Skip to content

Sara

Share |

Hausawa na cewa, ‘Sarki goma, zamani goma.’ Haƙiƙa kowane zamani yana zuwa ne da irin nashi yayin ta hanyoyi iri daban-daban. Duba da cewa Hausawa su ma mutane ne da ke zaune a cikin wannan duniyar, wadda ita kuma kullum cikin samun sabbin sauye-sauye take, su ma sauyin yana zuwa musu gwargwadon yadda ci gaban al’ummarsu ke samu kamar sauran al’ummomi.

A cikin kowane zamani, al’ummar Hausawa na samun ci gaba sosai ta hanyoyi masu tarin yawa da ba za su lissafu ba. Kama daga fannin adabi, kasuwanci, kiwon lafiya da dai sauransu, duk in da mutum ya leƙa zai ga cewa lallai ci gaba na samuwa a wannan ɓangaren.

Wanda hakan ke nufin baƙin al’amura suna shigowa, wasu masu kyau, wasu kuma akasin hakan. Sara na ɗaya daga cikin rassan adabin gargajiya wanda Hausawa suka gada tun iyaye da kakanni kuma suka riƙe ta har zuwa wannan zamani.

Ma’anar sara

Sara wani irin salo ne na magana da ke ƙunshe da ƙirƙirarrun zantuka waɗanda kan yi tashe ko yayi a wani lokaci. Waɗannan Zantuka sukan ba da ma’ana ta musamman ga wanda ya san su. Wani lokaci yayin wata sara yakan wuce, sai wani sabo ya shigo. Wani lokaci kuma akan samu sarar da kan jima ba a manta da ita ba, ko da kuwa an samu wata sabuwa ta zo a bayanta Haka nan kuma, sara na iya nufin wani yayi ko salo na yin magana da abokai ke yi a tsakaninsu wanda ya gama gari. Sara ta fi cin kasuwarta a tsakanin matasa kuma takan shafi salon magana ce ko tufafi ko kuma yanayin tafiya da dai sauransu

Akwai hikimar sarrafa harshe a cikin sara matuƙa, domin kuwa irin kalmomin da ake amfani da su, da irin halin da ake amfani da su, abin sha’awa ne. Ko da yake wani lokaci, sara kan zama tsokana ce ga wani ko cin fuska a fakaice.

Misalan sara

* Kai Baba Faisal! (akan faɗi hakan ne yayin da mutum ya faɗi wani abu da ake ganin ƙarya ne)

* Sa yau! (da an ji mota ko babur yana irin cijewar nan da abin hawa ke yi)

* Gaya Wa Ƙeya, Ɗankwali Ya Ba Ka Amsa! (mata ne kan faɗi hakan tare da turo ɗankwali gaban goshi idan aka faɗa musu wata maganar da ba ta gamshe su ba)

* Shiga Na Duba Ma! (akan faɗi hakan ne yayin da mutum ya taho a guje bisa abin hawa)

* Yanzu haɗama ba laifi ba ne, abin da ba a so shi ne handama da babakere da tanganegane (akan faɗi hakan ne wani lokaci domin nuna wa mutum cewa munin abinda yake yi fa bai gaza daga na abin da yake magana a kai ba)

* Kin iya kunu? (mace ake yi wa wannan tambayar, musamman ‘yar birni wadda ke nuna wayewa tare da iya dafa abinci kala-kala na zamani domin a ji ko ta iya na karkar)

Asalin sara

Babu wata shaida da za a iya amfani da ita wajen bayyana asalin samuwar sara ko wanda ya fara aiki da ita. Abin da kawai ya tabbata shi ne, Hausawa sun daɗe suna amfani da wannan al’ada tun gabanin zuwan Musulunci, kuma duk da irin sauye-sauyen da suka samu sakamakon cuɗanya da Larabawa da kuma Turawa a lokuta mabanbanta, hakan bai sa wannan al’ada ta ɓace ba.

