Binance wata shahararriyar manhajar musaya da hada-hadar kuɗaɗen cryptocurrency ce. Tana da ɓangarori da abubuwa masu jan hankali sosai wajen ciniki da hada-hadar kuɗin altcoin. Binance tana da tsarin ciniki na crypto-to-crypto ga kuɗaɗen yanar gizo fiye da 350 waɗanda suka haɗa da bitcoin (BTC), ether (ETH), litecoin (LTC), dogecoin (DOGE), da kuma nau’in kuɗin kamfanin Binance ɗin, mai alamar BNB.

A ranar 21 ga Nuwamba, 2023, kamfanin Binance da Shugabansa, Changpeng Zhao, suka amsa laifin satar kuɗaɗen haram. Kamfanin Binance ya amince ya biya Dalar Amurka biliyan 4.3 don daidaita caji; Changpeng Zhao ya sauka daga muƙaminsa na shugaba kuma ya amince ya biya Dala miliyan 50 don sasantawa. Wannan ya faru ne wata ɗaya bayan da kamfanin Binance ya dakatar da duk wata hada-hada da dalar Amurka, cirewa, da cinikayya a ranar 17 ga Oktoba, 2023, don mayar da martani ga Hukumar Tsaro da Canjin Kasuwanci (SEC) da aka shigar a kan manhajar da aka keɓe don Amurkawa wato Binance.US a ranar 5 ga Yuni, 2023.
Tarihin manhajar Binance
Changpeng Zhao, ya kirkiro manhajar Binance a cikin 2017, Zhao, sanannen ɗan kasuwa, mai zuba hannun jari, kuma injiniyan software ne. Ya samar da manhajar a watan Yuli, kuma a cikin watanni shida da suka gabata, manhajar ta bunƙasa ta zama ɗaya daga cikin manyan manhajojin musayar crypto a duniya.
A farko dai wannan manhaja tana aiki don kasuwancin crypto-to-crypto, wato tsakanin nau’ikan cryptocurrency guda biyu. Binance tana da mafi ƙarancin kuɗin canji hada-hadar cryptocurrency. Tana da jari mai yawa kuma tana ba da rangwame ga masu amfani da nau’in kuɗi mallakin Binance ɗin mai alamar BNB.
A cikin shekarar 2019, an dakatar da manhajar Binance a cikin Amurka saboda matsalar na tsaro. Kamfanin sai ya samar da Binance.US, manhajar da ta dace da dokokin ƙasar Amurka. Ba a yarda mazauna yankin Hawaii, New York, Texas, da Vermont su yi amfani da Binance.US har zuwa watan Yuni na shekarar 2023 bayan samar da ita.
Hada-hada a manhajar Binance
Kamar sauran manhajojin musanyar crypto, Binance tana ba da damar yin hada-hada kamar ciniki, jera kuɗaɗe, ajiyar kuɗaɗe, cire kuɗaɗe, da kuma janye kuɗaden cryptocurrencies daga cikin jerin kuɗaɗe. Masu sha’awar harkar cryptocurrency da ke son ƙaddamar da kuɗaɗensu na iya amfani da manhajar Binance wajen tara kuɗaɗe ta hanyar tsarin Initial Coins Offering (ICOs). Miliyoyin ‘yan kasuwa ne ke amfani da manhajar Binance don hada-hadar musaya da zuba hannun jari a kasuwar cryptocurrencies daban-daban.
Don fara hada-hadar kuɗaɗen crypto, dole ne masu amfani da manhajar su cika mahimman sharuɗɗan fasahar (KYC). Bayan samun nasarar ƙirƙirar asusun ciniki, za su iya zuba kuɗi zuwa adireshin wallet wanda Binance take samarwa don fara cinikayya.
Binance Markets Limited, wani reshen kamfanin da ke Burtaniya, an dakatar da shi daga ƙayyade ayyukansa ga abokan ciniki a Biritaniya da Hukumar Kula da Ayyukan Kuɗi (FCA), hukumar kula da harkokin ƙasar, a cikin watan Yuni 2021. Sanarwar hukumar ta hana reshen samar da damar hada-hada da ciniki a ɓangare hada-hadar crypto da abubuwan da suke da alaƙa da abokan ciniki a Biritaniya. Kazalika sashen watsa labaran kamfanin ya fayyace cewa haramcin bai shafi ayyukan samar da sabis ba, kamar cinikayya, ga masu amfani da manhajar a cikin Britaniya.
Ba a cajin kuɗin cryptocurrency ko ajiyar kuɗi. Sai dai cirar kuɗi na iya kasancewa ba kyauta ba, ana cajin kuɗi kuma ya bambanta dangane da wane irin kuɗaɗen cryptocurrency ne ake son cirewa da kuma adadinsu.

A watan Yunin 2023, Binance ta hana ajiye dalar Amurka ga duk masu amfani da manhajar a fadin duniya. Amma ta bayar da izinin ajiye wasu kuɗaɗen ‘fiat’ guda 27, wanda suka haɗa 5 Yuro.
