Labarin ”Ruwan Bagaja” labari ne daga cikin sanannu kuma shahararrun ayyukan adabin Hausa da suka bayar da gudunmawa wajen tabbatuwar rubutaccen adabi a shekaru da dama da suka shuɗe. Littafin Ruwan Bagaja, yana daga cikin jerin littafan Hausa da suka fara bayyana tun a zamanin Turawan mulkin mallaka. Littafin wanda shahararren marubucin nan mawallafin Magana Jari Ce, wato Malam Abubakar Imam ya wallafa yana ƙunshe da darusa na ilimi da nishaɗi. Littafin har ila yau, yana koyar da juriya da neman ilimi da gaskiya da kuma haƙuri. An wallafa Ruwan Bagaja a karon farko a shekarar 1934, kuma marubucinsa shi ne Malam Abubakar Imam, ɗaya daga cikin fitattun marubutan Hausa a tarihi.
Ruwan Bagaja labari ne ƙirƙirarre, littafin yana taka rawa sosai wajen biyan buƙatun makaranta kasancewar ya yi daidai da tsarin adabin gargajiya da na zamani, inda marubucin ya yi amfani da kyakkyawan salo ya isar darusan rayuwa ta sigar zube mai sauƙin fahimta. Labarin ya tara ɗimbin taurari da dama da suka taka rawa a ɓangarori daban-daban.
Ruwan Bagaja na da kamanceceniya da wasu fitattun littattafai na duniya, musamman wajen amfani da tafiya a matsayin salo na bayani da ci gaban halayya. Misali, littafin Pilgrim’s Progress na John Bunyan, wanda aka wallafa tun a ƙarni na 17, yana da kusanci da Ruwan Bagaja a wajen yadda jarumi ke tafiya yana fuskantar gwagwarmaya har sai ya cimma burinsa. Sai dai Ruwan Bagaja ya fi karkata zuwa al’ada da falsafar Hausawa, inda ya dogara da tatsuniyoyi da maganganun hikima da al’adun gargajiya. Wannan ya bambanta shi da littattafan Turawa waɗanda suka fi karkata ga addini ko ra’ayoyin falsafa na Turai.
Littafin Ruwan Bagaja yana daga cikin fitattun kayan adabi da suka kafa tarihi a Hausa. Rubutunsa da jigonsa da kuma yadda ya tsarasu ya sa ya zama ɗaya daga cikin ginshiƙan adabin Hausa na zamani. Marubucin littafin, ya zamo abin alfahari ga al’ummar Hausa da ma Najeriya. Ruwan Bagaja ba kawai littafi ba ne na nishaɗi, amma wata gadar da ke haɗa tarihi, al’ada, da ƙima da falsafar rayuwa.
Jigon littafin Ruwan Bagaja
Babban jigon littafin Ruwan Bagaja shi ne wayo da neman maganin warkar da yarima. Labarin ya nuna irin ƙoƙarin da Alhaji ya yi wajen neman Ruwan Bagaja, wani irin ruwan sihiri da ake cewa yana warkar da kowace irin cuta. A tafiyarsa, ya gamu da ƙalubale daban-daban da suka ƙunshi. A ƙarshe, labarin yana ƙarfafa cewa gaskiya, ƙwazo, da ilimi su ne hanyoyin da za su ceci mutum da al’umma gabaɗaya daga duhu da jahilci.
Wannan littafi yana ƙarfafa tunanin cewa rayuwa tana bukatar ilimi da jajircewa wajen fuskantar ƙalubale. Haka kuma, yana nuna cewa haƙuri da ƙoƙari su ne mabuɗin nasara. Ta hanyar hanyoyin da Alhaji ya bi, littafin yana koya wa masu karatu muhimmancin sadaukarwa da ladabi da koyi da nagarttattun ɗabi’u.
