Skip to content

Siffofin namiji da mata ke so

Share |

Siffofin namiji da mata ke so suna da yawa. Kowace mace na burin ganin ina ma mijinta ko saurayinta ya san wasu ababe da take son ya sani game da ita da kuma dabi’arta ta mace. Ita mace ba kamar mota bace da ke zuwa da dokoki ko ka’idoji na yadda za a sarrafa ta. Da yawan maza na samun sabanin ra’ayi da matan da suke so, babban matsalar a nan ita ce ta rashin sanin takamaimai mi matan ke so.

Zan jero kadan daga cikin siffofin maza da mata ke fatan ina ma mazajensu na da su. 

1. Namiji mai jajircewa

Kamar yadda na fada a farko cewa mata na amfani da zuciyarsu ne wajen aiwatar da harkokin rayuwarsu hakane. Misali za ka bata wa mace rai, a lokacin za ta yi amfani da zuciyarta ne wajen yanke ma hukunci. Tana iya cema ku rabu, amma hakan ba yana nufin da gaske take ba.

Tana son ka zama mai kafiya a lokacin, maimakon ka ce ma ta ku rabun sai ka jajirce ka nuna kai a lokacin ma ka fara sonta. Ka bata duk wata kulawa da take bukata, kafin kace mi za ta sakko. Saboda tayi hakan ne dama don ta san shin har lokacin kana sonta ko a’a.

2. Namiji mai sauraro

Yana daga cikin halittar mata yawan surutu, saboda hakan ne mace ke son namijin da zai zama kamar aboki a wajenta yanda take surutu da kawayenta. Burin mace shine a duk lokacin da take magana ka saurare ta, koda kuwa maganar ba ta da wani amfani a gare ta.

Tana son namijin da zai ce ma ta “a duk lokacin da kike bukatar magana ina tare da ke” ko wanda zai ce “a shirye nake idan kina bukatar wani abu ki kira ni”. Hakan na nuna ma ta cewa kai mai sauraro ne, tabbaci hakika duk wata damuwarta ba za ta boye ma ba, saboda ka ba ta kunnuwarka. Tabbas, mata a duk inda suke su na son a saurare su, saboda sun dauki magana a matsayin babbar waraka ta damuwarsu. Misali mace idan tana cikin damuwa babban abinda take so shine wa zata fada ma cikinta koda kuwa ba za ka magance ma ta ba, wannan fadin da tayi ya rage wani kaso daga cikin damuwarta.

3. Isashshen namiji

A duk inda mace take tana son ta nunawa duniya cewa wannan ne mijinta ko saurayinta. Tana alfahari da cewa namijin da take so ya isa. Abin nufi a nan ya zama gwarzo a fannin shi, misali idan shi Malamin makaranta ne babban burinta a ce babu Malami kamar shi. A ko’ina take za ta bugi kirji cewa wannan mijinta ne.

4. Namiji dan gayu

Mace na son gayu da kyale-kyale saboda suna matukar saurin daukar hankalinta, komi na mace kyale-kyale ne. Mafi yawan mata basu son namiji kazami.

Na taba hira da wata matashiya take fada min cewa abu na farko da take fara kallo a gun duk namijin da ya tunkare ta shine kafarsa. Idan ta ga kafar da datti, an tara kumba, ga faso ko kaushi, to ta san kazami ne.

Kowace mace na da tastes dinta ga namiji. Burin kowace din dai ta ga namiji fes-fes ya sha gayu. Komin rashin tsadarsu, matukar namiji ya san yanda zai dau wanka zai birge mace.

5. Namiji ya san mi ke saurin sa mace farin ciki da bakinciki

Mata na da rauni saboda haka ne abu kadan ke saurin raunana musu zuciya. Bature yace “Women are sensitive creatures”. Abun da zai samu farin ciki sai ya zama namiji na ganin ba wani abu bane ba, a wajen mace kuwa abu ne babba. Misali mace tayi kwalliya tana son a yaba wannan kwalliyar ta ta, amma da zarar kayi kamar ba ka san tayi ba, zai bakanta ma ta rai.

Ka furta cewa “My dear, kin yi kyau”, farin cikin da zai sa ta ba kadan ba, sannan kai ma za ka dandana cikin farin cikin. A duk lokacin da ka farantawa mace babban burinta a lokacin mi zata yi ta kyautata maka.

6. Kar namiji ya yaba wata mace a gaban wacce yake so 

Duk yadda mace ta kai ga son namiji matukar zai hada ta da wata to nan za a samu matsala. Ita dai ace namiji nata ne ita kadai bai hada ta da kowa ba. Abu kankani sai yasa mace kishi. Sannan hada macen da kake so da wata na saurin kashe soyayya, ita tunanin ta ba ta kai mace ba, wato she is not enough for you. Sai ta ji duk ta muzanta. A duk inda take tana son a nuna a duk duniyar nan babu kamar ta koda kuwa hakan ba gaskiya bane.

