Skip to content

Venus

Venus ita ce duniya ta biyu daga rana a jere kuma tana da zafi sosai wanda ake auna a digiri 462 na ma’aunin celcius ko’ina ka je. Ita ce duniya mafi zafi a tsarin hasken rana, baya ga Mercury.

Venus wata duniya ce da ba ta da teku kuma yanayinta mai matuƙar nauyi ne wanda abin ke kewaye da shi galibi na carbon dioxide ne kuma kusan babu tururin ruwa a cikinta.

Venus ce duniya ta biyu a jerin duniyoyin da ke kewaye da solar system.

Binciken masana ya kwatanta kamanceceniya tsakanin duniyarmu ta ɓangaren girma, sai dai kuma wasu hotuna da aka ɗauka sun nuna yadda take da tsari irin na tsaunuka da manyan duwatsu. Wanda hakan ke nuna a zahiri wannan kaɗai zai iya nuna kamanceceniyarsu. Baya ga haka kuwa ba su da wata kamanceceniya.

Wani nazarin ya sake tabbatar da yadda duniyar take ƙunshe da sinadarin iska gurɓatacciya, kuma mai kauri wanda za a iya kwatanta ta da irin sinadaran da kamfanonuwa ke fitarwa masu ɗauke da gurɓataccen yanayi.

Girman Venus

Venus ta yi kusan girman duniyar Earth, kuma tana da wahalar gani saboda kaurin iskar carbon dioxide da ke ciki. Wannan yanayi mai ya sa saman Venus ya yi zafi saboda zafin ba ya komawa sararin samaniya.

Yanayin a Venus

Yanayi a Venus yawanci carbon dioxide ne, kuma gajimare na sulfuric acid ya rufe duniyar gabaɗaya. Yanayin yana kama wani ɗan ƙaramin makamashin hasken rana wanda ya isa saman tare da zafin da duniyar da kanta ke bayarwa. Wannan tasirin ya sanya ƙasa da ƙananan yanayin Venus ɗaya daga cikin wurare mafi zafi a cikin solar system.

Abin mamakin a Venus

Venus ta kanta duniya ce mai ban mamaki ta hanyoyi da yawa. Misali, tana jujjuyawa a saɓanin sauran duniyoyi, ciki har da duniyar Earth, ta yadda a kan Venus rana tana fitowa ne ta yamma.

Masana kimiyya har yanzu suna mamakin juyawa, ko koma bayan jujjuyawar Venus. Tawagar masana kimiyya daga cibiyar bincike ta Faransa Astronomie et Systemes Dynamiques sun fitar da sabon bayani. Wannan bayani ya yi iƙirarin cewa Venus asalinta tana jujjuyawa daidai da sauran taurari.

Ma’ana, tana jujjuyawa daidai da yadda ta saba, sai juye-juye kawai, ta yadda idan aka kalli sauran duniyoyi daga, jujjuwar ta kasance kamar tana juyawa ta baya ne.

Halayen duniyar Venus

Venus tana da halaye na musamman waɗanda suka sa ta bambanta da sauran duniyoyi. Ɗaya daga cikin waɗannan halayen shi ne motsi na musamman, kamar yadda duniyar Venus ke juya kanta a cikin motsi na agogo. Wannan al’amari ya bambanta Venus daga kasancewa ita kaɗai ce duniya duniya da ke yin haka a cikin tsarin solar system.

Wannan motsi na sauran duniyoyi a cikin tsarin solar system wani abu ne da ke tayar da sha’awar masana kimiyya masu sha’awar nazarin ilmin taurari. Ko da yake masana kimiyya har yanzu ba su kai ga bayar da cikakken bayani game da wannan lamari ba, amma gabaɗaya an lasafta shi a matsayin al’amari na halitta da ke da alaƙa da abubuwan gravitational Venus da kuma tasirinsu a kan siffarta da tsarinta na ciki.

Bugu da ƙari, ana tunanin cewa juyawar agogon Venus na iya zama da alaƙa da saurin jujjuyawarta. Ba kamar sauran duniyoyin da ke cikin tsarin solar system ba, waɗanda ke jujjuyawa a bigire ɗaya, wanda hakan ke ba su damar kammala cikakken zagaye a sararin samaniya cikin dogon lokaci. Venus tana da saurin jujjuyawar gaske. Saboda haka, wannan saurin jujjuyawar an yi imanin zai haifar da keɓantaccen zagaye na agogo wanda kowa zai iya lura da shi.

Kodayake kasancewar wannan juyawa ta baya na iya zama ta musamman da sabon abu, bai ya shafi rayuwa kai tsaye a cikin Venus ba. Duniyar na ci gaba da kewaya rana kuma tana fuskantar hasken rana da sauran yanayi kamar yadda muka saba. Don haka wannan yunkuri ya kasance wani lamari ne na musamman wanda ke tayar da sha’awar masana kimiyya kuma yana bukatar ci gaba da nazari da bincike don gano ainihin dalilan da ke tattare da hakan.

Yadda Venus take

Sama da shekara 20 duniyar Mars ta handame mafi yawan kuɗaɗen da NASA ke warewa na zuwa sauran duniyoyi. A gefe guda kuma, masu bincike kan duniyar Venus sun damu kan yadda ba a bai wa duniyar muhimmanci.

Amma hakan ya fara sauyawa, saboda sabbin fasahohi, fahimta da kuma yadda sabbin mutane ke faɗaɗa fahimtarsu kan maƙwabciyar duniyar tamu. Wasu na tunanin akwai yanayi da mutane za su iya nazari a kai, da yiwuwar ana samun aman wuta lokaci zuwa lokaci. Wataƙila an taɓa samun tekuna a biliyoyin shekarun baya a tarihi.

Masana kimiyya da suka sadaukar da ƙwarewarsu don fahimtar wannan duniya na cike da farin cikin cewa a ƙarshe batun bincike a Venus ya dawo teburin NASA.

Lissafi a duniyar Venus

Venus ita ce ta biyu a layin kusanci da rana, sannan ita ce tafi ko wacce duniya kusanci da tamu a girma. Shekara ɗaya a Venus ya kama kwana 225 na duniyarmu. Amma kwana ɗaya a venus kwanaki 117 ne na duniyarmu. Duniyar Venus ba ta juyawa da gudu kamar sauran duniyoyi. Doron ƙasar venus tarin duwatsu ne masu aman wuta, saboda haka a iya bincike ba abin da zai iya rayuwa a doronta.

Zafin da duniyar Venus take ɗauka

Masana kimiya da kuma bincike sun bayyana cewa, yanayin zafin saman duniyar Venus yawanci ya kan wuce ma’aunin 700 kelvins, zafin da zai iya narkar da dalma.

Yanayin ma’aunin zafin sararin duniyar Venus ya kai 900 F (465 C), wacce karfin zafinta kan iya ragargaza tare da hallaka duk wata halitta.

Manazarta

Admin, L. (2022, December 19). Manyan abubuwa 10 masu ban sha’awa game da duniyar Venus. Abincin Lafiya Kusa Da Ni.

Ishaq, M. (2017, September 24). Ilimin Taurari: Shin menene Solar System? Kuma a ina duniyar nan tamu take a falakin sammai? Legit- Nigeria News.

Portillo, G. (2018, August 29). Duniyar Venus. Meteorología En Red.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×