Rana siffarta tamkar ƙwallo take, tana ƙunshe da iskar hydrogen da helium, kuma masana kimiyya na hasashen ta samu ne shekara biliyan 4 da miliyan 500 da suka wuce. Kuma hasken rana da muke samu a duniyarmu ta Earth, shi ne jigon tafiyar da rayuwar mutane da dabbobi da duk wasu halittu da ke rayuwar a duniyarmu ta Earth. Wato ma’ana dai, ita ce ke ciyar da rayuwarmu da dukkan abubuwan da Allah Ya halitta a ƙarƙashinta.
Asalinta
Hasashen masana kimiyya ya nuna ta samu ne ta yadda fashe-fashen nukiliya a tumbinta suka amayo da ƙwayoyin halitta, waɗanda suka yi ta maƙaluwa suna goyon juna ta hanyoyi iri-iri, har sai da halittu suka tsiro daga gare su.
Akwai duniyoyi tara da suke zagaye rana a unguwar tamu ta Solar system , sannan akwai dubun-dubatar curarrun duwatsu masu zagaya rana cikin ƙwambarsu da aka fi sani da asteroids, da kuma comets har tiriliyan uku da ke zagaye ta.
Mene ne Comets?
Comets wata curarrar aba ce mai kan ƙanƙara amma kuma tana feshin gas da ƙura, da suke ziyartar unguwar rana su zagaya su koma.
Rana tana cikin birnin Milkyway Galaxy ne, a can wata ƴar kwana a hannun Orion na Birnin Milkiwe ɗin, amma tana da nisan shekarun haske 30,000 zuwa dandalin birnin, don haka ta kasance tamkar ɗigon allura a cikin kafatanin birnin, kamar yadda masana suka tabbatar.
Nisan rana daga duniyarmu ta Earth tafiyar kilomita miliyan 150 ce, wato a lissafin shekarar haske kuma ba ta wuce minti takwas da sekon ɗaya na saurin haske ba. Idan a mota ce mai tafiyar kilomita 100 cikin awa ɗaya, kuma za a yi tafiya ba tare da hutawa ba, to za a iya isa inda rana take a cikin shekara 106. Idan kuwa a jirgin sama jannati za a tafi wanda yake tafiyar kilomita 246,960 a duk sa’a ɗaya, to akwai yiwuwar shafe awa 606 ko kwana 25 yana tafiya daga duniyar Earth zuwa wajen rana.
Faɗin rufaffen kumbonta daga gefe zuwa gefe wato diameter ya kusa kilomita miliyan ɗaya da dubu 300, wato ya ninka duniyarmu ta Earth sau 109 a faɗi.
Tumbinta kuwa, ya ninka na duniyar Earth sau fiye da miliyan ɗaya da dubu 300.
Daga nan duniyar Earth muna hango rana ne tamkar faifai, sai dai ba ta da turɓaya don jikinta na garwashin wuta ne da iskar gas. Saboda tsananin wutar, takan fesa harsunanta cikin samaniya fiye da dubban kilomitoci. Zafin harsunan wutar kan kai fiye da digiri 10,000 sannan sukan yi tsiri a sararin samaniya fiye da kilomita 160,000 zuwa 300,000 da fadin kilomita 8,000 zuwa 10,000. A wasu lokutan sai harshen wutar ya yi watanni ko ma shekaru yana tsiri cikin fishi da kurari.
Wani ɗakin kimiyya mai shawagi a sararin samaniya ta hanyar amfani da na’urorinsa ya taɓa auna irin wannan harshe na wutar rana a ranar 19 ga watan Disamban 1973. A nan ne suka ga harshen ya feso da tsibirin kilomita 588,000. Wannan tsibirin na harshen wutar ta rana ya ninka faɗin duniyar Earth sau 45.
Zafin tumbinta ya fi digiri miliyan 16, amma a kan doronta zafin ba ya wuce digiri 6,000. Hakan ne ma ya sa haskenta ya ninka na wata sau 400,000, duk da yake dama daga jikinta ne watan yake samo haskensa.
Nauyinta
Nauyin rana kuwa ya nunka na duniyar Earth sau 333,000, amma duk da nauyin tana tafiya zagayenta da saurin kilomita 2,150 a kowane sekan na agogo. Sannan ta kan ɗauki tsawon shekara 250 kafin ta yi kewaye ɗaya.
Makarinta da yadda take husufi
Rana tana da makarinta na atmosfiya da ake kira corona. Sannan ita ma duniyar Earth tana da nata makarin wato ozone layer da yake kare ta daga illar da zafin rana ke iya yi wa duk wani abu mai rai da ma muhalli a kan doron Earth ɗin. Ozone layer na da nisan kilomita 15 zuwa 30 daga saman Earth.
