Majina wata aba ce ta al’ada, mai santsi, yanayin ruwa-ruwa wadda yawancin tantanin da ke cikin jiki ke samarwa. Tana da mahimmanci ga aikin jiki kuma tana aiki a matsayin mai kariya da samar da damshi don kiyaye gabobin da ke da mahimmanci daga bushewa. Majina tana aiki a matsayin tarko ga wasu abubuwa masu rikitarwa kamar ƙura, hayaki, ko ƙwayoyin cuta. Ta ƙunshi ƙwayoyin inganta garkuwar jiki da ƙwayoyin bakteriya masu kashe enzymes don taimakawa wajen yaƙar cututtuka.

Lokacin da ƙwayar cuta ko wasu abubuwan suka shiga cikin hanyoyin iska, suna cin-karo da tarkon majina mai ɗaci. Sannan jiki ya yi kokarin kawar da su ta hanyar tari da atishawa. Shi ya sa samar da majina ke yawaita lokacin da ake rashin lafiya: Jiki yana ƙara yawanta yayin da yake aiki tuƙuru don yaƙi da cututtuka.
Jiki yana samar da majina da yawa, kimanin lita 1 zuwa 1.5 kowace rana. Ba a damu da ganin majina kwata-kwata ba sai dai idan adadinta ya ƙaru ko kuma ingancinta ya canja, kamar yadda zai iya faruwa dalilin cututtuka da yanayi daban-daban.
Sassan jikin da ke samar da majina
Ana samun majina a wurare da yawa a cikin jiki ta hanyar tantanin majina da ke cikin sassan gaɓoɓin jiki da yawa, da suka haɗa da:
- Hunhu: Hunhu gaɓa ce ko waje da ake samar da majina, ana kiran majinar cikin hunhu da ‘sputum’ ko ‘phlegm’.
- Sinuses: Sinuses wuri ne shi ma da ake samun majina. Majinar da ake samu a cikin sinus tana fita ta cikin hanci.
- Baki: A ciki baki ma ana samun majina sosai, majinar baki tana aiki a matsayin sinadarin ruwa da ake bukata domin motsawar wasu gaɓoɓin, kuma tana aiki a matsayin mai ba da kariya.
- Maƙogwaro: Ana samun majina har a cikin makogwaro, majinar cikin maƙogwaro ita ana kiran ta da phlegm ko sputum.
- Hanci: Yawan majina a cikin hanci zai iya haifar da yoyon hanci.
- Gastrointestinal tract: Majina tana kiyaye ƙwayar gastrointestinal da ɗanɗano kuma tana aiki a matsayin shingen kariya daga shigar ƙwayoyin cuta, enzymes masu narkar da abinci mai narkewa da gubobi masu alaƙa da abinci.
Yawaitar majina a cikin hanci na iya haifar da komawarta cikin makogwaro. Wannan yana haifar da tarin ƙwayoyin cuta a cikin makogwaro, yanayin da kan zama matsala ga lafiyar jiki.
Bambanci tsakanin majina da phlegm
Phlegm ita ce kalmar da ake amfani da ita wajen yin nuni ga majinar da tsarin numfashi ke samarwa, musamman lokacin da aka same ta da yawa kuma aka yi kakin ta. A lokacin kamuwa da cuta, majina tana ƙunshe da ƙwayoyin cuta ko ƙwayoyin cuta da ke da alhakin haifar da cuta ga ƙwayoyin garkuwar jiki (white blood cells).
Phlegm a karan kanta ba ta da haɗari, amma idan akwai adadi mai yawa, tana iya toshe hanyoyin iska. Yawanci ana fitar da phlegm ta hanyar tari, kuma wannan yawanci yana tare da alamomi kamar cushewar hanci, yoyon hanci, da ciwon makogwaro ko zazzaɓi.
Dalilan yawaitar majina
Cututtukan na numfashi kamar mura da sinusitis su ne abubuwan da ke haifar da haɓakar majina da kuma tari. Abubuwan da ke haifar da rashin lafiya, su ma dalili ne na yawaitar samuwar majina. Ko da cin abinci mai yaji na iya haifar da ƙarin manina a cikin hanci a tsakanin wasu mutane.
A yayin da ake rashin lafiya dalilin kamuwa da cutar numfashi, za a iya lura da majina mai kauri wanda za ta iya bayyana da duhu fiye da na al’ada. Wannan majinar mai kauri tana da wahalar sharewa fiye da asalin majina wacce ba ta larura ba ce. Wannan majina tana da alaƙa da yawancin alamomin mura. Tana iya bayyana launin rawaya zuwa koriya a lokacin da ake cikin rashin lafiya.
