Skip to content

Kyauta

Ƙamusun Hausa (2006:271) ya bayar da ma’anar kyauta da cewa: “Bai wa mutum wani abu don ra’ayi ba tare da ya yi wani aiki ba, ko a ba da gyara a ciniki. Duk da yake wasu masana suna ganin sa gyara a ciniki ba ƙyauta ba ce, an gyara abin da aka yi ne na algusu ko tauyewa.

Ma’anar kyau a wani lokaci kan taƙaita ga nagarta, wadda ta ƙunshi gaskiya da halin kirki, kamar karimci da ‘yangaranci da ƙana’a. Waɗannan ma’anoni sun nuna cewa kyauta halin kirki ne wanda mutum ke yi ga wani domin kyautata mu’amala da jin daɗi.

Kyauta na ƙara danƙon zumunta

A takaice dai yauta na nufin wani aiki ne wanda mutum kan yi ta hanyar bayarwa , ko mika wani abin hannunsa (kudi ko tufafi ko abinci ko dabba, ko wani abu) zuwa ga wani. Ta hanyar mikawa hannu da hannu, ko kuma ta hanyar aikawa da dan aike. Akan kira mai yin kyauta namiji da karimi, mace kuma ma’abuciyar kyauta, idan jam’i ne kuma a kirasu masu karamci.

Dalilan yin kyauta

Dalilan da ke sa a yi kyauta suna da yawa. Amma, za a yi amfani da wasu dalilai da ake ganin suna sanya yin kyauta tsakanin mutam biyu da wannan yanayi ya faru ko ya shiga tsakaninsu. Ga dalilan kamar haka:

Jin daɗi

Mutumin da ke cikin wani yanayi na jin daɗi da ya samu a dalilin abin da ransa ke so ko wani abu da yake nema, yakan yi kyauta saboda murnar samun wannan abu. Misali, mutumin da ya samu labarin wurin da zai je wata matsala ta rashin lafiya ko wata bukatar rayuwa da yake nema ta biya, yana yin kyauta saboda jin daɗin wannan labari. Haka kuma, duk lokacin da aka aiko wa da mutum wani albishir na faruwar wani abu da ya yi wa rai daɗi, yakan yi kyauta saboda jin daɗi.

Neman shiga

A lokacin da mutum yake neman karɓuwa wurin mutane, kyauta tana daga cikin hanyoyin da zai yi amfani da ita domin samun goyon bayansu. Misali, saurayi idan yana neman ya karɓu wurin budurwa, kyauta tana daga cikin mizani da za a yi amfani da ita domin neman yarda saboda rai yana son mai kyautata masa kullum. Haka nan ɗan siyasa kan yi wa mutane kyauta don ya samu karɓuwa a wajensu. Baya ga haka, yin kyauta ga fadawa hanya ce da masu sarautu a fada suke samun karɓuwa wurin fadawan Sarki. Rashin kyauta ke kawo yawan zambo tsakanin makaɗan Sarakun da masu riƙe da sarauta a fadojin ƙasar Hausa.

Karimci

Duk wanda aka kyautatawa, ana samu shi ma ya kasance mai yin karamci ga wasu. Wanda aka yi wa kyauta ba ya rasa yin alheri musamman ga wanda ya zo da saƙon wannan kyauta. A nan ne batun tukuici ke shigowa ga ɗan aike idan an yi wa wani kyauta. A dunƙule, waɗannan dalilai suna cikin abin da ke sa Hausawa yin kyauta a rayuwar yau da kullum.

Ire-Iren Kyauta

Kyauta tsakanin masoya

A nan idan aka ce masoya, to ma’anar ba ta taƙaita ga saurayi da budurwa ko bazawari da bazawara ba. Ana ganin kyauta tsakanin masoya ta shafi duk wata tarayya wadda soyayya ta haɗa tsakanin mutuum biyu, za a samu cewa akwai kyauta tsakanin waɗannan mutane biyu na abin da zai faranta ran aboki. Misali, saurayi yakan yi wa budurwa kyauta domin soyayyar da yake yi mata. Haka kuma, aboki yana yi wa aboki kyauta ta abin da ya ga abokinsa yana da buƙata. Irin waɗannan kyautuka a rayuwar Hausawa suna ƙara danƙon soyayya tsakanin wanda ya yi da wanda aka yi wa kyautar.

Kyautar abokan ciniki ko kasuwanci

Kyauta tsakanin mai saye da mai sayarwa ƙari ne na abin da mutum ya saya wanda mai sayarwa ke bayarwa ga mai saye da nufin kyautata masa domin ya ji daɗi. Masu sayar da kaya suna yin irin wannan kyautar ne idan suka ji daɗin sayayya mai yawa da aka yi masu saboda sun tabbatar sun sami alfanu ƙwarai cikin wannan ciniki. Wasu kuma suna yin kyauta ga abokin ciniki ne saboda sabo da jin daɗin da aka yi na ciniki tsakani. A wannan zamani kuma, akwai lokuta na musamman wanda masu sayar da kayayyaki suke bayar da kyauta ga masu sayen kayansu. Misali, lokacin azumi, da ƙarshen shekara, da dai sauransu.

Kyautar albishir

Kyautar albishir na wani labari tana aukuwa ne a inda aka zo wa mutum da wani labari na farinciki, sai ya ba da kyauta nan take. Irin wannan hanya ta kyauta ta kasance ɗabi’ar Hausawa a duk lokacin da aka sami labarin wani abin farin ciki.

Kyautar ganin ido

Kyautar ganin ido ita ce kyautar da ake yi wa mutuum saboda ganin wani naka ko ganin idon wasu ba tare da an yi niyya ba. Irin wannan kyauta tamkar ta dole ce saboda babu niyya, to amma ganin wasu da ake jin nauyinsu ya sa an yi irin wannan kyauta. Misali, a yi wa yaro kyauta gaban iyayensa domin a faranta masu rai. Ta yiwu da iyayen ba su kusa ba za a yi masu kyautar ba.

Muhimmancin kyauta

1. Kyauta kan ƙara ƙulla zumunci ta inda za ka samu ɗa ya yi wa iyayensa, ko yaya ya yi wa ƙanninsa, ko aboki ya yi wa abokinsa, ko maƙwabci da maƙwabci.

2. Ƙauna, duk kuwa inda kyauta ta ratsa ko ta gitta, to lallai za ka samu ƙauna a tsakani. Akwai wasu kalmomi da akan faɗa in za a yi kyauta, kamar ungo ko amshi ko karbi ko debi ko dauki ko bar shi da sauransu.

3. Bahaushe ya ɗauki kyauta da muhimmanci, don kuwa Bahaushe ya ɗauke ta kamar wata igiya ce da ke ƙulla zumunci ko kuma ƙara wa babba girma, da kauna da kwar jini ga sauran jama’a.

4. Akwai inda kyauta kan zama don tausayawa a inda za ka ga mutum na cikin yanayi na bukatar taimako, amma fa ya sha bamban da sadaka.

5. Bayan wannan kuma, sai inda kyauta kan zama abin neman fada, kamar dai cin hanci ko toshiyar baki ko kuma rashawa. Ko da yake akan yi mata lullubi a ce mata na goro, a nan kuwa ta kan taso ne a inda wani mutum yake neman wani abu a wurin wani mutum mai mukami ko kuma dai makamantansu.

Manazarta

Abdullahi, I. S. S. (2008) “Jiya Ba Yau Ba: Wiwayen Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa Na Aure da Haihuwa da Mutuwa” Kundin Digiri na Uku,
Sashen Harsunan Nigeriya.
Sokoto: Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo.

Umar, M. B. (1985). Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Hausawa. Kano: Triumph

Sani, S. (1979). Sunayen Hausawa na Gargajiya da Ire-Iren Abincin Gargajiya. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading