Skip to content

Tsargiya

Tsargiya cuta ce mai saurin yaɗuwar gaske kuma ta daɗe tana yaɗuwa ta hanyar ƙwayoyin da ke haddasa ta. Mutane suna kamuwa da cutar yayin ayyukan gona, na gida, sana’o’i waɗanda ake aiwatar da su a gurɓataccen ruwa. Rashin tsafta da zuwa koguna yin ninkaya ko kamun kifi a cikin kududdufai yana haifar da cutar ga yara.

depositphotos 99084980 stock photo parasite in stool
Ƙwayar cutar da ke haddasa tsargiya.

Tsargiya ta shafi kusan mutane miliyan 240 a duk faɗin duniya, kuma sama da mutane miliyan 700 da ke zaune cikin yankuna masu kyau. Yaɗuwar cutar ta fi ƙamari a wurare masu zafi, a cikin al’ummomi marasa ƙarfi waɗanda ba sa samun ruwa tsabta. Alkaluma sun nuna cewa a kalla mutane miliyan 251.4 ne suka bukaci maganin riga-kafi a shekarar 2021. Maganin riga-kafin wanda ya kamata a yawaita amfani da shi na tsawon shekaru, zai rage tare da hana kamuwa da cutur. An ba da rahoton yaɗuwar cutar tsargiya a ƙasashe 78.

Gangamin yaƙi da cutar tsargiya yana mayar da hankali kan rage kaimin cutar a lokaci-lokaci, ana kawar da cutar ta hanyar gangamin bayar da riga-kafin maganin praziquantel; wato hanyar da ta fi dacewa da yaƙar cutar ta haɗa da tsaftace ruwan sha, ingantacciyar tsaftar muhalli za su rage yaɗuwar cutar.

Yadda cutur tsargiya ke yaɗuwa

Tsargiya dai galibi tana shafar matalauta da al’ummomin karkara, musamman masu noma da kamun kifi. Matan da ke yin ayyukan gida a cikin ruwa mara kyau, kamar wanke tufafi, su ma suna cikin haɗari kuma suna iya kamuwa da cutar tsargiya ta mata. Rashin tsafta da cuɗanya da ruwan da ke ɗauke da cutar na sa yara musamman saurin kamuwa da cutar.

Mutane suna kamuwa da wannan cutar yayin da tsutsa nau’in ƙwayar cutar, wanda dodon koɗin ruwa suke saki – suna shiga cikin fata yayin da aka shiga ruwa. Yaɗuwar tana faruwa ne lokacin da mutanen da ke fama da tsargiya suka gurɓata ruwan da najasa (kashi ko fitsari mai ɗauke da ƙwayaye), waɗanda ke ƙyanƙyashewa a cikin ruwan.

A cikin jiki, tsutsotsin suna girma su zama manya. Manya tsutsotsin suna rayuwa a cikin hanyoyin jini inda mata daga cikinsu suke sakin ƙwayaye. Wasu ƙwayayen suna fita daga cikin jiki a cikin kashi ko fitsari domin ci gaba girma a tsarin rayuwarsu. Wasu kuma sun zama a cikin tantanin jiki, suna haifar da raunin garkuwar jiki tare da ci gaba da lalacewar gaɓoɓi.

Tsargiya ta zama ruwan dare a wurare masu zafi musamman a cikin al’ummomi marasa galihu, wato inda ba a samun tsaftataccen ruwan sha kuma babu isasshiyar tsafta. An kiyasta cewa aƙalla kashi 90% na waɗanda ke buƙatar maganin tsargiya suna zaune ne a nahiyar Afirka.

Ƙaura zuwa yankunan birane da tafiye-tafiyen jama’a suna haifar da yaɗuwar cutar zuwa sabbin yankuna. Ƙaruwar yawan jama’a da buƙatun abubuwan more rayuwa da ruwa sukan haifar da tsare-tsaren ci gaba, kuma gyare-gyaren muhalli yana sauƙaƙe yawaitar yaɗuwar cutar.

Ta fuskar yawon shakatawa da balaguro zuwa yankuna masu nisa, da yawan masu yawon buɗe ido suna kamuwa da cutar ta tsargiya. A wasu lokuta, masu yawon bude idon suna isar da cutar tare da kamuwa da nau’i mai tsanani da matsalolin da ba a saba gani ba ciki har da gurguncewa.

Tsargiya nau’in urogenital ana la’akari da ita a matsayin nau’i mai haɗarin gaske wanda kan haifar kamuwa da cutar HIV, musamman a cikin mata.

Nau’ikan ciwon tsargiya

Akwai manyan nau’ikan cutar tsargiya har guda biyu:

  • Tsargiyar cikin hanji (intestinal schistosomiasis)
  • Tsargiyar mafitsara (urogenital schistosomiasis).

Alamomin cutar tsargiya

Alamomin cutar tsargiya ana bayyana su ne ta fuskar rabe-raben cutar kamar yadda za a gani a ƙasa:

  • Tsargiyar hanji za ta iya haifar da ciwon ciki, zawo, da jini a cikin bahaya. Ana iya fuskantar karuwar girman hanta a yayin cutar mai tsanani masu wanda akan danganta hakan da taruwar wani ruwa a ciki da hauhawar jijiyoyin jini na ciki. A irin waɗannan lokuta ana iya samun haɓakar sa.
  • Alamar tsargiyar mafitsara ita ce ganin jini a cikin fitsari. Lalacewar koda da fibrosis na mafitsara da ureter wani lokaci suna zama alamomin a yayin da cutar ta tsananta. Ciwon dajin mafitsara kan iya afkuwa idan cutar ta ci gaba da yin ƙamari. A cikin mata, tsargiyar mafitsara na iya haifar da raunuka na al’aura, zubar da jini, zafi a lokacin jima’i. A cikin maza, tana iya haifar da cututtuka masu illa ga marena da ta samuwar maniyyi da sauran gaɓoɓi. Wannan cuta na iya haifar da matsaloli na dogon lokaci da ba za a iya jurewa ba, gami da rashin haihuwa.

Tasirin tattalin arziki wajen kula da cutar tsargiya yana da yawa, cutar tana illatawa fiye da yadda take kashewa. A cikin yara, tsargiya na iya haifar da anemia, rashin girma da kuma dakushe basira, kodayake ana iya kawar da tasirinta da magani. Cutar tsargiya har ila yau na iya shafar kuzarin mutane na yin aiki kuma a wasu lokuta tana iya kaiwa ga mutuwa.

Adadin mace-mace ta dalilin cutar tsargiya yana da wuya a iya kimantawa saboda ɓoyayyun cututtuka kamar gazawar hanta da koda, ciwon daji na mafitsara da cikin mahaifa ta dalilin tsargiya ga mata. A halin yanzu an kiyasta mace-mace a sakamakon cutar tsargiya ya kai 11792  a duniya a kowace shekara.

Gwaje-gwajen cutar tsargiya

Ana gano cutar tsargiya ta hanyar gano ƙwayaye a cikin bahaya ko na fitsari. Ƙwayoyin kariya ga jiki da/ko ƙwayoyin da ke haifar da shigar antibodies cikin jini da aka gano a cikin jini ko samfuran fitsari su ma alamomin kamuwa da cutar ne.

Ga tsargiyar mafitsara, ana gwajin tsargiya ta hanyar tace fitsarin ta amfani da wani yadi nau’in nylon, ko wata takarda ko polycarbonate, ita ce tsayayyar hanyar gwajin tsargiyar mafitsara. Yaran da ke da S. haematobium kusan koyaushe suna samun jini ƙanƙane a cikin fitsarinsu.

Ana iya gano ƙwayayen tsargiyar hanji a cikin samfurin bahaya ta hanyar amfani da methylene blue-stained cellophane wanda aka jiƙa a cikin glycerin ko gilashi, wanda aka sani da fasahar Kato-Katz.

Ga mutanen da ke zaune a wuraren da ba su da lahani ko ƙarancin yaɗuwa, gwaje-gwajen serological da na garkuwar jiki na da amfani wajen gano kamuwa da cuta da buƙatar cikakken bincike, magani da kuma bibiya.

Hanyoyin riga-kafi da kariya

Kariya daga cutar tsargiya ya dogara ga samar da ingantaccen magani ga jama’a masu ɗauke da cutar, samar da ruwa mai tsafta, inganta tsaftar muhalli, wayar da kai game da tsafta da canjin ɗabi’a, kula da dodon koɗi da kuma kula da muhalli gabaɗaya.

A cikin sabon jadawalin cututtukan wurare masu zafi da aka yi watsi da su 2021-2030, da Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da shi, ta sa a matsayin manufofin duniya na kawar da cutar tsargiya a matsayin matsalar kiwon lafiyar jama’a a duk ƙasashen da ke fama da cutar.

