Skip to content

Agriculture

    Aika

    Agriculture, a hausance za a iya fassara shi da “Kimiyyar Noma”, fannin ilimi ne da ke mayar da hankali kan nazarin harkokin noma da sauran ayyukan da suka shafe shi, ta amfani da ilimin kimiyya da kuma ƙwarewar aikace-aikace. Wannan fanni yana haɗe da karatun ka’idojin kimiyya da ayyukan hannu domin koyar da ɗalibai yadda ake shuka amfanin gona, yadda ake kiwon dabbobi, yadda ake sarrafa ƙasa, da yadda ake tace ko sarrafa kayan amfanin gona.

    School farm0 1
    Dalibai ke nan a wata gonar makarantarsu suna koyon aikin gona a aikace.

    A makarantu, wannan fanni yana nufin koya wa ɗalibai ilimin kimiyya baya ga harkokin noma, kamar ilimin halittar tsirrai, tsarin jikinsu, sinadaran ƙasa, da kuma yadda ake yaƙi da cututtuka da ƙwari, tare da ba su ƙwarewar aikace-aikace irin su yin shuka, cire ciyawa, girbi, da amfani da kayayyakin aikin gona.

    Kimiyyar Noma kuma tana koyar da yadda noma ke ba da gudummawa ga tattalin arziki, yadda ake amfani da sabbin fasahohi a noma, da kuma yadda ake yin noma mai dorewa domin kare muhalli ga al’ummomi masu zuwa.

    Manyan rassan Agriculture

    A matsayin fanni na ilimi, Agriculture na da rassa masu yawa da ake nazarin su a makarantu a matakai daban-daban:

    1. Agronomy: Wannan reshe yana koyar da ilimin shuka amfanin gona na filaye da fahimtar ƙasar da suke girma a ciki. Ɗalibai suna koyo game da jujjuyawar amfanin gona, ban ruwa, amfani da takin zamani, da sarrafa ciyawa.

    2. Horticulture: Wannan reshe yana mayar da hankali kan shuka ‘ya’yan itatuwa, kayan lambu, furanni, da tsire-tsire na ado. Ɗalibai na iya koyon aikin nursering, tsirrai da sarrafa gonaki.

    3. Animal Science: Reshe da ke nazarin kiwon dabbobin gona domin nama, madara, ƙwai, fata, da ulu. Ana koyar da yadda ake ciyarwa, haifuwa, gina matsuguni, da hana cututtuka.

    4. Soil Science: Wannan fanni yana fayyace halaye, siffofi, rabe-rabe, yalwa, da yadda ake kula 6 ƙasa. A makarantu, ɗalibai kan tattara samfurin ƙasa domin gwaji.

    5. Agricultural Engineering: Wannan reshe yana koyar da yadda za a yi amfani da kayayyakin aikin gona, injina, tsarin ban ruwa, da wuraren ajiya.

    6. Fisheries and Aquaculture: Wannan ma muhimmin reshe ne na kimiyyar Agriculture. Yana koyar da kiwon kifi, gina tafkuna, ciyarwa, da kamawa, har ma da sauran dabbobin ruwa.

    7. Forestry: Wannan shi ne fannkn nazarin daji. Yana kotar nazarin shuka da sarrafa dazuka, shuka itatuwa, sare bishiyoyi, da kula da namun daji.

    8. Plant Pathology: Wannan reshe ne da yake ba da damar nazarin cututtukan tsirrai. Yana fayyace cututtukan tsirrai, asalinsu, da hanyoyin magance su.

    9. Agricultural Economics: Wannan fage yana amfani da ka’idoji da manufofin tattalin arziki wajen gudanar da harkar noma, ciki har da tsara kasafin gona, rubuta bayanai, da sayar da amfanin gona.

    10. Entomology: Wannan reshen yana nazarin ilimin sanin ƙwari. Yana koyar da nazarin ƙwari musamman waɗanda ke lalata amfanin gona ko yaɗa cuta ga dabbobi, da kuma hanyoyin magance su.

    Muhimmancin Agriculture a makarantu

    Agriculture ba wai kawai yana da amfani a rayuwar noma ba ne, har ma a matsayin fannin ilimi a makarantu domin yana koyar da ɗalibai ilimi da aikace-aikace, wanda zai ba su damar bayar da gudummawa ga fannin noma da ci gaban ƙasa.

    1. Samar da Ilimi da ƙwarewa

    Ɗalibai suna koyon ka’idojin kimiyya game da shuka da kiwon dabbobi, sarrafa ƙasa, maganin kwari, da gudanar da harkar aikin gona. Misali, ɗalibin da ya koyi yadda ake noman tsirrai zai iya samar da shuke-shuken nursery masu kyau don lambun makaranta ko na gida.

    2. Ƙarfafa dogaro da kai

    Ta hanyar koyon ƙwarewar noma, kamar kiwon kaji, sarrafa kayan lambu, da kiwon kifi, ɗalibai na iya fara sana’ar noma tun kafin su gama makaranta. Wannan zai rage zaman banza da dogaro da aikin gwamnati.

    3. Alaƙa da wasu darusa

    Kimiyyar Agriculture tana da alaƙa da darusa kamar Biology, Chemistry, Geography, da Economics. Misali, sanin sinadaran ƙasa yana taimakawa wajen gano irin takin da ya dace da amfanin gona.

    4. Samar da abinci

    Lokacin da ɗalibai suka yi amfani da abin da suka koya, suna ƙara yawan samar da abinci. Misali, aikin gonar makarantar da ya samar da masara na iya ƙara yawan abinci a yankin.

    5. Wayar da kai kan kare muhalli

    Ɗalibai suna koyo muhimmancin noma mai ɗorewa kamar sauya nau’in amfanin gona, amfani da takin gargajiya, da shuka itatuwa domin hana lalacewar muhalli.

    6. Damar samun sana’a

    Karatun kimiyyar Agriculture na iya kai ɗalibi zuwa ga samun ayyukan yi kamar bincike kan noma, ayyukan wayar da kan manoma, kasuwancin amfanin gona, gudanarwa tare da kula da gonaki, da sauransu.

    7. Warware matsaloli

    Kimiyyar noma tana ƙarfafa wa ɗalibai gwiwa su yi tunani mai zurfi kan matsalolin noma, kamar ƙwari ko zaizayar ƙasa, sannan su kuma nemo mafita ta kimiyya.

    8. Ci gaban tattalin arziki

    Ta hanyar samar da ƙwararrun matasa masu gudanar da gonaki ko kasuwancin amfanin gona, Agriculture na taimaka wa ci gaban tattalin arzikin ƙasa ta hanyar samarwa, sarrafawa, da kasuwancin kayan gona.

    Muhimmancin kimiyyar noma ga dukkan al’umma

    Kimiyyar Noma tana da matuƙar muhimmanci a matsayin a fanni na rayuwa saboda tana bayar da ilimi da fasaha da ake buƙata don samar da abinci, albarkatun gona, da kuma kare muhalli. Ga wasu daga cikin muhimmai:

    Samar da Abinci

    Agriculture na koyar da hanyoyin noman amfanin gona da kiwon dabbobi yadda za a samar da abinci mai yawa da inganci ga jama’a. Misali, amfani da tsarin ban-ruwa na zamani da ingantattun iri don samun karin amfanin gona.

    Tattalin arziki

    Noma babban ginshiƙi ne na tattalin arzikin ƙasa. Ta hanyar koyon Kimiyyar noma, ɗalibai suna fahimtar yadda noma ke samar da kuɗin shiga, ayyukan yi, da kuma albarkatun fitarwa ƙasashen waje.

    Cigaban fasaha

    Ta hanyar bincike da ƙirƙira, Agriculture na samar da sabbin hanyoyi da na’urori don sauƙaƙa aikin noma. Misali, injinan shuka da girbi, da kayan sarrafa amfanin gona.

    Inganta lafiyar jama’a

    Ta hanyar samar da ingantaccen abinci, Agriculture na rage yunwa da rashin abinci mai gina jiki, wanda ke taimakawa wajen kiwon lafiya.

    Matsalolin Agriculture a Najeriya

    Agriculture yana da muhimmanci wajen koya wa ɗalibai ilimin noma, kiwo, sarrafa kayan gona da kuma muhimmancin abinci a rayuwa. Amma akwai tarin matsaloli da suke hana darasin samun inganci a makarantu.

    Rashin kayan aikin koyarwa

    Mafi yawancin makarantu ba su da gonar koyarwa, kayan aikin gona kamar fatanya, lauje, matattarar shuka, kayan kiwo, ko kayan gwaje-gwaje. Wannan yana sa darasin ya tsaya a kan nazari kawai ba tare da koyo da hannu (practical) ba.

    Karancin malamai ƙwararru

    Malaman da aka horar musamman kan darasin Agriculture sun yi kaɗan. Wasu makarantu suna ɗaukar malamai daga wasu fannoni su ba su koyar da Agriculture ba tare da cikakkiyar ƙwarewa ba.

    Rashin gonar koyarwa

    Yawancin makarantu a Najeriya ba su da gonar koyarwa. Ko da akwai, ba a kula da ita yadda ya kamata, ba a yin amfani da ita wajen koyo.

    Tsadar kayan aiki da takin zamani

    Kayan aikin gona, iri da takin zamani sun yi tsada sosai, hakan yana sa makarantu ba sa iya saya don yin amfani da su wajen koyarwa.

    Rashin sha’awar ɗalibai

    Wasu ɗalibai suna ganin Agriculture a matsayin darasi mai wahala ko kuma darasi na masu zuwa aikin noma kawai. Rashin nuna muhimmancin fannin a aikace yana rage sha’awa.

