Apple Inc. babban kamfani ne na fasaha wanda ya kafa tarihi mai ƙarfi a duniya ta hanyar ƙirƙirar na’urorin lantarki da manhajoji masu inganci. Kamfanin yana haɗa hardware da software cikin tsari mai inganci, inda kowace na’ura ke aiki tare da manhajojin da aka tsara musamman dominta. Wannan tsari yana ba masu amfani da na’urorin damar gudanar da ayyuka cikin sauƙi, tsaro, da kwanciyar hankali, kuma hakan ce ta sanya Apple ya bambanta da sauran kamfanoni a kasuwar fasahar zamani.
Tambarin kamfanin Apple shi ne alamar Tufa.
Apple ya taka muhimmiyar rawa wajen sauya yadda mutane ke amfani da na’urorin zamani, musamman a fannin wayoyin hannu, kwamfutoci, tablets, da agogunan zamani. Kamfanin ya shahara saboda ƙirƙire-ƙirƙire masu inganci, misali haɗa na’urorin cikin da’irar Apple, inda manhajoji da na’urorin ke aiki a matsayin tsari guda. Wannan tsarin yana bai wa mai amfani da na’urar kamfanin damar fara aiki a iPhone, ya ci gaba a iPad, sannan kuma ya kammala a Mac ba tare da wata matsala ba. Hakan ta ƙara darajar amfani da na’urorin Apple.
Haka kuma, Apple ya yi fice wajen ƙirƙirar sababbin fasahohi kamar Face ID, Privacy, da AirDrop, waɗanda suka sauƙaƙa sadarwa, nishaɗi, aiki, da karatu a rayuwar yau da kullum. Tasirin kamfanin ya wuce ƙera na’urori kawai, ya bayyana misalin yadda kamfanoni ke haɗa hardware da software a duniya baki ɗaya.
Tarihin kamfanin Apple Inc.
Apple Inc. an kafa shi ne a shekarar 1976 a Amurka karkashin haɗakar matasa masu fasaha: Steve Jobs, Steve Wozniak, da Ronald Wayne. Farkon kayayyakin kamfanin sun haɗa da Apple I da Apple II, waɗanda suka taimaka wajen isar da kwamfuta ga jama’a a wani lokaci da kwamfuta ta kasance abu mai wuyar samu. Apple I ta kasance kwamfuta ta farko da aka ƙera don amfanin gida, yayin da Apple II ta zama ɗaya daga cikin kwamfutocin farko da aka yi amfani da su a makarantu da ofisoshi.
Jagoranci da cigaban kamfani
Shugabancin Steve Jobs ya kasance mai tasiri wajen ƙirƙira da bunƙasa kamfanin. Jobs ya mayar da hankali kan abubuwa masu kyau, inganci, da fahimtar masu amfani da na’urorin, wanda hakan ya bambanta Apple da sauran kamfanoni a kasuwa. A ƙarƙashin jagorancinsa, Apple ta fitar da kayayyaki da na’urori masu jan hankali kamar Macintosh, wanda ya sauya yadda mutane ke kallon kwamfuta a gida da ofis.
Bayan rasuwar Jobs a shekarar 2011, Tim Cook ya karɓi ragamar jagorancin kamfanin, inda ya ci gaba da bunƙasa Apple ta hanyar fitar da sababbin kayayyaki, ƙara amfani da iPhone da iPad a kasuwannin duniya, da faɗaɗa ayyukan Apple Music, iCloud, da App Store. A ƙarƙashin Cook, kamfanin ya ƙara ƙarfi a kasuwannin duniya, musamman a Asia da Afirka, inda kayayyakin Apple ke samun karɓuwa sosai.
Ƙirƙirar na’urori da manhajoji
Apple ya kasance jagora wajen haɗa hardware da software cikin tsari mai inganci. Wannan ya sa kowace na’ura da kamfanin ke ƙeraws tana aiki daidai da tsarin aiki da manhajojin da aka tsara musamman dominta. Wannan bambanci ne da ya sa kayayyakin Apple su kasance na musamman, inda masu amfani ke samun fahimtar amfani da su cikin sauƙi da kwanciyar hankali, wanda ba a ko’ina ake samu a sauran na’urorin lantarki.
Apple na samar da wayoyin hannu na zamani masu ɗauke da manhajojin iOS.
