Warin baki wani ne yanayi ne ko cuta da yake adabar mutane da dama, wanda wasu dalilai ne ka iya haifar da shi. Ko dai dalilai na lalura ko kuma dalilai na rashin kula. Warin baki na takurawa masu fama da shi, ta yadda ba sa iya yin wani kataɓus cikin al’umma musamman wurin taro. Asalin matsalar warin baki tana faruwa ne dalilin bakteriyar dake fannin wannan wuri na baki. Wadda idan aka kuskurewa tsarin yadda tafiyarta take kan haifar da ɗa mara ido.
Kamar dai yadda aka sani warin baki ya kan faru ne bisa dalilin cin wani abu wanda yake zuwa ya samu matsuguni a tsakanin haƙora ko kuma kan haƙorin kansa. Sai su kuma ƙwayoyin bakteriyar su yi rayuwa daga wannan abincin, ta yadda wannan abuncin shi ne abin da zai ginasu ya ba su damar ‘yantuwa daga matattu zuwa rayayyu, daga nan sai su fara sako sinadarin sulfur mai wari da ɗoyi.
Idan ba a wanke ko kuma goge wannan abinci ba, su kan ba wannnan ƙwayoyi tare da wannnan bakteriya damar rayuwa a wuri guda. Hakan zai sa su samu wuri su danƙare.
Yawaitar masu fama da warin baki
Adadin masu fama warin baki yana da yawan gaske, yana shafar kusan duk mutum 1 daga cikin 4 a duniya. Wani bincike da ya haɗa sakamakon maƙaloli guda 13 ya gano cewa warin baki yana shafar kusan 31.8% na al’ummar duniya.
Alamomin warin baki
Babbar alamar alamar warin baki ita ce wari mara daɗin shaƙa daga baki. Warin na iya zama mai ƙarfi wanda har wasu mutane kan iya jin sa a hancinsu.
Abincin da ke danƙarewa a baki
Duk wani nau’in abinci kan danƙare a kan haƙora ya kuma haifar da warin baki matuƙar babu kulawa. Haka nan tafarnuwa da albasa suna iya haifar da warin baki wanda su kuma ba sa maƙalewa a kan haƙora. Sai dai warinsu yana samun matsuguni a cikin baki ya riƙe idan har babu kulawar da ta dace.
Ire-iren warin baki da dalilin afkuwarsu
Dalilan da suka fi yawan haifar da warin baki su ne rashin tsaftar baki. Idan ba a kula da tsaftar baki yadda ya kamata kamar goge haƙora, amfani da man baki da kuma tsaftace haƙora akai-akai ƙwayoyin cuta masu cutarwa na shiga cikin baki su kuma yawaita ba tare da kulawa ba.
Warin baki na lalura
Duk da cewa rashin tsaftar baki shi ne dalilin da ya fi yawan haifar da warin baki, sai dai masana sun bayar da tabbacin ba shi ne kaɗai abin da ke kawo shi ba. Akwai wasu yanaye-yanaye da ka iya haifar da warin baki.
Irin wannan warin bakin, ya kan iya samuwa ta dalilin wani ciwo ko wani abu makamantasu. Don haka ba zai zama lallai domin rashin kula yake zuwa ba, haka kuma sababban haɗuwa da shi suna da yawa. Kamar masu fama da:
Amosanin Baki
Amosanin baki lallura ce mai girma, tana kuma iya samun kowa da kowa yaro da babba ko kuma mace ko namiji. Masu fama da lalurar amosanin baki suna fama da warin baki sosai, wanda ko da sun wanke baki da man goge baki za ka ji ƙamshin man yana fita daban haka ma warin yana fita daban. A wasu lokutan ma har ya kan zubar musu da jini ko kuma fitar haƙori.
Ciwon haƙori
Ciwon haƙori lalura ce mai rikitarwa, wadda ta kan iya hautsina mai fama da ita. Akasari ciwon haƙori ya fi faruwa ne a lokacin sanyi. Kuma dalilai da yawa na kawo shi, kamar yawaitar shan abu mai sanyi ko kuma mai zaƙi. Masu fama da lalurar ciwon haƙori su ma suna iya fama da warin baki musamman a lokacin sanyi da ya fi matsa musu fiye da kowa ne lokaci.
Sankarar baki
Cutar daji ta baki wadda aka fi sani da kyansar baki. Cuta ce mai matuƙar haɗari tana iya haifarwa da mai ita warin baki mai tsanani. Hasalima idan ta ta’azara tana iya kawo wasu irin ƙuraje masu ruwa a gefen baki. Yayin da take haifar da daddarewar fatar baki a wasu lokutan ko kuma fitar haƙora idan ta yi tsanani.
Reflux Gastroesophageal (GERD)
Wannan wata cuta ce ta narkewar abinci inda acid ko ruwa daga ciki ke dawowa cikin esophagus, wanda shi ne bututun da ke ɗaukar abinci daga baki zuwa ciki.
Ciwon dasashi
Wato cutar da take kama dasashi wacce da Turanci ake kira da ( gum disease). Wannan cuta tana sanya kumburin dasashi wanda zai iya haifar da yin ja, kumburi da zubar jini. Cutar na faruwa ta hanyar taruwar abinci ko wani abu mai ɗanɗano wanda ke taruwa a kan haƙora.
Hanyar guje wa kamuwa da ita shi ne, ta goge haƙora da man wanke baki. Idan ba a kula da cutar ba, za ta iya haifar da periodontitis, wanda ke lalata dassashi da kuma haifar da asarar haƙora da ƙasussuwan kusa da haƙora.
Ciwon hanta da ƙoda
Masu fama da wannan lalura na cikin haɗarin kamuwa da cutar warin baki dalili kuwa; lokacin da hanta da ƙoda ke aiki yadda ya kamata, suna tace gubobi daga jikin ɗan Adam. Amma cikin haɗarin cututtukan mutanen da ke da cutar hanta ko ƙoda, waɗannan gubobi ba sa yin aikin su yadda ya kamata na tace guba. Wannan na iya haifar da warin baki
Warin baki na rashin kula
Rashin kula da baki na taka muhimmiyar rawa wurin haifar da warin baki, wanda kan faru dalilin rashin tsafta. Wasu mutanen kan kwana uku huɗu ba su wanke bakunansu ba ko da da man wanke baki ko kuma da asuwaki. Wasu lokutan sai mutum ya ci abinci ya kwanta bai wanke bakinsa ba, musamman da daddare hakan kan sa sauran abincin da ya maƙale ya narke ya bi sassan haƙora ya danƙare ya haifar da wanin baki.
Matsalar warin baki
Cikin kowane lungu da saƙo na faɗin duniya, cutar warin baki takan jefa mai fama da ita cikin damuwa a kullum, ta yadda ba ya iya samun kwanciyar hankali na shiga da kuma mu’amala tare mutane. Matsalolin warin baki suna da matuƙar yawa, suna haifar da abubuwa da dama wanda kan sa mai ɗauke da cutar cikin takura ko kuma wani yanayi. Daga cikin matsalolin warin baki akwai:
- Kunyar shiga mutane: Duk wanda yake fama da warin baki, yana jini kunya ko kuma ya dinga jin muzanta musamman idan yana cikin mutane.
- Gani-gani: Masu fama da warin baki ba sa iya sakewa cikin mutane domin ana yi musu gani-gani ko kuma kyamar zama kusa da su.
Abubuwan da suke kawo warin baki
Shan taba sigari
Shan sigari ko kum duk wani abu da ya danganci kayan shaye-shaye na haifar da warin baki. Domin duk wasu nau’in kayan shaye-shaye suna ba da damar da baki zai bushe ya zamana babu gudanar miyu. Rashin gudanar miyau kuma kan iya haifar da warin baki.
Rashin wanke baki
Rashin wanke baki kodayaushe musamman kwanciya bayan anci abinci yana iya kawo warin baki.
Bayan haka akwai sauran ababuwan da ke haddasa matsalar warin baki da dama wanda suka haɗa da: bushewar baki da matsalolin haƙora da wasu cututtukan da ke ɓoye a jiki da cututtukan baki da kuma wasu magungunan.
Masana sun tabbatar da cewa ƙaurace wa cin abinci, ita ce babbar hanyar da ke haifar da warin baki. Dalilin shi ne, idan ba ka ci abinci ba, to ana samun ƙarancin miyau a baki. Domin shi miyu amfaninsa da yawa ga lafiyar dan Adam da kuma gudanar da wasu lamura na fanin tafiyar abincinsa. Ba wai kawai wanke dattin ragowar abincin a baki miyau ke yi ba, a’a yana taimakawa wajen narkar da abincin ta yadda zai shige ta makogoro cikin sauƙi. Mutanen da ke rage yawan abinci nau’in carbohydrate a cimarsu, ana ganin sun fi samun matsalar warin baki.
Hanyoyin kariya
- Gujewa shan kayan zaƙi kafin a kwanta bacci.
- Guje wa cin tafarnuwa ko kuma albasa musamman kusa da lokacin bacci kuma a kwanta ba a wanke baki ba da man baki ko kuma asuwaki.
- Guje wa shan taba sigari ko kuma kayan maye kamar giya.
- Cin abinci mai tsafta.
- Yawaita shan ruwa akai akai ko da ba aci abinci ba.
- Yawaita kula da tsaftar bakin ta hanyar yin burushi a kai-a kai musamman bayan cin abinci da lokacin kwanciya.
- Yana da kyau a dinga yawaita kuskure baki da ruwan ɗumi da gishiri don yana kashe ƙwayoyin cutar da ke bakin waɗanda ka iya jawo wari.
- Amfani da kanunfari ta hanyar tauna shi a bar shi a baki tsayin wani lokaci na taimakawa lafiyar baki da kuma tabbatar da ƙamshi a baki.
- A dinga yawan sakace don cire ragowar abincin da ke maƙalewa a bakin. Amma a kula domin yawan sakace kan iya haifar da ciwon haƙori.
- Yawan wanke kan harshe yayin da aka zo yin burushi.
- A guji barin baki ya bushe. Yawaita shan ruwa na rage hamamin baki ko da kuwa an yini ba a ci komai ba.
- Tauna cingam ko alawa musamman marasa zaƙi na taimaka wa wajen sa baki ya yi wasai ba za a ji warinsa ba. Kamar alawar da ta danganci mai yaji irin ta mura.
- A riƙa ziyartar likitan haƙori a kai-a kai musamman don su za su fi gano ko akwai haƙorin da ya ruɓe wanda ka iya jawo warin bakin.
Manazarta
Mayo Clinic (n.d.) Bad breath – Symptoms and causes. Mayo Clinic.
Cleveland Clinic. 2024, May 1) Bad breath (Halitosis). Cleveland Clinic.
The Healthline Editorial Team. (2020, December 7). Bad breath (Halitosis). Healthline.