Husufin rana
Husufin rana kan faru ne a lokacin da wata ya shiga tsakanin duniyarmu ta Earth da rana, kuma saboda nisan da ke tsakanin wata da rana, sai watan ya rufe rana ruf tamkar girmansu ɗaya. Amma hakan kan faru ne a lokacin da wata ya yi nesa da rana, to ya kan ɗan bar haske ya leƙo daga bisanin faifan rana, shi ma hasken a zagaye tamkar husufi mai ƙawanya.
A yayin cikakken husufi kuwa, inuwar wata kan dira a kan doron duniyar Earth, kuma ta bazu fiye da kilomita 268 a kasashen da inuwar ta sauka. Ko da yake ba ko ina ake ganin inuwar ba, amma yawanci inda gari a waye yake, wato bangaren Earth da ke fuskantar rana a wannan lokacin suna iya ganin husufin.
A yayin kuwa da watan yake ƙasa-ƙasa, to kaɗan daga fuskar rana yake iya rufewa; don haka, inuwar take zama ƙarama a hali irin wannan na ƙaramin husufi, wato partial eclipse.
Bambancin rana da wata
Rana tana da matuƙar nisa daga wannan duniyarmu ta Earth, nisan ma na kimanin kilomita miliyan 150
Shi kuwa wata a nan-nan kusa da duniyarmu yake da nisan kilomita 384,400 kacal
Faɗin rana ya kai kilomita miliyan 1.4, yayin da faɗin wata bai fi kilomita 3,474
Rana haskenta nata na kanta ne, shi kuma wata daga jikin rana yake aro haskensa
Rana jikinta iskar gas ce ta cika, shi kuwa wata dandaryar ƙasa ce
Dukkan rana da wata ana amfani da su wajen auna lokaci
Ana iya zuwa duniyar wata don a tarihi ɗan’adam ma an jejje, amma zuwa rana abu ne mai kamar wuya don ko fara gwada hakan ma ba a yi
Rana ta nunka wata girma sau 400 sannan ta fi shi haske sau fiye da 450,000.
Launukanta
Kamar yadda muke gani daga duniyar Earth, launukan rana kan sassauya, wani lokacin ta zama ja ko ruwan ɗorawa (yellow) ko ruwan goro (orange) ku kuma fara fat.
Dalilan ba wasu masu tsauri ba ne da suka wuce hakan na faruwa ne a lokacin da take ɓullowa ta sararin samaniyar Earth wato wayewar gari, da lokacin da ta take a samaniyar da kuma lokacin da take shirin ɓacewa a samaniyar can da magariba ke nan.
A yayin da take ɓullowa a lokacin wayewar gari da kuma lokacin da almuru ya durfafo rana ta kan zama yalo ko ja ko ruwan goro ne. Kuma hakan kan faru ne saboda yadda ainihin kalolinta na kurkusa wato kore da shuɗi da shanshanbale (violet) ke tarwatsuwa ne a sararin samaniyar duniyar Earth. Don haka ne mu daga nan duniyar ba abin da za mu gani sai kala uku; ko yalo ko ja ko ruwan goro. Idan kuma rana ta zo ƙololuwar samaniya wato ta take, to a lokacin ne sai a ga ta yi fari fat a sama.
Muhimmancin rana ga duniyar Earth da halittunta
Rana tana feso wa duniyar earth burbuɗin ƙwayoyin halitta daga fashe-fashen nukiliyoyin tumbinta. Haskenta da ɗuminta su ne ainihin abincin rayuwar dukkanin halittu a wannan unguwa tata ta solar system.
Daga silin haskenta tsiranni suke samun abin gina ɓargonsu, su tofo furanninsu da ƴaƴansu, abinci gare mu.
Daga ɗuminta ruwan teku yake tashi ya zama hadari wanda ɗuminsa ke sake fasa shi, ruwan sama ya sauko mana; abin shan furanninmu, dabbobinmu da mu kanmu.
Daga hasken rana muka sami launukan da muke amfani da su wajen rayuwarmu da kimiyyarmu, kamar wadanda “Bakan Gizo” ko gilashi suke nunawa.
Daga hasken rana muke iya bambance ranakunmu da lokutanmu don mu iya tsara rayuwarmu cikin lumana da nasara.
Daga ɗumin rana muke iya tatsar wutar girkin tawalli, ko daga makamasan da suka rayu daga taimakonta.
Haka lantarkinmu da duk abubuwan da muke amfani da su a na’urorinmu daga jirin zafi na rana (radiation) muke samun su.
Idan fetur ne, to gurɓataccen man daga ayyukan zafin rana a kan wasu ƙasusuwa da duwatsu muke samunsa.
Idan nukiliya ne, to da ma shi ne garwashin rana, wanda ɓurɓurshinsa yake ɗauke da elements masu iya gauraya su haifar da nukiliyar.
Hasken rana magani ne na yawancin cututtuka, kuma sauran magunguna ana haɗa su ne daga abubuwan da rana ta haifar, ko da tsiranni ne ko da kuwa sinadarai ne.
Hatta hasken wata wanda yake da nasa amfanin, daga rana yake samunsa, ya haska mu da dare, mu kuma yi lissafi da tafiyarsa.