Skip to content

Littafin ‘Musaddam Ne Zabina’ na Safna Aliyu Jawabi

Share |

Kodayake mahaifin Musaddam ya rasu tun yana `karami, amma shi da `kanwarsa Safna sun taso cikin so da `kauna tare da kulawa ta musamman daga mahaifiyarsu. Kyakkyawan saurayi ne, gwanin `kawa, ga kuma tarin dukiya. Abin burgewa; duk da wannan tarin dama da ya samu, sam ba shi da girman kai, hasali ma, shi mutum ne mai matu`kar tausayi tare da taimakon talakawa. Bugu da `kari, yana bai wa manya girmansu; wannan ya sa mahaifiyarsa take matu`kar alfahari da shi, domin duk abin da ta umarce shi yakan fara aiwatarwa nan take. Idan har tana da matsala da shi, bai wuce yadda take burin ganin ya fito da matar aure ba, shi kuwa ya gaza cika mata burinta sakamakon jiran wata buduruwa da kullum take zuwar masa a mafarki.

Ana tsaka da wannan dambarwa, Suwaiba (yayar mahaifinsa) ta haɗa kai da mahaifiyarta, da yayanta Saleh, suka shiga bokaye suka farra`ka tsakaninshi da mahaifiyarsa, inda ya ri`ka jifan mahaifiyarsa da kalamai masu dafi, har ma ya ri`ka `ko`karin kashe ta. Abokinsa Faruk ne ya ri`ke shi, ita kuwa mahaifiyarsa, babu shiri ta d`auki Safna suka bar gidan zuciyarta cike da `kuna; d`an da ta haifa (yaro mai tsananin biyayya da `kaunarta) yana neman kashe ta da kansa. Duk da ta san shekaru talatin da suka shud`e Salma (mahaifiyar Suwaiba) ita ta kashe mata miji, ba ta tsammaci a yanzu za su dawo kansu, ita da gudan jininta ba. Don ba ta zaci son abin duniyarsu ya kai haka ba.

Da yake munafurci dodo ne, mai shi yake ci, sai ya kasance duk da Salma da ‘ya’yanta; Saleh da Suwaiba, sun haɗu a kan a`kida d`aya, watau kawar da Musaddam da mahaifiyarsa don su mallake dukiyarsu, amma a junansu kowa `ko`karin cin dunduniyar d`an’uwansa yake. A `karshe ma, Saleh da Suwaiba da suka je boka ya yi musu wani sihiri, ya bu`kaci sai sun sadaukar da jinin mace kuma tsohuwa, sai suka yanke shawarar bayar da mahaifiyarsu tasu (wacce ita ta d`ora su a wannan hanya ta neman duniya ta kowace irin hanya) a nata lissafin da zarar an kwaso dukiyar za ta kar`be daga hannunsu.

Bokayensu sun yi aiki iri-iri, silar haka: Wasu sun jigata. Wasu sun tsorata. Wasu sun haukace. Wasu bacci ya `kauracewa idanunsu. A `karshe, `kai`kayi ya koma kan mashe`kiya; Suwaiba ta makance ga cutar shanyewar `barin jiki, Salma ta shiga tashin hankali ga cutukan tsufa, Saleh kuwa ya saduda (nadamar dole ta riske shi) ya koma ga Allah, musamman da ya kasance bayan tonuwar asirin `kulle-`kullen da suka yi mahaifiyarsu ta sanar da su cin amanar mijinta ta yi ba shi ya haife su ba, ba su da ala`ka ta jini da Musaddam.

A bangaren Musaddam ya yi nasarar had`uwa da buduruwar da take zuwa mafarkinsa, sun yi aure.

Jigon littafi

Babban jigon labarin shi ne soyayya, kamar yadda sunan littafin ma ya nuna. Har wa yau, tun shafin farko, zuwa na `karshe babu abin da aka tattauna a kai kamar soyayya ta fuskoki da dama kamar; yadda ake jin zafin rabuwa da masoyi kamar yadda muka ga Ummi ta shiga damuwa a lokacin da take ganin tamkar ta rasa Musaddam, da yadda Musaddam ya suma lokacin da ya tsammaci da waninsa aka ɗaura auren Ummi, har zuwa yadda Mummy ke zubar da hawaye a duk lokacin da ta tuna mijinta wanda mutuwa ta zama gatarin gwarin da ya datse aurensu. Haka nan an nuna farincikin da ake tsintar kai yayin da aka mallaki abin so, kamar yadda rayuwar Musaddam da Ummi ta kasance bayan sun mallaki juna. Sannan an nuna yadda masoyi ke yi wa masoyiya kwarjini, kamar; duk da Ummi takan je `kofar gidansu Musaddam ta labe don kawai ta ga fitowarsa, amma lokacin da ya zo makarantarsu (ya zo kusa da ita) sai ta kasa d`aga kai ta kalle shi, a duk sa’in da ya yi mata magana sai ta ji fad`uwar gaba, hakan ya sa ta gaza furta ko kalma d`aya. Haka nan an nuna soyayya na da `karfin da za ta had`a talaka da attajiri, ta had`a mabambantan `kabilu su rungumi tuta guda.
Bayan wannan akwai `kananan jigogi kamar; makirci, cin amana, asiri da sauransu.