Alamomin yawaitar majina
Samuwar majina da yawa ba kasafai take zama babbar matsalar likitanci ba, amma ba ta da daɗi kuma tana haifar da damuwa, musamman idan ta toshe hanci ko ƙofofin numfashi ko kuma ta haddasa tari. Majina mai kauri da yawaitarta suna haifar da alamomi marasa daɗi da yawa kamar:
- Yoyon majina ta hanci
- Toshewar hanci
- Ciwon makogwaro
- Ciwon kai
- Tari
Ire-iren launukan majina
Launuka daban-daban na majina da phlegm na iya bayyana wanda suka haɗa da:
Majina mai kauri
Majina mai kauri da ke tattare da cututtuka da yawa mafi akasari ta fi duhu da launin rawaya idan aka kwatanta da majinar da ba ciwo ne ya haifar da ita ba. Majina launin rawaya a cikin makogwaro ko hanci na iya zama alamar kamuwa da cuta. Idan kamuwa da cutar ya daɗe, majinar na iya zama koriya. Canji a cikin launin majina galibi alama ce mai mahimmanci da ya kamata a nemi shawarar masana kiwon lafiya.
Koriyar majina
Koriyar majina tana cewa cewa majinar tana ƙunshe da ƙwayoyin cuta masu illa ga ƙwayoyin jini (white blood cells) masu yaƙi da kamuwa da cuta. Koriyar majina a cikin hanci na iya nuna cewa an kamu da cutar sinus ko wasu cututtuka, kamar mura.
Farar majina
Farar majina na iya zama alama ce ta farkon matakan kamuwa da cuta ko cinkushewa. Kumburin tantanin hanci, sau da yawa ƙwayoyin cuta ko abubuwan da ke haifar da ke rikitarwa ne kan haifar da shi, suna jinkirta kwararar majinar, hakan kan janyo ta rasa danshi kuma ta zama mai kauri da duhu. Farar majina na iya zama alamar ciwon hanci ko sanyi.
Majina mai launin ja ko ruwan ƙasa
Majina mai launin ja ko launin ruwan kasa ita ma tana da yawa kuma tana tattare da cututtukan gaɓoɓin numfashi na sama, musamman idan cikin hancin ya rikice ko ya karce.
Yayin da jini kaɗan a cikin majina ba ya zama da wata matsala, akan samu faruwar hakan. Amma ya kamata a ziyarci ƙwararrun ma’aikatan kiwon lafiya idan akwai zubar jini mai yawa daga hanci.
Yadda ake kawar da majina
Saline nose rinses, gami da pot neti, na’urori ne da ake amfani da su wajen kawar da majina ga waɗanda ba sa son shan magunguna. Bulb syringes and squeeze bottles, su ma wasu ƙarin na’urori ne ko hanyoyin kawar da majina daga cikin hanci. Saline sprays, maganin shaƙa ne na hanci, shi ma zai iya taimakawa.
Duk waɗannan fasahohin suna ɓatar da majina kuma suna taimakawa buɗe hanyoyin iska ga kofofin hanci. Koyaushe a yi amfani da ruwa mai tsaftataccen ruwa. Yin amfani da ruwan famfo marar tsabta yana da ɗan haɗari da kuma damar shigar da cuta a cikin hanyoyin iska da ƙofofin hanci. Wasu magunguna suna iya inganta majina da kuma ƙara wa jiki kuzarin fitar da ita.
Magungunan kawar da majina
Yawancin magunguna na da ake kira over-the-counter (OTC) na iya taimakawa wajen rage yawaitar majina ko taimakawa wajen kawar da ita. Masu hana samuwar majina mai kauri (decongestants) da kuma masu yaƙar abubuwan da ke rikitar da jiki da haifar ciwo kamar zazzaɓi da sanyi (antihistamines) nau’ikan magunguna ne guda biyu wanda za su iya taimakawa daƙile cututtuka na mura ko sanyi.
Decongestant yana rage kwararar jini zuwa sassan jikin hanci da makogwaro, don haka jiki na iya samar da majina kaɗan. Za su iya taimaka wajen yin numfashi cikin sauƙi lokacin da hanci ya toshe, amma saboda suna bushewa, za su iya yin tasirin da ba a buƙata na yin kauri da ke nan. Ya kamata a yi amfani da maganin kawai bisa umarnin likita ga mutanen da ke da cutar hawan jini ko ciwon zuciya.
Antihistamines suna toshe ko iyakance ayyukan ‘histamines’, abubuwan da suka faru yayin rashin lafiyar da ke haifar da tantanin hanci ya samar da ƙarin majina mai yawa. Magungunan antihistamines na baya ko na farko na iya zama masu kwantar da hankali, amma ana iya ɗaukar sabbin nau’ikan maganin a lokacin rana, zai haifar da yanayin jin bacci ko yin baccin amma ba sosai ba.
Wani ƙarin nau’in magani wanda zai iya taimakawa kawar da majina shi ne ‘guaifenesin’. Guaifenesin wani nau’in magani ne da ake kira expectorant. Wannan magani yana sanya mijina ta tsinke ta yi laushi, domin a sami sauƙin fitar da ita ta hanyar tari.
Manazarta
Benadryl (n.d.). What is a Mucus? Symptoms, Causes & Treatment. . Benadryl.com
Gangemi, A. J., MD. (2023, March 17). All of your questions about mucus, answered. Temple Health.
NIH News in Health. (2024, June 17). Marvels of mucus and phlegm. NIH News in Health.
StÖPpler, M. C., MD, & D, D. J. P. (2024, November 11). Mucus: Causes, symptoms, excessive production & treatment. MedicineNet.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.