Skip to content

Aminu Alhassan Dantata

Alhaji Aminu Dantata hamshakin dan kasuwa ne ɗan Najeriya kuma mai taimakon jama’a wanda yana ɗaya daga cikin masu tallafawa gidauniyar jihar Kano, gidauniyar bayar da tallafi da tallafawa harkokin ilimi da bayar da tallafi ga ƙananan ‘yan kasuwa a Kano. Shi ne shugaban rukunin kamfanonin da ke kula da kadarorinsa da sauran harkokin kasuwanci. Dantata shi ne wanda ya kafa Kamfanin Mai na Express Petroleum & Gas Ltd kuma ɗaya daga cikin masu shirya Bankin Ja’iz a Najeriya. A 1978, ya kasance memba na National Movement, kungiyar da daga baya ta rikiɗe zuwa jam’iyyar National Party of Nigeria. (NPN)

Haihuwarsa

An haifi marigayi Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata a ranar 19 ga watan Mayu na shekarar 1931, a cikin birnin Kano da ke arewacin tarayyar Najeriya. Mutum ne mai kunya da ƙarancin nuna kai a kafafen yada labarai, hamshakin attajirin, wanda ya shafe sama da shekaru 70 yana harkokin kasuwancin, suka shafi kasuwanci, gine-gine, kadarori, banki, masana’antu, mai da iskar gas, ba a bayyana shi sosai a kafafen watsa labarai, saboda ya ƙi amincewa da bukatar yin hira da manema labarai har kusan ƙarshen rayuwarsa.

Tarihin gwagwarmayar rayuwa

Dantata haifaffen gidan marigayi Alhaji Alhassan Dantata ne, shi ne ɗa na goma sha biyar a cikin‘ya’ya goma sha bakwai da aka haifa a gidansu. Daga shekarar 1938 zuwa 1945 ya yi karatunsa a makarantar firamare ta Dala sannan ya kammala karatunsa ta hanyar karatun gida a wata makaranta mai zaman kanta da mahaifinsa ya gina a shekarar 1949. Bayan ya kammala karatunsa ya shiga harkar kasuwancin da ya wayi gari a ciki, ya fara aiki a kamfanin nasu na Alhassan Dantata & Sons a 1948 a matsayin mai sayar da kayayyaki sannan kuma daga baya ya yi aure. A shekarar 1955 ya zama manajan kasuwancin kamfanin na gundumar Sokoto.

Alhaji Dantata and Shetimma
Marigayi Alhaji Aminu Ɗantata tare da mataimakin shugaban kasar, Kashim Shetima.

”A cikin dukkan mutanen da na sani, da ƙyar idan zan iya kirga mutane 10 da suke raye ba. A cikin dukkan dangina da ’yan’uwa maza da mata, ni kaɗai ne har yanzu da rai. Kuma abokaina da muka girma tare, ba na tsammanin akwai mu fiye da uku. Kamar yadda nake a yanzu, ina jiran lokaci na ne kawai. Ba zan ƙara jin daɗin rayuwa ba.” A cewar dattijon marigayin.

Duk da yanayin rayuwarsa da yawan shekaru kafin ya rasu, wani abu da ya fito fili shi ne cewa duk da ya tsufa ɗin ƙwaƙwalwarsa tana aiki, ya kasance yana ba da labarin abubuwan da suka faru daga shekarun 1950 da kuma bayan haka cikin sauƙi. Tun a shekarar 1956, ya ziyarci kowace babbar ƙasa a duniya, ciki har da Australia, Indiya, Sin, Brazil, Yugoslavia, Rasha da dai sauransu. A shekara ta 1961, ya gama zagaye na dukan ƙasashen Larabawa da Isra’ila.

Marigayin, a wani lokaci da ya shuɗe ya bayyana cewa, “Duk lokacin da muka tafi ƙasar Saudiyya aikin hajji a farkon shekarun 1950 zuwa 1960, hukumomin Saudiyya za su yi duk mai yiwuwa don jinkirin dawowar mu saboda suna son mu ƙara kwana a kasarsu. Manufarsu a nan ita ce, idan muka daɗe a ƙasar za mu ƙara kashe kuɗaɗe, kuma hakan zai ƙara musu kuɗin shiga. Sukan riƙe fasfo dinmu da sauran takardun balaguro na wasu ‘yan kwanaki bayan kammala aikin hajji”

Harkokin kasuwanci

Shekarar 1955 ita ce lokacin da mahaifinsa ya rasu kuma daga baya aka raba hannun jari ga ‘ya’yan. A shekarar 1958, Dantata ya zama mataimakin manajan darakta na kamfanin tare da yayansa Ahmadu, shi ne.manajan darakta. Lokacin da Ahmadu ya rasu a shekarar 1960, Aminu Dantata ya zama shugaban kamfanin.

