Skip to content

Jenereta mai amfani da gas cooker

Share |

Babu shakka na san wasu za su yi mamaki cewa wai generator na amfani da gas cooker. To a hakikanin gaskiya, wannan kimiyya ta fi shekara talatin a duniya amma sai kwananan ta iso Nigeria, domin rashin wutan lantarki ingantacce ya sa ta zama kasa cikin jerin kasashen da suka fi amfani da jenereta.

Har ila yau nasan da yawan mutane za su ji tsoron-tsoron sayan irin wannan jenereta ganin yadda ake jin labarin gobarar gas yau da gobe. Wannan kimiyya ba ya da hatsari sosai irin yadda mutane ke tinani saboda an inganta shi. Duk wata hanya da ke jawo gobarar gas an toshe ta.

Shi wannan jenereta asalinsa na fetir ne wato da fetir ya ke amfani amma irin baiwa da bincike irin na yan fasaha, sai Allah Ya sa suka gano mana wannan hanya. Akwai kafireto, wato caburator da mutum zai sayo wanda shi wannan kafireto an yi shi ne babu inda iska zai fita, wato ko ina a toshe ya ke. Sai ka cire kafireton da jeneretanka ya zo da shi ka maye gurbinsa da wannan na gas din. Insha Allah da zaran ka hada daidai zai fara aiki.

Shi wannan jenereta yana iyayin aiki na tsawon awa arba’in kafin gas din ya kare, sannan refilling na gas din bai wuce N2500 ba, wanda idan da fetir ne sai ka sha man N3500 kafin ya maka awa 40. Kun ga kenan yafi jenereta rashin shan mai.

Wannan shine takaitaccen bayani game da wannan kimiyya da fasaha wanda ta shigo Najeriya ba da jimawa sosai ba.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading