Azumin Ramadan na daga cikin ayyukan da Allah Ya wajabta wa bayinsa, kuma rukuni ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, kamar yadda ya tabbata a Hadisin da Abdullahi bin Umar (R.A.) ya rawaito, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: “An gina Musulunci akan abubuwa guda biyar; Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, da kuma shaidawa Annabi Muhammad Manzon Allah ne, da tsayar da sallah, da bada zakkah, da aikin hajji, da azumin watan Ramadan”. Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Lallai yana daga cikin ni’imomin da Allah Ya yi wa bayinsa yadda ya sanya musu lokuta masu falala da daraja don yin ibadoji masu girma, ta yadda bayinsa ke yawaita ayyukan alheri a wadannan lokutan. Kuma Allah yana kankare zunubai, yana ninninka ladan ayyuka, Ya kuma saukar da rahamominsa. Daga cikin wadannan lokuta akwai watan Ramadan wanda Allah Ya saukar da Al-Kur’ani a cikinsa kamar yadda ya fada: “Watan Ramalãna ne wanda aka saukar da Alƙur’ãni a cikinsa yana shiriya ga mutãne da hujjõji bayyanannu daga shiriya da rarrabawa”. (Suratul Bakara, aya ta: 185)
Watan Ramadan wata ne mai albarka da alkhairai masu yawa, watan azumi ne da nafilfilun dare, watan rahama ne da gafara da kuma yantar da bayi daga wuta, watan kyauta da sauran ayyukan alheri.
Yadda za mu amfana da falalar watan Ramadan
Akwai abubuwa da dama da ya dace Musulmi ya yi don fiskantar watan Ramadan. Ga kadan daga cikinsu:
1. Addu’a
Yawan addu’a Allah Ya kai mu wata mai albarka na Ramadan, saboda haka magabata suka kasance suna yi, suna rokon Allah har tsawon wata shida da ya nufe su da kaiwa watan Ramadan, sa’an nan bayan azumi suna yin addu’a na tsawon wata shida kan Allah Ya karba musu ayyukan da suka yi a watan.
Idan watan Ramadan ya tsaya akwai addu’ar da ake yi kamar yadda ya tabbata a hadisi. Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yana cewa: “Allahumma ahillahu alaina bil amni, wal iman, was salaamati, wal Islam, Rabbi, wa Rabbukal Laah”. Hakim ne ya rawaito wannan hadisi.
Ma’anar Adduar ita ce: Yaa Allah kasa (wannan wata ya kasance) na samun tsaro, da imani, da zaman lafiya, da Musulunci, Mahaliccina, kuma Mahaliccinka Allah.
2. Godiya ga Allah
Yin godiya ga Allah wanda Ya raya mu, Ya kuma nuna mana watan Ramadan, watan da ake yin rige-rigen ayyukan alheri a cikinsa. Mutum nawa ne yayi azumin bara tare da mu, amma bana Allah bai nuna masa na wannan shekarar ba, Allah Ya dauki ran shi, yana cikin kabari, yana neman addu’ar yan uwansa musulmai, yana burin ina ma da Allah zai dawo da shi duniya ya samu wannan daman ta yin ibada a watan Ramadan? Lallai wannan ni’ima ce babba, dole mu gode wa Allah a kan ta.
Imam An-Nawawi a cikin littafinsa “Al-azkar” ya ce: “Ka sani, an so ga wanda wata ni’ima ta zahiri ta jaddadu agare shi, ko kuma aka tunkude masa wani bala’i ko musiba, yayi sujudar godiya ga Allah Madaukakin Sarki, kuma ya gode masa, kuma yayi yabo gare Shi da abinda ya dace da matsayinsa”
3. Farin ciki da zuwan watan Ramadan
Ya tabbata a Hadisi Manzon Allah S.A.W., ya kasance yana yi wa sahabbansa albishir da zuwan watan Ramadan, yana cewa: “Ramadan ya zo muku, wata mai albarka, wanda Allah Ya wajabta muku azumtar shi, ana bude kofofin sama (Aljannah), ana kulle kofofin wuta, ana kuma daure shaidanu. Akwai wani dare a cikin watan wanda ya fi dare dubu. Duk wanda aka haramtawa alherinsa, to hakika ya haramtu”. Imam Ahmad ne ya rawaito wannan hadisi.