Wasu matallafan (ƙananan) jigogi da ke cikin labarin sun haɗa da:
- Yaƙi da jahilci
- Neman gaskiya a cikin duhu
- Fahimtar dabi’un mutane
- Siyasa da salon mulki
Labarin Ruwan Bagaja, wanda Abubakar Imam ya rubuta, ya na ɗauke da darussa masu yawa waɗanda suka dace da rayuwar yau da kullum, musamman ga matasa da masu mulki.
Salo da zubi da tsarin littafin
Ruwan Bagaja yana ɗauke da salo na ban dariya a wasu sassa, da kuma salo mai ƙayatarwa wanda ke jan hankalin mai karatu. Abubakar Imam ya yi amfani da harshen Hausa cikin sauƙi da ƙa’ida, inda ya haɗa da karin magana, misalai, da kwaikwayo da siffantawa. Wannan salo ya sa littafin ya ɗore kuma yake ci gaba da jan hankalin al’ummu gabaɗaya.
Littafin ya kunshi bayani mai zurfi cikin sauƙin fahimta. Tsarin labarin mai zurfi ne, inda kowanne ɓangare ke da saƙo na musamman da ya shafi al’adu, zamantakewa, da siyasa. An tsara littafin a tsari babi-babi inda yake da babi har guda (8). Wani salo da marubucin ya yi amfani da shi a littafin shi ne yadda ya ɗora labarin kan tsarin tatsuniya da kuma hikimomi na gargajiya. Akwai abubuwa da dama da ke nuna alamar tatsuniya, irin su halittun ban mamaki da wuraren sihiri, amma duk suna da saƙo na tarbiyya da hikima.
Darusan da labarin ya ƙunsa
- Ilmi: Labarin yana nuna cewa neman ilimi shi ne mafita ga duk wata matsala da jama’a ke fuskanta.
- Haƙuri da Juriya: Misali, Alhaji ya nuna haƙuri da juriya a yayin tafiyarsa mai cike da cikas da ƙalubale.
- Tarbiyya: Littafin ya haskaka cewa mutum zai iya sauya halayensa ta hanyar ilmantarwa da kyakkyawan tunani.
- Riƙon gaskiya: A cikin tafiyar Alhaji, akwai wurare da dama da ya fuskanci jarabawa, amma ya tsaya kan gaskiya da amana.
- Sadaukarwa: Alhaji ya sadaukar da kansa saboda ƙaunarsa ga al’umma.
Muhimmancin littafin
Littafin Ruwan Bagaja ya taka muhimmiyar rawa wajen ilimantar da al’umma da kuma bunƙasa adabin Hausa. Ana yin amfani da littafin a matsayin kayan koyarwa a makarantu, kuma an fassara shi zuwa wasu harsuna. Har wa yau, littafin ya zamo abin nazarta ga sauran marubuta wajen tsara labaran zube na Hausa.
Haka kuma, littafin ya taimaka wajen tabbatar da cewa Hausa za ta iya kasancewa harshen adabi na zamani kamar kowane harshe. Imam ya yi nasarar ƙirƙirar littafi mai cikakken salo, mai ɗauke da darusa, da kuma kayatarwa ga masu karatu.
Tasirin littafin ga makarantu
Ruwan Bagaja ya zamo ginshiƙi ga nazarin adabin Hausa a manyan makarantu da jami’o’i. Yana ɗaya daga cikin tsofaffin littafan Hausa da suka fara bayyana a matsayin rubutaccen adabi. Har wa yau, ana gudanar da bincike da nazari a kansa a fannoni daban-daban ciki har da nazarin harshe, al’ada, da ilimin ɗabi’a.
Baya ga wannan, littafin ya zama abin kwaikwayo ga wasu marubuta da ke ƙoƙarin rubuta littafan da za su haifar da sauyi cikin tunanin matasa. Ana amfani da saƙonnin da ke cikin littafin wajen koyar da ɗabi’a da zamantakewa mai kyau.
