Skip to content

Argon

Argon na ɗaya daga cikin sinadarai da ke wanzuwa a sigar iskar gas, kuma muhimmi ne cikin sinadarai masu daraja. Sinadarin shi ne na shida a rukunin 18 (VIIIA) na teburin sunadarai na lokaci-lokaci (Periodic Table). Wannan teburi ginshiƙi ne wanda ke nuna yadda abubuwan sinadaran ke da alaƙa da juna. A wasu lokuta ana kiran iskar gas mai daraja saboda sinadaran rukuni na 18 (VIIIA) suna haɗuwa su samar da wani abu da wasu sinadarai kaɗan. A zahiri ma, ba a taɓa samar da sinadari daga argon ba.

images 3
Argon sinadari ne da ke wanzuwa a sigar iska.

An gano sinadarin Argon a cikin shekarar 1894 ta hannun masanin ilmin sinadarai ɗan ƙasar Ingila John William Strutt, wanda aka fi sani da Lord Rayleigh, ya rayu a tsakanin (1842-1919), da kuma William Ramsay wanda shi ma ya rayu a tsakanin (1852-1916). Sinadarin shi ne farkon iskar gas mai daraja da aka ware daga cikin iskar sararin duniya.

Rayleigh da Ramsay sun gano argon ta hanyar da ake kira “fractional distillation of liquid air” a Turance. Franctional Distillation na nufin ba da dama ga iska mai nau’in ruwa-ruwa ta yi ɗumi sannu a hankali. Yayin da iska ke ɗumama, abubuwa daban-daban suna canjawa daga ruwa-ruwa zuwa iskar gas. Ɓangaren iska da ke canjawa zuwa gas a -185.86°C (-302.55°F) shi ne ke zama sinadarin argon.

Tarihin ganowa da kuma suna

An gano Argon a shekara ta kamar yadda ya gabata a sama 1894. Sai dai kuma, masanin kimiyya ɗan kasar Ingila Henry Cavendish, wanda ya rayu a tsakanin shekarun (1731-1810) ya yi hasashen samuwar argon shekaru 200 da suka gabata. Lokacin da Cavendish ya fitar da iskar oxygen da nitrogen daga cikin iskar duniya, ya gano cewa ɗan ƙaramin adadin iskar gas ne ya rage. Ya zaci wani abu ne a cikin iska, amma ya kasa gane ko mene ne.

Lokacin da Ramsay ya maimaita gwaje-gwajen da Cavendish ya aiwatar a cikin shekarun 1890s, shi ma, ya sami irin wannan ɗan ƙaramin adadin iskar gas da ba a tantance ko mene ne ba. Amma Ramsay ya ɗarar wa Cavendish wata da fa’ida; ya yi amfani da fasahar spectroscopy, wadda babu ita a zamanin Cavendish. Fasahar spectroscopy shi ne tsarin nazarin hasken da aka samar lokacin da wani sinadari ya yi zafi. Spectrum (jam’in shi ne: spectra) wani sinadari ne da ya ƙunshi jerin layuka masu launi kuma ya bambanta ga kowane.

Ramsay ya yi nazarin wannan sinadari na (spectrum) da ba a tantance ba. Ya samo jerin layukan da ba na wani sinadari ba ne. Wannan ya tabbatar cewa ya samo sabon sinadari. A hannu guda kuma, Rayleigh yana yin irin wannan aiki a kusan lokaci guda. Ya yi bincikensa ne a daidai lokacin da Ramsay ya yi nasa. Masanan biyu sun yanke shawarar ba da sanarwar tare. Sunan argon ya fito daga kalmar Girkanci ta ”argos”, wanda ke nufin “the lazy one” a Turance. Sunan ya dogara ne a kan gazawar argon ta samar da wani sinadarin.

