Skip to content

Farar ƙasa

Farar ƙasa wacce ake kira limestone a turance, dutse ne nau’in sedimentary wanda akasari yake ƙunshe da sinadarin calcium carbonate (CaCO₃). Wani lokaci kuma yana haɗuwa da magnesium carbonate wanda ake kira da dolomite. Farar ƙasa na samuwa ne a sakamakon taruwar halittun cikin teku kamar ƙwayoyin halitta, ƙasusuwan kifaye da sauran tarkacen halittu da suka mutu tsawon dubban shekaru. A wasu lokutan, ana iya ganin alamar waɗannan halittun a saman dutsen, duk da cewa wasu nau’ikan limestone ɗin suna da ƙananan ƙwayoyin da sai an yi amfani da na’urar gani kafin a hango su.

limestone 1Luninkan duwatsun sedimentary.

Asalin farar ƙasa

Farar ƙasa tana samuwa ne a cikin duwatsun sedimentary. Yawanci ana samun ta a tsofaffin teku da koguna da suka bushe, inda tsokoki, ƙwari, da wasu tsirrai na ruwa da suka mutu suka taru a ƙasa, bayan tsawon lokaci suke zama dutsen. Wasu nau’ukan farar ƙasa kuma ana samun su ne ta hanyar precipitation na calcium carbonate daga ruwan can ƙasa.

A duniya, farar ƙasa tana samuwa sosai a ƙasashe kamar Amurka, Birtaniya, China, Indiya, da Nijeriya. A Najeriya, ana samun farar ƙasa musamman a jihohi kamar Kano, Ogun, Enugu, da Cross River.

Siffofin farar ƙasa

Siffa mafi shahara da farar ƙasa take da ita, ita ce launin ruwan toka, amma kuma tana iya zama fara, rawaya ko ruwan ƙasa. Ta ɓangaren ƙarfi kuwa, farar ƙasa tana da porous, wato tana da ramuka da danshin za a iya fasata cikin sauƙi, amma duk da haka tana da ɗan ƙarfi fiye da wasu dutsen sedimentary kamar sandstone.

Har ila yau, Idan aka zuba acid kamar vinegar ko hydrochloric acid a kan farar ƙasa, tana yin ƙanƙara ko kumfa saboda calcium carbonate na yin reaction da acid. Sannan Dutse ne mai jumurin shan ruwa saboda porosity ɗinsa. Wani nau’in farar ƙasa ɗin na iya canzawa zuwa marble idan ya fuskanci matsanancin zafi da matsin lamba a ƙarƙashin ƙasa.

Farar ƙasa a kimiyyance

A kimiyyance, farar ƙasa tana ɗauke da sinadaran kimiyya da suka haɗa da: Calcium carbonate (CaCO₃) a cikin kaso mai yawa, sannan wasu lokuta tana ɗauke da ƙaramin kaso na magnesium carbonate (MgCO₃), silica, da sauran sinadarai.

Nau’o’in farar ƙasa

Masana ilimin dutse sun rarraba farar ƙasa zuwa nau’o’i daban-daban, daga cikinsu akwai:

Chalk

Chalk wata nau’in farar ƙasa ne mai launin fari sosai da kuma taushi, sannan kuma tana ɗauke da ramuka a jikinta. Tana samuwa ne daga taruwar ƙananan halittun ruwa da suka mutu a cikin teku shekaru masu yawa da suka wuce. Yawanci chalk na ɗauke da sinadarin calcite sama da kashi 90%, wanda ke sa ta laushi da sauƙin fasawa ko narkawa musamman idan ta haɗu da acid.

Ana amfani da ita a gona domin rage yaw acidity na ƙasa, sannan ana yin alli da ita, har ila yau ana amfani da ita a gine-gine da kayan ado

Live limestone / Quicklime

Wannan nau’in na farar ƙasa ba ta samuwa kai tsaye a cikin ƙasa, sai dai ana samar da ita ne ta hanyar ƙona farar ƙasar a zafi mai tsanani (sama da 900°C). Wannan tsari ana kiransa calcination, a wannan yanayin kuma farar ƙasa tana rasa carbon dioxide, sai ta koma Calcium Oxide.

Tana da zafi sosai idan ta haɗu da ruwa, kuma tana da ƙarfi wajen lalata ƙwayoyin cuta, sannan tana da sinadarin alkaline mai yawa. Ana amfani da ita a masana’antar ƙarafa, tana daidaita pH a masana’antu, tana gyaran ƙasa mai rauni da sauransu

Slaked limestone

Wannan nau’in na farar ƙasa tana samuwa ne idan quicklime ta haɗu da ruwa, wanda ke haifar da Calcium Hydroxide (Ca(OH)₂), ana kiran ta slaked lime ko hydrated lime. Tana da launin fari, sannan fodarta mai laushi ce, kuma bata  da zafi kamar quicklime. Tana da sauƙin  narkewa idan ta haɗu da wasu sinadarai. Ana amfani da ita a gonaki da lambuna, ana yin siminti da ita, tana tsabtace ruwa, tana gyaran ƙasa mai acidity.

Layered limestone

Wannan nau’in farar ƙasar tana samuwa ne a shimfiɗu na cikin ƙasa. Yawanci tana da ƙarancin jure ruwa, saboda haka tana iya lalacewa da sauri idan tana cikin yanayin da ruwa ke yawan taɓa shi. Saboda rashin ƙarfinta tana tarwatsewa cikin sauƙi, tana kuma shan ruwa sosai. Ana gina gida da ita a wuraren da ba ruwa sosai, ana yin dutsenta don haɗa shinge, sannan ana ayyukan gine-ginen wasu na gargajiya da ita.