Tarihin Apple ya nuna yadda ƙirƙira, graphics mai kyau, da tsaro suka kasance ginshiƙai na nasarar kamfanin, kuma sun zama abin koyi ga sauran kamfanoni a duniya baki ɗaya.
Manyan kayayyakin Apple
Apple yana da kayayyaki masu yawa waɗanda suka haɗa na’urori da manhajoji cikin tsari mai inganci da haɗin kai. Wannan tsari yana ba masu amfani da na’urorin damar gudanar da ayyuka cikin sauƙi, samun tsaro, da fahimta cikin sauƙi. Kayayyakin sun haɗa da wayoyin hannu, kwamfutoci, tablets, agogon zamani, na’urori masu sauti da nishaɗi, da manhajoji da ayyukan yanar gizo. Kowanne kayan Apple yana aiki a matsayin tsari guda wanda ke ba masu amfani da su damar amfani da na’urori da manhajoji a sauƙaƙe.
Wayoyin iPhone
Wayoyin iPhone sun fara fitowa a shekarar 2007, inda suka kawo sauyi babba a harkar wayoyin hannu. iPhone sun shahara saboda haɗa manhajar iOS da na’urori cikin tsari mai sauƙi, wanda hakan ke bai wa mutane damar fahimta cikin sauƙi da inganci. Daga iPhone ta farko zuwa ta yanzu, Apple ya ƙara sabbin manhajoji kamar (Face ID), kyamara mai inganci, da tallafi ga manhajojin zamani.
Wayoyin iPhone sun kasance ginshiƙai a kasuwar wayoyin duniya, musamman saboda haɗin kai da sauran na’urorin kanfanin Apple. Haka kuma, suna da ƙarfi wajen gudanar da ayyuka da yawa lokaci guda, suna bai wa mutane damar yin kiran waya, rubuta saƙonni, yin kasuwanci, nishaɗi, da karatu daga wuri guda ba tare da matsala ba. iPhone sun kuma taimaka wajen bunƙasa kasuwar manhajoji, inda manhajoji masu zaman kansu suka samu damar bunƙasa a kasuwa ta hanyar App Store.
Kwamfutoci (Mac)
Apple yana ƙera kwamfutoci da ake kira Mac, waɗanda suka haɗa MacBook, MacBook Pro, MacBook Air, iMac, Mac Mini, da Mac Studio. Kwamfutocin Mac suna amfani da manhajar macOS, tsarin aiki mai sauƙin amfani, tsaro, da haɗin kai tare da sauran na’urorin Apple. Wannan tsari yana bai wa masu amfani damar ci gaba da aiki daga iPhone ko iPad zuwa Mac cikin sauƙi ba tare da katse aikin ba.
MacBook da MacBook Pro suna ba da nagartacce kuma kyakkyawan tsari na manhajoji daban-daban ga masu zanen hoto, da masu aiki a ofis, yayin da MacBook Air da iMac suka fi dacewa ga ɗalibai da masu amfani na yau da kullum. Mac Mini da Mac Studio sun kasance na musamman ga ayyuka masu nauyi, misali sarrafa bidiyo, zane-zane, da ayyukan bincike1.
iPad
iPad sun haɗa da nau’ikan iPad, iPad Pro, iPad Air, da iPad Mini, waɗanda ke sauƙaƙa karatu, nishaɗi, da aiki. Suna amfani da manhajar iPadOS, tsarin aiki da aka tsara musamman domin fuska mai taɓawa da gudanar da manhajoji da ayyuka masu yawa lokaci guda.
iPad sun zama mataimaka ga ɗalibai, malamai, da masu sana’a, saboda suna ba su damar yin aiki a hannu ko a gida ba tare da buƙatar kwamfuta mai tsada ba. Haka kuma, haɗin kai da Apple Pencil da sauran manhajoji ya ba masu amfani damar yin rubutu, zanen hoto, da ƙirƙira cikin sauƙi da inganci.
Agogon Apple Watch
Apple Watch yana amfani da manhajar watchOS, kuma yana taimakawa wajen lura da lafiyar mai amfani, motsa jiki, da ayyukan yau da kullum. Agogon yana bai wa masu amfani da shi damar sadarwa ta hanyar kiran murya, aika saƙonni, da samun sanarwa kai tsaye daga iPhone.
Agogon kamfanin Apple mai amfani da manhajar watchOS.