Gano argon ya haifar da matsala ga masana kimiyya. Domin shi ne iskar gas ta farko da aka fara ganowa. Ina ya kamata ya shiga cikin teburin sunadarai? A lokacin, teburin ya ƙare ne da rukunin 17 (VIIA) a dama. Ramsay ya ba da shawarar cewa za a iya tsawaita teburin. Ya ba da shawarar ƙara sabon rukuni a kan teburin. An kuma sanya wannan rukunin zuwa dama da rukuni na 17 (VIIA).

An kuma yarda da shawarar Ramsay, amma ta haifar da sabuwar matsala mai ban sha’awa ga masanan. Idan akwai sabon rukuni a cikin teburin, to ina sauran sinadaran da za su kasance cikin rukunin?

Abin sha’awa shi ne, masanan kimiyyar sun fahimci yadda waɗannan sinadarai da babu za su yi kama. Domin kuwa duk sinadaran da ke cikin rukuni ɗaya suna kama da juna sosai. Masanan sun nemi ƙarin iskar gas makamantan argon, waɗanda ba sa iya haɗuwa ko samar da wani sabon sinadari. A cikin shekaru biyar masu zuwa, sun samu nasarar gano ragowar sinadaran rukunin da suka kasance: helium, krypton, neon, radon, da xenon.

An yi amfani da alamar A don wakiltar sunan sinadarin argon har zuwa shekarun 1950s lokacin da masana kimiyya suka yarda su yi amfani da alamar harafi biyu Ar don wakiltar sunan sinadarin.

Siffofin sinadarin argon

Argon ba shi da launi, ba shi da wari, ba shi da ɗanɗano. Nauyinsa shi ne gram 1.784 a kowace lita ɗaya ta sinadarin. Nauyin iska, idan za a kwatanta, yana da kusan gram 1.29 a kowace lita ɗaya. Argon yana canjawa daga gas zuwa nau’in ruwa-ruwa a yanayin -185.86°C (-302.55°F). Sannan kuma ya canjawa daga ruwa-ruwa zuwa daskararre a yanayin -189.3°C (-308.7°F).

Sinadaran da argon ya ƙunsa

Argon ba ya samar da wasu sinadarai domin ba ya haɗuwa da wasu. Amma a wasu lokutan da ba kasafai ba, a ƙarƙashin matsanancin yanayi, yana haifar da wani abu mai rauni, kamar siffofin abubuwa.

Samuwar argon a ɗabi’a (natural)

Yawan sinadarin argon a cikin yanayin iskar duniya ya kai kusan kimanin kashi 0.93 bisa dari. Haka nan ana samun shi a  dandaryar ƙasa har kusan sassa 4 a kowace miliyan guda.

Samar da sinadarin argon

Ana iya samar da Argon daga iska mai nau’in ruwa-ruwa ta hanyar Fractional Distillation kamar yadda aka yi bayani a baya. Haka nan ana iya samar da shi ta hanyar ɗumama iskar nitrogen daga sararin samaniya tare da magnesium mai zafi ko  calcium. Magnesium ko calcium suna haɗuwa da nitrogen don samar da nitride.

Ƙaramin adadin argon koyaushe yana samuwa wanda ba tatacce ba tare da nitrogen. Ya kasance a baya saboda ba ya hulɗa da magnesium ko calcium. Har ila yau argon yana wanzuwa a cikin rijiyoyin tare da iskar gas. Lokacin da aka tace iskar gas, ana iya samun wani adadi na argon a matsayin ƙarin alfanu.

Rabe-raben argon (Isotopes)

Akwai nau’ikan argon (isotopes) guda uku da ke wanzuwa ta tsarin ɗabi’a (natural). Su ne argon-36, argon-38, da kuma argon-40. Isotopes nau’ika biyu ne ko fiye na wani sinadari. Isotopes sun bambanta da juna ta fuskar yawan adadinsu. Lambar da aka rubuta a dama da sunan sinadaran ita ce Mass Number. Wannan lamba tana wakiltar adadin protons da neutrons a tsakiyar ƙwayar zarra (atom). Adadin protons ne ke ƙayyade kashi, amma adadin neutrons a cikin atom na kowane sinadari ɗaya na iya bambanta. Duk wani banbanci da ake samu shi ke haifar da samuwar isotope.

Amfanin sinadarin argon

Ana amfani da Argon a yanayin da ake buƙatar kariya daga oxygen ko wasu iskar gas. Misali mai kyau shi ne ƙwan fitilar lantarki mai haske, wanda ya ƙunshi waya ta ƙarfe a cikin zagayen gilashi ko kwalba mai haske. Makamashin lantarki yana ratsa wayar, yana sa ta yi zafi sosai kuma ta ba da haske. Oxygen na haɗuwa da ƙarfe mai zafi cikin sauƙi, tana samar da muhallin ƙarfe da oxygen. Wannan fili ba zai samar da makamashin lantarki da kyau ba, wanda hakan zai iya sa fitilar ta daina ba da haske.

Duk da haka, ana amfani da argon don dakatar da wannan daga faruwa. Saboda sinadarin argon ba shi da ƙarfi, ba zai yi aiki da waya mai zafi ba, zai bar ƙarfen wayar ya yi zafi na dogon lokaci. Fitilar za ta daina ba da haske lokacin da ƙarfen wayar ya katse. Kuma ba zai iya sake dakon makamashin lantarki ba.

Haka nan ana amfani da argon wajen aikin walda. Walda ita ce hanyar da ake haɗe karafa da juna. A mafi yawan lokuta, karafa biyu suna ɗaukar zafi sosai. Yayin da suka ɗauki zafi, suna iya narkewa tare.

Sai dai a yayin da karafan suka yi zafi, suna fara yin hulɗa tare da iskar oxygen. A cikin wannan yanayi, ana samar da wani fili na ƙarfe da oxygen. Yana da matukar wahala a haɗa ƙarafa biyu idan sun samar da fili, don haka amfani da argon a cikin fasahar walda yana inganta haɗin gwiwar ƙarafa.

Har ila yau ana amfani da argon a cikin na’urar lasers ta argon da lasers ɗin rini. Laser na’ura ce da ke samar da haske mai launi ɗaya (yawanci). Ana amfani da laser na argon don magance yanayin fata. Laser tana haskaka haske mai launin shuɗi-kore a kan wurin da fata ta shafa. Ƙarfin wutar lantarki daga na’urar Laser yana ɗaukar ƙwayar sinadarin haemoglobin kuma ya canjawa zuwa zafi. (Haemoglobin shi ne sinadarin furotin a cikin ƙwayoyin halittar jini jajaye (Red blood cells). Tana ɗaukar iskar oxygen zuwa tantanin halitta (tissues) da carbon dioxide daga gare su. Hanyoyin jini sukan lalace, har ma sai su toshe, hakan na sa su ruɓe kuma a sake shigar da su cikin jiki. Yanayin girman da ba a buƙata, ana daƙile shi har ma da tabon fata.

Ana amfani da Laser argon-dye wajen tiyatar ido. Za a iya daidaita launi na haske ta hanyar na’urar laser zuwa madaidaicin adadi. Ana iya yin shi don samar da haske a jere kama daga launin kore zuwa shuɗi. Kowane inuwa ta kore ko shuɗin hasken tana da ɗan nisan zango daban-daban. Tana iya shiga sosai ko kaɗan cikin ido. Za a iya saita na’urar Laser don magance wani yanki na musamman na ido. Ana amfani da argon-dye don magance cutuka, lalacewar magudanar jini, cutukan da ke tattare da ƙwayar ido, da sauran nau’ikan matsalolin ido.

Tasirin argon ga lafiya

Har kawo yanzu ba a gano sinadarin Argon yana da wani tasiri mai kyau ko marar kyau ga lafiyar tsirrai ko dabbobi ba.

Manazarta

Admin. (2022a, June 24). Argon. BYJUS.

 Periodic Table (n.d.).  Argon – Element information, properties and uses | Periodic Table.

Pappas, S. (2015, February 20). Facts about Argon. Live Science.

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×