Zubi da tsari

Sosai marubuciyar ta yi `ko`kari wurin yi wa labarin shimfiɗa mai kyau, haka ma yadda aka sa`ka zarrukan labarin, ta yadda ana tafiya labarin na `kara armashi. A yadda aka zuba labarin kowace ga`ba na `karfafar ta gabanta ne. Misali: Tun farko an nuna Musaddam na neman Ummi ne wacca ya saba da jin muryarta a mafarkinsa, a zahiri kuma ya yi ta fafutukar nemanta, labarin bai `kare ba sai da ya nemo ta har ya mallake ta ko na ce suka mallaki juna, saboda tun da fari aka nuna yadda Ummi ke matu`kar `kaunarsa tun kafin ya iso gare ta ya furta mata kalmar so. An yi amfani da sakin layi a wuraren da suka kamata, kodayake dai ba a yi amfani da dabarar kasa labarin zuwa babi-babi ba.

Taurarin labarin

Musaddam: Farawa da babban tauraro, Musaddam, ya kasance mutum mai tsafta, kullum fes-fes yake cikin ado na alfarma. Mutum ne mai yawan kyauta, da sadaka tare da tallafawa talakawa. Sannan yana da saurin sabo ta yadda aka nuna nan da nan ya yi sabo da Kakan Ummi da ma ahalinta gabaɗaya, sai dai kuma ya kasance mai zurfin ciki, ta inda ya gaza furta wa Ummi kalmar so duk da kuwa tun kafin ya fara ganinta ya fara `kaunarta. Mahaifiyarsa da ma`kota da kusan duka al’umma suna yabon d`abi’u da halayensa, kodayake yana da miskilanci, wanda shi ya haifar masa da zurfin cikin da `kiris ya rage Ummi ta ku`buce masa.

Ummi: Yarinya ce mai ilmin addini, da dattako, tare da nutsuwa, har wa yau, gwanar barkwanci ce, ga ta kuma da shagwa`ba. Sai dai ita ma kamar Musaddam, ta yi zurfin ciki inda ta gaza fayyace soyayyarta gare shi har hakan ya jawo ta kusa rasa shi. Mace ce mai matu`kar tausayi, sannan gwana ce wurin cancand`a kwalliya. Haka nan tana da daurin shiga rai kamar yadda Mummy ta had`a tun a ranar da ta fara ganinta.

Mahaifiyar Musaddam: Mace mai sau`kin hali da sakin fuska. Jaruma ce da ta yi tsayuwar daka ta raini marayun ‘ya’yanta cikin kulawa da kyakkyawar tarbiya; kullum cikin umarni da kyakkyawan aiki take gare su.

Salma: Mace ce mai matu`kar son abin duniya ta kowace irin fuska; watau a iya cewa irin mutanen nan ne da suke da d`abi’ar ciki (yayin da suka ga dukiya ba sa `koshi) da kuma d`abi’ar `kuda ta yadda sam ba ta `kyamar haramun. Hakan ya sa ta koyar da ‘ya’yanta zuwa wurin boka, a kuma haka ne mugun halin da ta ɗora ‘ya’yanta, inda a `karshe ta tashi a tutar babu: Ba ta samu dukiyar ba, ga shi kuma d`iyarta ta zama nakasasshiya silar muguwar turbar da ta d`ora ta.

Saleh: Matashi marar ra’ayin kansa, wanda hakan ne ya sa da mahaifiyarsa ta kawo masa `kazamin shiri bai tsaya wani tantance daidai da akasinsa ba, kawai ya afka. Kodayake a `karshe da komai ya rinca`be ya yi hanzarin dawo da tunaninsa jikinsa ya watsar da muguwar hanyar da mahaifiyarsa ta d`ora shi, ya bi shiriya.

Faruk: Tsayayye kuma jajirtaccen aboki, irin abokan nan ne da suke sadaukar da duk wani farincikin su don Samar da murmushi a fuskar abokansu kamar yadda ya yi wa abokinsa Musaddam. Sannan, yana da d`abi’ar bayar da Shawara tagari ko da ba za a kar`ba ba.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue Reading