Matashin jarumin da ludayinsa ke kan dawo a masana’antar shirya fina-finai ta Hausa (Kannywood). Goggagen jarumi, mai ƙwarewa ta fannoni da daban-daban na gudanar da rayuwar yau da kullum. Kamar yadda ya yi shura ta fanin sunansa Sarki Ali (The King). Gidajen jaridu da dama kamar BBC Hausa sun bayyana cikakken sunansa da Ali Nuhu Muhammad.
Haihuwarsa
An haifi Ali Nuhu a ranar 15 ga watan March a shekarar 1974 a Maiduguri, Jihar Borno, ya girma a jihar Kano, iyayen sa kuma ƴan Balanga ne a jihar Gombe dake arewacin Nigeriya. Shekarun sa 50, domin a ranar 15-3-2024 ya cika shekara 50, abokan sana’arsa sun ta ya shi murna sosai.
Karatunsa
Ali Nuhu ya karanci geography a jami’ar Jos wato “University of Jos” a turance.
Laƙaninsa/Inkiyarsa
Mutane suna yi masa inkiya da “Sarki Ali Nuhu/ King of kannywood, wanda a ƙalla zuwa yanzu ya fito a fina-fina sama da 500+ wanda ya samu lambobin yabo da dama. Domin ko a shekarar da ta gabata sai da ya samu lambar yabon “best actor award in the Nollywood Europe Golden Award (NEGA 2023)”. Wani ƙarin armashi shi ne muƙamin da shugaban ƙasa ya ba shi na matsayin shugaban film na najeriya baki ɗaya. Wanda hakam ya farantawa duk wani ɗan kannywood domin suna kyautata masa zaton kawo ci gaba na musamman. An yi itifaƙin ɗan Arewa bai taɓa samun matsayinsa sai a kansa.
Ƙabilarsa
Ali Nuhu ba Bahaushe kamar yanda wasu ke fada ya fito daga ƙabilar “WAJA”. cikakken sunan mahaifinsa shi ne “NUHU EMANUEL POLOMA”
Girmansa
Shafin wikipedia ya bayyana cewa; Ali Nuhu ya girma a hannun mahaifiyar sa a jihar Kano bayan sun rabu da mahaifinsa sakamakon bambancin addini, mahaifiyar sa ta rasu a shekarar 1999 shi kuma mahaifinsa ya rasu a shekarar 2020, a halin yanzu Ali Nuhu yana bin addinin Musulunci kamar mahaifiyar sa.
Aikinsa
Ali Nuhu jarumi ne, marubuci, mai ba da umarni kuma furodusa a masanatar shirya fina-finai ta kannywood da Nollywood. Sannan kuma yakan yi rawa a wasu fina-finai.
Ali Nuhu yakan yi fina-finan sa cikin harshen Hausa da turanci, sannan kuma yana cikin manyan jarumai da suka kafa masana’antar shirya fina-finai ta kannywood.
Ya fara harkar finafinai tun a shekarar 1999 wato shekarar da mahaifiyar sa ta rasu da wani fim mai taken “ABIN SIRRI NE” ya kuma fito a fina-finan masana’antar shirya fina-finai ta kudancin Nigeria NOLLYWOOD irin su Tout too, The Ghost, The Millions and Diamonds in the Sky, da dai sauransu.
Iyalinsa
Jarumin yana da aure mata ɗaya mai suna Maimunatu da kuma yara biyu Ahmad da Fatima.
