Skip to content

A Game of Throne

A game of Throne, shi ne na farkon a jerin litattafai bakwai da aka tsara a cikin kundin ‘A Song of Ice and Fire,’ na Ba’amurken marubucin nan wato George R. R. Martin. An fara buga shi ne a ranar 6 ga watan Agusta 1996.

Bangon littafin A Game of Throne, na marubuci, George R.R Martin, 1996.

A Game of Throne, ya ƙunshi labarin iyayen gida da ‘yammata da sojoji da matsafa da masu kisan kai har ma da ‘ya’yan da aka haifa ba da aure ba, waɗanda suka kasance a wani lokaci mai tsanani. A nan wata runduna ce ta mayaƙa mai ban mamaki, da ke da takubba na musamman, waɗanda ba irin na ɗan’adam ba da aka sani.  A cikin labarin akwai faɗace-faɗace da cin amana da nasara da ta’addanci da cuɗanya da abokan gaba.

Jigogin da littafin ya ƙunsa

  • Adalci
  • Cin amana
  • Ɗaukar fansa
  • Mulki da iko
  • Sihiri da gaskiya
  • Siyasa da al’umma
  • Rashin fahimta
  • Tashin hankali da mace-mace
  • Balaga da ƙaunar mata

Kyautuka da littafin ya samu

  • Nebula Award Nominee for Best
  • Novel (1997), Locus Award for Best
  • Fantasy Novel (1997), World Fantasy
  • Award Nominee for Best
  • Novel (1997), Premio Ignotus for Mejor
  • Novela Extranjera (2003)
A Game of Throne, littafin na farko a jerin littafai na kundin ‘A Song of Ice and Fire’

Bayanin littafin a taƙaice

Marubuci: George R. R. Martin

Sunan littafi: A Game of Throne

Ƙasa: United States

Harshe: Turanci

Kundi: A Song of Ice and Fire Genre(s) Fantasy

Maɗaba’a:

  • Bantam Books (US)
  • Voyager Books (UK)

Kwanan watan ɗab’i: 6 August 1996

Tsara bango: Steve Youll Media

Adadin shafuka:

  • 694 (US Hardback)
  • 672 (UK Hardcover)
  • 835 (US Paperback)
  • 804 (UK Paperback)

Lamabr ISBN:

  • 0553103547 (US Hardback)
  • 0002245841 (UK Hardback)
  • 0553573403 (US Paperback)
  • 000647988X (UK Paperback)

Taurarin cikin littafin

• Brandon Stark
• Catelyn Stark
• Tyrion Lannister
• Daenerys Targaryen
• Eddard Stark
• Theon Greyjoy
• Robb Stark
• Arya Stark
• Jaime Lannister
• Joffrey Baratheon
• Robert Baratheon
• Tywin Lannister
• Lysa Arryn
• Petyr Baelish
• Sansa Stark
• Viserys Targaryen
• Varys Hodor
• Beric Dondarrion
• Thoros of Myr
• Sandor Clegane
• Samwell Tarly
• Tommen Baratheon
• Stannis Baratheon
• Mace Tyrell
• Septa Mordane
• Jon Snow
• Cersei Lannister
• Jorah Mormont

Ra’ayoyin wasu makaranta littafin

Sarah

“Na tsani wannan littafin, na tsane shi sosai dole ne in samu sabon kwafin littafin bugagge don karantawa, kuma na lura da duk sassan da nake ƙi game da shi, samnan na dawo na bayyana su a kafar Goodreads.

Lokacin da jerin shirye-shiryen talabijin na labarin suka fito na yi fushi, da fushi na kalla har sau biyu. Na kuma sayi DVD guda shida, saboda na kasa yarda da yadda zan iya zan bayyana ƙiyayyata da labarin. Na kwashe lokaci mai tsawo ina tattaunawa a kan yadda nake ƙin wannan littafi, tare da dukan abokaina, waɗanda su ma suka ƙi shi, na yanke shawarar zana hoton George R.R Martin a cinyata don nuna yadda ƙiyayyata ta kasance ga aikinsa.”

Sean Barrs

“Na kusan manta yadda nake son wannan littafi, bayan wasan kwaikwayo na talabijin ya ƙara mini son shi sosai. Kuma bayan jira na dogon lokaci don littafi na gaba a cikin jerin, na fara ɗaukar wannan jerin littattafan da wasa. Don haka na san lokaci ya yi da zan sake karantawa don tunatar da kaina littafin da ya sa na yi samu sha’awar karantu shekaru da yawa da suka wuce.

Ba na bukatar in faɗi abin da wannan littafin ya yi da kyau ko marar kyau, saboda ya sami irin wannan matsayin babban, maimakon haka kawai zan faɗi yadda ya shafi rayuwata. Shi ne littafi na farko da ya sa ni yin karantu da gaske. Dalilin haka sai na canja salon karatuna na makaranta, kuma na kware a adabi. Yanzu ina rubuta PhD dina.”

J.G. Keely

“Akwai mawallafan fantasy da yawa waɗanda ke da’awar yin wani abu daban tare da nau’ikan abubuwan ban mamaki, sau da yawa suna rubuta littattafan da za a iya tsinkaya duka, kamar yadda Goodkind da Paolini suka tabbatar. Kodayake ban san dalilin da ya sa suke haka ba. Babban labarin jarumta da mugunta da soyayya mai zurfi a duniyar da za a tsira kamar ba za tsufa ba. Labari ne mai girma idan an ba da shi da kyau. A mafi kyau, yana da ban sha’awa, ban mamaki, kuma yana da inganci matuƙa.”

Kare

“Ba zan sake karanta wannan ba littafin ba. bayan shekaru gungun masu tsananin bakin ciki, suna zuwa wurina, suna tambayar wani game rubutun  George r.r. Martin, ko ya saki sabon littafi?”

Taƙaitaccen tarihin marubucin

An haifi George Raymond Richard Martin a ranar 20 ga Satumba, 1948, a Bayonne, New Jersey. Mahaifinsa shi ne Raymond Collins Martin, wani mai aikin dauke kaya daga jirgin ruwa, mahaifiyarsa ita ce Margaret Brady Martin. Yana da ‘yan’uwa mata biyu, Darleen Martin Lapinski da Janet Martin Patten.

Martin ya halarci makarantar Mary Jane Donohoe da Marist High School. Ya fara rubutu tun yana ƙarami, ya kasance yana sayar da labaran dodanni ga sauran yara abokansa. Daga baya ya zama mai sha’awar littafin barkwanci, kuma ya fara rubuta almara. An fara sayar da littafan Martin a shekarar 1971, lokacin yana da shekaru 21 da haihuwa. Littafin da aka sayar shi ne ‘The Hero’, wanda aka sayar ga Galaxy, an buga shi a watan Fabrairu, fitowar 1971.

George RR Martin, Ba’amurke, marubuci.

A shekarar 1970 Martin ya samu shaidar B.S. a fannin Aikin Jarida daga Jami’ar Northwestern, Evanston, Illinois, yana kammalawa kuma ya ci gaba da M.S. a fannin aikin Jarida dai a shekarar 1971, a sai wannan jami’a. A shekarar 1975, ya auri Gale Burnick, sai dai sun rabu a shekarar 1979, ba su da yara. Martin ya zama cikakken marubuci a shekarar 1979.

Marubuci Martin, a ɗakin karatunsa.

A masana’antar shirya fina-finai ta Hollywood, Martin ya rattaba hannu a matsayin editan labarin nan na ‘Twilight Zone’ na gidan talabijin ɗin CBS a shekarar 1986. A cikin 1987 Martin ya zama babban mashawarcin labarin ‘Beauty da Beast.’ Yayin da a shekarar 1988 ya zama Furodusan shirin. Ya kuma kasance babban mai gabatarwa a Columbia Pictures Television.

Manazarta

Goodreads (n.d).  A Game of Thrones (A Song of Ice and Fire, #1) Goodreads.

Life and Times (n.d.). George R.R. Martin.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×