Skip to content

Shin wai haka muslunci yake ne?

Share |

Tambayar da nake faman amsawa kenan wa wasu turawa da muke mutunci da su har ma da wasu matasan da aka haife su a cikin Musulunci amma yanzu ba sa ra’ayin addinin.

Saboda suna ganin abubuwan da ke faruwa a cikin al’ummar musulmi wadanda ke nuna cewa kamar babu wata kauna ko rahama a cikin addinin.

Musuluncin kuma ba haka yake ba! Kowace Surah a cikin Al Qur’ani mai girma ana bude ta ne da “Bismillah Ar-Rahman Ar-Raheem” wato “Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai,” don jaddada girman Rahama da nuna jinkai. Sannan Annabi ya ce, “Ar Rahimun yarhamu humurRahman. Irhamu man fil ardh yarhamukum man fis samaa’ wato Allah wanda shi ne mafificin yin rahama zai yi rahama ga mutanen da ke nuna rahama ga wasu. Don haka ku nuna rahama ga mutane domin ku ma Allah ya yi muku rahama.

Amma sai mu rika yin abu kamar wadanda sakonnin nan ba su isa a gare mu ba? Mutum ya yi laifi maimakon a jawo shi kusa a yi masa wa’azi cikin hikima amma an bi shi da zagi da tsinuwa? Sannan ya fito ya nemi gafara amma ina! Wasu duk da haka ba su gamsu ba. Abun namu fa ya lalace. Wanda ya yi maka laifi ya kuma zo ya ba ka hakuri ya gama da kai babu kuma wata sauran magana.

Gaskiya dole mu sake yin nazari kan halayyarmu don muna korar jama’a musamman matasa daga addinin. Zamani ya sauya, kullum mutanenmu suna cikin karo da salon rayuwa na daban wanda ya fi daukar ido. Ga matashin da ke faman fahimtar rayuwa, wannan na iya janye shi gaba daya daga musuluncin saboda can an karbe shi; ko da ya yi laifi ba a bin shi da zagi da tsinuwa.

Idan mutum ya yi laifi ba kaurace masa zamu yi ba don dukkaninmu masu laifi ne kuma kullum muna fama da yadda za mu tsare imaninmu.

Malama Yasmin Mogahed ta ce:
“Ba a kara tunkuda mutumin da ya kusa nutsewa a cikin ruwa. Idan mutum yana yin kuskure a addini, bai kamata a kunyata shi ko a yanke masa hukunci ba. Kamata ya yi a mika masa igiya ya kama domin a ceto shi daga halaka.”  

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading