China da Brazil suna daga cikin manyan kasuwannin da Bolivia ke fitar da kayayyaki zuwa gare su.
Bolivia tana da wuraren yawon buɗe ido da suka shahara a duniya, musamman Salar de Uyuni, wanda shi ne mafi girman fili mai gishiri a duniya. Wannan wuri yana jan hankalin masu yawon buɗe ido daga ƙasashe daban-daban saboda kyawun yanayinsa da irin hotunan da ake iya ɗauka a cikinsa. Haka kuma, tsoffin wuraren tarihi, al’adun mutanen ƙasar da tsaunukan Andes suna ƙara mata daraja a fannin yawon buɗe ido.
Matsaloli da ƙalubale
Ƙasar Bolivia tana fuskantar matsaloli da ƙalubale daban-daban waɗanda ke shafar ci gabanta a fannonin tattalin arziki, siyasa, zamantakewa, tsaro, muhalli da bunƙasa rayuwar al’ummarta.
Duk da cewa ƙasar tana da albarkatun ƙasa masu yawa, musamman Lithium, azurfa, zinariya, tin da iskar gas, akwai matsalolin da ke hana ta amfani da waɗannan albarkatu yadda ya kamata domin samun ci gaba mai ɗorewa. Manyan matsaloli da ƙalubalen da Bolivia ke fuskanta sun haɗa da:
Matsalolin tattalin arziki
Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen Bolivia shi ne tabarbarewar wasu sassa na tattalin arzikinta. Ƙasar tana fuskantar ƙarancin kuɗaɗen shiga daga ƙasashen waje, raguwar samar da iskar gas, hauhawar farashin kayayyaki da kuma ƙarancin kuɗaɗen ajiyar ƙasa.
Wannan matsala tana shafar harkokin kasuwanci, masana’antu da rayuwar jama’a. Rahoton Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) na shekarar 2025 ya bayyana cewa tattalin arzikin ƙasar yana fuskantar matsin lamba sakamakon raguwar kuɗaɗen shiga da kuma ƙarancin ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje.
Rashin aikin yi da talauci
Bolivia tana fuskantar ƙalubalen samar da isassun ayyukan yi ga al’ummarta, musamman matasa da mutanen da ke zaune a yankunan karkara.
Wasu daga cikin ma’aikata suna gudanar da ƙananan sana’o’i ba tare da cikakkiyar kariyar ma’aikata ko tabbataccen albashi ba. Haka kuma, akwai bambanci tsakanin yanayin rayuwar mutanen birane da na ƙauyuka. Talauci da ƙarancin samun muhimman abubuwan more rayuwa suna ci gaba da zama matsaloli a wasu yankunan ƙasar.
Rikicin siyasa
Bolivia ta sha fuskantar rikice-rikicen siyasa da rashin jituwa tsakanin jam’iyyun siyasa da wasu ƙungiyoyin al’umma. Rashin fahimtar juna tsakanin ƴan siyasa kan wasu muhimman manufofi ya sha kawo tsaiko wajen amincewa da dokoki da shirye-shiryen gwamnati. Haka kuma, zanga-zanga da toshe hanyoyi a wasu lokuta suna kawo cikas ga harkokin sufuri, kasuwanci da gudanar da ayyukan yau da kullum.
Ƙarancin man fetur da kuɗaɗen ƙasashen waje
A shekarun baya-bayan nan, Bolivia ta fuskanci ƙarancin man fetur, musamman fetur da dizal, wanda ya shafi harkokin sufuri da kasuwanci.
Haka kuma, ƙarancin dalar Amurka a kasuwannin cikin gida ya jawo matsaloli wajen shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje. Wannan ya ƙara tsadar wasu kayayyaki tare da haifar da matsin lamba ga ƴan kasuwa da masu amfani da kayayyaki.
Matsalolin muhalli da sauyin yanayi
Bolivia tana fuskantar matsalolin da suka shafi muhalli da suka haɗa da fari, ambaliyar ruwa, gobarar daji da zaizayar ƙasa. Musamman gobarar daji tana zama barazana ga dazuzzukan ƙasar da namun daji da ke rayuwa a cikinsu. Sauyin yanayi yana kuma shafar noma da samar da abinci, domin wasu yankuna suna fuskantar ƙarancin ruwan sama yayin da wasu ke fama da ambaliyar ruwa. Wannan matsala tana ƙara wahalar rayuwa ga manoma da mutanen da suka dogara da albarkatun ƙasa.
Sufuri da rashin hanyar shiga teku
Bolivia ƙasa ce da ba ta da bakin teku, domin tana kewaye da sauran ƙasashe. Wannan yanayi yana haifar da ƙarin ƙalubale wajen jigilar kayayyaki zuwa kasuwannin duniya. Duk da cewa tana amfani da hanyoyin sufuri ta ƙasashen da ke makwabtaka da ita, jigilar kayayyaki zuwa tashoshin jiragen ruwa na iya ƙara kuɗin sufuri da tsawon lokacin da ake buƙata wajen gudanar da cinikayya. Daga cikin wasu ƙalubalen kuma akwai ta fannin lafiya da ilimi, inda wasu yankuna na karkara da tsaunuka basa samun su yadda ya kamata.
