Skip to content

Tsangwama a shafukan sada zumunta

Share |

Kamar yadda kowa ya sani, mata mutane ne masu yanci, da daraja, da kima, da girma, da mutunci, da karamci, tare da girmamawa a cikin al’umma. Amma irin tsangwana da suke fuskanta a shafukan sada zumunta, wato social media, wurin wasu mazaje al’amarin ba’a cewa komai. Watakila inda wadannan maza sun san dalilan da ke kawo matan wadannan shafuka da za su basu uzuri.

Mata sun kasu kaso shida a shafukan sada zumunta:

  1. Na farko sun zo social network ne domin su sada zumunta ga yan uwansu, kawayensu na makaranta, tare kuma da yin wasu sababbi na kawayewa daga nan gida Najeriya da kuma da kasashen ketare.
  2. Kashi na biyu kuma sun zo ne domin kawai sun ga kawayensu suna yi, ko kuma saboda jin labarinsa da  suke yi a gari da kuma kafafen yada labarai, wato dai suma sun zo ne su ga me ake yi a ciki.
  3. Kaso na uku kuwa sun zo ne neman saurayi dan kwalisa, mai iya kalaman soyayya, mai abin hannu (ga yammata kenan), ko kuma bazawari (ga zawarawa).
  4. Na hudu kuwa kawai sun zo ne domin neman ilmin addini, ko ilmin sana’a, ko kuma ilmin boko, domin kuwa babu kalar zaure, watau group din da babu.
  5. Kaso na biyar kuwa, kawai gasu nan ne, babu wata hujja ko dalili na zuwan nasu. In ta yi dadi suyi dariya, idan kuma ta baci suyi Allah wadarai.
  6. Kaso na shida kuwa sune wadanda suka hada biyu, ko uku koma hudu daga cikin hujjojin da aka lissafa a sama, wato dai su hujjar zuwansu tafi daya.

Amma duk da wadannan hujjoji na zuwan matan social network, wasu mazan basa duba haka, burinsu kawai matan su tsaya su sauraresu, ko da kuwa abinda suka zo dashi ba mai ma’ana bane. Na kan tausayawa mata idan na tuna tarin sako cikin inbox nasu, kuma kowa muradinsa a mayar masa da martani, wato a yi masa reply. Haka na faruwa da mace musamman idan mace ta saka hotonta, ko kuma ta fiye yawan magana.

Akasarin mazan dake yawan turawa mata irin wadannan wasiku, za ka samu kowa babban burinsa maccen ta saurareshi shi kadai, baya tunanin sauran masu irin halayyarsa. Idan kuwa aka samu akasin haka, to ranar zata sha zagi da tsinuwa.

Baya ga aika wa yan matan da yawan wasiku, haka kuma, za ka ga ana dibarsu ana zubawa a zauruka, wato group daban-daban, mai amfani da mara amfani.

Abin tambayar a nan shine, wai shin masu irin wannan halayyar an gaya musu saboda su matan suka zo social network ne
Babu yan mata da zawarawa ne a garinsu ne? Ko kuwa wani mugun hali garesu da baza su iya neman na garinsu ba? Shin ko kun san da cewa akwai aljanun gaske a cikinsu kuwa? Ko kun san da cewa ba dukansu ne matan ba? Akwai maza da ke amfani da sunan matan? Ko kun san da cewa da yawa daga cikin matan suna da samarin da suke so?

Wadannan tambayoyi da makamantansu suna nan jibge, amma fa sai anyi tunani. Don haka ya kamata mu gane kuma mu gyara.

You cannot copy content of this page

Discover more from Bakandamiya

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue Reading