A tsawon shekaru da dama da suka shuɗe, Aminu Dantata ya faɗaɗa harkokin kasuwanci da ayyukansa zuwa sassa daban-daban na harkokin siyasa da tattalin arzikin Najeriya. A farkon shekarun 1960, Dantata yana da kamfanin gine-gine wanda ya samu goyon baya daga gwamnatin Najeriya, an ba wa kamfanin kwangilar gina wani ɓangare na Makarantar Sufurin Jiragen Sama a Zariya. A shekarar 1961, yana cikin wasu ‘yan kasuwa guda uku a matsayin wani ɓangare na kungiyar masu fafutuka ta fuskar tattalin arziki guda 23 a duniya, wato manufa ta farko a duniya da wata gwamnati mai zaman kanta ta aiko a Najeriya.

A shekarar 1964, ya kasance daga cikin shugabannin kwamitin gudanarwa na bankin bunkasa masana’antu ta Najeriya. A shekarar 1968, aka naɗa Dantata Kwamishinan Raya Tattalin Arziki, Ciniki da Masana’antu na Jihar Kano a karkashin gwamnatin Audu Bako, ya riƙe muƙamin har zuwa 1973.

A lokacin tsarin wanzuwar tsarin kasuwanci na Indeginasation na shekarun 1970s, rukunin kamfanin Dantata ya sayi hannun jari tare da riƙe manyan hannayen jari a kamfanonin Mentholatum, SCOA, Funtua Cotton Seed Crushing Co da Raleigh Industries.

Daga cikin irin abubuwan da ke bakanta wa Aminu Ɗantata shi ne yadda tattalin arzikin ƙasashen yammacin duniya ya bunƙasa da kuma yadda ƙasashensu suka ci gaba daga albarkatun Afirka.

A matsayinsa na wanda ya ga al’ummomi da dama da kuma yadda zamani da mutane suka canza, Marigayi Alhaji Aminu Dantata ya damu da irin halin da al’umma ke ciki a yau. Wani abin da ya riƙa ci wa hamshakin attajirin tuwo a kwarya shi ne rugujewar masana’antu ba a jihar Kano kaɗai ba, har ma a Arewacin Najeriya baki ɗaya.

Ya koka da yadda aka rufe daruruwan masana’antu tsakanin Kano da Kaduna, wanda ya jawo asarar ɗaruruwan ayyukan yi. Ya alakanta lamarin da rashin kwazo na ‘yan kasuwa. Ya tabbatar da cewa yana da hannun jari a kusan dukkanin masana’antun da suke gudanar da harkokin ƙasar nan, da kuma duk wani kamfani da ya yi aiki a Kano ko Kaduna cikin shekaru 20 da suka gabata.

Adadin yawan duniyar Aminu Ɗantata

Duniyar Aminu Ɗantata a ƙiyasin shekarar 2023 ta kai dala biliyan 1. Dantata ya karɓi ragamar shugabancin kamfanin Alhassan Ɗantata and Sons a shekarar 1960. Wanda mahaifinsa ya kafa a matsayin kamfanin sayar da kayan masarufi da gyaɗa da goro da sauran wasu kayayyaki, daga baya Dantata ya zuba jari a wasu kamfanoni na ƙasashen waje dake aiki a Najeriya. Yana cikin manyan attajirai a Najeriya

Tsakanin shekarun 1960 zuwa 1980, ya buɗe wasu sassa na kamfanin kamar haka: Ɓangaren gine-gine  wanda kwangilolin da ya aiwatar kawo yanzu sun haɗa da gina makarantar sojoji da ke Kaduna (Defence Academy, Kaduna), har zuwa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da makarantar horar da jiragen sama a Zariya. Sashen kasuwanci da aka kafa a tsakiyar shekarun 1970 na cinikin kayan gini a Arewacin Najeriya. Wato Northern Amalgamated and Marketing Company Limited, wannan rukunin yana da manyan sassa guda biyu, sashin samar da taki ga gwamnatoci da sashin fasaha da ke samar da kayan gini na Barford.

Kamfanin ya kula da wani yanki wanda ke riƙe da dillancin kamfanin motoci na Mercedes Benz da kuma wani sashen wanda ke kula da tashar jiragen ruwa ta Warri. Ya zuwa shekarun 1990, kamfanin ya gyara sunansa ya koma Dantata Organization tare da ƙarin saka hannun jari a aikin haƙo mai ƙarƙashin kamfanin Express Petroleum.