Ya dan uwa mai albarka, yaya ka ke ji idan wani bako mai daraja da kake jiran sa tsawon shekara zai zo maka, ya kake ji idan ya zo maka? To ga Ramadan nan ya zo mana. Wani tanadi ka masa? Shin ka shirya tarban sa ta hanyan aikata kyawawan ayyuka a cikinsa?
4. Biyan bashin azumin baya da yake kan ka
Wajibi ne ga duk wanda ake bin shi bashin azumi, ya gaggauta biya kafin watan Ramadan ya riske shi. Hadisi ya tabbata, Nana Aisha (RA) tana cewa: “Ramakon azumin Ramadan yana kasancewa a kaina, bana samun damar biya sai a cikin watan Sha’aban”.
5. Neman sanin hukunce-hukuncen azumin Ramadan kafin zuwan watan
Wajibi ne ga musulmi ya nemi sanin yadda zai bautawa Allah, ciki har da yadda zai yi azumin Ramadan, saboda baya halatta musulmi ya bauta wa Allah cikin jahilci. Daga cikin hanyoyin neman sani; tambayar Malamai. Allah Ya ce: “Ku tambayi ma’abota ilimi in kun kasance baku sani ba”. (Suratul Anbiya, aya ta 7).
Mai littafin Akh-dhari yace: “Baya halatta (ga musulmi) ya aikata wani aiki har sai ya san hukuncin Allah a cikinsa. Kuma Ya tambayi maluma (don neman sani)…”.
6. Tuba ga Allah Madaukakin Sarki kan ayyukan zunubai da ka aikata a baya
Mutum ya tuba ga Allah, sannan kuma ya yi kekkyawan niyya kan ba zaka koma aikata sabon ba, saboda fiskantar watan gafara da rahama.
Allah ma daukakin Sarki Ya yi kira ga bayinsa da su rika tuba zuwa gare shi kamar yadda ya fada: “…. Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo”. (Suratul Nur, aya ta 31).
Mai Akh-dhari yace: “Sharudan tuba sune: Nadama kana bin ya cude, da kuma niyya kan ba zai koma zuwa aikata zunubai ba cikin abinda ya saura na rayuwar sa, kuma ya bar aikata sabo nan take in ya kasance ya cudanya da shi”.
8. Yin kyakkyawar shiri don ribatan watan Ramadan
Saboda kwanaki yan kadan ne masu saurin karewa, yana da kyau mutum ya yi kyakkyawar shiri don ribatar lokacin. Idan mutum bai yi haka ba, to yayi asara.
Allah Ya ce: “Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda su gabace ku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa. Kwanuka ne ƙidãyayyu“. Suratul Bakara, aya ta 183-184
9. Daura kyakkyawar niyya don azumtar watan Ramadan mai daraja, tare da imani da neman lada
Manzon Allah S.A.W yace: “Duk wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada, to Allah zai kankare masa abinda ya gabata na zunaban shi”. Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.
10. Kwadaitarwa kan ciyar da masu azumi
Ya zo a Hadisin Manzon Allah S.A.W. ya ce: “Duk wanda ya ciyar da mai azumi abin buda baki, to yana da lada kwatankwacin ladan mai azumin, ba tare da an rage wa mai azumin ladan sa ba”. Imam Ahmad da Tirmizi da Ibn Majah ne suka rawaito shi.
11. Shiri na musamman game da karanta Al-Kur’ani da fahimtar ma’anoninshi
Mala’ika Jibril A.S. ya kasance ya na haduwa da Manzon Allah S.A.W. sau daya a kowane watan Ramadan don su yi darasin Al-Kur’ani. Ya kuma hadu da shi sau biyu a shekarar da ya rasu.
Wasu daga cikin magabata sun kasance suna karanta Al-Kur’ani gaba dayan sa a cikin kwana uku na watan Ramadan, har a kan samu wasu daga cikinsu suna sauke shi a kowani dare a cikin kwanaki goman karshe na watan.
12. Shiri na musamman don kyautata mu’amala da mutane
Musulmi ya yi shirin kyautata mu’amalarsa da mutane, ya kuma kiyaye harshesa da gabobinsa, da kuma kauracewa abinda Allah Ya haramta
Manzon Allah S.A.W. ya ce: “Duk wanda bai bar karya da kuma aiki da shi ba, to Allah baya bukatar ya bar abincinsa da abin shansa”. Buhari ne ya rawaito wannan hadisi.
Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan da Musulmi ya kamata ya yi a lokacin shigowar Ramadan mai albarka.
Falalar azumin Ramadan
Watan Ramadan yana da falala masu yawa wanda ya kebanta da su kan sauran watanni. Ga kadan daga cikin cikinsu:
An saukar da Al-Kur’ani a watan Ramadan
Allah Ya ce: “Watan Ramalãna ne wanda aka saukar da Alƙur’ãni a cikinsa yana shiriya ga mutãne da hujjõji bayyanannu daga shiriya da rarrabawa”. (Suratul Bakara, aya ta: 185).
Azumin watan Ramadan yana kara taƙawa
Allah Ya ce: “Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda su ka gabace ku, tsammãninku, zã ku yi taƙawa”. (Suratul Bakara, aya ta 183)
A watan Ramadan a na bude kofofin Aljannah
An karbo daga Abu-Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: ‘Yayin da watan Ramadan ya tsaya, sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Hakika Ramadan ya zo muku, wata ne mai albarka, (wanda) Allah Ya wajabta muku azumtar sa. Ana bude kofofin Aljanna a cikinsa, kuma ana rufe kofofin wuta a cikinsa, ana kuma daure shaidanu a cikinsa. A cikinsa akwai wani dare wanda ya fi dare dubu, duk wanda aka haramtawa alkhairinsa, toh hakika ya haramtu”’. Imam Ahmad da Nasa’I ne suka rawaito wannan Hadisi.
Azumin watan Ramadan yana kankare zunubai
Daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: ‘Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Salloli biyar, daga Juma’a zuwa Juma’a, da kuma Ramadana zuwa Ramadana, suna kankare abin da ke tsakaninsu, idan an nisanci manyan zunubai”’. Muslim ne ya ruwaito shi.
A wani Hadisin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Wanda ya yi azumin watan Ramadan, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Allah na ‘yanta bayinsa daga wuta
An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: ‘Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Idan daren farko na Ramadan ya kasance, akan ɗaure shedanu da aljanu masu taurin kai, kuma akan rufe ƙofofin Wuta, ba a buɗe koda ƙofa ɗaya daga cikinsu, kuma akan buɗe ƙofofin Aljanna, ba a rufe koda guda ɗaya daga cikinsu. Sai mai shela ya yi kira: Ya mai neman alheri ka kusanto. Ya mai neman sharri, ka taƙaita. Kuma Allah yana da waɗanda yake ‘yantawa daga shiga Wuta, wannan kuma a cikin kowane dare”. Imam Ahmad da Tirmizi da Nasa’I da Ibn Majah ne suka rawaito Hadisin.
Ana ninninka ladar aikin Umurah
Daga Abdullahi Bin Abbas (R.A), Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Umrah a cikin Ramadan tana daidai da aikin Hajji, ko (tana daidai da) Hajji tare da ni”. Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Malamai sun yi bayani cewa wannan Hadisin yana nuni kan umrah a Ramadan tana daidai da aikin hajji a lada ne, ba wai umrar tana zama madadin Hajji na farilla ba. Duk wanda bai taba yin aikin Hajji ba, to in ya yi Umrah a cikin watan Rahamada ba za ta dauke masa aikin Hajji ba.