Apple Watch yana taimakawa wajen gudanar da ayyukan kiwon lafiya, misali lura da bugun zuciya, yawan motsa jiki, da sa ido kan barci. Haka kuma, yana amfani wajen ayyukan nishaɗi da wasanni, inda masu amfani ke iya samun ƙarin bayanai da haɗin kai tare da sauran na’urorin Apple.
Na’urorin sauti da nishaɗi
Apple na ƙera na’urorin sauti da nishaɗi kamar AirPods da HomePod, waɗanda ke ba da ingantaccen sauti da haɗin na’urori marar waya da sauran na’urorin Apple. AirPods sun shahara wajen amfani a wajen aiki, karatu, da nishaɗi, musamman saboda damar haɗa iPhone da iPad. HomePod na amfani da manhajojin Apple don samar da sauti mai inganci da haɗa na’urorin gida cikin sauƙi.
Haka kuma, Apple yana samar da shafukan nishaɗi na intanet kamar Apple Music da Apple TV, inda masu amfani ke iya sauraron kiɗa, kallon fina-finai, da yin amfani da ayyuka masu haɗin kai da sauran na’urori.
Manhajoji da ayyukan yanar gizo
Apple na bayar da manhajoji da damar ayyukan yanar gizo kamar iCloud, Safari, Apple Maps, da Apple Pay. iCloud yana taimakawa wajen ajiye bayanai da haɗin kai tsakanin na’urori, Safari yana ba da damar binciken yanar cikin tsaro, Apple Maps yana taimaka wajen jagora da nuna taswira, yayin da Apple Pay ke sauƙaƙa biyan kuɗi cikin sauri da tsaro.
Manhajojin Apple suna aiki tare da na’urorin lantarki na kamfanin, suna ba masu amfani da su damar gudanar da ayyuka cikin inganci, haɗin kai, da tsaro. Wannan haɗin kai yana ƙara fahimtar masu amfani da na’urorin a rayuwar yau da kullum, kuma ya sanya Apple ya zama jagora wajen haɗa na’urorin lantarki da manhajoji cikin tsari mai dorewa da inganci.
Tsarin aikin manhajar Apple
Apple yana da tsarin aiki na musamman wanda ke sarrafa kayayyakin kamfanin, yana ba masu amfani damar gudanar da ayyuka cikin sauƙi, tsaro, da haɗin kai tsakanin na’urorin. Tsarin aikin Apple ya bambanta da sauran tsarin aikin kamfanoni na duniya saboda yana haɗa na’urori da manhajoji cikin tsari guda ɗaya mai inganci, wanda ke samar da fahimta ga masu amfani sa su cikin sauƙi da kwanciyar hankali ga miliyoyin mutane a duniya.
Manhajar iOS
iOS tsarin aiki ne na wayoyin iPhone da iPod Touch, wanda aka tsara musamman domin sauƙaƙa amfani da wayoyi masu fasaha. iOS yana ba masu amfani damar sarrafa manhajoji, sadarwa, nishaɗi, da ayyuka na yau da kullum cikin sauƙi da tsaro.
Tsarin iOS ya shahara saboda sauƙin amfani, inda kowane mutum zai iya fahimtar yadda ake amfani da na’ura cikin sauri, ba tare da dogaro da ilimi na musamman ba. Haka kuma, tsarinta na tsaro yana kare bayanai da manhajojin da ake shigarwa, yana hana kutse da ayyukan damfara. iOS na aiki cikin haɗin kai da sauran na’urorin Apple kamar iPad, Mac, Apple Watch, da ayyukan yanar gizo na iCloud. Wannan tsarin yana ba mutane damar canja aiki daga na’ura guda zuwa wata ba tare da katsewar ayyuka ba.
Manhajar macOS
macOS tsarin manhaja ne na kwamfutocin Mac, wanda aka tsara domin gudanar da ayyuka masu ƙarfi kamar aikin ofis, zane-zane, shirye-shirye, da bincike. macOS tana da tsari mai inganci da haɗin kai tare da iOS da sauran tsarin Apple, wanda hakan ke bai wa masu amfani damar musayar bayanai tsakanin na’urori cikin sauƙi da inganci.
Haka kuma, macOS tana amfani da ingantattun manhajoji da fasahohi masu zaman kansu, misali Finder da Spotlight, waɗanda ke sauƙaƙa bincike da sarrafa da fayil-fayil. Haɗin kai tsakanin macOS da sauran na’urori na Apple yana bai wa mutane damar ci gaba da aiki daga iPhone ko iPad zuwa Mac ba tare da matsala ba.
Manhajar iPadOS
iPadOS tsarin aiki ne ko manhaja ta na’urorin iPad, wanda aka tsara domin amfani da fuska mai taɓawa da gudanar da ayyuka masu yawa a lokaci guda. iPadOS tana amfani da manhajojin iOS, amma tana ƙunshe da wasu fasaloli na musamman kamar Split View da goyon bayan Apple Pencil, wanda ke sauƙaƙa aikin karatu, rubutu, zanen hoto, da ƙirƙira.
iPad da iPadOS suna taimakawa ɗalibai, malamai, da masu sana’a wajen gudanar da ayyuka a hannu ko a gida ba tare da buƙatar kwamfuta ba. Tsarin aikin iPadOS yana sauƙaƙa gudanar da manhajoji masu yawa lokaci guda, yana ba mutane damar yin aiki mai inganci, kallo, da nishaɗi a wuri guda.
Manhajar watchOS
watchOS tsarin aiki ne na Apple Watch, wanda ke ba agogon damar gudanar da ayyuka na yau da kullum da lura da lafiyar mai amfani da shi. Apple Watch yana taimaka wajen sadarwa ta hanyar kiran murya, saƙonni, da samun sanarwa kai tsaye daga iPhone.
Na’urar kwamfuta nau’in Apple MacBook
Bugu da ƙari, watchOS tana lura da lafiyar mai amfani ta hanyar bibiyar bugun zuciya, yawan motsa jiki, da barci. Haka nan tana taimakawa a wasanni da ayyukan nishaɗi, inda masu amfani ke iya samun bayanai kai tsaye da haɗakar sauran na’urorin Apple.
Haɗin kai tsakanin na’urori Apple
Ɗaya daga cikin manyan fasalolin Apple shi ne Apple ecosystem, wato haɗin kai tsakanin dukkan na’urorin kamfanin. Wannan tsarin yana bai wa mutane damar canja aiki daga iPhone zuwa iPad ko Mac cikin sauƙi, ajiye bayanai a iCloud, da samun damar amfani da su a dukkan na’urorin. Haka kuma, mutane za su iya karɓar sanarwa daga Apple Watch ko iPhone ba tare da katsewar ayyuka ba.
Tsarin aikin Apple yana tabbatar da cewa na’urori da manhajoji suna aiki tare cikin daidaito da kwanciyar hankali, wanda hakan ke ba masu amfani da su damar fahimta da sarrafawa cikin sauki da inganci. Wannan haɗin kai ya sa Apple ya zama na musamman a kasuwa, kasancewar ba a fiye samun irin wannan tsari mai haɗa dukkan na’urori da manhajoji cikin tsari guda ba.
Apple da fasahar buɗaɗɗen tsari
Apple yana amfani da tsarin aiki da manhajoji na kulle, wato closed system, wanda ke nufin cewa lambar ginin na’urorinsa (codes) da manhajojin da ke aiki a kansu ba a buɗe suke ga jama’a ba. Wannan tsari ya bambanta Apple sosai da Android, wadda take amfani da buɗaɗɗen tsari (open source), inda kamfanoni da masu ƙirƙirar manhajoji ke da damar gyara tsarin aiki, ƙara fasali, ko ƙirƙirar manhajoji da suka dace da buƙatunsu.
Kullallen tsarin Apple
Wannan tsari na Apple yana nufin cewa masu amfani ba su da damar yin gyare-gyare ko ƙara fasali a tsarin aiki kamar yadda ake yi a Android. Wannan tsarin yana bai wa Apple ikon tabbatar da daidaito tsakanin na’urori da manhajoji, wanda hakan ke haifar da fahimta da kwanciyar hankali ga masu amfani da na’urorin Apple. Tsaro yana da ƙarfi saboda manhajojin da aka amince da su a App Store ne kawai za su iya aiki a iPhone, iPad, ko Mac. Wannan yana rage haɗarin kutse, damfara, da cutarwa ga na’urori. Hakan ya sa Apple ya zama ɗaya daga cikin kamfanoni masu tsaro sosai a duniya.
Bugu da ƙari, wannan tsari yana kuma tabbatar da cewa duk sabuntawa da gyare-gyare ga manhajoji suna fitowa cikin tsari mai kyau, da ke sauƙaƙa sarrafa na’urori da kare bayanan masu amfani. Wannan haɗin kai da daidaito yana inganta tsarin Apple ecosystem, inda dukkan na’urorin ke aiki tare cikin tsari, kuma mutane za su iya canja aiki daga iPhone zuwa iPad ko Mac ba tare da matsala ba.