Abokansa
Duk wanda ya san Ali Nuhu a duniyar kannywood ya ta so ya same shi da Ahmad S Nuhu da kuma Babbale Hayatu. Wanda tsantsar shaƙuwarsu da marigayi Ahmad ne ya sa shi yi masa takwara da ɗan wurinsa Ahmad a wata majiya da wasu shafukan suka bayyana. Babbale Hayatu kuwa, har zuwa yanzu suna tare, duk da sauyi da wadata da muƙamai da suka mammaye rayuwar jarumin bai zubar da abota ba. Sai dai a kwanakin nan yadda hotunansa suke yawan yawo tare da ƙananun faifan majigi da Abba Almustaph mu kan iya cewa ya samu ƙarin abokin da alaƙarsu ta bayyana a idanun duniya. Sai dai kuma akasari majigin ko hoton ya kan fita ne su uku. Babbale Hayatu. Abba Almustapha da kuma Ali Nuhun. Haka kuma cike da mutuntawa bakin Abba Roda ke furta,
“Yaya Babbale an yi kaza”
Wato dai tsohuwar zuma na nan a gurbinta. Akwai wani abu da Baushe ke cewa, nuna mini abokinka ni kuma zan nuna maka ko kai wane ne kai, idan muka duba wannan ta kowace fuska za mu iya yi masa kyakkyawar shaida, domin mutanen biyu dake kewaye da shi suna da kyakkyaear shaidar mu’amala.
Wata majiya ta bayyana cewa akwai alaƙa mai ƙarfi tsakaninsa da matashin ɗan ƙwalon ƙafar nan wato Ahmad Musa. A wata faɗar an tabbatar da shi ne yake kula da duk wani abu mai muhimmanci nasa a ƙasar idan ba ya nan. Haka kuma wata majiyar na ba da tabbacin yaronsa Ahmad na tare da shi yana horar da shi abin da ya shafi ƙwallon ƙafa.
Mu’amalarsa
Jarumi Ali Nuhu mai kyakyawar mu’amala ne tsakaninsa da abokan kasuwancinsa. Wani abu mai jan hankali shi ne, yadda abokan sana’arsa suka yi ta tururuwar taya shi murnar samun muƙaminsa. Haka kuma ranar murnar haihuwarsa da ta gabata akwai waɗanda suka dinga ta ya shi murna da kiransa da sunaye mabambanta wanda kyautata mu’amala ne kaɗai zai gadar da hakan. Misali: M Sharif ya kira shi da King. Minal Izzar So da Momi Gombe sun kira shi sa Father. Saƙo mai cike da mutuntawa da ɗaukar hankali kalaman mutuntawa su ne na Maryam Both. Ta kirashi da sunaye na martabawa kuma cikin mutuntawa.
Takatsan-tsan
Ali Nuhu mutum ne mai matuƙar takatsa-tsan da kuma tsare gida da kiyaye martabar kai. Da wuya ka same shi ana cece ku ce da shi kan wata sabga ta harkar ‘yan fim. Ba ya ɗaya daga cikin masu tsoma baki kan abin da bai shafe shi ba. Kamar yadda sauran abokan sana’arsa ke yi na fitowa su yi martani idan wani abu ya faru. Hasalima ko a kansa aka yi magana shiru ita ce take zama amsarsa.
Taimako
Yana daga cikin mutane masu tallawa na ƙasa da shi da ɗago zuwa sama musamman a harkar fim da kuma fuskar rayuwa. Ni ɗin nan jiyau ce kuma ganau. Akwai wata jaruma da ta taɓa yin harkar film ‘yar gaban unguwarmu ce kaɗan, ƙanwarta na zuwa gidan mu kitso sa’i da lokaci. Ta yi shura a lokacinta, a bakin ƙanwarta na taɓa jin tana ba da labari Ali Nuhu ne ya ba yayarta shawara ta yi aure. Kuma ya taɓa biyawa mahaifinsu kuɗin asibiti. Yana ɗaya daga cikin masu yin kyauta ba tare da hagunsu ta sani ba.
Ƙalubalensa
Ƙalubale mafi ƙoluluwa a rayuwarsa shi ne, yadda mutane suke yawan magana kan kasancewarsa da mace guda ɗaya tilo, sai dai har zuwa wannan lokacin ba a taɓa jin bakinsa ya tanka ba game da hakan.
Manazarta
Contributors to Wikimedia projects. (2024, April 20). Ali Nuhu. Wikipedia.
Shonekan dai lauya ne da kasar Ingila ta horar da shi, masanin masana’antu, kuma tsohon shugaban kuma Manajan Darakta na… Read More »Cif Ernest Shonekan