Kebantar watan Ramadan da sallar Tarawihi
Watan Ramadan ya kebanta da sallar tarawihi wadanda suke da falaloli masu yawa (dukkan Malamai sun hadu akan sunnah ne yin su)
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Wanda ya yi tsayuwar sallah a watan Ramadan, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito Hadisin.
Imam An-Nawawi yace: “Fadin Manzon Allah S.A.W (Wanda ya yi tsayuwar Ramadan) wannan sigar tana nuna kwadaitarwa da kuma (nuna yin sallolin) mustahabbi ne, ba wajibi ba ne. Kuma Malamai sun hadu akan tsayuwar Ramadan (sallolin tarawihi) ba wajibi ba ne, mustahabbi ne”.
Akwai daren lailatul ƙadri cikin Ramadan
Allah Yace: “Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur’ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja). To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul Ƙadari? Lailatul Ƙadari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu”. (Suratul Kadri, aya ta 1 – 3).
Imam Al-Baghawi yace: “Ma’anar wannan aya itace: Aiki nagari a cikin lailatul Kadiri ya fi alheri kan ayyuka a dare dubu in an cire lailatul Kadiri a cikinsu”.
Ya tabbata a Hadisi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Wanda ya yi tsayuwar daren lailatul Kadiri, yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito Hadisin.
Watan ciyarwa da kyauta da sadaka
An karbo daga Abdullahi Ibn Abbas Allah ya yarda da shi, ya ce: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance ya fi dukkan mutane kyauta, kuma ya kasance lokacin da yafi kyauta shi ne a cikin Ramadan, lokacin da Mala’ika Jibrilu yake haduwa da shi. Kuma mala’ika Jibrilu ya kan hadu da shi a kowane dare a cikin Ramadan, sai ya yi bitar Al-kur’ani tare da shi. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya fi iska mai kadawa alheri”. Buhari da Musulim ne suka rawaito Hadisin.
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Duk wanda ya ciyar da mai azumi abin buda baki, to yana da lada kwatankwacin ladan mai azumin, ba tare da an rage wa mai azumin ladan sa ba”. Imam Ahmad da Tirmizi da Ibn Majah ne suka rawaito shi.
Yin itikafi a watan Ramadan
An karbo daga Nana Aisha Allah ya yarda da ita, ta ce: “Annabi (tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana itikafi a kwanaki goman karshe na Ramadan har Allah Ya dauki ran shi, sa’an nan sai matansa suka yi itikafi bayan sa”. Buhari da Muslim ne suka rawaito wannan Hadisi.
Abubuwan da ke karya azumi
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako.
A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka kawo kadan daga cikinsu. A yau za mu duba wasu daga cikin abubuwan da za su iya batawa mutum azumi. Ga su nan kamar haka:
1. Cin abinci ko shan abin sha da gangan
Allah Ya ce: “Kuma ku ci ku sha har farin igiya ya bayyana a gare ku daga bakin igiya daga alfijir, sa’an nan kuma ku cika azumi zuwa dare”. Suratul Bakara, aya ta 187.
Saboda haka, duk wani abin da aka saka a baki ya wuce makogoro zuwa cikin ciki, to yana karya azumi, haka nan duk abinda ya shiga ta hanci ya wuce makogoro har ya isa ciki, to shi ma yana karya azumi.
Amma duk wanda ya ci ko ya sha bisa mantuwa, to azumin sa bai karye ba. Saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: “Wanda ya manta yana azumi sai ya ci ko ya sha, to ya cika azuminsa, Allah ne Ya ciyar da shi, Ya kuma shayar da shi”. Buhari da Musulim ne suka rawait Hadisin.
Wannan Hadisi yana nuna idan da gangan mutu ya ci ko ya sha, to azuminsa ya karya, sa’banin in a mantuwa ya ci ko ya sha.
2. Duk abinda ya ke daukan ma’anar ci da sha
Abubuwan da suke daukar ma’anar ci da sha suna karya azumu, misali:
- Karin jinni da za’a yiwa mara lafiya yana karya azumi, saboda yana madadin ci ko sha ga mai jinya.