    Rashin tallafi daga gwamnati

    Gwamnati ba ta bayar da isasshen tallafi na kayan aiki, horar da malamai, ko samar da gonakin makarantu yadda ya kamata.

    Rashin haɗa darasin da fasahar zamani

    A duniya ana amfani da modern technology a noma, amma a makarantu a Najeriya darasin ya tsaya ne kan tsofaffin hanyoyi kawai. Rashin amfani da kwamfuta, injinan noma da fasahar kiwo yana hana darasin tafiya da zamani.

    Cunkoson ɗalibai a aji

    Yawan ɗalibai a ajin da bai dace da adadin kayan koyarwa ba yana sa ba a iya gudanar da darasi na ainihi yadda ya kamata.

    Rashin ɗakunan gwaje-gwaje

    Makarantu da yawa ba su da dakin gwaje-gwaje (laboratory) na Agriculture. Hakan ya rage wa ɗalibai damar yin bincike da gwaje-gwaje.

    Matsalolin tattalin arziki da yanayi

    Rashin kwanciyar hankali ta fuskar tattalin arziki da matsalolin yanayi (kamar fari, ambaliya, da sauyin yanayi) suna tasiri a wajen koyar da darasin, saboda yawanci darasin yana buƙatar misalai daga ainihin yanayin noma na ƙasa.

    Hanyoyin magance matsalolin Agriculture a makarantu

    Samar da kayan aiki da gonar koyarwa

    Gwamnati da makarantu su samar da gonar makaranta (school farm), wajen kiwo, da kayan aikin noma na zamani. Wannan zai ba ɗalibai damar koyon darasin a aikace ba a baki kawai ba.

    Horar da malamai ƙwararru

    A shirya ƙarin kwasa-kwasai da tarukan horarwa (seminars & workshops) ga malamai. A kuma ɗauki malamai ƙwararru da suka yi karatun Agriculture don koyarwa.

    Samar da kayan aiki masu araha

    Gwamnati ta tallafa wa makarantu wajen samun iri, takin zamani, magungunan kashe ƙwari, da sauran kayan aikin noma a farashi mai sauƙi.

    Ƙarfafa sha’awa ga ɗalibai

    A tsara darusa da nune-nune masu jan hankali, a shirya gasar noma ko kiwo tsakanin makarantu. Hakan zai sa ɗalibai su ga darasin ba kawai karatu ba ne, har da aikin da ke kawo riba da ci gaba.

    Haɗa darasin da fasahar zamani

    A koyar da ɗalibai amfani da fasahar noma ta zamani (agricultural technology), kamar irrigation system, greenhouse farming, hydroponics, aquaculture da mechanized farming. A kuma koyar da su amfani da kwamfuta wajen lissafi da tsara aikin gona.

    Tallafin gwamnati da ƙungiyoyi

    Gwamnati, NGOs, da ƙungiyoyin masu zaman kansu su shiga tallafa wa makarantu da kayan aikin noma, littattafai, da kuɗin gudanar da gonar makaranta.

    Haɗin gwiwa da manoma

    Makarantu su haɗu da ƙungiyoyin manoma a yankin domin ɗalibai su ga aikin noma a zahiri, su yi aikin haɗin gwiwa da manoma.

    Rage cunkoso a aji

    A samar da ƙarin malamai da ƙarin kayan aiki don raba ɗalibai zuwa ƙungiyoyi ƙanana (groups) yayin darusa da aiki a gonar makaranta.

    Ƙarfafa bincike da gwaje-gwaje

    A gina ɗakunan gwaje-gwaje (laboratories) na Agriculture a makarantu. Wannan zai taimaka wa ɗalibai wajen yin bincike da fahimtar kimiyya baya ga aikin noma.

    Daƙile matsalolin yanayi

    A koya wa ɗalibai dabarun zamani na shawo kan sauyin yanayi, kamar yadda ake amfani da takin zamani na bio-fertilizer, maganin kwari na gargajiya, da fasahar adana ruwa.

    Manazarta

    Adeniyi, M. O., et al. (1999). Countdown to Senior Secondary Certificate Examination: Agricultural Science. Ibadan: Evans.

    Akinsanmi, O. (2000). Junior Secondary Agricultural Science. UK: Longman.

    Are, L. A., et al. (2010). Comprehensive Certificate Agricultural Science for Senior Secondary Schools. Ibadan: University Press Plc.

    Falusi, A. O., & Adeleye, I. O. A. (2000). Agricultural Science for Junior Secondary Schools (Books 1–3). Ibadan: Onibonoje.

    *** Tarihin Wallafa Maƙalar ***

    An kuma sabunta ta 18 August, 2025

    *** Sharuɗɗan Editoci ***

    Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

    Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

    Maƙalar ta amfanar?
    EAa

    You cannot copy content of this page

    ×