Basir wata cuta ce da ke faruwa a ƙarshen hanji da dubura, inda jijiyoyin jini da ke wannan wuri suke kumbura su faɗaɗa fiye da yadda ya kamata. Wannan kumburi na jijiyoyi ne yake haifar da ƙulli ko kumburi a ciki ko wajen dubura, wanda zai iya jawo zafi, ƙaiƙayi, ko zubar jini yayin yin bayan gida. Basir na iya kasancewa a cikin dubura ko kuma a wajenta, kuma yana daga cikin cututtukan da suka fi shafar manya musamman waɗanda ke fama da bayan gida mai tauri ko zama na dogon lokaci.
A ilimin likitanci, basir na nufin kumburin jijiyoyin jini da ke cikin tantanin dubura da ƙarshen hanji, wanda yawanci yake faruwa sakamakon matsin lamba mai yawa a wannan yanki. Wannan matsin lamba yana sa jijiyoyin su yi laushi su kumbura, daga nan sai basir ya bayyana.
Muhimmancin sanin cutar
Sanin cutar basir yana da muhimmanci saboda yana daga cikin cututtukan da mutane da yawa ke fama da su amma sukan ji kunyar faɗa ko neman magani. Idan ba a gane shi da wuri ba, basir na iya tsananta har ya jawo matsaloli kamar yawan zubar jini, tsananin zafi, ko buƙatar tiyata. Ilimi game da basir yana taimaka wa mutane su gane alamominsa, su san hanyoyin kariya, da kuma lokacin da ya kamata su nemi taimakon likita.
Haka kuma, fahimtar cutar yana taimakawa wajen rage yaɗuwar jita-jita da kuskuren fahimta da ake da su a tsakanin jama’a, domin wasu suna danganta basir da abubuwan da ba su da tushe daga kimiyya.
Rabe-raben cutar basir
Ana rarraba cutar basir zuwa nau’o’i daban-daban gwargwadon wurin da ya bayyana da kuma yadda yake nuna kansa. Wannan rarrabuwar tana taimaka wa likitoci wajen tantance irin maganin da ya dace, domin ba dukkan basir ne suke da tsanani ko alamomi iri ɗaya ba.
Basir na cikin
Basir na cikin ana kiran shi (internal haemorrhoids) a turance. Yana samuwa ne a cikin dubura, wato a cikin ƙarshen hanji kafin bakin dubura. Saboda yana cikin jiki, yawanci ba a ganinsa da ido kai tsaye, kuma sau da yawa baya haifar da zafi a farkon lokaci domin wurin ba shi da jijiyoyin jin zafi masu yawa. Duk da haka, yana iya haifar da zubar jini yayin bayan gida, wanda galibi jini ne launin ja mai haske.

Basir na ciki yana iya kasancewa na ɗan lokaci ba tare da mutum ya lura da shi ba, sai dai idan ya tsananta ko ya fara zubowa waje. Ana rarraba basir na ciki zuwa matakai huɗu gwargwadon yadda yake tsananta:
- Mataki na I: Basir ɗin yana cikin dubura kawai, bai fito waje ba. Alamarsa mafi yawa ita ce zubar jini ba tare da zafi ba.
- Mataki na II: Basir yana iya fitowa waje yayin yin bayan gida, amma yana komawa ciki da kansa bayan an gama.
- Mataki na III: Basir yana fitowa waje yayin bayan gida kuma babya komawa ciki sai an mayar da shi da hannu. A wannan mataki ana iya jin zafi ko rashin jin daɗi.
- Mataki na IV: Basir yana waje dindindin kuma ba zai koma ciki ba ko da an yi ƙoƙarin mayar da shi. Wannan mataki shi ne mafi tsanani, kuma yana iya haifar da raɗaɗi mai yawa da matsaloli kamar kamuwa da cuta ko daskarewar jini.