- Allura da ake yi wa mara lafiya wanda yake madadin abinci ko abin sha, shima yana karya azumi, haka nan ruwa da ake daura wa mara lafiya.
3. Yin Jima’i
Wannan shine mafi girma cikin abubuwan da suke karya azumi, kuma laifinsa ya fi ko wanne girma. A duk lokacin da mai azumi yayi jima’i, to azuminsa ya karye, azumin farilla ne, ko na nafiya.
Idan jima’in ya auku ne a watan Ramadan da rana ga mai azumi, to dole ya tuba ga Allah Madaukakin sarki akan wannan zunubi mai girma, kuma ya kame bakinsa na wannan ranar da yayi jima’i, tare da biyan azumin wannan ranar, da kuma kaffara mai tsanani akan shi. Kaffarar itace: ‘Yanta baiwa mumina. In kuma bai samu ba, to zai yi azumin kwana sittin a jere. In kuma bai samu wannan ba, to zai ciyar da miskinai sittin.
Dalili a kan wajabcin kaffara shine Hadisin Abu Haraira (Allah Ya yarda da shi), yace: ‘Wata rana mun kasance muna zaune wajen Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) sai wani mutum ya zo masa, yace na halaka! Sai (Annabi) ya ce masa: “Me ya same ka?” Sai (mutumin) ya ce: Na sadu da matata alhalin ina azumi. Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Shin zaka samu baiwa ka ‘yanta ta?”. Sai ya ce: A a. Sai ya ce: “Shin zaka iya yin azumi watanni biyu a jere?” Sai ya ce: A a. Sai ya ce: “Shin kana da damar ciyar da miskinai sittin?” Sai ya ce” A a. Sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya zauna, muna nan cikin wannan hali, sai aka zo wa Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da wani masaki mai dabino a cikinsa. Sai ya ce: “Ina mai wancan tambayar?” Sai ya ce: Ni ne. Sai ya ce: “Karbi wannan, ka yi sadaka da shi”. Sai Mutumin ya ce: Ya Manzon Allah! Shin akwai wanda ya fini talauci? Na rantse da Allah tsakanin duwatsun Madina guda biyu babu wasu iyalai da suka fi iyalaina talauci. Sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi dariya har sai da fikokinsa suka bayyana. Sa’an nan ya ce: “Ka je ka ciyar da shi ga iyalanka”. Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.
4. Yin abinda zai fitar da maniyyi
Fitar maniyyi ta hanyar rungumar mace ko shafa jikinta, ko sumbatar ta, ko ta hanyar wasa da al’aura, ko ta hanyar kallon mata, duk wannan baya halatta ga mai azumi, saboda suna cikin abubuwan da ya wajaba ga mai azumi ya nisance su. Ya zo a Hadisil kudusi, Manzon Allah ya ce: ‘Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “Yana barin abincinsa da abin shansa da sha’awarsa don ni”’. Buhari da Muslim ne suka rawaito Hadisin.
Duk wanda ya aikata wadannan abubuwa da aka ambata har maniyyi ya zuba masa, to azuminsa ya karye, dole ya tuba ga Allah Madaukakin Sarki, kuma ya kame daga ci da sha a wannan ranar, kuma zai biya azumin wannan ranar, amma babu kaffara akan sa.
Amma duk wanda maniyya ya fito masa ba da son shi ba, kamar ta hanyar mafarki, ko ta hanyar duka da aka masa ko ta wata hanyar ta daban da ba ta hanyar sha’awa ba, to azuminsa bai karye ba.
Idan kuma maziyyi ne ya fitowa mai azumi ta hanyar sumbatar mace ko taba jikinta ko makamancin haka, to malamai sun yi sabani kan karyewar azuminsa. Amma Magana mafi rinjaye itace azuminsa bai karye ba, sai dai ya kamata mai azumi ya kauracewa abinda zai jawo masa fitar maziyyin.
