Skip to content

Balaga

Lokacin balaga lokacin ne da ɗaukacin halittar ɗan adam ta zahiri da ta baɗini kan sauya daga halittar ƙananan yara zuwa ta manyan mutane. Wannan sauyin halitta ba abu ne da ke faruwa dare ɗaya ba, yakan ɗauki wani ɗan lokaci da ba zai kasa wasu ‘yan shekaru ba. A cikin wannan lokaci yara suna buƙatar kulawa ta musamman daga wurin iyaye saboda akwai matsalolin da kan iya aukuwa da za su shafi yadda  yara ke gudanar da rayuwar su har abada.

Alamomin balaga ga maza da mata

Lokacin fara balaga

A takaice, lokacin balaga lokaci ne da yara suke manyanta kuma hakan yana jawo sauye-sauye a jikinsu da kuma yadda suke ji. A wannan lokacin, yara suna zama a shirye don haihuwa. Yayin da mutum yake balaga, jikinsa na sakewa nan da nan kuma kwayoyin jikinsa za su manyanta da wuri.

Ƙananan yara mata suna fara balaga ne a lokacin da suke tsakanin shekara takwas (8) zuwa shekara goma sha uku (13). Su kuma yara maza suna fara balaga ne a lokacin da suke tsakanin shekara tara (9) zuwa shekara goma sha huɗu (14). Wannan shi ne lafiyayyen wa’adin da mafi yawancin yara suke fara nuna alamomin balaga wanda likitoci masu ƙwarewa ta musamman a fannin kiwon lafiyar yara suka yarda dashi.

Balaga ga maza

Ƙwaƙwalwa ita ce ke sarrafa dukkan gangar jikin ɗan’adam. Yayin da ɗan’adam ya kai mizanin balaga wani sashe na ƙwaƙwalwar sa da ake kira da hypothalamus-pituitary-gonadal-axis ya kan yi umurni ta hanyar fitar da wasu sinadaran hormones da ake kire leutenizing hormone (LH) da follicle stimulating hormone (FSH) zuwa cikin jini.

Sauyin da balaga ke haifarwa ga yara maza

A jikin maza, waɗannan sinadaran hormones na LH da FSH sukan yi umurni ga ‘ya’yan maraina (testes) da su fara fitar da wadatattun sinadaran hormones na androgens. Wadatuwar sinadaran androgens waɗanda ‘ƴa’yan maraina ke ƙirƙira kuma su fitar da su a cikin jinin yaro matashi a yayin da ya fara balaga shi ne yake sanya duk wani canji da ke faruwa ga yaro a lokacin balaga.

Waɗannan sinadaran hormones na androgens su ne ke kula da sauya halittar yaro ƙarami zuwa baligin namiji, su ne ke kula da sha’awar namiji da kuma dukan abin da ya shafi harkokinsa na jima’i. Muhimman sinadaran hormones na androgens guda uku ne kamar haka:

  • Testosterone
  • Dihydrotestosterone
  • Androstenedione

Ƙirƙirar waɗannan sinadaran hormones na androgens yana ƙaruwa sosai a lokacin da yaro ya kai mizanin shekarun balaga, wannan shi ne musabbabin duk wani sauyin yanayi da ake samu yayin balaga.

Alamomin balagar maza

Alamomin balagar maza suna fara bayyana ne ga ‘ya’an maraina (testes) da kuma fatar da ke ɗauke da su (scrotum).

  1. ‘Ya’yan maraina zasu ƙara girma
  2. Fara fitowar gashi a mara
  3. Fitowar gashi a fatar da ke ƙunshe da ƴaƴan marina
  4. Azzakari zai ƙara girma da kauri
  5. Azzakarin yaro zai kama miƙewa akai-akai, musamman idan yaro yana bacci.
  6. Fitar da ruwan maniyyi
  7. Mafarkin jima’i tare da fitar da ruwan maniyyi
  8. Fitar gashi a ƙarƙashin hamata
  9. Fitar gashi a fuska; gemu, saje da gashin baki
  10. Muryar yaro za ta ƙara kauri
  11. Wasu maza sukan samu fitar nono guda ko duka biyu, wanda daga baya zai zo ya ɓace bayan watanni 6 zuwa 18.
  12. Kafaɗar yaro zata ƙara girma ƙirjin sa ya buɗe.
  13. Jikin yaro zai ƙara girma sosai
  14. Yaro zai fara sha’awar mata da sha’awar yin jima’i.

Balaga ga mata

Idan mace ta kai mizanin balaga ita ma sashen ƙwaƙwalwarta da ake kira hypothalamus-pituitary-gonadal-axis yakan yi umurni ga ovaries ɗinta domin su fara fitar da wadatattun sinadaran hormones na mata da ake kira estrogens da progesterones. Waɗannan sinadaran hormones su ne ke sauya halittarsu daga ƙananan yara zuwa ‘yammata.