Yadda basir yake zazzgowa waje
Zazzagowar basir na ciki waje yana faruwa ne lokacin da jijiyoyin da suka kumbura suka raunana suka zame daga matsayinsu na asali. Yin tusa mai ƙarfi yayin bayan gida, bayan gida mai tauri, ko zama na dogon lokaci na iya ƙara matsin lamba har ya sa basir ya fito waje. Da zarar ya fara zazzagowa, yana iya ƙara tsananta idan ba a samu magani ba.
Basir na waje
Basir na waje ana kiran shi external hemorrhoids a turance, yana samuwa ne a ƙarƙashin fata a wajen bakin dubura. Saboda yana wajen jiki, ana iya ganin sa ko taɓa shi a matsayin kumburi ko ƙulli. Wannan nau’in basir yana da jijiyoyin jin zafi masu yawa, shi ya sa yakan fi haifar da raɗaɗi da rashin jin daɗi fiye da na ciki.
Basir na waje yana iya haifar da zafi musamman lokacin zama, tafiya, ko bayan gida. Haka kuma yana iya jawo ƙaiƙayi saboda kumburi da fitar ruwa daga wurin. Wasu mutane na iya jin kamar akwai wani abu a bakin dubura wanda ke hana su zama cikin kwanciyar hankali.
Samuwar daskerar jini
A wasu lokuta, jini na iya taruwa a cikin basir ta waje ya daskare, abin da ake kira thrombosed haemorrhoid a turance. Wannan yanayi yana sa kumburin ya yi duhu ko shuɗi, kuma yana haifar da tsananin zafi. Idan hakan ta faru, mutum na iya buƙatar kulawar likita cikin gaggawa domin rage raɗaɗi da kuma kauce wa matsaloli.
Harɗaɗɗen basir
Harɗaɗɗen basir yana nufin lokacin da mutum ya kamu da basir na ciki da na waje a lokaci guda. Wannan yanayi na iya sa alamomin su kasance masu rikitarwa, domin mutum zai iya fuskantar zubar jini daga na ciki tare da zafi da kumburi daga na waje.
Irin wannan basir na iya zama mai tsanani fiye da nau’i guda ɗaya, kuma sau da yawa yana buƙatar kulawa ta musamman. Idan basir na ciki ya fito waje ya haɗu da na waje, zai iya ƙara girman kumburi da raɗaɗi. Saboda haka, irin wannan yanayi yana daga cikin dalilan da ake ba da shawarar a nemi likita da wuri domin samun maganin da ya dace.
Dalilan samuwar basir
Basir yana samuwa ne sakamakon matsin lamba mai yawa da ke da tasiri ga jijiyoyin jini a yankin dubura da ƙarshen hanji. Wannan matsin lamba na iya samo asali daga abubuwa na yau da kullum, yanayin lafiyar mutum, ko wasu sauye-sauyen halitta da jiki ke fuskanta a rayuwa.
Dalilan kai tsaye
Dalilai na kai tsaye su ne abubuwan da ke haddasa matsin lamba kai tsaye ga dubura a lokacin yin bayan gida ko matsalolin narkewar abinci. Bayan gida mai tauri na daga cikin manyan sanadin basir, wanda hakan ke tilasta mutum yin yunƙuri da nishi mai ƙarfi domin fitar da shi, kuma wannan yunƙuri yana matsa wa jijiyoyin dubura har su kumbura. Haka kuma, yin tusa da ƙarfi ko ɗaukar lokaci mai tsawo a banɗaki na iya ƙara matsin lamba a wurin ko da bayan gidan bai yi tauri ba. Gudawa mai tsawo ita ma na iya haifar da basir, domin yawan zuwa bayan gida akai-akai yana fusata dubura, yana sa jijiyoyin wurin su kumbura tare da raunana. Waɗannan abubuwa uku suna daga cikin muhimman dalilan da ke sa basir ya fara samuwa ko ya tsananta.