Dantata ya bayar da gudummawar kuɗaɗen da gine-gine ga cibiyoyi daban-daban da ke kewayen Kano. Ya bayar da gudummawar cibiyar Alhassan Dantata Haemodyalysis ga asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano. Ya kasance Shugaban Jami’ar Al-Qalam na farko da ke Katsina. Mutum ne mai alfahari da jama’a a jiha ta biyu mafi yawan al’umma a Najeriya.

Harkokin siyasa

Dantata ba ya ɗaukar kansa a matsayin ɗan siyasa, amma yana gogewa ta siyasa. Ya taɓa zama ɗan majalisar tarayya a Kaduna a jamhuriya ta farko. Bayan sojoji sun hambarar da gwamnati sai ya dawo Kano, kuma marigayi Audu Bako, gwamnan Kano a lokacin mulkin soja na Janar Yakubu Gowon ya naɗa shi kwamishina a majalisarsa.

67b268c490d284870
Tsohon shugaban ƙasa Janar Muhammadu Buhari tare da marigayi Alhaji Aminu Ɗantata.

A lokacin da aka kafa jamhuriya ta biyu wadda ta samar da marigayi Alhaji Shehu Shagari a matsayin shugaban ƙasa, Dantata ya bayyana cewa wasu fitattun mutane sun tuntuɓe shi domin ya tsaya takarar shugaban kasa. Haka kuma wasu mutane kamar marigayi Malam Aminu Kano, sun yi kira gare shi da ya tsaya takarar gwamnan jihar Kano. Sai dai dukkan waɗannan taye-taye ya watsar da su. Dalilin hakan kuwa abu ne mai sauƙi, kamar yadda marigayin ya bayyana a wani lokaci gabanin ya rasu. “A matsayina na ɗan kasuwa mai dimbin nauyi, na yi imani Allah ya riga ya zaɓar mini sana’a, ta yadda zan taka rawa wajen ci gaban jihata da ƙasa da kuma bil’adama baki ɗaya”.

A ɗaya daga cikin ra’ayoyinsa a lokacin da ya karɓi baƙuncin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, kafin ya zama mataimakin shugaban ƙasar, wato Kashim Shettima, tare da tawagarsa a wani katafaren gidansa da ke Koki Quarters a cikin birnin Kano, hamshakin attajirin ya yi wata magana wadda da yawan jama’a ke kallon ta a matsayin ‘mai zurfi fiye da yadda ake zato.

Marigayin ya faɗa wa mataimakin shugaban ƙasar cewa, “ya daina jin daɗin rayuwa kuma yana jira ne kawai lokacin da zai bar duniya ya riske shi.” Ya ƙara da cewa, ”ya yi imanin cewa ya yi duk abin da ya kamata ya yi kuma ya zagaya kowace jiha a cikin tarayyar Najeriya. Ya tuna cewa da yawa daga cikin waɗanda suka girma tare sun mutu.”

A cewar marigayi Alhaji Aminu Ɗantata, ya yi watsi da bukatar yin hira da su, domin mahaifinsa (Alhaji Alhassan Ɗantata) ko wansa (Alhaji Ahmadu Ɗantata) ba su yi hakan ba a rayuwarsu; don haka, ba a fara da shi ba. Amma yana ba da dama don tattaunawa a gidansa, kuma baƙi na iya naɗar duk abin da ya faɗa su buga.

Mutuwarsa

Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu a daren Juma’a, ranar 28 ga watan Yuni na shekarar 2025, a Abu Dhabi. Ya rasu ya bar ‘ya’ya ashirin da hudu da jikoki da dama. Iyalan marigayin, sun bayyana cewa za a binne shi a Madina kusa da kabarin matarsa, Hajiya Rabi’a, wacce ita ma ta rasu a can, a shekarar 2023, kamar yadda ya yi fata.

Bayan rasuwar tasa an gudanar da sallar jana’izar a Kano a ranar Asabar. Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta shirya Salatul Ghaib; addu’a ta musamman da ake yi wa mamaci a lokacin da gawar ba ta nan.

Manazarta

BBC News Pidgin. (2025b, June 28). Aminu Dantata: Nigeria businessman die at di age of 94.

Saleh, S. K. (2025, June 28). A Na roki Allah kada ya ba ni abin da mutane ba za su amfana ba – Aminu Ɗantata. Aminiya.

Tanvirali. (2025b, June 28). Who is Aminu Dantata? Wife, Family & Net Worth. GTV News Latest Breaking Pakistani News | GTV News HD.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×