Fa’idojin kullallen tsarin Apple
Kullallen tsarin Apple yana da fa’idodi masu yawa. Da farko, yana ba da inganci da haɗin kai tsakanin na’urori, inda manhajoji da na’urori ke aiki a matsayin tsari guda mai dorewa.
Haka nan, tsaro ya fi ƙarfi saboda dukkan manhajojin da aka amince da su ne kawai za su iya aiki a na’urorin Apple, wanda ke kare bayanai daga damfara, kutse, da cutarwa.
Bugu da ƙari, tsarin yana sauƙaƙa gudanar da sabuntawa da kula da kayayyakin aiki, saboda dukkan tsarin na ƙarƙashin kulawar Apple, wanda hakan ke tabbatar da daidaito da kwanciyar hankali a dukkan lokacin amfani.
Ƙalubalen kullallen tsarin Apple
Duk da fa’idojin da aka bayyana, tsarin yana kawo wasu ƙalubale. Rashin sassauci yana nuna cewa masu amfani da Apple ba sa iya yin gyare-gyare ko ƙara abubuwa masu yawa a tsarin aikin na’urorin. Wannan ya sa masu son yin abubuwa daban-daban da kansu, ko amfani da manhajoji masu zaman kansu, suke fuskantar ƙuntatawa.
Haka kuma, farashin na’urori da manhajojin Apple ya fi tsada, saboda kamfanin na kula da duk tsarin daga farko zuwa ƙarshe, wanda hakan ke ƙara darajar kayayyakin amma kuma yana rage yanci ga masu amfani da su.
Bambancin Apple da Android
Bambanci tsakanin Apple da Android yana bayyana a fili a wannan tsarin. Android na da buɗaɗɗen tsari, inda kamfanoni da masu ƙirƙirar manhajoji ke da damar gyara tsarin aiki, ƙara sabbin fasaloli, da ƙirƙirar manhajoji masu dacewa da buƙatunsu. Wannan yana bai wa mutane damar zaɓi da sassauci, amma sau da yawa yana rage haɗin kai da tsaro, musamman a wayoyin da ba a sabunta su akai-akai.
Apple, a gefe guda, yana amfani da kullallen tsari, yana tabbatar da daidaito, haɗin kai, da tsaro, wanda ke haifar da sauƙin fahimta ga masu amfani cikin sauƙi da inganci. Wannan bambanci ya sa Apple ke samun Apple ecosystem mai ƙarfi, inda duk na’urori da manhajoji ke aiki tare cikin tsari guda mai dorewa. Duk da rashin sassauci, wannan tsarin ya sa Apple ya zama jagora wajen haɗa na’urorin lantarki da manhajoji cikin tsari mai sauƙi da inganci.
Tasirin Apple a duniya
Apple Inc. ya kasance ɗaya daga cikin kamfanoni mafi tasiri a duniyar fasahar zamani, inda ya sauya yadda mutane ke mu’amala da na’urori da manhajoji. Kamfanin ya kafa ƙa’idoji da misalai a masana’antar lantarki, wayoyin hannu, kwamfutoci, tablets, da sauran na’urorin zamani. Tasirin Apple ba kawai yana bayyana a kasuwanni ba ne, har ma yana cikin fasaha da rayuwar yau da kullum, inda miliyoyin mutane ke dogaro da kayayyakin kamfanin.
Tasirin kasuwa
Apple ya kafa kasuwa mai ƙarfi a duniya, inda kayayyakinsa suka mamaye sassa daban-daban na rayuwar yau da kullum. Wayoyin iPhone sun zama ginshiƙi a kasuwar wayoyin hannu, suna jan hankalin mutane daga kowane rukuni na al’umma, kama daga matasa masu amfani da manhajoji, zuwa masana kasuwanci da ke gudanar da ayyuka na yau da kullum.
Tasirin fasaha
Apple ya taimaka wajen haɓaka sabbin fasahohi a fannoni daban-daban. Kyamarorin wayoyin iPhone sun ƙara inganci sosai tare da fasahar Face ID, wacce ke ba masu amfani damar samun tsaro da sauƙin shiga na’urori. Manhajojin sadarwa da nishaɗi kamar Apple Music, Apple TV, da iCloud suna ba mutane damar yin aiki, sauraron kiɗa, kallon fina-finai, da ajiye bayanai cikin sauƙi da tsaro.
Tasirin rayuwar jama’a
Apple ya sauƙaƙa rayuwar mutane ta hanyar na’urorin lantarki masu sauƙin amfani, wanda ke ba su damar yin aiki, karatu, nishaɗi, da sadarwa cikin sauƙi a gida, ofis, ko makaranta. Kamfanin ya taimaka wajen bunƙasa ilimi, kasuwanci, da ayyukan yau da kullum a birane da wuraren da ake amfani da fasahar zamani sosai.
Matsaloli da ƙalubalen kamfanin Apple
Duk da shahara da tasiri da Apple Inc. ke da shi, kamfanin na fuskantar wasu matsaloli da kalubale a kasuwa da fannin fasaha. Waɗannan ƙalubale suna shafar kasuwanci, damar masu amfani, da ci gaban sabbin fasahohi, amma kamfanin yana ci gaba da ƙoƙarin magance su ta hanyar ƙirƙira da inganta kayayyaki.
Tsadar kayayyaki
Daya daga cikin manyan ƙalubalen Apple shi ne tsadar kayayyaki. Wayoyi, kwamfutoci, iPads, da sauran na’urorin Apple sun fi tsada idan aka kwatanta da na’urorin Android ko Windows. Wannan farashi mai tsada yana rage damar wasu rukunin al’umma, musamman a kasashe masu ƙarancin samun kuɗi, wajen mallakar na’urorin Apple.
Kullallen tsarin (Closed system)
Wannan tsari na Apple yana da fa’idodi da yawa, musamman wajen tsaro da kwanciyar hankali. Amma tsarin yana rage sassauci ga masu amfani da na’urorin kamfanin. Mutane ba za su iya gyara tsarin aiki ko ƙara wasu fasaloli da yawa kamar yadda ake yi a manhajar Android ba, wanda hakan ke iyakance damar daidaita na’urori da manhajoji gwargwadon bukatun mutum.
Gasa da sauran kamfanoni
Apple na fuskantar ƙalubale daga kamfanoni masu fafatawa kamar Android/Google, Microsoft, da Samsung. Kasuwar wayoyi, kwamfuta, da na’urorin zamani tana cike da gasa mai ƙarfi, inda kamfanoni ke ƙoƙarin kawo sababbin kayayyaki da sabunta fasaha don jan hankalin mutane.
Na’urar tablet nau’in Apple
A wannan yanayin, Apple dole ne ya ci gaba da ƙirƙira sababbin kayayyaki, haɓaka manhajoji, da inganta haɗin kai tsakanin na’urorinsa don tabbatar da kasancewa a sahun gaba. Rashin cigaba zai iya haifar da raguwar ciniki ko rasa wasu daga cikin masu amfani da kayayyakinsu ga masu fafatawa.
Bukatar sabunta fasaha
Fasahar zamani na ci gaba da bunƙasa, musamman AI, VR/AR, da IoT. Apple na fuskantar ƙalubale wajen tabbatar da cewa na’urorinsa da manhajojin suna ci gaba da dacewa da waɗannan sabbin fasahohi. Kamfanin na buƙatar sa ido da ƙirƙira akai-akai don kasancewa jagora a masana’antar fasaha.
Hakan ya sa Apple ke gudanar da bincike da haɓaka (R&D) mai zurfi, inda ake ƙirƙirar sabon fasali da kayayyaki masu inganci. Duk da ƙalubalen, wannan ya sa kamfanin ya ci gaba da kasancewa jagora wajen haɗa na’urori da manhajoji cikin tsari mai dorewa da inganci.
Makomar Apple
Ana sa ran Apple Inc. zai ci gaba da kasancewa jagora a duniyar fasahar zamani, inda zai ƙara haɓaka sabbin kayayyaki, sabunta na’urori, da manhajoji domin dacewa da bukatun zamani. Makomar kamfanin ta haɗa da haɓakar fasaha, haɗin kai tsakanin na’urori, sabbin kayayyaki, da cigaban kasuwanci, wanda hakan ke tabbatar da cewa Apple zai ci gaba da kasancewa abin koyi a duniya baki ɗaya.
Manazarta
Apple Inc. (2025). iOS, macOS, iPadOS, watchOS.
Encyclopædia Britannica. (n.d.). Apple Inc. Britannica
ICN. (2025, June 25). History of Apple company.
Statista. (2025, January). Global market share of smartphone operating systems.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.