5. Fitar jini ta hanyar yin kaho
An karbo daga Sauban, Allah ya yarda da shi, yace: ‘Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: “Wanda ya yi kaho azuminsa ya karye, da kuma wanda aka masa kahon”. Imam Ahamd da Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne saka rawaito shi.
Wannan shine abinda Imam Ahmad da wasu malaman fikihu masu yawa suka tafi a kai. Haka kuma an nakalto maganar daga wasu Sahabbai da Tabi’ai kamar Aliyu Bin Abi Dalib da Abu Huraira da Nana Aisha (Allah Ya yarda da su) da Al-Hassanul Basari da Ibn Sirin da Ada’u da sauransu. Kuma shine zabin Sheikhul Islam Ibn Taimiyya da almajirinsa Ibnul Kayyim da Ibn Baz da Ibn Usaimin.
6. Kwakulo amai dagangan
An karbo daga Abu Hurarira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: ‘Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Wanda amai ya rinjiye shi, to babu ramako akansa, wanda kuma ya janyo amai da ganganci, to ya rama”. Imam Ahmad da Tirmizi da Ibn Majah ne suka rawaito shi.
7. Fitowar jinin haila ko jinin biki
Idan mace ta yi azumi, sai jinin haila ko kuwa jinin biki, wato jinin haihuwa, ya zo mata, to azumin ta ya karye, sai ta ci ta sha. Amma zata rama wannan azumin. An karbo daga Abu Sa’id Al-Khudri (Allah Ya yarda da shi), yace: ‘Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: “Shin mace ba ta kasance idan tana haila, bata yin sallah, kuma bata azumi ba? To wannan yana daga cikin tawayar addininta”. Buhari ne ya rawaito shi.
Wannan Hadisi ya ambaci jinin haila kadai, amma ana hadawa da jinin haihuwa, saboda hukuncinsu daya ne wajen hana sallah da azumi.
8. Ridda
Yana daga cikin abubuwan dake bata a zumi yin ridda. Idan mai azumi ya yi ridda (wa iyazu billah) to azuminsa ya warware, saboda musulunci na cikin sharudan karban azumi.
Duk wadannan abubuwan masu karya azumi suna karya shi ne idan an samu sharuda guda uku, amma banda fitowar jinin haila da na biki:
- Ya zama mai azumi ya san abubuwan suna karya azumi
- Ya zama ya aikata su da gangan, ba bisa mantuwa
- Ya zama da zabinsa ya aikata, ba tilasta masa aka yi ba.
Wadannan sune abubuwan da suke karya azumi, kuma wajibi ne duk mai azumi ya nisanci aikata su ko kuwa ya kiyaye aukuwansu gareshi. Da fatan Allah Ya karba mana ibadunmu baki daya.
Kura-kuran masu azumi
Kura-kuran masu azumi na da dama, wadanda ake bukatar duk mai azumi ya lura da su don inganta ibadarsa. Ga kura-kuran na kasa su kamar haka:
Na farko: Kura-kurai lokacin fuskantar watan Ramadan
- Yin azumi kwana daya ko biyu kafin shigowar Ramadan. Yin hakan ya saba wa sunnah. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Kada ku rigayi Ramadan da azumtar yini daya, ko biyu, sai dai ga mutumin da ya kasance yake yin wani azumi (na nafila), to ya azumce shi”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
- Rashin kulawar wasu Musulmai ga lissafin kirgen watan Sha’aban.
- Dogaro da abinda masu ilimi falaki suka fada wajen ganin watan Ramadan. Allah Ya ce: “To duk wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi“. Suratul Bakara, aya ta 185. Kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Idan kuka gan shi –wato jinjirin wata- sai ku yi azumi, idan kuma kuka gan shi, sai ku ajiye azumi, idan kuma aka yi muku hazo, sai ku kaddara masa”. A wata riwayar: “Idan aka yi muku hazo, to sai ku cika kirgen sha’aban talatin”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
- Dogaro da ganin wata na wata kasa.