Amfanin sara

Amfanin sara yana da yawa sosai a wajen al’ummar Hausawa. Domin kuwa sara kan nuna tsantsar ƙwarewar mutum wajen iya sarrafa harshen Hausa tare da faɗaɗa rumbun kalmomi. Sau da dama akan tsara sara ne game da wani mutum ko wasu mutane ko wani abu ko wasu abubuwa domin yabawa, ko kushewa ko gorantawa ko zolaya ko ƙarfafawa. Baya ga haka kuma, akan yi amfani da ita wajen isar da wani saƙo ga wanda ake so a taƙaice.

Ana yin sara a garuruwan Hausawa ko unguwanni da sauransu tun dauri kuma har zuwa yau ba a daina ba. A taƙaice dai, zai yi wuya ka haɗu da Hausawan da suka haura mutum biyu, a ko’ina suke ba tare da ka same su suna amfani da wata sara ba.

Bayani game da misalan sara

Duk da cewa mafi yawancin sarar da Hausawa ke amfani da su sun yi daɗewar da ba za a iya cewa ga asalin daga inda sukd fito ba, sarar ‘Kin Iya Kunu?’ ta fita dabam, domin ita ta zo ne a zamanin da ilimi da ƙoƙarin taskace bayanai suka yawaita. A bisa wannan dalili ita an samu asalinta da kuma yadda ta yaɗu.

Sarar ‘Kin iya kunu?’ Wata sara ce da kawai wayar gari aka yi aka tsince ta a bakin jama’a. Duk da cewa ba sabon abu ba ne samuwar sabuwar sara a tsakanin al’ummar Hausawa, wanzuwar shafukan sada zumunta irin su Facebook, Tiktok da X ya taimaka sosai wajen yaɗuwar sarar cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. A yau an wayi gari kusan a iya cewa babu wani sashe ko lungu na ƙasar nan da sarar ba ta ratsa ba.

Asalin sarar ‘kin iya kunu?’

Asalin wannan sara ta ‘Kin Iya Kunu?’ ya samu ne daga wani shahararren jarumin barkwanci mai suna Kabiru Muhammad wanda aka fi sani da King Kabeer.

King Kabeer ya kasance yana ɗora aiyukansa na barkwanci ne a manhajar Tiktok. Kuma ya yi bidiyoyi masu yawan gaske waɗanda duka suna magana ne akan abu guda, wato kunu. Misali, akwai bidiyon da yake magana akan an hana shi bashin kunu da kuma wanda ake sakin mai kunu da dai sauransu. Wannan soyayya tasa ga kunu ce ta kai shi ga shirya wani ɗan ƙaramin bidiyo mai taken ‘Kin Iya Kunu?’. A cikin wannan bidiyo, an nuno shi da budurwarsa inda take bayyana masa irin kalolin abincin da ta iya kuma za ta dinga yi masa bayan sun yi aure. Sai dai duk waɗannan abubuwa da take lissafawa ba su dame shi ba, domin kuwa tambayar da yake ta maimaita mata ita ce, ‘Kin iya kunu?’

A taƙaice dai yana nuna mata Shifa duk abubuwan nan da take lissafo masa tare da cewa ta iya su to fa in dai ba kunu ta iya ba shi Ba ta burge shi ba. Yana kuma nuna mata cewa shi fa kunu ya fiye masa duk abubuwan nan da take lissafawa.

Wannan shi ne asalin samuwar wannan sara ta ‘kin iya kunu?’

Ma’anar sarar ‘kin iya kunu?’

Idan muka yi duba da asalin sarar da kuma yanayin da ta fito, to a ƙalla za mu iya fahimtar ma’anoni guda biyu kamar haka:

Na farko: shi asalin wanda sarar ta samo asali daga gare shi masoyin kunu ne sosai, saboda haka a nashi ra’ayin in dai mace ba ta iya kunu ba, to fa babu wani abu da za ta yi da za ta burge shi.

Na biyu: halin matsi da tsadar rayuwa irin wadda aka tsinci kai a ciki a wannan ƙasa ta Nijeriya ya sa duk sauran kalolin abincin da aka saba ci ba su dame shi ba tun da ba shi da yadda zai yi ya same su. Amma zai iya samun kunu a cikin sauƙi domin shi yana da arha akan sauran kalolin abincin.