Dalilan salon rayuwa
Salon rayuwa yana taka muhimmiyar rawa wajen samuwar basir, musamman a wannan zamanin inda mutane da yawa ke rayuwa cikin yanayi na rashin motsa jiki. Rashin cin abinci mai wadataccen sinadarin fiber, kamar kayan lambu, ‘ya’yan itatuwa, da hatsi, yana sa bayan gida ya yi tauri, wanda hakan ke ƙara matsin lamba a dubura. Zama na tsawon lokaci, musamman ga masu aikin ofis ko direbobi, yana hana jini zagayawa yadda ya kamata a yankin ƙasan jiki, wanda ke haifar da kumburin jijiyoyi.
Ɗaga kaya masu nauyi akai-akai shi ma yana ƙara matsin lamba a cikin ciki da dubura, musamman ga masu aikin da ya shafi ɗaukar kaya. Bugu da ƙari, ƙiba tana ƙara nauyin da ke takura wa jijiyoyin dubura daga ciki, wanda ke sa su kumbura cikin sauƙi. Haɗuwar waɗannan halaye na rayuwa na iya sa mutum ya fi fuskantar haɗarin kamuwa da basir ko kuma ya tsananta idan ya riga ya samu.
Dalilan halitta da lafiya
Wasu sauye-sauyen halitta da yanayin lafiyar jiki na iya ƙara yiwuwar samuwar basir ba tare da alaƙa kai tsaye da halayen rayuwa ba. Mata masu juna biyu suna yawan fuskantar basir saboda girman mahaifa yana takura wa jijiyoyin dubura, sannan sauyin ƙwayoyin hormones yana sa jijiyoyi su yi laushi su kumbura cikin sauƙi. Tsufa shi ma yana da tasiri, domin yayin da mutum ke tsufa, jijiyoyin jiki suna rasa ƙarfi da juriya, wanda ke sa su faɗaɗa cikin sauƙi a ƙarƙashin matsin lamba. Haka kuma, tarihin dangi ta fuskar lafiya, domin wasu mutane suna da sauƙin kamuwa da basir saboda gadon tsarin jijiyoyi ko yanayin jiki daga iyaye. Waɗannan dalilai na halitta suna nuna cewa basir ba cuta ce da ke samuwa daga hali kawai ba, har ma yana da alaƙa da tsarin jiki da sauye-sauyen da ke faruwa a rayuwar mutum.
Hanyoyin tantance basir
Tantance basir yana da muhimmanci domin tabbatar da cewa alamomin da mutum ke fuskanta daga basir ne, ba daga wata cuta mai kama da shi ba. Likitoci na amfani da hanyoyi daban-daban domin gano nau’in basir da matakin tsananinsa.
Binciken likita
Mataki na farko shi ne likita ya tattauna da mara lafiya domin jin irin alamomin da yake fuskanta, kamar zubar jini, zafi, ko kumburi. Bayan haka, likita zai iya duban wajen dubura domin ganin ko akwai basir ta waje ko kumburi. Wannan dubawa na taimakawa wajen gano matsalar cikin sauƙi, musamman idan basir yana waje.
Gwaje-gwajen dubura
Idan ana zargin basir na ciki ne, likita na iya yin gwajin dubura ta hanyar sanya safar hannu da man shafawa sannan ya saka yatsa a hankali cikin dubura domin jin ko akwai kumburi ko wani abu da ba daidai ba. Wannan hanya na taimakawa wajen gano basir da kuma ware shi daga wasu cututtuka.
Gwaji da na’urori (misali proctoscope)
A wasu lokuta, ana amfani da kayan aikin gwaje-gwaje ciki kamar proctoscope domin ganin cikin dubura kai tsaye. Wannan na’ura tana da haske kuma tana ba likita damar duba cikin dubura da ƙarshen hanji domin gano basir, girmansa, da kuma ko akwai zubar jini. Wannan hanya tana da amfani musamman idan alamomin suna nuna yiwuwar basir mai tsanani ko kuma idan ana buƙatar ƙarin tabbaci kafin a fara magani.
