An haifi hamshakin ɗan kasuwa Alhaji Aliko Ɗangote a ranar 10 ga Afrilu 1957 a cikin birnin Kano da ke Arewacin Najeriya. Mahaifinsa shi ne Mohammed Dangote da mahaifiyarsa Hajiya Mariya Dangote. Mahaifinsa ɗan kasuwa ne, yayin da mahaifiyarsa ta kasance jika ga babban ɗan kasuwa Alhaji Alhassan Ɗantata. Dangote ya yi aure sau biyu kuma yana da ‘ya’ya mata uku da kuma ɗan riƙo.
Shi ne ya assasa kuma shugaban kamfanin Dangote Group, wanda ke kan gaba a masana’antu a yammacin Afirka, ya yi matukar tasiri ga tattalin arzikin Najeriya, ta yadda ake gudanar da harkokin kasuwancinsa, tun daga samar da siminti zuwa sarrafa abinci.
Aliko Dangote yana zaune ne a birnin Lagos na Najeriya, kuma ya mallaki jiragen sama guda biyu. Yana da ɗabi’ar jajircewa a kan aikinsa, yana aiki sa’o’i 12 a rana, kuma yana kula da yanayin motsa jiki.
Ɗangote ya shahara sosai da ayyukan jin ƙai, tare da haɗin gwiwar gidauniyar Bill & Melinda Gates wajen kiwon lafiyar jama’a da bayar da gudummawa don yaƙar cutar Ebola, tallafa wa ‘yan Najeriya da rikicin Boko Haram ya shafa, da yaƙi da COVID-19. A fagen kwallon kafa ma, Dangote ya bayar da tukuicin kuɗi ga ‘yan wasan kwallon kafar Najeriya da suka zura kwallo a raga a gasar cin kofin Afrika.
Karatunsa
Ya fara karatunsa a Madrasa Sheikh Ali Kumasi, inda ya kammala karatun firamare, sai ya wuce makarantar Capital High School da ke Kano, da kuma Kwalejin Gwamnati da ke Birnin Kudu. Daga nan ya ci gaba da karatun digiri na farko a fannin kasuwanci da harkokin gudanarwa a jami’ar Al-Azhar da ke birnin Alkahira na ƙasar Masar.
Harkokin kasuwanci
An rawaito cewa sha’awarsa ga harkokin kasuwanci ta fara ne a lokacin da yake makarantar firamare a Kano, inda yakan sayi katan-katan ɗin alawa yana sayarwa tare da samun riba.
Dangote ya kafa rukunin kamfanonin Dangote a matsayin ƙaramin kamfani na kasuwanci a shekarar 1977. A tsawon shekaru, ya faɗaɗa kamfanin zuwa babban kamfani na masana’antu a Najeriya. Kamfanin Dangote ya samar da sana’o’i daban-daban da suka haɗa da masana’antar Dangote Sugar da Dangote Cement da Dangote Flour da masana’antar gishiri da jigilar da shinkafa da kifi da taliya har ma da taki. Har ila yau, kamfanin yana fitar da auduga da goro da cocoa da riɗi da citta zuwa ƙasashe da dama. Bugu da ƙari, Dangote yana da manyan jari a ɓangaren gidaje da bankuna da harkar sufuri da masaƙu da gidajen mai da iskar gas.
Nasarorin kasuwancinsa
Dangote ya samu gagarumar nasara a harkokin kasuwanci a tsawon shekaru.
- Daya daga cikin manyan nasarorin da Dangote ya samu shi ne haɗa hannu da kamfanin Stellantis don kafa cibiyar haɗa Peugeot a Najeriya, wadda ke ƙera motocin Peugeot.
- Ya zama hamshakin attajiri na farko a Najeriya a shekarar 2007, ya kuma ƙara dala biliyan 9.2 a cikin dukiyar sa a shekarar 2013, inda ya zama na 30 a duniya a lokacin.
- Kawo watan Yunin 2022, an kiyasta dukiyarsa ta kai dalar Amurka biliyan 20, wanda hakan ya sa ya zama mutum mafi arziki a Afirka.
- Ya kuma ƙaddamar da matatar man Dangote da ke Lekki a Najeriya da nufin fitar da rarar man fetur da dizal, wanda hakan zai sa Najeriya ta zama cibiyar fitar da man fetur zuwa ƙasashen waje.
- Dangote ya kuma taka rawar gani a siyasar Najeriya. Ya taka rawar gani wajen bayar da tallafin kudi na sake tsayawa takarar shugaban kasa Olusegun Obasanjo a shekarar 2003.
- Ya kuma ba da gudunmawa ga Masallacin ƙasa da ɗakin karatu na fadar shugaban kasa.
- Shugaba Goodluck Jonathan ya naɗa shi shugaban wani kwamiti na tattalin arziki a shekarar 2011.
Ɗangote ya yi tunanin tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 2019, amma sai ya fasa, ya shiga kwamitin ba da shawara na musamman kan yaƙin neman zaɓen Muhammadu Buhari.
Lambobin yabo da karramawa
- An ba shi kyautar Grand Commander of the Order of the Nigeria (GCON), lambar yabo mafi girma a Najeriya.
- Har ila yau, an ba shi kyautar Forbes na Afirka a shekarar 2014 kuma an sanya shi cikin jerin mutanen da suka fi tasiri a duniya na mujallar Time da Bloomberg Markets.
- Dangote yana zaman mamba da muƙamai na jagoranci a kungiyoyi irin su Corporate Council on Africa da United Nations Secretary-General’s Global Education First Initiative da Clinton Global Initiative da kuma World Economic Forum.
Takaitattun bayanai game da Ɗangote
- Ya fara sana’arsa ne da rancen Naira 500,000 (kimanin $3,000) daga hannun kawunsa.
- Dangote masanin kimiyya ne kuma yana jin harsunan Hausa, Ingilishi, Larabci, da Faransanci.
- Mutum ne mai kishin addinin Musulunci kuma ya bayar da gudunmawa sosai a harkokin addinin Musulunci da suka hada da gina masallatai da bayar da gudunmawa ga kungiyoyin agaji.
- Dangote mai sha’awar wasanni ne kuma ya mallaki kungiyar kwallon kafa ta Dangote. Ya kasance wanda ya samu kyautar gwarzon ɗan kwallon Afrika na Forbes, wanda ya lashe a shekarar 2014.
- Dangote dai ya shahara wajen ayyukan jin kai, kuma ya bayar da gudummawar miliyoyin daloli ga wasu abubuwa da suka hada da ilimi, kiwon lafiya, da kuma rage raɗaɗin talauci.
Ƙalubalen kamfanin Ɗangote
Rukunin kamfanonin Dangote na fuskantar kalubale da dama da suka hada da:
- Sufuri: Kanfanin simintin Ɗangote na fuskar ƙalubalen da suka shafi zirga-zirgar siminti kamar yawan shingen binciken ababen hawa da rashin kyan hanyoyi da matsalar fashi da makami da haɗɗura da yawaitar cunkoson ababen hawa.
- Yanayin tattalin arziki: Yanayin tattalin arziki a Afirka, wanda ke tattare da rashin tabbas da ƙarancin aikin yi da ƙarancin jari da rashin kwanciyar hankali da matsalolin siyasa na haifar da ƙalubale ga ayyukan kamfanin Dangote.
- Matatar mai: An samu jinkiri a ci gaban matatar ta hanyar jan-ƙafa a aikin sakamakon rashin aiwatar da manufofi da kuma zargin rashin adalci daga masu ruwa da tsaki na cikin gida da na waje.
- Samar da danyen mai: Matatar man na shan wahala wajen samo ɗanyen mai daga manyan kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa (IOCs) kuma tana fuskantar farashi mai tsada.
- Faɗuwar darajar Naira: Dangote ya ayyana faduwar darajar Naira a matsayin babban ƙalubalensa a shekarar 2023.
Manazarta
Aliko Dangote. (n.d.). Forbes.
Aliko Dangote – Welcome to Dangote Cement Plc. (2022, April 7). Dangote Cement Plc.
Dictionary of African Biography. (2011). In Oxford University Press eBooks.
Sparks, K. (2024, September 11). Aliko Dangote | Biography, businessman, group, foundation, & Facts. Encyclopedia Britannica.