Skip to content

Aku

    Aika

    Aku (Parrots) na cikin tsuntsaye dangin Psittaciformes. Waɗannan tsuntsaye sun shahara da wayo, ban dariya da kuma basira. Haka nan sun shahara wajen kwaikwayo da koyi sosai, ciki har da yin magana irin ta ɗan’adam da kuma sautuka masu yawa. Aku suna a matsayin dabbobin gida, suna bayar da nishaɗi ta hanyar sautuka da launuka masu ban sha’awa.

    couple blue yellow macaw0 1
    Aku, mata da miji masu launin ɗorawa da shuɗi.

    Kalmar ‘parrot’ da ake ambaton aku a turance, ana kyautata zaton ta samo asali ne tun a farkon ƙarni na 16, daga kalmar Faransanci ‘perrot’. Perrot sauyin suna ne na Peter, wanda a asalin Helenanci ke nufin “dutse” ko “ƙasa mai tauri.”

    Sunan aku a kimiyyance

    Aku na cikin masarautar dabbobi ta Animalia da sashen Chordata. Rukunin Aves ne kuma danginsu shi ne Psittacopassarae. Dangin aku sun kasu zuwa manyan rukuni uku. True parrots ana kiran su da Psittacoidea. Cockatoos parrots kuma ana kiran su Cacatuoidea. Sai kuma New Zealand parrots ana kiran su Strigopoidea. Akwai kusan nau’o’i har guda 400 na aku a duniya.

    Tarihin wanzuwar aku

    Binciken ƙwayoyin halitta ya nuna cewa cockatoos da sauran psittaciforms sun rabu tun kusan shekaru miliyan 65 da suka wuce. Sauran nau’ikan aku sun fara bayyana kusan shekaru miliyan 60–65 da suka wuce lokacin da Australia da New Guinea suka fara rabuwa da Gabashin Antarctica. An kiyasta cewa manyan dangin aku sun kafu tun shekaru miliyan 30 da suka wuce, lokacin da Australia, Antarctica da Kudancin Amurka suka rabu gabaɗaya.

    A bisa shaidar ɓurɓushin halittu da aka daidaita shekaru miliyan 50 da suka wuce, wannan rabuwar ta faru shekaru miliyan 45.04 da suka wuce, jim kaɗan kafin Australia ta rabu da Antarctica. Nau’in aku na yankin Neotropical sun fara haɓaka shekaru miliyan 33 da suka wuce, lokacin da Kudancin Amurka ta rabu da Yammacin Antarctica.

    Shaidu sun nuna cewa asalin aku shi ne Australia saboda yawan jinsunan da ke nan, wasu daga cikinsu suna kusa da tushen bishiyar psittaciform. Haka kuma, rabuwar nau’o’in New Zealand parrots shaida ce cewa asalin su a Gondwana ne a lokacin Cretaceous. Cockatoos rukuni guda ne na monophyletic, amma yawancin aku polyphyletic ne. Babu alaƙa mai bayyana tsakanin wasu nau’o’in aku da sauran tsuntsaye na zamani.

    Nau’o’in aku da aka fi sani

    • Grey Parrot: Wannan matsakaiciyar aku ce daga Afirka. Launinta ruwan toka ne da baƙi a baki da ja a wutsiya.
    • Macaw: Wannan nau’i na aku na da tsawon inci 12, mafi ƙanƙanta zuwa babba babba mai tsawon inci 40. Asalinsu daga Mexico, Amurka ta Tsakiya da Kudanci. Suna da dogayen wutsiya da manyan baki.
    • Cockatiel: Ƙananan ne daga Australia, suna da dogayen wutsiya. Ajiya ta nuna launuka daban-daban, amma na daji suna da launin ruwan toka da farin ɗigo a jikin fuka-fuki da kuma ja a gefen fuska.
    • Budgerigar: Wannan nau’i ana kiran su parakeet. Ƙananan ne masu doguwar wutsiya. Su koraye ne masu haske da rawaya a kai da layin baƙi a fukafukansu. Asalinsu daga Australia ne.
    • Amazon Parrot: Matsakaiciya ce, mai gajeriyar wutsiya, asalinta daga Kudancin Amurka, Tsakiyar Amurka da Caribbean. Launinta kore ne da haɗin wasu launuka masu haske, ya danganta da nau’in.