Hanyoyin magani
Maganin basir yana danganta da nau’insa da matakin tsananinsa. A mafi yawan lokuta, ana farawa da hanyoyi masu sauƙi kafin a koma ga magungunan asibiti ko tiyata. Manufar magani ita ce rage kumburi, zafi, da zubar jini, tare da hana basir ya ƙara tsananta ko dawowa.
Magani da dabaru a gida
Daidaita abinci
Daidaita abinci yana daga cikin muhimman hanyoyin maganin basir. Cin abinci mai wadataccen fiber kamar kayan lambu, ‘ya’yan itatuwa, wake, da hatsi yana taimakawa wajen laushin bayan gida domin ya fita ba tare da wahala ba. Haka kuma, shan ruwa mai yawa yana hana bayan gida bushewa. Wannan daidaita abincin yana rage taurin bayan gida da tusa mai ƙarfi, wanda hakan ke ba jijiyoyin dubura damar murmurewa.
Yin wanka da ruwan ɗumi
Wanka da ruwan ɗumi, musamman bayan yin bayan gida, yana taimakawa wajen rage kumburi, ƙaiƙayi, da zafi a yankin dubura. Wannan hanya tana sa jini ya riƙa gudana yadda ya kamata a wurin, wanda hakan ke taimakawa wajen warkewa. Ana iya zama a cikin ruwan ɗumi na mintuna kaɗan sau da dama a rana domin samun sauƙi.
Magungunan shafawa
Akwai man shafawa da ake amfani da su kai tsaye a wurin basir domin rage zafi, ƙaiƙayi, da kumburi. Wasu daga cikinsu suna ɗauke da sinadarai masu sanyaya wurin ko rage kumburi. Waɗannan magunguna suna taimakawa musamman ga basir mai sauƙi ko wanda bai tsananta ba.
Magungunan asibiti
Ƙwayoyin da man shafawa
Idan maganin gida bai wadatar ba, likita na iya rubuta ƙwayoyin ko maganin shafawa na musamman. Waɗannan magunguna suna taimakawa wajen rage kumburi, dakatar da zubar jini, da kuma sauƙaƙa ciwo. Wasu ƙwayoyin suna ƙarfafa jijiyoyin jini domin su koma yadda suke a da.
Magungunan rage kumburi da zafi
Ana iya ba marar lafiya magungunan rage radadi da kumburi domin ya sami sauƙin zama da tafiya. Waɗannan magunguna suna da muhimmanci musamman idan basir yana haifar da tsananin zafi ko rashin barci. Likita ne kawai zai tantance irin maganin da ya dace gwargwadon yanayin mara lafiya.
Hanyoyin tiyata
Rubber band ligation
Wannan hanya tana ɗaya daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen maganin basir na ciki. Likita yana sanya ƙaramin zare na roba a ƙasan basir domin toshe jinin da ke zuwa wurin. Da zarar jini ya daina kaiwa, basir yana bushewa ya faɗi da kansa bayan wasu kwanaki.
Sclerotherapy
A wannan hanya, likita yana allurar wani magani a cikin basir wanda ke sa jijiyoyin su ƙanƙance su kuma su daina kumbura. Wannan hanya tana da amfani ga basir mai sauƙi zuwa matsakaici.
Infrared coagulation
Wannan hanya tana amfani da haske mai zafi domin ƙona jijiyoyin da ke haifar da basir da jini. Sakamakon haka, basir yana ƙanƙancewa ya daina haifar da matsala. Hanya ce mai sauƙi wadda ba ta buƙatar babbar tiyata.
Tiyatar cire basir
Idan basir ya yi tsanani ko ya gagara magungunan da aka ambata, ana iya yin tiyata domin cire shi gabaɗaya. Wannan hanya ita ce mafi inganci ga basir mai tsanani, musamman wanda yake waje ko wanda ya zazzago ya kasa komawa ciki. Kodayake tiyatar na iya buƙatar lokaci kafin warkewa, tana ba da mafita ta dindindin ga matsalar.
Hanyoyin kariya daga basir
Kariyar daga basir na da muhimmanci domin rage yiwuwar kamuwa ko tsananta wanda yake akwai. Hanyoyin kare kai sun haɗa da canje-canje a salon rayuwa, abinci, motsa jiki, da tsaftar yankin dubura.
Cin abinci mai fiber
Cin abinci mai wadataccen fiber yana taimakawa wajen samun bayan gida mai laushi wanda ba ya buƙatar nishi mai ƙarfi. Kayan lambu, ‘ya’yan itatuwa, wake, da hatsi na narkewa cikin sauƙi, yana rage bayan gida mai tauri da matsin lamba a dubura. Wannan hanya na rage haɗarin samuwar basir ko tsananta wanda yake akwai.
Motsa jiki
Motsa jiki akai-akai yana ƙarfafa jiki baki ɗaya, musamman aikin hanji da zagayawar jini a cikin dubura. Haka kuma motsa jiki yana rage kiba, wanda hakan ke rage matsin lamba ga jijiyoyin dubura. Ana ba da shawarar tafiya, gudu, ko wasu ayyukan motsa jiki masu sauƙi a kullum domin daƙile basir.
Guje wa zama na tsawon lokaci
Zama na dogon lokaci yana ƙara matsin lamba a dubura, musamman idan mutum yana zama sosai a wurin aiki ko ofis. Ba da tazara, tsayawa akai-akai, ko motsa jiki a lokacin hutu yana rage haɗarin samuwar basir.
Yin bayan gida cikin nutsuwa
Yin bayan gida cikin natsuwa da tsari yana taimakawa wajen rage nishi mai ƙarfi. Ana ba da shawarar kada a yi gaggawa, kada a riƙa amfani da waya ko karatu a banɗaki, da kuma tsaftace wurin bayan gida yadda ya kamata. Wannan hanya na taimakawa wajen kare jijiyoyin dubura daga kumburi da basir.
Illolin da basir ke haifarwa
Idan basir ya tsananta ko ba a kula da shi ba, yana iya haifar da wasu matsaloli masu tasiri ga lafiyar jiki da rayuwar yau da kullum.
- Rashin jini: Zubar jini daga basir, musamman na cikin lokaci mai tsawo, na iya haifar da ƙarancin jini a jiki. Wannan yanayi na sa mutum ya ji gajiya, rashin ƙarfi, da laushin fata.
- Daskarar jini: A wasu lokuta, jini na iya taruwa a wurin da basir yake, abin da ake kira thrombosed haemorrhoid. Wannan na haifar da tsananin zafi da kumburi, kuma yana buƙatar kulawar likita domin rage raɗaɗi da guje wa wasu matsalolin.
- Kamuwa da cuta: Basir mai tsanani ko wanda ba a tsaftace wurin ba yana iya haifar da cuta, musamman idan akwai raunuka a fata ko wajen dubura. Kamuwar cuta na iya jawo radadi, kumburi, zafi, da sauran alamomin da ke buƙatar magani da sauri.
Matsalolin rayuwa da aiki: Basir na iya shafar rayuwar yau da kullum ta hanyoyi da dama. Zafi da rashin jin daɗi na iya hana mutum yin ayyukan yau da kullum, zama na dogon lokaci ko tafiya na iya zama da wahala, sannan wasu na iya jin tsoro wajen zuwa wuraren jama’a saboda matsalolin basir. Wannan na iya rage ƙwazon aiki da jin daɗin rayuwa baki ɗaya.
Basir a rukuni na musamman
Basir na iya shafar kowa, amma wasu rukuni na mutane suna cikin haɗari na musamman saboda yanayin jiki ko sauye-sauyen rayuwa. Fahimtar yadda basir ke shafar waɗannan rukuni yana taimakawa wajen rigakafi da kulawa ta musamman.
