Bashir Tofa wanda aka fi sani da ɗan takarar jam’iyyar Republican Convention (NRC) a Najeriya wanda aka soke zaɓen da ya sha kayi na ranar 12 ga Yuni, 1993, ɗan siyasar Najeriya ne kuma hamshakin attajiri. Ya fito daga jihar Kano.
Haihuwarsa
An haifi Bashir Usman Tofa ne a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, a ranar 20 ga watan Yuni 1947. Bashir Usman Tofa ya fito ne daga kabilar Kanuri.
Karatunsa
Ya yi karatun firamare a Shahuci Special Primary School, Kano, sannan ya ci gaba da karatu a City Senior Primary School a Kano. Daga 1962 zuwa 1966, ya halarci kwalejin lardi da ke Kano. Bayan kammala karatunsa a Makarantar Lardi, ya yi aiki da Kamfanin Inshorar Royal Exchange daga 1967 zuwa 1968. Daga 1970 zuwa 1973, ya halarci Kwalejin City of London.
Harkokin siyasarsa
Tofa ya fara siyasa ne a shekarar 1976 lokacin da ya zama kansila a karamar hukumar Dawakin Tofa, a shekarar 1977, an zabe shi ɗan majalisar wakilai, lokacin jamhuriya ta biyu ta Najeriya. Tofa a lokuta daban-daban ya kasance sakataren jam’iyyar NPN reshen jihar Kano, daga baya ya zama sakataren kudi na jam’iyyar na ƙasa kuma ya kasance mamba na kwamitin koren juyin juya hali na kasa. A lokacin jamhuriya ta uku, yana cikin ƙungiyar masu sassaucin ra’ayi wadda ta misalta zuwa ga Yarjejeniyar Liberal lokacin da ba a yi mata rajista a matsayin jam’iyyar siyasa ba.
A lokacin zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar, ya doke Pere Ajunwa, Joe Nwodo da Dalhatu Tafida inda ya samu tikitin NRC. Ya kasance abokin Halilu Akilu, babban jami’in tsaro a lokacin. Abokin takararsa a zaben shi ne Sylvester Ugoh, wanda ɗan kabilar Inyamurai ne. Dukkansu biyun ‘ya’yan rusasshiyar jam’iyyar ta ƙasa ce.
Tofa shi ne dan takarar shugaban kasa na NRC a zaben Yuni 12, 1993. A yayin zaben, Tofa ya fafata da MKO Abiola na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), wanda ake zaton shi ne ya lashe zaben. Amma gwamnatin Babangida ta soke zaben.
A zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yuni, Tofa ya sha kaye a zaben shugaban kasa da abokin hamayyarsa Cif Moshood Kashimawo Olawale Abiola, abokin Babangida kuma dan kabilar Yarbawa daga Kudu-maso-Yammacin Najeriya. Sai dai gwamnatin Babangida ba ta fitar da sakamakon a hukumance ba. An tilastawa Babangida ya sauka daga mulki a watan Agustan 1993 bayan zanga-zangar neman sakamakon zaɓen.
A zaɓen dai da aka a watan Yuni, sakamakon da hukumar zabe ta ƙasa ƙarƙashin Farfesa Humphrey Nwosu ta sanar kafin sojoji su dakatar da aikin, ya nuna cewa Tofa ya samu kuri’u miliyan 2.3 yayin da Abiola ya samu kuri’u miliyan 4.3. Ya lashe jihohi 11 yayin da Abiola ya lashe jihohi 19 a zaben. Tofa ya sha kaye a jihar sa Kano.
Kafin ranar 12 ga watan Yuni, Tofa yana da dangantaka mai kyau da Abiola lokacin da shi ne shugaban jam’iyyar NPN na jihar Ogun, a lokacin da yake sakataren kuɗi na jam’iyyar na ƙasa a jamhuriya ta biyu, siyasa ce ta raba su. Kafin rasuwarsa, ba ya cikin kowace jam’iyyar siyasa, walau jam’iyyar APC mai mulki ko kuma jam’iyyar PDP.
Kasuwancinsa
Tofa hamshakin dan kasuwa ne kuma masanin masana’antu. Ya kasance shugaban Kamfanin Petro-Energy Company (IPEC) da Abba Othman and Sons Ltd. Ya kuma kasance memba a hukumar Impex Ventures, Century Merchant Bank da General Metal Products Ltd.
A shekarar 2011, ya rubuta littafinsa mafi shahara a cikin harshen Hausa. mai suna “Tunanin Ka Kamannin Ka”’ da aka fassara da harshen Turanci mai ƙunshe da shafuka 219.
Matsayinsa na marubuci
Rubuce-rubucen da ya yi a cikin harshen Hausa a fili yake cewa adabin Hausa ya samu karɓuwa sosai a tsakanin kowanne bangare na al’umma. A matsayinsa na dattijo uban ƙasa, an san shi da yin magana iri-iri game da matsalolin zamantakewa da rashin adalci. Ya rubuta littafai da dama cikin harshen Hausa, wasu daga cikinsu sun hada da:
- Tunaninka Kamanninka
- Kimiyyar Sararin Samaniya
- Gajerun Labarai
- Amazadan a Birnin Aljanu
- Amazadan da Zoben Farsiyas
- Rayuwa Bayan Mutuwa
- Arewa Daga Ina, Zuwa Ina?
Mutuwarsa
Alhaji Bashir Usman Tofa ya rasu ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano, a ranar Litinin 3 ga Janairu, 2022, yana da shekaru 74 a duniya. Ya rasu bayan wata gajeriyar rashin lafiya.
Ana tunawa da shi a matsayin marubuci wanda ya yaɗa yadda ake amfani da harsunan gida don magance matsalolin al’umma.
Manazarta
Oyeleke, S. (2022, January 3). Bashir Tofa: 10 things to know about MKO Abiola’s opponent who opposed June 12 as Democracy Day. Punch Newspapers.
Shuaib, Y. A. (2022, January 6). Bashir Tofa: The publisher who had the finest mansion — an internship experience | TheCable. TheCable.
THISDAYLIVE. (2022, January 4). The politics and literary works of Bashir Tofa THISDAYLIVE.
Yusuf, O. (2022, January 10). Bashir Tofa: The life of the Businessman who Contested against Abiola in 1993 Presidential election. Neusroom.