7. Namijin da zai so mace a yanda take

Duk yadda mace take tana son namijin da zai so ta a yadda take. Idan ita baka ce ya so ta don yana son baka ba wai ya zo yace ma ta yana son ta koma fara ba, haka idan siririya ce ita ya zo yace ala dole sai tayi kiba. Ko kuma hakanan ya kalle ta ya muzanta ta.

Mace ta tsani wadannan abubuwan, a nan ina jan hankalin maza musamman matasa masu shirin aure da su tabbatar da cewa macen da suke so lallai sun tabbata suna son su, ma’ana tastes din su ce. Rashin samun hakan na daya daga cikin abubuwan dake rusa aure a wannan zamanin.

8. Namiji mai nuna so da kulawa

A nan Arewa da yawan mata na korafin mazansu basa nuna masu kulawa ta bangaren soyayya saboda kunya da kuma yanayin al’adunmu. Hakan yasa muka tafka muhawara a shafin Twitter a ranar … da maudu’i mai taken “Why Arewa Men Are Not Romantic”.

An samu amsoshi daban-daban wanda mafi rinjaye shine al’ada. A Arewacin Nijeriya ba kasafai ake ganin maza na rike wa mata jaka ba, ko a ga mata da miji sun fita yawo rike da hannun juna. Duk wadannan ba dabi’unmu bane, amma abubuwa ne masu kyau da kara shakuwa a tsakanin mata da miji.

Mafi yawan lokuta mata na jin kunyar fara nunawa namiji soyayya, wata zuciyarta za ta raya mata cewa ‘idan na kira shi ko na tura masa sakon SMS zai ce na cika naci, ko banda kamun kai, ko kar ajina ya tsinke da sauran su. Hakan ba shi ke nuna bata son ka ba. Amma idan ka kasance mai yi, yau da gobe zai sa ta saba ita ma tana yi.

9. Namijin da zai tsaya ya zama garkuwa ga mace

Da yawan mata na son miji ko saurayin da zai tsaya masu a harkokin su na rayuwa. Ba wai kowane lokaci bane kalmar “Ina sonki ina mararinki” ke tasiri a zuciyar mace ba. Abinda take bukata ka nuna ma ta son a aikace, ba a baki ba. Ka ba ta duk wata gudunmuwa da kake gani za ta taimaka ma ta a rayuwa wajen cikar burin ta.

Na taba tattaunawa wasu yan mata dake fafutukar ganin sun tsaya da kafafunsu a kan zasu iya auren namijin da zai hana su abinda suka sa a gaba kuwa? Biyu daga cikinsu yan kasuwa ne, daya kuma mai burin ganin ta taimaki al’umma ce ta kowane fanni na rayuwa. Budar bakin daya daga ciki ta nuna ba za ta iya auren namijin da zai hana ta kasuwancinta ba, babab burinta auri wanda zai bata goyon baya. Wanda har ta bani misali da saurayin da ta so ta aura Allah bayyi ba, har yau har gobe bata daina son sa ba, saboda gudummawar da ya bayar wajen ganin ta dogara da kanta. 

Duk macen da ke da basira ta wani abu tana son namijin da zai karfafa ma ta gwiwa, zai tsaya tsayin daka wajen ganin cigabanta. Ko a ina yake zai bugi kirji cewa wannan matata ce ko budurwa ta ce kuma ina alfahari da ita.

10. Namiji mai hakuri da fahimta

A duk inda mace take tana son namijin da zayyi hakuri da ita saboda yanayin halittar ta, tana da rauni. Wasu mazan kan yi kuskuren daukar mata kamar yadda suke daukar kansu bayan akwai bambance-bambance a tsakani. Abu kadan kan iya hargitsa mace wanda dole sai anyi hakuri da ita an kuma fahimci yanayin halittar ta ta. Shiyasa mace ta kan yi saurin fadawa soyayyar namijin da ke jin tausayinta da fahimtarta. Misali ko da aikin gida, idan son samu ne a taya ta koda da mafi kankantar aikin ne. Idan girki tayi, ko da bayyi dadi ba kar a tsawata ma ta, a nuna ma ta kuskurenta cikin ruwan sanyi ta hakan ne zata fi fahimta. Sannan hakan na kara shakuwa a tsakanin masoya.

Kadan kenan daga cikin ababen da mata ke jin ina ma mazan da suke tare da su sun sani game da su din, don ba kasafai suke iya fada wa mazan ba. Idan kuna da wasu siffofin da ku ke gani suna da matukar mahimmanci baya ga wadannan da na lissafo, sai ku yo tsokaci a kansu, wato ku fade su a comment.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue Reading