Basir ga mata masu juna biyu
Mata masu juna biyu suna daga cikin rukunin da basir ya fi shafa saboda girman mahaifa yana takura wa jijiyoyin dubura da ƙarshen hanji. Haka kuma, sauyin hormones a lokacin renon ciki yana sa jijiyoyin su yi laushi su kumbura cikin sauƙi. Wannan na iya haifar da zubar jini, raɗaɗi, ko kumburi a wurin dubura. Ana ba da shawarar mata masu juna biyu su mai da hankali wajen cin abinci mai fiber, shan ruwa mai yawa, da motsa jiki mai sauƙi domin rage haɗarin kamuwa da basir.
Basir ga tsofaffi
Tsofaffi na fuskantar haɗari saboda jijiyoyin jiki na rasa ƙarfi da juriya yayin tsufa. Wannan raunanewar na sa basir ya fi sauƙin samuwa, kuma kumburi ko zubar jini na iya kasancewa mai tsanani. A wannan rukunin, kula da abinci mai kyau, motsa jiki, da ganawa da likita akai-akai suna da matuƙar muhimmanci.
Basir ga yara
Kodayake basir ba a yawan samun shi a yara, amma wasu na iya fuskantar shi sakamakon gudawa mai tsawo, rashin cin abinci mai fiber, ko wasu yanayi na musamman. Alamomin da yara ke fuskanta sun haɗa da zubar jini a bayan gida, jin ƙaiƙayi, da ƙunci yayin bayan gida. Kulawa da tsafta, abinci mai fiber, da sa idon likita suna da muhimmanci idan basir ya faru a wannan rukuni.
Wasu kurakurai da mutane ke yi
Yayin da ake fama da basir, mutane da yawa suna ɗaukar wasu ƙa’idoji ko fahimta marasa inganci game da cutar. Fahimtar waɗannan kurakurai yana taimakawa wajen rigakafi da magani mai tasiri.
Kuskure na farko
Mutane da yawa na tunanin cewa basir yana faruwa ne saboda rashin tsaftar dubura, wanda ba gaskiya ba ne kai tsaye. Basir yana faruwa ne sakamakon kumburin jijiyoyin jini a dubura da ƙarshen hanji, wanda yawanci ya samo asali daga yin bayan gida mai tauri, nishi mai ƙarfi, ko wasu dalilai na rayuwa da halitta. Tsafta na iya taimakawa wajen rage kamuwa da cututtuka masu alaƙa, amma ba ita ce babban sanadin basir ba.
Kuskuren na biyu
Wasu suna tunanin basir na faruwa ne kawai ga tsofaffi, sai dai a zahiri yana iya shafar kowa, har da matasa da yara. Amma, haɗarin na iya ƙaruwa yayin tsufa saboda raunin jijiyoyi da raguwar ƙarfinsu.
Kuskure na uku
Mutane da yawa na tunanin cewa duk basir yana buƙatar tiyata, sai dai yawanci basir na iya warkewa ko samun sauƙi ta hanyar magani na gida, canjin abinci, da magunguna na asibiti. Tiyata tana zama zaɓi ne kawai ga basir mai tsanani ko wanda ya gagari magunguna.
Kuskure na huɗu
Wasu suna ganin zubar jini daga basir ba shi da haɗari. Amma idan jini ya yi yawa ko ya daɗe yana zuba, zai iya haifar da ƙarancin jini wanda ke shafar lafiyar jiki baki ɗaya.
Manazarta
Felman, A. (2025, May 28). What to know about piles (hemorrhoids). Medical News.
Daflon (n.d.). Menene basur? (n.d.). Daflon
News-Medical. (2023, May 26). What are piles? News Medical.
Website, N. (2025, December 19). Piles (haemorrhoids). nhs.uk.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da ku ka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta tare da sa idon kwamitin ba da shawara na ƙwararru. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.
