Skip to content

Zabiya

Zabiya wani yanayi ne na kwayoyin halitta da ba kasafai ba wanda ke haifar da raguwa ko rashin sinadarin melanin. Melanin wani sinadari ne mai ƙunshe da launi wanda ke ba wa fata, gashi, da idanu launukansu. Mutanen da ke da cutar zabiya suna da launin fatar da ba a saba gani ba, kuma suna shan wahala a cikin rana da yanayin haske. Babu maganin wannan yanayi na zabiya, amma wasu hanyoyin na taimakawa wajen kula da alamomin bayyanar cutar da canje-canjen salon rayuwa na iya taimakawa wajen samun kariya daga hasken rana mai cutarwa wato ultraviolet (UV).

7 3
Zabiya cuta ce da ke da alaƙa da karanci ko rashin sinadarin melanin wanda ke samar da launi ga fata, idanu da kuma gashi.

Akwai nau’ikan zabiya da yawa, waɗanda ke faruwa sakamakon sauyi a cikin kwayoyin halittar da ke samar da sinadarin melanin da rarraba shi. Iyaye ne ke samar da wannan ƙwayoyin halittar ga yaransu. A Amurka, kusan mutum 1 a cikin 20,000 ana haifar shi da matsalar zabiya. A wasu sassan duniya, kamar yankin kudu da Sahara, kusan ɗaya daga cikin mutane 3,000 na fama da wannan cuta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ware kowacce ranar 13 ga watan Yuni a matsayin ranar tunawa da miliyoyin masu lalurar zabiya a duniya. Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna a duk mutum 17,000 ana samun zabiya guda.

Yawaitar cutar zabiya

Zabiya nau’i ne na halitta sakamakon rashin sinadarin melanin wanda ke ba wa fatar jiki kariya daga tsananin zafin rana da kuma yuwuwar kamuwa da cutar kansa. Bincike ya nuna cewa kaso 67% na zabiya suna fama da cutar kansar fata a matakin farko kuma kaso 61% ‘yan ƙasa da shekaru 40.

Rahotannin sun nuna cewa a cikin mutane uku zuwa biyar na zabiya suna mutuwa ne sakamakon cutar kansa a kowanne wata shida kuma kaso 2% ne ke rayuwa har su kan shekaru 40 a duniya.

Cutar kansar fata ta zama ruwan dare a tsakanin zabiya inda aƙalla mutane biyu ke mutuwa a kowanne wata a Najeriya sakamokon cutar, a cewar shugaban ƙungiyar zabiya ta Najeriya (AAN), Bisi Bamishe.

Bayanai sun nuna cewa mutum ɗaya cikin duk mutane 5,000 a Afirka ta Kudu da Hamadar Sahara, suna rayuwa da yanayin zabiya. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce duk mutum ɗaya cikin mutane 20,000 a Turai da Kudancin Amurka yana da yanayin zabiya.

Nau’ikan zabiya

Akwai nau’ikan zabiya da yawa waɗanda aka kasabsu zuwa manyan nau’ika guda biyu: wato oculocutaneous da ocular a Turance. Nau’ikan sun bambanta bisa ga abin da ƙwayoyin halittar suka ƙunsa da kuma yadda suke shafar fata, ido, da launin gashi.

Oculocutaneous

Mafi yawan mutane da ke fama da cutar zabiya, nau’in oculocutaneous albinism (OCA) ce, tana shafar fata, gashi, da idanu. Akwai ƙananan nau’o’i takwas da ke ƙarƙashin OCA, kowannensu yana haifar da sauyawa ko rashin nau’in kwayar halitta daban-daban da ke da alhakin samar da sinadsrin launin wato melanin.

Nau’ikan OCA sun bambanta ta yadda suke shafar launi da kuma gani (idanu). Mutanen da ke da wasu nau’ikan OCA na iya samun sauyin launin fata mai haske ko launin ruwan hoda, farin gashi, da ƙarin matsalolin gani. Mutanen da ke da wasu nau’ikan nau’ikan OCA na iya samun fata mai launin cream ko jaja-jaja, gashi mai launin rawaya ko ja, da raunin gani.

Ocular

Ocular Albinism (OA), ko X-linked ocular albinism, shi na nau’i ne na zabiya wanda ke shafar idanu kawai. Irin wannan nau’in cuta ta zabiya ba ta shafar fata ko launin gashi, amma ga wasu mutanen, suna iya samun fata da gashi kaɗan idan aka kwatanta da sauran ‘yan’uwansu. Wannan nau’i na zabiya ya fi shafar mutanen da aka ƙaddara za su kasance maza a lokacin haihuwa, waɗanda aka haifa da matsalolin gani (kamar raunin gani) suna da idanu marasa launin baki.

Alamomin cutar zabiya

Cutar zabiya tana haifar da rukunin alamomi a jiki da alamomin da ke da alaƙa da ido, waɗanda suka bambanta dangane da nau’in cutar da mutum ke dauke da ita.

Alamomin jiki

Zabiya tana haifar da ƙarancin melanin (sinadarin launi), tana haifar da bambance-bambancen jiki wanda zai iya haɗawa da:

  • Fata:  Tskan zama kodaddiya ko mai tsananin haske fiye da hasken fata na al’ada.
  • Gashi: Shi ma gashi kan zama fari mai haske, ko launin ruwan ƙasa mai haske, ko launin jaja-jaja.

Alamomin idanu

  • Idanu: Idanu sukan taɓu su sauya launi zuwa launin pink ko shuɗi mai haske ko idanu masu launin toka. Sinadarin melanin yana da mahimmanci ga ci girman ido da lafiyarsa. Rashin wannan sinadari yana haifar da matsalolin ido da nakasar gani. Dukkan waɗanda ke da ƙarancin sinadarin melanin suna da matsalolin gani.

Abin da ke haifar da cutar zabiya

Zabiya wani yanayi ne na ƙwayoyin halitta wanda ke samuwa tun daga haihuwa. Sauyin da ake samu a cikin ɗaya daga cikin kwayoyin halittar da ke samarwa ko rarraba sinadarin melanin shi ke haifar da samuwar zabiya.

Ana haifar yaro tare da cutar zabiya lokacin da iyayensa biyu suke dauke da ƙwayar halittar da ke haddasa cutar zabiya. Zabiya wani yanayi ne na koma baya, kuma yawancin mutanen da aka haifa da wannan larura, iyayensu ba su kasance masu siffar zabiya ba, amma duka iyayen biyu suna ɗauke da kwayar cutar. Iyayen da ke ɗauke da ƙwayar cutar mai alaƙa da zabiya suna da kashi 25% na yiyuwar haihuwar zabiya. Wato a cikin yara huɗu da za su haifa ɗaya zai iya kasancewa zabiya.

Sauyi a cikin kwayoyin halitta daban-daban yana haifar da nau’ikan zabiya daban-daban. Oculocutaneous tana faruwa ne saboda sauyi a cikin kwayoyin halitta guda bakwai. Kowane ɗaya daga cikin waɗannan kwayoyin halitta suna taka rawa wajen samar da sinadarin melanin. Tsarin nau’in OCA da ake da shi ya dogara da wane nau’in ƙwayar cutar aka gada. Sauyi a cikin kwayar halittar GPR143, wanda ke taka rawa wajen samar da melanin a cikin idanu, yana haifar da cutar zabiya mai shafar idanu.

Abubuwa masu haɗari game da cutar zabiya

Akwai wasu abubuwan da kan iya ƙara haɗarin kamuwa da cutar zabiya, waɗannan abubuwa sun haɗa da:

  • Tarihin dangi: Mutanen da ke da ‘yan uwa masu dauke da cutar zabiya na iya zama masu ɗauke da ƙwayoyin halittar da ke da alaƙa da yanayin zabiya.
  • Launin fata: Zabiya tana shafar mutane na kowane jinsi da ƙabila, amma ta fi shahara a yankin kudancin Afirka fiye da ko’ina. Misali, ɗaya cikin mutane 1,400 a Tanzaniya da daya a cikin 1,000 a Zimbabwe suna fama da wannan cuta.
  • Jinsi: Cutar zabiya ta ido tana shafar mutanen da aka ƙaddarawa jinsin namiji a lokacin haihuwa. Yanayin halittar wannan nau’in zabiya yana wucewa daga X chromosome. Matan da ke ɗauke da ƙwayar halittar GPR143 suna da kashi 50% na yiyuwar gadar da wannan nau’in zabiya ga ‘ya’yansu maza.