Dolomite limestone

Itama wannan nau’in farar ƙasar na ɗauke da sinadarin Calcium Magnesium Carbonate (CaMg(CO₃). Saboda haka ta fi wasu nau’ukan farar ƙasar ƙarfi da juriya. Tana   jure ruwa da matsin lamba, ba ta lalacewa da wuri. Ana yin manyan gine-gine da shi, da suka haɗa da hanyoyi da gadoji da masana’antar ƙarfe.

Silica limestone

Wannan nau’in farar ƙasar na da yawan sinadarin silicon (SiO₂) a cikinsa. Silicon kuma yana ƙara mata ƙarfi da taurin gaske wanda ke sa ta jure zafi da matsin lamba. Itama ana gina manyan masana’antu da ita haɗe da tituna, da kuma wuraren da ake buƙatar dutse mai ƙarfi sosai

Tufa rock

Tufa rock ita ma wata nau’in farar ƙasa ce mai ramuka da ɗan nauyi. Tana samuwa ne lokacin da sinadaran carbonate suka taru daga ruwan zafi, musamman a wuraren da ruwa ke fitowa daga ƙasa, tana da sauƙin sarrafawa, ita ma ana amfani da ita a samar da kayan ado da ayyukan gine-gine.

Travertine limestone

Travertine tana samuwa ne a kusa da rafuka, magudanan ruwa, da rijiyoyin ruwa mai zafi ko sanyi. Tana ɗaya daga cikin farar ƙasa mafi shahara a gine-ginen zamani, launikanta sun haɗa da fari, ruwan kasa, ko rawaya. Ana amfani da ita a shimfiɗar bene, gine-ginen zamani da kuma ado ga bangon ciki da waje.

Kowace nau’in farar ƙasa na da siffofi na musamman, da amfanin na daban, inda fahimtar bambancin nau’o’inta na taimakawa wajen amfani da ita ta hanya mafi dacewa.

Amfanin farar ƙasa

Gine-gine da kankare: Farar ƙasa ita ce babban kayan haɗa siminti da kankare, saboda tana ɗauke da calcium wanda yake taimakawa wajen samar da ƙarfi da ingancin gine-gine.

Amfanin masana’antu: Ana amfani da farar ƙasa a masana’antun steel, glass, da paper. Sannan tana taimakawa wajen tsaftace ruwan sha da rage acidity a masana’antu.

Fannin noma: Ana amfani da farar ƙasa a matsayin soil conditioner don rage acidity a cikin kasa, wanda yake inganta amfanin gona.

Kiwon lafiya: Calcium carbonate da ke cikin farar ƙasa yana zama muhimmin sinadari d ke ƙarfafa ƙashi, gashi, da haƙora. Ana amfani da shi a cikin supplements na calcium.

Abubuwan da ke lalata farar ƙasa

Canjin yanayi: Ruwan sama, iska, sanyi da zafi na iya sa farar ƙasa ta lalace a hankali. Ruwan sama  na iya narkar da ita gabaɗaya, ko kuma rage ƙarfinta da kyawunta.

Iska/guguwa: Iska mai ɗauke da ƙura ko yashi na iya shafe saman dutsen farar ƙasa su ɓatar da shi, musamman a wuraren da ke fuskantar iska kai tsaye.

Rushewa: Wasu nau’ukan farar ƙasa na iya rushewa ko narkewa saboda gishiri, musamman idan ana amfani da de-icing salts ko akwai matsalar danshi daga ƙasa.

Tsagewa: Tsagewa na faruwa ne sakamakon nauyi, motsin ƙasa ko amfani da mortar mai ƙarfi fiye da ƙima.

Gishiri: Bayyanar farin gishiri a saman dutsen farar ƙasa alama ce ta motsin gishiri da danshi a ciki, wanda ke nuna matsalar ruwa.

Danshi: Danshi na daga can ƙasa na iya tasowa har a cikin farar ƙasa, ya haddasa taɓo, tsagewa da lalacewa.

Illolin farar ƙasa

Duk da muhimmancin farar ƙasa, tana da illolin da suka haɗa da:

Lalata muhalli da ruwa: Yawan haƙar farar ƙasa na iya lalata ƙasa, rage itatuwa da ciyayi, tarwatsa muhallin dabbobi. Idan ƙurar farar ƙasa ta shiga koguna ko rijiyoyi, tana canja ɗanɗanon ruwan.

Gurɓata iska: A lokacin da ake sarrafa farar ƙasa musamman a ma’aikatar yin siminti, ana fitar da hayaƙi da ƙura, wannan kuma na iya jawo cututtukan numfashi.Shaƙar ƙura ko hayaƙin farar ƙasa na iya haifar da tari da matsalar huhu, ciwon ido da fata.

Illa ga amfanin noma: Yawan farar ƙasa a ƙasa na iya canja acidity (pH) na ƙasa, ya sa wasu amfanin gona su kasa girma. Wuraren da ake haƙar farar ƙasa suna zama ramuka masu muni, suna rage kyan gani da amfani da ƙasa.

A taƙaice, farar ƙasa wani muhimmin dutsen sedimentary ne wanda take taka muhimmiyar rawa a fannin kimiyya, masana’antu, gine-gine, noma, da kiwon lafiya. Tana da sauƙin samuwa a duniya, kuma tana ɗauke da calcium carbonate mai amfani sosai. Fahimtar farar ƙasa da siffofinta a kimiyyance yana taimakawa mutane wajen amfani da ita cikin hikima da kuma kiyaye muhalli.

Manazarta

Types of limestone. (n.d.). SHC Group Vietnam- SHC Techmicom.

U.S. General Services Administration (2016, October 13).. Limestone: Characteristics, Uses and problem. U.S. General Services Administration.

Sharuɗɗan Editoci

Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×