Ra’ayoyin masu karatu
Wadanda suka karanta Ruwan Bagaja sun haɗa da malamai, ɗalibai, marubuta, da iyaye. Kowa na bayyana yadda littafin ya shafe shi ta wani fanni, ko dai ta hanyar saƙon tarbiyya, ko kuma tsarin rubutu, ko kuma irin salo na nishaɗi da hikima da Imam ya nuna. Wannan ya nuna cewa Ruwan Bagaja ba kawai littafi ba ne na tarihi ko adabi, littafin yana taka rawa a gyaran tunani da ɗabi’ar jama’a tun daga yara har zuwa manya.
Labarin Ruwan Bagaja ya samu ɗimbin makaranta kuma yana ci gaba da samu, kuma cigaban zamani ya sa har su makaranta kan iya tofa albarkacin bakinsu cikin sauƙi ta hanyar kafafen watsa labarai na zamani. Ga wasu daga cikin ra’ayoyin da masu karatu da masana suka bayyana kan littafin Ruwan Bagaja, wanda hakan ya ƙara tabbatar da matsayinsa cikin fitattun littafan Hausa:
Malam Bala Muhammad (Masanin Adabin Hausa)
“Ruwan Bagaja littafi ne da ya ƙayatar da ni tun lokacin da na fara karantawa a makarantar sakandare. Abu na farko da ya burge ni shi ne yadda Abubakar Imam ya ɗauki wata ƙaramar tatsuniya ya juya ta zuwa babban labari mai cike da darussa. Wannan yana nuna basirar marubucin.”
Hajiya Fatima Usman (Malamar makaranta)
“Ruwan Bagaja yana ɗaya daga cikin littafan da nake amfani da su wajen koyar da ɗalibai darussa kamar gaskiya, haƙuri, da sadaukarwa. Yana da sauƙin karantawa kuma yana cike da darussa da suka dace da kowane zamani.”
Musa Salihu (Dalibi a Jami’a)
“Ina ganin littafin Ruwan Bagaja yana da matuƙar tasiri wajen fahimtar tarihin adabin Hausa da salon rubuce-rubuce na gargajiya. Kamar yadda jarumin littafin yake ƙoƙarin neman mafita ga al’ummarsa, haka nake ganin matasa na yau ma ke buƙatar irin wannan ƙwarin gwiwa.”
Dr. Hauwa Gidado (Masaniyyar Harshen Hausa a Jami’a)
“A cikin littafin Ruwan Bagaja, Abubakar Imam ya nuna irin fasahar harshe da hikima da kwarjini da rubutun Hausa ke da shi. Wannan littafi na da kima a tarihi da al’adu fiye da yadda mutane ke tsammani.”
Audu Adamu (Mai sha’awar karatun littattafan Hausa)
“Na karanta Ruwan Bagaja fiye da sau uku. Kowanne lokaci da na sake karantawa sai na samu sabon abu da ban lura da shi a baya ba. Labarin tafiyar jarumin yana tunatar da mu yadda rayuwa ke da ƙalubale, amma da jajircewa za a kai ga nasara.”
Malama Jamila Haruna (Matar aure mai karatun Hausa)
“Na karanta littafin Ruwan Bagaja tun lokacin da nake sakandare, kuma yanzu ma ina karantawa wa ‘ya’yana domin su koyi darussa daga ciki. Littafin ya cika da saƙonni masu muhimmanci waɗanda suke koya wa yara yadda za su zama masu gaskiya da haƙuri.”
Manazarta
Auyo, A. (2023, January 24). Tarihin Alhaji Abubakar Imam, shahararren marubuci a ƙasar Hausa (kashi na ɗaya). Neptune Prime Hausa.
Awwal, S. (2023, September 25). Littafin Ruwan Bagaja A Ma’aunin Matakan Rayuwar Bahaushe. Amsoshi.
New page 2. (n.d.).
RUWAN BAGAJA. . .. . .. . . (2025, July 10). KanoOnline.com Forum.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.