    Siffofi da halayen aku

    Aku suna da launuka masu ƙayatarwa, kowanne jinsin da nasa launin. Mutane da dama sukan ɗauke su a matsayin tsuntsaye masu launin kore da baƙi mai duhu. Aku suna tsayuwa sosai, sukan riƙe fuka-fukansu ko kuma su yi tafiya a ƙasa da ƙafafu.

    Ba dukkan jinsunan ne launi ɗaya ba, kamar macaw, tana da launuka mabambanta. Macaw da yawancin aku ba sa nuna bambanci tsakanin mace da namiji, amma wasu nau’o’i kamar Eclectus suna nuna bambanci sosai.

    A halayensu, sukan kasance masu nuna ƙauna da soyayya, dalilin da ya sa aka riƙe su a matsayin dabbobin gida tsawon ƙarnuka. Duk da haka, ƙarfinsu ya fi ƙarfin masu kiwon dabbobi da ba su da ƙwarewa. Sukan nuna tausayi sosai. Amma yadda mutane ke mu’amala da su yana taka muhimmiyar rawa ga yanayinsu.

    Akwai wasu jinsunan da za su iya zama masu haɗari da tashin hankali idan aka razana su. Misali, Senegal parrot ƙarama ce amma za ta iya cizo da ƙarfinta har ta jawo ciwo mai tsanani idan ta shiga haɗari.

    Yawancin lokaci, aku ba sa kai hari sai idan suna cikin yanayin haɗari, a matsayin kariya ta dabi’a. A cikin gida ko gidan namun jeji (zoo), sukan zubar abinci ko fasa keji idan suka fusata ko suka ji tsoro. Aku suna da hayaniya sosai, suna yin waƙa da magana da yamma da dare, suna kuma kwaikwayon sautuka.

    Aku masu dabbobi ne masu hankali sosai. Idan aka kiwata su a gida, suna haɗa zumunci da masu su. Suna son kasancewa kusa da jama’a a cikin gida, suna gina amintaccen zumunci na dogon lokaci.

    Muhallin da aku ke rayuwa

    Aku sun fi dacewa da wuraren da ke da zafi da danshi. Amma ba dole ne sai wannan muhallin ba, saboda haka ana samun su a wuraren masu zafi a duniya. Asalinsu daga Australia, Kudancin Amurka da Tsakiya.

    A daji, aku suna gina gidajensu a bishiyoyi masu faɗin ganye da tsirrai masu kyau, amma na kiwatawa a gida suna iya daidaita da duk inda ake kiwon su.

    Abincin aku

    Aku dabbobi ne masu cin komai wato (omnivorous). A matsayinsu na dabbobin gida, abincinsu ya kamata ya yi kama da na daji: kayan lambu ɗanye ko dafaɗɗe, ’ya’yan itatuwa, goro, tsaba, da hatsi. Idan akwai, abinci na organic ya fi dacewa don guje wa sinadarai masu haɗari.

    Yawancin abincin aku sun haɗa da ’ya’yan itatuwa, goro, tsaba, furanni da ƙwai. Wasu nau’o’i suna rayuwa da nectar (darɓa) kaɗai. Suna cin kayan lambu ɗanyu ko dafaffu, kuma wani lokaci suna cin ƙwari, tsutsotsi, ɓeraye ko ƙananan macizai idan ba su sami ƙwari ba.