Har ila yau a cikin matsalolin akwai ƙarancin fasahar sarrafa lithium, domin yana buƙatar jari mai yawa, matsalolin yarjejeniyoyin zuba jari da kuma muhawara kan yadda za a gudanar da albarkatun. Haka kuma, aikin haƙar Lithium yana shafar muhalli da kuma ruwan da al’ummomin yankunan da ake haƙar ma’adinin suke amfani da shi.
Jerin shugabannin Bolivia tun daga farko
Tun bayan samun ƴancin kai a ranar 6 ga Agusta, 1825, ƙasar Bolivia ta samu shugabanni da dama. Inda a tsawon tarihinta, ta sha fama da sauye-sauyen shugabanci, juyin mulkin soja, rikice-rikicen siyasa da kuma sauyin gwamnatoci.
Shugabannin ƙasar sun haɗa da waɗanda aka zaɓa ta hanyar zaɓe, waɗanda suka hau mulki ta hanyar maye gurbin shugaba, da kuma waɗanda suka jagoranci gwamnatin rikon kwarya. Ga jerin shugabannin bisa tsarin tarihi:
1. Shugabannin Bolivia daga 1825 zuwa 1899
1. Simón Bolívar (1825)
2. Antonio José de Sucre (1825–1828)
3. José María Pérez de Urdininea (1828)
4. José Miguel de Velasco (1828–1841, ya koma mulki a wasu lokuta)
5. Pedro Blanco Soto (1828–1829)
6. Andrés de Santa Cruz (1829–1839)
7. Sebastián Ágreda (1841)
8. Mariano Enrique Calvo (1841)
9. José Ballivián (1841–1847)
10. Eusebio Guilarte (1847–1848)
11. Manuel Isidoro Belzu (1848–1855)
12. Jorge Córdova (1855–1857)
13. José María Linares (1857–1861)
14. José María Achá (1861–1864)
15. Mariano Melgarejo (1864–1871)
16. Agustín Morales (1871–1872)
17. Tomás Frías (1872–1873; 1874–1876)
18. Adolfo Ballivián (1873–1874)
19. Hilarión Daza (1876–1879)
20. Narciso Campero (1880–1884)
21. Gregorio Pacheco (1884–1888)
22. Aniceto Arce (1888–1892)
23. Mariano Baptista (1892–1896)
24. Severo Fernández Alonso (1896–1899)
25. José Manuel Pando (1899–1904)
2. Shugabannin Bolivia daga 1900 zuwa 1999
26. Ismael Montes (1904–1909; 1913–1917)
27. Eliodoro Villazón (1909–1913)
28. José Gutiérrez Guerra (1917–1920)
29. Bautista Saavedra (1920–1925)
30. Felipe Segundo Guzmán (1925–1926)
31. Hernando Siles Reyes (1926–1930)
32. Carlos Blanco Galindo (1930–1931)
33. Daniel Salamanca (1931–1934)
34. José Luis Tejada Sorzano (1934–1936)
35. David Toro (1936–1937)
36. Germán Busch (1937–1939)
37. Carlos Quintanilla (1939–1940)
38. Enrique Peñaranda (1940–1943)
39. Gualberto Villarroel (1943–1946)
40. Néstor Guillén (1946)
41. Tomás Monje (1946–1947)
42. Enrique Hertzog (1947–1949)
43. Mamerto Urriolagoitia (1949–1951)
44. Hugo Ballivián (1951–1952)
45. Víctor Paz Estenssoro (1952–1956; 1960–1964; 1964; 1985–1989)
46. Hernán Siles Zuazo (1956–1960; 1982–1985)
47. René Barrientos (1964–1969)
48. Luis Adolfo Siles Salinas (1969)
49. Alfredo Ovando Candía (1969–1970)
50. Juan José Torres (1970–1971)
51. Hugo Banzer Suárez (1971–1978; 1997–2001)
52. Juan Pereda (1978)
53. David Padilla (1978–1979)
54. Wálter Guevara (1979)
55. Alberto Natusch (1979)
56. Lidia Gueiler Tejada (1979–1980)
57. Luis García Meza (1980–1981)
58. Celso Torrelio (1981–1982)
59. Guido Vildoso (1982)
60. Jaime Paz Zamora (1989–1993)
61. Gonzalo Sánchez de Lozada (1993–1997)
3. Shugabannin Bolivia daga 2000 zuwa 2026
62. Jorge Quiroga (2001–2002)
63. Gonzalo Sánchez de Lozada (2002–2003)
64. Carlos Mesa (2003–2005)
65. Eduardo Rodríguez Veltzé (2005–2006)
66. Evo Morales (2006–2019)
67. Jeanine Áñez (2019–2020)
68. Luis Arce (2020–2025)
69. Rodrigo Paz Pereira (2025–zuwa yanzu).
Manazarta
Bolivia: Chronology of Presidents. (n.d.).
Bolivia Hop. (2026, October 5). Bolivian Culture Guide 2026: Cholitas, Aymara Traditions & Customs.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta, manazarta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.