Duba da cewa waɗannan ma’anoni guda biyu duka masu kyau ne kuma ana iya karɓarsu a yi amfani da su domin raha ko kuma samun nutsuwa ko nishaɗi, ashe ba laifi ba ne don saurayi ya yi wa budurwarsa irin wannan tambaya a cikin hirar su ta yau da kullum a bisa ɗaya daga cikin waɗannan ma’anoni.

Ina matsalar take?

Jim kaɗan bayan bayyanar wannan sara sai gashi mata da yawa sun fara fitowa kafafen sada zumunta suna ƙorafi da irin yadda mazaje da dama ke yawan damunsu da wannan tambaya ta ‘Kin Iya Kunu?’ Matan kuma har’ilayau sukan yawaita tambayar ‘shin kunu dai da suka sani ake nufi ko wani abu can daban?

Hakan kuwa ya biyo bayan irin sigar da wasu ke amfani da ita ne wajen yin irin wannan tambaya. Hakan ya sa lamari ya yi ƙamarin da har ta kai ga wasu matan na ɗaukar matakin mayar da martani ko jan layi ga duk wanda ya yi musu irin wannan tambaya saboda rashin yarda da manufar yin tambayar. A cikin shekarar 2023 wata budurwa a garin Kano har ƙarar wani saurayi ta kai zuwa ga hukumar ‘Yansanda saboda ya yi mata irin wannan tambaya.

To inda wannan matsalar take shi ne, sau da dama ‘yan kwalta ko kuma a ce ‘yan bariki kan ba wa abubuwa sannanu tasu irin ma’anar ta daban domin kaucewa faɗar abin kai tsaye ko da zai je kunnen wanda ba sa so. Wannan shi ne dalilin da ya sa lamarin wannan sara ya ƙara yin tsamari. Domin kuwa sun ba shi irin tasu ma’anar kamar haka:

Na farko: in aka cewa namiji; ‘ka yi kunu’ ana nufin ka yi kwaɓa ko shirme. Wani lokaci kuma ana nufin ya yi kwanciyar aure da wata.

Na biyu: mace kuma in aka ce mata ‘kin iya Kunu?” ana nufin kin iya salon kwanciyar aure kala -kala?

To in muka lura da waɗannan ma’anoni da kyau za mu iya fahimtar inda matsalar take da kuma yadda za a bi a magance matsalar.

Kammalawa

Zamani kullum canzawa yake yi, don haka ba laifi ba ne don mutane sun bi wannan canji, amma a duk lokacin da irin wannan canji ya zo da tarnaƙi ko wani salo mai rikitarwa, to kuma ya zama wajibi a yi duba da idon basira kafin a shige shi domin a kiyaye hawa keken ɓera.

Daga ƙarshe, wajibi ne a jinjina wa wanda ya ƙirƙiro ita wannan sara duba da irin gudummawar da ya ba wa adabi a wannan ɓangare tare da fatan matasa da yawa za su maida hankali wajen kawo wa harshen Hausa ci gaban da ya kamata.

Manazarta

Dangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kamfanin “TRIUMPH” gidan Sa’adu Zungur Kano.

Wani rubutun Malam Yahuza Mai Daraja daga shafin Facebook

Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. (1992)

I.Y. Yahaya, Zaria M. S., Gusau M.S., da ‘Yar Aduwa T.M.

Ibadan: University Press Plc

Shafin Tiktok na Kabiru Muhammad (King Kabeer)

Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 2. (1992)

I.Y. Yahaya, Zaria M. S., Gusau M.S., da ‘Yar Aduwa T.M.

Ibadan: University Press Plc

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002). Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Spectrum Books Limited, Ring Road, Ibadan – Nigeria.

Jagoran Nazarin Hausa. (1986)

I.Y. Yahaya da Abdulƙadir Ɗangambo.

Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Limited.

www.amsoshi.com

Kabiru Yusuf Fagge Anka (wani rubutunsa da ya ɗora a shafin sada zumunta na Facebook a 2023)

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading