Na’ura ce da ake amfani da ita wurin cirar kuɗi. Na’urar ana amfani da ita ne ta hanyar daddana lambobi domin fitar da kuɗi. Haka kuma tana aiki ciki sauri da ƙwarewa tare da fitr da adadin abin da aka danna yayin dannawar. Masana sun bayyana cewa; a ranar 27 ga watan Yuli na shekarar 1967 ne wani banki a birnin Landan ya fara amfani da wannan na’urar. Hakan ya kawo cigaba sosai tare da janyo hankulan mutane kan amfani da ita na’urar ta ATM.
Dalilin samar da na’urar
An samar da na’urar ne domin sauƙaƙawa mutane al’amuran da suka shafi cirar kuɗi ko kuma tura kuɗi daga wani wuri zuwa wani wuri ko kuma banki. Haka kuma na’urar na aiki musamman ta fuskar cire kuɗi idan buƙatar gaggawa ta taso. Sakammakon hakan an samu sauƙin abubuwa musamman wurin rage cincirindon jama’a a cikin banki yayin buƙata cirar kuɗi ko kuma shigar da su.
Ƙasar Koriya ta Kudu ita ce ƙasar da ta fi ƙasashen duniya yawan wannan na’urar inda take da guda dubu 278, sai Australia da ta bi mata, sannan Japan. A sahun ƙasashen nahiyar Afirka kuwa, Afirka ta Kudu ita ta fi sauran ƙasashen nahiyar Afirka yawanta. Najeriya ma na daga cikin ƙasashen Afirkan da suke da yawan ATM. Ƙiyasi ya nuna cewa, akwai na’urar ATM guda miliyan uku a duniya.
Fa’idojin na’urar ATM
Na’urar na da amfani daban-daban ta fuskar samar da cigaba wuri hada-hadar shige da ficen kuɗi kamar:
- Ana amfani da ATM wurin cirar kuɗi ko kuma saka kuɗi.
- Ana amfani da ATM wurin sayan katin waya.
- Ana amfani da ATM wurin biyan kuɗi a asibiti.
- Ana amfani da ATM wurin biyan kuɗin makarantar yara.
- Ana amfani da ATM wajen tura kuɗi zuwa kowane ɓangare na duniya.
Matsalolin Na’urar ATM
Komai na rayuwa yana da amfani da rashinsa. Don haka ita ma wannan na’ura ta ATM tana da ta ta matsalar. Daga cikin matsalolin na’urar ATM akwai,
Matsalar karɓar kati
Rashin karɓar kati na ɗaya daga cikin matsalolin da ake yawan fuskanta a tare da na’urar ATMs. Wannan na faruwa ne lokacin da na’urar dake karɓar katin ba za ta iya karɓar katin kuɗin ba, wanda hakan kan faru sakammakon lalacewa ko tarin datti. Wannan na iya haifar da jinkiri ga masu son cirar kuɗi, idan kuma aka matsa wurin sai ta karɓa katin kan iya maƙalewa.
Ɓata Lokaci
Wasu lokutan wannan na’ura na ɓata wa mutane rai ko kuma lokaci, saboda a kan samu dogayen layin jama’a masu jiran su ciri kuɗi. Amma daga ƙarshe sai ka samu wasu na ƙorafin ta ɗauke ko kuma ta ƙame.
Matsalar fitar kuɗi
Wani lokacin kuma, na’urar za ta nuna an kwashe wa mutum kuɗi a asusun ajiyar sa, idan ya yi amfani da ita, haka kuma wannan kuɗi da suka fita akasari ba sa dawowa mai su domin banki ba zai biya shi ba. Daga ƙarshe ma sai dai mutum ya ɓige da zarya a banki yana cike-cike da ɓata lokaci.
Riƙewar katin cirar kuɗi
Wasu lokutan na’urar takan riƙewa mutane katinsu na banki, sai mutum ya sha wuya kafin katinsa ya dawo. Wannan yana nuna cewa, duk da cewa na’urar ATMs tana da matuƙar amfani, ana iya fuskantar matsaloli da dama waɗanda zasu iya shafar abokan ciniki har ma ta kawo musu tangarɗa a cinikayyarsu.
Wuraren da ake samun na’urar ATM
Wurare da dama ana samun na’urar ATM kamar:
- Bakin bankuna
- Asibitoci
- Kasuwanni
- Coci
- Gidajen Mai
- Bakin tituna
Waɗanda suka fi amfani da ATM
Galibi ma’aika masu ɗaukar albashi sun fi amfani da ATM sai kuma ɗalibai tare da ‘yan kasuwa. Musamman ‘yan kasuwar dake tura manyan kuɗaɗe akai-akwai kuma zuwa wurare mabambanta musamman ƙasashen ƙetare.
Ire-Iren Na’urar ATM
Cash dispensers
Nau’in na’urar cirar kuɗi ce da ake amfani da ita wurin cirar kuɗi ko kuma tabbatar da adadin kuɗin da suke cikin asusun mamalakin asusun wato (Withdrawal) ko kuma (Check balance). Na’urace da take da matuƙar ƙoƙari yayin gudanar da aiki, akasari ana amfani da ita wurare mabanbanta kamar wuraren cin abinci, ko gidajen mai, ko kuma wuraren siyayya. Tana ɗaya daga cikin na’urorin da suka zama ruwan dare a wurare daban-daban. Domin akwai yawaitar su.
Full-service ATMs
Daya ne daga nau’ikan na’urar cirar kuɗi dake da amfani da yawa a banki. Ana amfani da wannan na’ura ta fuskar fitar da kuɗi ko kuma bincike wurin ƙidayar kuɗi. Wannan na’ura tana taka muhimmiyar rawa wurin ajiya, ko kuma canja kuɗi daga wannan asusu zuwa wannan asusu. Haka kuma daga cikin aikinta akwai sabunta littafin baki wato (check).
Intelligent ATMs
Intelligent ATM ɗaya ce daga na’urar da aka samar ta hanyar fasahar zamani. Idan aka ce intelligent kamar yadda muka sani ana magana ne kan abu na musamman wanda ya kasance yana gudanar da aiki na musamman. Samunta na’urar Intelligen ya kawo sauyi da ci gaba da yawa ta fuskar samar da abubuwa da dama. Domin na’ura ce da take gudanar da aikin da ya wajaba akanta ba tare da an umarceta da yin hakan ba, ma’ana dai ta kan sarrafa kanta da kanta yayin gudanar da aikin kuma cikin ƙwarewa da sanin makamar aikin. Daga cikin aikin na’urar Intelligent akwai; karanta takardun kuɗi da da kuma ƙirga kuɗi ba tare da amfani da wani abu ba, karɓar ajiyar kuɗi masu yawa, da kuma mu’amala da software ta banki don bayar da shawarwari game da cigaban banki bisa wasu tsare-tsare.
Drive-through ATMs
Na’ura ce da ake amfani da ita a shahararrun wurare da dama na faɗin duniya, musamman a ƙasar Amurka. Na’urar na da sauƙin gudanar da harkokin banki, ta kan ba da damar gudar da harƙala tsakanin masu mu’amala da banki ko da suna daga kan abin hawansu ko kuma gidajensu. Wannan na’ura an tsarata ne domin bayar damar saurin fitar da kuɗi da ajiya ba tare da buƙatar mai ajiyar ya taso daga inda yake ba, wanda hakan kan yi amfani musamman a lokacin yanayi mara kyau ko buƙatun masu ajiya na musamman. Haka kuma wannan nau’in na’ura tana da amfani matuƙa musamman ga masu gudanar da kasuwanci dake kan hanyoyi masu cunkoso ko kuma nesa da bankuna.
Recycling ATMs
Na’ura ce da aka samar domin amfani da kuɗi, na’ura ce da aka ƙirƙira wacce ke sarrafa hanyar fitar da kuɗi cikin sauri tare da taimakawa abokan mu’ala yin aiki cikin sauƙaƙawa. Aiyukan na’urar na da dama kamar sabunta kuɗi, wato fito da sababbin kuɗi kuma tana aiki akai akai ba tre da gajiyawa ba. Haka kuma na’urar bata tsaya iya nan ba har ma da taimakawa wurin fitar da kuɗi masu inganci tare da tabbatar da nagartarsu.
Bitcoin ATMs
Na’urar Bitcoins na’ura ce da ake amfani da ita wurin tsarin cryptocurrency. Wadda ta taka rawar gani wurin kawo ci gaba a harkar abin da ya shafi Crypto. Tare da tasirin cryptocurrency, ATMs na Bitcoin sun fara bayyana a wurare daban-daban na birane a duniya. Waɗannan ATMs suna ba wa masu amfani damar saye ko sayar da bitcoins ta hanyar amfani da kuɗi. Wasu samfuran suna kuma goyon bayan wasu cryptocurrencies kamar Ethereum ko Litecoin. Wanda hakan ya kawo muhimmin ci gaba ga masoya crypto da ke buƙatar samun sauƙi don saye ko sayar da kuɗin dijital ɗin su.
Mobile ATMs
Mobile ATMs nau’in na’ura ce da ake amfani da ita wurin ɗaukar hoto, musamman ake amfani da ita a lokutan buƙatar sabunta wani abu na banki. Sai dai kuma amma ba ta da sauƙin samu. Ana iya samunta a wurare kamar wurarren kiɗa, bukukuwa, ko manyan wurare na taron jama’a. Na’urar tana yin aiki yadda ya kamata kamar fitar da kuɗi. motoci da za a iya motsawa kamar yadda ake buƙata.
On-Site and Off-Site ATMs
Na’urar cirar kuɗi ce wadda ta kasance a cikin banki. Tana da matuƙar tsaro da kuma sauƙi wurin cirar kuɗi ko kuma turawa. Haka kuma takan taimaka wurin abokan cinikayar dake yawaita ziyartar banki akai akai. Wanda hakan ka bayar da kyakyawar mu’amal tsakanin banki da kuma abokanan hulɗa. Har illa yau kuma na’urar ana iya samunta a wurare daban-daban. Kamar;Kasuwani da filayen jirgin sama, da kuma shagunan abinci. Na’urar kan inganta hanyar cirar kuɗi fiye da ƙima tare da tabbatar da abokan mu’amal sun samu kuɗinsu cikin kwanciyar hankali.
Manazarta
Wavetec. (2024, November 27). Common ATM Problems and solutions: Enhancing ATM reliability. Wavetec.
Wikipedia contributors. (2001, December 8). ATM. Wikipedia.
“FNSRTS307A – Maintain Automatic Teller Machine (ATM) services”. training.gov.au. Archived from the original on 7 April 2014.