    Barazanar da aku ke fuskanta

    Aku sukan zama abinci ga manyan tsuntsaye masu farauta. Amma babbar barazanarsu ita ce mutane. Ayyukan mutane kamar sare dazuzzuka, mamaye muhalli da masana’antu suna lalata wuraren da suke. Wannan yana jawo asarar abinci da rashin daidaito a haihuwa da girmansu.

    Kusan kashi uku bisa uku na nau’o’in aku suna cikin barazanar ƙarewa. Ayyukan ɗan’adam ne mafi yawa ya jawo hakan sare dazuzzuka, rarraba wurare, kamawa da sata daga cikin shekarsu. Sauran matsalolin sun haɗa da sauyin yanayi, cututtuka da gurbatar muhalli.

    Ana kama aku daga daji a sayar a matsayin dabbobin gida. Kusan kashi 80% na waɗanda aka kama suna mutuwa kafin su isa kasuwa saboda cuta, yunwa ko rauni. Ana sare bishiyoyi don kama su, abin da ke lalata muhallinsu da sauran dabbobi.

    Haihuwa da tsawon rayuwar aku

    Yawancin aku suna zama da miji guda ɗaya. Suna rayuwa tare da shi har lokacin da ba sa cikin zangon haihuwa. Sun fi so su haihu a lokacin zafi, musamman a bazara saboda akwai abinci mai yawa. A lokacin, suna sakin ƙwayoyin hormones na jima’i, suna jan hankalin juna don haihuwa.

    Suna saka ƙwai guda 2 zuwa 8, kuma suna yin kwanci tsawon kwanaki 18 zuwa 30 kafin ƙyanƙyasa. Ƙananan nau’o’in aku suna rayuwa shekaru 15 zuwa 20, amma manyan nau’o’i suna iya rayuwa har tsawon shekaru 80. Wasu nau’ikan an bayyana cewa sukan rayu shekaru 100.

    Yawan aku a duniya

    Adadin aku a duniya na da wuyar bayyanawa daidai, amma ana da fiye da nau’o’i daban-daban har guda 350, ciki har da macaw, grey parrot da monk parakeet. Farauta da lalacewar muhalli ya jawo kusan rabin nau’o’in aku shiga cikin haɗarin ƙarewa a duniya. Misali, citron-crested cockatoo ana sayar da su sosai a kasuwannin ba bisa ƙa’ida ba har gwamnati ta ɗauki matakan hanawa a wasu ƙasashe.

    Basirar koyon abubuwa

    Aku suna iya furta kalmomi da ma’anarsu, suna faɗar jimloli masu sauƙi. Wannan hali na gama-gari ne a cikin tsuntsaye masu basira kamar crows da ravens. Aku ana ɗaukar su a matsayin tsuntsaye mafi basira, saboda girman ƙwaƙwalwarsu daidai da ta birai masu wayo. Maimakon cerebral cortex, ƙwaƙwalwarsu na amfani da mediorostral HVC wajen tunani.

    An fahimci basirar aku ne ta hanyar gwaje-gwaje na kimiyya, amfani da harshe, kayayyakin aiki da warware matsaloli. Koyo tun suna ƙanana yana da muhimmanci, kuma hulɗar zamantakewa na taimakawa sosai. Suna yin wasa da ’yan’uwansu ko sauran tsuntsaye, suna haɗa zumunci  tsakanin masu su.

    Manazarta

    Nolan, S. (2025, March 21). Everything you need to know about parrots – BirdLife International.

    Staggs, J. (2018, March 12). Ten reasons you shouldn’t get a parrot. VIE Magazine.

    The Editors of Encyclopaedia Britannica. (2025, July 30). Parrot | Description, Types, & Facts. Encyclopedia Britannica.

    WPTSuperAdmin. (2025, March 20). Encyclopaedia. World Parrot Trust.

    *** Tarihin Wallafa Maƙalar ***

    An kuma sabunta ta 10 September, 2025

    *** Sharuɗɗan Editoci ***

    Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

    Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

    Maƙalar ta amfanar?
    EAa

    You cannot copy content of this page

    ×