Sauyin da balaga ke haifarwa ga yara mata

Bugu da ƙari, waɗannan sinadaran hormones guda biyu su ke kula da sha’awar mace, yanayin jinin al’adar ta da kuma duk wasu harkokinta na jima’i.

Glands ɗin ovaries da ke jikin mace su ke ƙirƙirar sinadaran estrogens da progesterones. Amma wani abin al’ajabi, su waɗannan glands na ovary suna fara ƙirƙirar sinadaran hormones na androgens ne sannan su yi amfani da wasu enzyme proteins da ake kira 3-BHSD da aromatase su mayar da androgens zuwa estrogens da progesterones. Wannan shi yasa za a iya samun sinadaran hormones na androgens waɗanda ba a mayar da estrogens ko progesterones ba a cikin jinin mace. Samun waɗannan sinadaran hormones na androgens da yawa a jinin mace shi yake sa mace ta siffantu da wasu siffofin maza, kamar babbar murya mai kauri, saje da kuma gashin baki.

Haka kuma shi ma namiji yana da waɗannan enzymes ɗin masu mayar da sinadaran hormones na androgens zuwa sinadaran mata na estrogens da progesterones (3BHSD da aromatase), amma enzymes ɗin ba su da yawa. Samun waɗannan enzymes ɗin da yawa a jinin namiji shi yake sa namiji ya siffantu da wasu siffofin mata kamar irin su, ƙaramar murya, namiji ya fitar da nono, da sauran siffofin mata. Wannan yana faruwa ne saboda enzymes ɗin za su mayar da mafi yawan sinadaran hormones na androgens zuwa sinadaran mata na estrogens da progesterones.

Alamomin balagar mata

Mafi yawancin mata farkon abinda ke fara nuna sun fara balaga shi ne fitar nono a ƙirjinsu. Fitar nono yana farawa ne da wani ƙaramin kumburi a ƙarƙashin kan nono, daga nan sai yaci gaba da girma. Sauran alamomin balaga sun haɗa da:

  1. Fitar da gashi a kumburin dinka ko kuma a manyan leɓɓan farji. (Labia majora).
  2. Fitar da gashin mara
  3. Fitar gashin hammata
  4. Fitar da nono
  5. Yanayin jikinsu zai sauya, kwankwasonsu (hips) zai ƙara girma ya buɗe, haka kuma za suyi manyan ɗuwawu
  6. Kitse zai taru a jikinsu, wannan zai ƙara musu girma da kuma laushin fata
  7. Fara yin jinin al’ada; mafi yawanci jinin al’ada ya kan fara ne bayan shekara ɗaya ko biyu da fara fitar da nono.
  8. Siririyar murya; A lura cewa yayin da yarinya take farkon balaga muryar ta takan iya fara kauri kamar ta maza kamin ta koma siririya irin ta mata daga baya.
  9. Yawan fitar da ruwan maziyyi ko yawan jin danshi a farji.
  10. Sha’awar namiji ko sha’awar yin jima’i.

Sauye-sauye bayan balaga

Ƙananan yara sukan samu ƙarin hankali, wayo da kuma zurfin tunani bayan sun balaga. Wannan shi ne zai taimaka musu domin daina wasu ɗabi’un yara da kuma shiga cikin manya. Kaɗan daga cikin abubuwan da ke faruwa sun haɗa da:

  • Rage dogara da iyaye
  • Ƙara kaifin basira da zurfin tunani
  • Jin kunya
  • Sanin ciwon kai
  • Sanya tufafi yadda ya kamata
  • Son sirri

Matsalolin da balaga ke iya kawo wa

  • Warin jiki
  • Ƙurajen balaga
  • Wasu yara sukan shiga yanayin ƙunci musamman mata sanadiyyar fitar da nono ko fara yin jinin al’ada
  • Ciwon mara a lokacin jinin al’ada
  • Sauyin yanayi – Mood changes
  • Yawan fitar wani ruwa daga farji ko azzakari
  • Sha’awar jima’i da zata iya sa yara lalacewa
  • Yaro kan iya fara wasa da al’aurar sa – Masturbation
  • Yin ƙiba ko taiɓa

Manazarta

Ceo. (2024, February 10). Bayani game da yadda maza da mata ke balaga da kuma sauyin halitta da ake samu bayan balaga (Puberty). Lafiyata.com

Springster | (n.d.) Mene ne balaga? – Nigeria.

Tambayoyin Matasa. (n.d.). Ta Yaya Zan Bi da Canje-canjen da Ke Aukuwa a Lokacin Balaga? JW.ORG. 

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×