Sauran ayyukan Binance
Baya ga samar da tabbataccen aikin da aka gina manhajar don shi, wato musaya da hada-hadar kuɗaɗen crypto, Binance kuma tana ba da wasu damarmakin aiki a manhajar. Wasu daga cikinsu su ne kamar haka:
• Damar samun kuɗi (Earning)
Binance Earn, wani sashe ne a cikin manhajar da ke ba da damar tara kuɗi ko samun riba ta hanyar saka kuɗaɗe da yin musaya. Ana duba yawan kuɗaɗen da kuma tsawon lokaci, sai manhajar ta ba masu zuba jarin damarmaki da yawa da kuma riba mai yawa ta kuɗaɗen.
• Bayar da rance
Binance card, shi ne katin kiredit na Visa wanda ke ba masu amfani da manhajar damar canja cryptocurrency zuwa tsarin kuɗin fiat, kuma su kashe su akan sayen wasu kadodri ko sabis a cikin manhajar. Canja kuɗaɗen ba ya buƙatar kuɗin caji, amma ana iya cajin wasu kuɗaɗe na daban, kamar kuɗaɗen hanyoyin sadarwar da kamfanoni sadarwa ke caja.
Lamunin Binance Crypto yana ba masu amfani da kamfanin damar rance domin aiwatar da hada-hada. Sharuɗɗan tsawon lokacin lamunin na iya zama kwanaki bakwai, 14, 30, 90, da 180, tare da kuɗin ruwa wanda ake lissafawa bisa ga adadin sa’o’in da rancen ya kasance.
• Smart Pool
Binance Smart Pool wani tsari ne da yake babwa masu yin mining damar canjawa tsakanin cryptocurrencies daban-daban don yin mining da bunƙasa samun kuɗaɗe, yayin da Binance Pay ke ba da damar amfani da cryptocurrency don biyan kuɗaɗen sayayya a duk faɗin duniya ba tare da yin caji ba. Za a samu wannan ɓangare kuma a yi amfani da shi a Binance Marketplace da ke cikin manhajar.
• Development
Binance tana da fasahar ‘blockchain incubator’ da ake kira ‘Binance Labs’, wanda ke mayar da hankali kan haɓaka ayyukan ICO a matakin farko. Wannan bangare yana taimaka ta hanyar samar da kuɗaɗen da ake buƙata don bunƙasawa, bayar da shawarwari kan wasu abubuwa, da sauran dabarun tara kuɗaɗe.
Haka nan Binance tana samar da wani shafin yanar gizon da ake kira LaunchPad domin saka sabbin ayyukan blockchain masu tasowa. A watan Yulin 2023, an ƙaddamar da sabbin ayyuka sama da guda 70.
Binance Coin (BNB)
Ana amfani da Binance Coin (BNB) domin sauƙaƙa kasuwancin crypto a kan manhajar Binance. An ƙaddamar da kuɗin kamfanin Binance mai alamar BNB a lokacin bikin bayyana kuɗin na farko da aka yi a cikin watan Yulin 2017. Binance ta ba da zunzurutun kuɗin BNB har miliyan 20 ga masu zuba jari na manya na duniya, sai miliyan 80 ga rukunin wanda suka ƙirƙiri kuɗin, yayin da sauran miliyan 100 kuma suka tafi ga masu ruwa da tsaki daban-daban ta hanyar ICO.
Kusan rabin kuɗaɗen da aka samu a lokacin da ake tsarin ICO, an yi nufin yin amfani da don da tallace-tallace inganta kamfanin, yayin da kusan kashi ɗaya bisa uku suka tafi wajen gina manhajar Binance da kuma yin gyare-gyaren da ya dace da tsarin yanayin manhajar.
Binance Coin da farko ya fara aiki a kan fasahar Ethereum Blockchain tare da tsarin ERC 20. Amma a cikin shekarar 2019, Binance Coin ya koma kan tsarin fasahar BNB Chain.
A watan Yulin 2023, BNB ɗaya ya kai darajar kusan Dalar Amurka 250. Shi ne na hudu mafi daraja a kasuwa.
Tsaro da amincin manhajar Binance
Manhajar Binance tana da miliyoyin masu amfani da ita da suka yi amannar cewa manhajar musanyar kuɗaɗen crypton tana da amince da nagarta kuma tana ƙoƙarin wajen sauƙaƙa hada-hadar crypto. Sai dai kuma, kasancewar manhajojin na da ɓangare na uku wato (third party) da ke da hannu a harkokin fasahar blockchain da crypto, manhajar na da raunin tsaro ga masu kutse, kamar yadda aka gani lokacin da masu kutsen suka sace $570 miliyan na kuɗin BNB a cikin shekarar 2022.
Manazarta
Jha, S. (2023, February 22). The complete guide to understand the foundation of what Binance is. Simplilearn.com.
Peters, K. (2023, November 22). Binance Exchange. Investopedia.
Blackstone, T. (2024, May 31). Is Binance a safe crypto exchange? | Security.org. Security.org.
Binance Square. (n.d). The most important features of the Binance platform. Binance Square.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.