- Akwai masu bakin ciki da zuwan Ramadan, ma’ana basu farin ciki da zuwan sa, wannan ma kuskure ne. Saboda ya tabbata Manzo Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana yiwa sahabbansa albishir da zuwan Ramadan. Daga Abu Huraira (R.A), yace: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Ramadan ya zo muku, wata mai albarka, Allah ya wajabta azumtar sa akan ku….”. Nisa’I ne ya rawaito shi.
- Rashin kwana da niyyar daukan azumi. Wannan kuskure ne. Duk wanda ya ji labarin ganin watan Ramadan, to dole ne ya daura niyya kafin ketowar alfijir. Saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Duk wanda bai kwana da niyyar azumi gabannin ketowar alfijir ba, to bashi da azumi”. Tirmizi da Nasa’I da Ibn Majah ne suka rawaito shi.
- Rashin kame baki ga wanda ya samu labarin ganin wata da rana.
- Jahiltar abubuwan da suke karya azumi ko suke bata shi.
- Tarbar watan Ramadan ta hanyar kade-kade da raye-raye.
Na biyu: Kura-kurai a sahur
- Wasu masu azumi sukan ki yin sahur, ko kuma su yi sahur tun cikin dare su kwanta bacci. Wannan ya sabawa sunnah. Mustahabbi ne mutum yayi sahur kafin ketowar alfijin, saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Ku yi sahur, saboda cikin yin sahur akwai albarka”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. Haka nan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya na jinkirta sahur.
- Wasu masu azumi na dogara wajen kame baki da kiran sallah a masallaci, basu san cewa mafi yawan masallatai basu san lokacin kiran sallah ba. Wajibi ne ga musulmi ya san lokacin sallah, ko ya dogara ga masallacin da suke kiran sallah akan lokaci.
- Cika ciki nak lokacin sahur, wanda hakan zai saka shi kasala.
- Yin bacci bayan sahur, wanda yin hakan zai iya jawo a rasa sallar Asuba.
Na uku: Kura-kurai a wunin Ramadan
- Gafala kan zikiran safe da yamma.
- Wasu masu azumi na tunani wunin azumi dama ce ta yin bacci da hutu. Sun manta watan Ramadan wata ne na nishadi da ibada, har ma akwai yakokin da Musulmai suka yi su a cikin watan Ramadan, kuma suka samu nasara, kamar yakin Badar.
- Wasu masu azumi sukan jinkirta yin sallan Azahar da La’asar, saboda yawan bacci da suke yi.
- Wasu masu azumi sukan yi sakaci a wunin azumi da kuma bata lokutan su ta hanyar taro a tituna ko dandali ko ta hanyar kallon fina-finai, da sunan rage lokaci.
- Wasu masu azumi kan yi zagi da karya da shedar zur a yayin da suke azumi.
Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Duk wanda bai bar zancen karya ba, da aiki da shi ba, to Allah baya da bukatar barin cinsa da shansa”. Bukhari ne ya rawaito shi. Haka nan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Azumi garkuwa ne, idan ranar azumin dayanku ya zo, to kada ya yi batsa, kada kuma ya yi shewa, idan wani ya zage shi ko ya nemi fada da shi, to ya ce: ‘Ni mai azumi ne’”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. Kuma Manzon Allah ya fada cewa: “Da yawa ana samun mai azumi baya samun komai a matsayin lada sai dai kawai yunwa da yake sha”. Ibnu Maja ne ya rawaito hadisin.
Na hudu: Kura-kurai a buda baki
- Wuce gona da iri wurin tanadar abincin buda baki, ta yadda mai azumi zai tanadi nau’uka daban-daban na abinci har ma su kai goma ko fiye da haka. Wannan zai shiga layin barna, wanda shari’a ta hana. Allah Ya ce: “Kuma ku ci, kuma ku sha, kuma kada ku yi barna. Lalle ne Shi (Allah) ba Ya son masu barna“. Suratul Araf, aya ta 31.