Dabarun na WHO na kula da cutar tsargiya suna mayar da hankali kan rage cututtuka ta hanyar lokaci-lokaci, an tsara yin amfani da maganin praziquantel ta hanyar babban gangamin duba mutanen da abin ya shafa. Dabarun sun ƙunshi gwaje-gwaje akai-akai ga duk rukunin mutane masu haɗari. A cikin ‘yan ƙasashe, inda ake samun ƙarancin yaɗuwar cutar, ya kamata a zabura don daƙile yaduwar cutar gabaɗaya.

Rukunin mutanen da aka tsara bawa magani su ne:

  • Yaran da ba su kai shekarun zuwa makaranta ba
  • Yaran da suka kai shekarun zuwa makaranta
  • Manya waɗanda ake ganin suna cikin hatsari a yankunan da ake fama da matsalar da masu sana’o’in da suka shafi cuɗanya da ruwa, kamar masunta, manoma da matan da ke ayyukan gida ke kawo musu cuɗanya da ruwa
  • Ɗaukacin al’ummomin da ke zaune a yankunan da ke fama da cutar.

WHO ta ba da shawarar kula da yaran da ba su kai shekarun zuwa makaranta ba kuma ‘ suka kamu da cutar bisa ga bincike da hukunce-hukuncen asibiti tare da shigar da su cikin gangamin ba da magani ta hanyar amfani da tsarin praziquantel na yara.

Ana kimanta yawan maganin da a yi amfani da shi ta hanyar duba girman cutar a cikin yaran da suka kai shekarun zuwa makaranta. A cikin wuraren da ake yawan samun yaduwarta, ana iya maimaita magani kowace shekara har tsawon shekaru da yawa. Sa ido na da mahimmanci don fahimtar tasirin ayyukan kulawa da daƙile cutar.

Manufar ita ce a rage raɗaɗin cutar da yaɗa ta domin kawar da ita a matsayin matsala ga lafiyar jama’a. Gangamin gwaje-gwaje na lokaci-lokaci ga mutanen da ke cikin haɗari zai kawar da ƙananan alamomin cutar kuma ya hana masu ɗauke da cutar kamuwa da cuta mai tsanani. Sai dai kuma, babban tarnaƙi ga yaƙi da cutar tsargiya shi ne ƙarancin wadatar maganin praziquantel, musamman domin kula da manya.

Bayanai a shekarar 2021 sun nuna cewa kashi 29.9% na mutanen da ke bukatar magani a duk faɗin duniya ne, tare da kashi 43.3% na yaran da suka kai shekarun zuwa makaranta da ke bukatar riga-kafin chemotherapy don magance cutar tsargiya. Ragowar kashi 38% idan aka kwatanta da na 2019 ya ƙaru ne, saboda cutar sankarau ta COVID-19 wacce ta dakatar da yaƙin daƙile cutar a a yankuna da dama da suka kamu da ita.

Praziquantel shi ne maganin da aka ba da shawarar yin amfani da shi a kan kowane nau’in tsargiya. Yana da tasiri, inganci da kuma farashi mai sauƙi. Sai dai akan iya sake kamuwa bayan an gama amfani da maganin, amma haɗarin kamuwa da cutar mai tsanani yana raguwa har ma cutar ta mutu idan aka ci gaba da maimata amfani da maganin ga yara.

An yi nasarar aiwatar da aikin kawar da cutar tsargiya a cikin shekaru 40 da suka gabata a ƙasashe da dama da suka hada da Brazil, Cambodia, China, Egypt, Mauritius, Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Oman, Jordan, Saudi Arabia, Morocco, Tunisia da sauransu. A cikin ƙasashe da yawa an sami damar bunƙasa maganin cutar tsargiya zuwa matakin ƙasa kuma yana da tasiri kan cutar cikin ‘yan shekaru. Amma har yanzu ana buƙatar aiwatar da bincike game da yawan yaɗuwar cutar a ƙasashe da yawa.

A cikin shekaru 10 da suka gabata an sami ƙaruwar gangamin bayar da magani ga masu cutar a kasashe da dama na kudu da hamadar Sahara, inda akasarin waɗanda ke ɗauke da cutar suke rayuwa cikin haɗari. Wannan gangamin bayar da magani ya haifar da raguwar yaɗuwar cutar a tsakanin yaran da suka kai shekarun zuwa makaranta da kusan 60%.

Manazarta

Cleveland Clinic. (2024, December 19). Schistosomiasis. Cleveland Clinic.

Mustapha, O. (2018b, May 27). Tambayoyi a kan wasu cututtukan mafitsara. Aminiya. 

World Health Organization: WHO. (2023, February 1). Schistosomiasis. World Health Organization

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page