Gwaje-gwajen cutar zabiya

Cutar zabiya takan faru ne a lokacin haihuwa bisa yanayin bayyanar fatar jariri, gashi, da idanunsa, wanda yawanci ya fi na iyayensa da sauran ’yan uwa. Gwajin kwayoyin halitta na iya tabbatar da cutar da kuma tantance nau’in zabiyar da yaro ke da shi.

Ga cutar zabiya ta ido, alamomin yanayin da ake iya gani ba koyaushe ake gani ba lokacin haihuwa. Don gano irin wannan nau’in zabiya, likitan ido (likita wanda ya kware kan lafiyar gani) zai yi binciken ido don neman matsalolin gani da ke da alaka da cutar zabiya. Likitan ido zai bincika motsin ido wanda mutum kan yi da niyya ko sauri da haɗewar idanu yayin gwaje-gwajen.

Magunguna

Babu magani ga cutar zabiya. Amma jiyya da kulawa suna taimakawa kan inganta gani da kare idanu da fata daga lalacewa dalilin hasken rana.

Kulawa da idanu

Idan ana fama da cutar zabiya, ya kamata a riƙa ganin likitan ido akai-akai don lura da yanayin gani da kuma samun maganin duk wata matsalar ido ko gani. Magani ko kulawa na iya haɗawa da:

  • Sanya tabarau don daidaita gani
  • Yin tiyata don gyara wasu matsalolin ido, kamar strabismus (crossed eyes) ko nakasar gani
  • Amfani da tabarau don kare idanu daga cutarwar hasken rana na UV.

Kariya ga fata

Ɗaukar ƙarin matakan kariya don kare fata daga rana yana da mahimmanci saboda ƙarancin ko rashin melanin zai iya sa fata zama mai rauni ga hasken UV na rana kuma yana ƙara haɗarin ƙunar rana. Bayan faɗuwar rana kuma yana ƙara haɗarin kamuwa da kansar fata. Matakan kare fata ga zabiya sun hada da:

  • Yin amfani da na’urar kariya daga rana (sunscreen) ko sun protective factor) (SPF) na tsawon 30 ko sama da sake shafa ta kowane awa biyu
  • Sanya kayan kariya, gami da huluna, dogayen riguna masu hannu da wando.
  • Gujewa rana a mafi yawan sa’o’in hasken ultraviolet, wanda ke tsakanin ƙarfe 10 na safe zuwa 2 na yamma ko ƙarfe 11 na safe zuwa 3 na yamma.

Hanyoyin daƙile cutar zabiya

Kasancewar cutar zabiya yanayi ne na ƙwayoyin halittar gado, ba a iya daƙile du. Kimanin 1 cikin mutane 75 ne masu ɗauke da kwayoyin halittar zabiya. Shawarwari game da ƙwayoyin halittar gado na iya taimaka wa masu fama da cutar da iyalansu su fahimci yanayinta kuma su ɗauki matakan kulawar da suka dace.

Rayuwar masu larurar zabiya

Rayuwa tare da cutar zabiya na buƙatar kulawa sosai ta musamman don kare fata daga hasken rana mai cutarwa na UV, tare da ziyartar likitan ido akai-akai don magance matsaloli masu alaƙa da gani. Idan aka samu kulawa mai kyau, yawancin mutanen da ke ɗauke da cutar zabiya za su iya yin tsawon rayuwa kamar kowa.

Mutanen da ke da zabiya sukan fuskanci tsangwama ko cin zarafi saboda launin fatarsu, gashi, da launin ido, musamman a lokacin ƙuruciya. Wannan na iya haifar da damuwa game da kamanninsu.

Idan yaro yana da cutar zabiya, samun damarmaki da abubuwan da ke inganta fahimta da wayar da kan jama’ar da yaran ke mu’amala da su da suka haɗa da dangi, malamai, da abokan zamansu zai iya taimakawa wajen wayar da kan jama’a da ƙarfafa fahimta da hada kai. Haka nan ba da shawara ta ƙwararru na iya taimakawa yanayin zamantakewa da rayuwa ga mutane masu fama da larurar zabiya.

Manazarta

BBC News Hausa. (2021b, June 13). Ranar masu lalurar Zabiya ta duniya.  BBC Hausa

Mayo Clinic (n.d.). Albinism – Symptoms and causes. Mayo Clinic.

Undefined, U. (2024, June 13). Yadda zabiya a Afirka ke shawo kan ƙalubalen rayuwa. Yadda Zabiya a Afirka Ke Shawo Kan Ƙalubalen Rayuwa – TRT Afrika.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page