- Barin yin addu’a lokacin buda baki. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance idan ya yi buba baki yana cewa: “ZAHABAZ ZAMA’U, WABTALLATIL URUKU, WA SABATAL AJRU IN SHA ALLAH“. Abu Dauda ne ya rawaito shi. Ma’ana: “Kishin ruwa ya tafi, jijiyoyin wuya sun jike, lada ya tabbata in Allah Ya so”. Kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Mutum uku ba a mayar da addu’o’insu; Shugaba mai adalci, mai azumi har sai ya yi buda-baki, da kuma addu’ar wanda aka zalunta”. Tirmizi da Ibnu Majah ne suka rawaito shi.
- Jinkirta buda-baki. Wannan ya sabawa sunnah. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Mutane ba zasu gushe suna kan alheri ba, matukar suna gaggauta buda-baki“. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
- Wasu masu azumi sukan jinkirta buda baki har sai bayan sun yi sallar magariba. Wannan kuskure ne, ya sabawa sunnar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi). Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana yin buda-baki kafin yayi sallar magariba koda da ruwa ne. An karbo daga Anas Bin Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana buda-baki da dayyen dabino gabanin ya yi sallah, in kuma bai samu danyen dabinon ba, sai ya yi buda-baki da busasshen dabino, in kuma bai samu ba, sai ya sha ruwa”. Abu Dauda da Tirmizi ne suka rawaito shi.
- Jinkintar sallar magariba da wasu masu azumi ke yi sakamakon shagaltuwa da ciye-ciye bayan buda-baki.
- Wasu masu shan taba da zaran sun ji kiran sallar Magariba, zasu dan ci wani abu kadan, sannan su gaggauta kunna sigari su sha, har ma ana iya samun wanda zai fara buda-baki da sigari, kafin ya ci wani abu. Ya kai dan uwa mai albaka! Watan Ramadan dama ce ka samu don ka nisanci shan shigari.
- Wasu masu azumi sukan shagalta da buda-baki, basu iya bibiyar mai kiran sallah.
- Wasu masu azumi basu yin buda-baki har sai ladan ya gama kiran sallah.
Na biyar: Kura-kurai a sallar tarawihi
- Wasu mutane sun jahilci falalar sallah tarawihi, hakan yake sa basa yin sallar. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Duk wanda yayi tsayuwar Ramadan (Sallah Tsarawihi) yana mai imani da neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
- Akwai mai yin sallar tarawihi shi kadai, da hujjar wai liman baya yin raka’a goma sha daya, ko kuma wai liman yana tsawaita karatu, ko kuma wai liman baya tsawaita ruku’u da sujada, da makamancin haka.
- Wasu masu sallar tarawihi tare da liman sukan bibiyi karatun limami su rika yi tare da shi, ko kuma su rike al-kur’ani suna kallo, da hujjar wai suna koyon karatu da kuma sanin inda liman yake karantawa. Wannan yana kore kushu’i na nitsuwa a cikin sallah, yadda mai yin hakan zai rika shagaltuwa da bude shafukan al-kur’ani, haka nan zai zama ya rike shi lokacin ruku’i da sujada ba zai sanya hannun sa inda ya dace ba, ko kuma ya ajiye Al-kur’anin a kasa, duk wannan ya sabawa siffar sallar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam.
- Wasu masu sallar tarawihi tare da liman su kan ki su jira su karasa sallar tare da liman, musamman in sun ga liman yana sallah fiye da taka’a goma sha daya ko raka’a goma sha uku. Abinda ya fi dacewa shi ne su yi hakuri su jira liman ya kammala sallar tare da su, saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Duk wanda ya tsaya tare da liman har ya kammala, to za’a rubuta masa ladan tsayuwar dare”. Abu Dauda da Tirmizi da Nasa’I da Ibn Majah ne suka ruwaito hadisin.
- Yin witiri sau biyu a dare daya, wannan ya sabawa sunnah. Saboda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Babu witiri biyu a dare daya”. Tirmizi ne ya rawaito shi.
An wallafa wannan makalar 18 February, 2023, sannan an sabunta ta 25 January, 2026.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.



