Skip to content

Biology

    Aika

    Biology reshe ne na ilimin kimiyya da ke nazarin halittu masu rai da muhallinsu. Wannan fanni na kimiyya yana da matuƙar muhimmanci domin yana taimaka wa ɗan’adam fahimtar yadda halittu ke rayuwa, suke girma, suke hayayyafa da yadda suke hulɗarsu da juna da kuma da ire-iren muhallan da suke rayuwa. Ana amfani da ilimin biology a fannoni da dama kamar kiwon lafiya, aikin gona da kiwon dabbobi, kimiyyar halittu ta likitanci, da sararin samaniya.

    Ma’anar Biology

    Biology kalma ce ta Turanci da ta samo asali daga kalmomin Girkanci guda biyu: wato ‘bios’ (wadda ke nufin ‘rayuwa’) da kuma ‘logos’ (wadda ke nufin ‘ilimi’). Don haka, Biology na nufin “ilimin rayuwa”.

    Manyan rassan Biology

    Waɗannan rassa su ne ginshiƙan da kimiyyar halittu ta ta’allaka a kansu. Kowane sashe na da amfani a fannoni daban-daban na rayuwa kamar lafiya, muhalli, noma, fasaha da kimiyya gabaɗaya. Ga wasu daga cikin muhimman sassa na ilimin Biology:

    Botany

    Botany shi ne reshen ilimin Biology da ke nazarin tsirrai da duk wani abu mai alaƙa da rayuwarsu. Wannan ya haɗa da yanayin girma da haɓakardu, tsarin jikinsu (structure), halayensu da siffofinsu, rabe-rabensu, da yadda suke hulɗa da muhallinsu.

    Muhimman fannonin Botany

    • Plant Morphology: Nazarin bayyanannun tsari da siffofin jikin tsiro (ganye, fure, tushe da sauransu).
    • Plant Physiology: Nazarin yadda tsirrai ke aiki, misali shakar iskar carbon dioxide, yin photosynthesis.
    • Plant Taxonomy: Rabe- rabe da tsara nau’o’in tsirrai bisa dangantaka.
    • Economic Botany: Nazarin amfanin tsirrai ga ɗan’adam (misali: samar da abinci, magani, man fetur, da sauran su).

    Alfanun fannin Botany

    Ana amfani da ilimin tsirrai wajen ayyukan noma, kiwon lafiya, haɗa magunguna (herbal medicine), kare muhalli da ƙirƙirar sabbin iri.

    Microbiology

    Microbiology sashe ne na Biology da ke nazarin ƙwayoyin halitta ƙanana waɗanda ba a iya gani da ido kai tsaye, kamar bakteriya, viruses, fungi da protozoa.

    Muhimman fannonin Microbiology

    • Bacteriology: Nazarin kwayoyin bakteriya kamar Escherichia coli.
    • Virology: Nazarin kwayoyin cuta kamar coronavirus, HIV da sauran su.
    • Mycology: Nazarin fungi kamar yeast, moulds.
    • Parasitology: Nazarin halittun parasites kamar Plasmodium da ke haddasa zazzaɓin cizon sauro.

    Alfanun fannin Microbiology

    Ana amfani da Microbiology wajen ƙirƙirar magungunan (antibiotics) don yaƙi da cututtuka. Samar da sinadarai daga fungi da kuma inganta tsaftar abinci da ruwa.

    Genetics

    Genetics na nazarin yadda halaye da ɗabi’u ke gudana ko matsawa daga iyaye zuwa ga ‘ya’ya, da kuma yadda sinadaran (DNA da RNA) ke sarrafa halaye da ayyukan jiki.

    Muhimman fannonin Genetics

    • Mendelian genetics: Nazarin ƙa’idojin gado na Gregor Mendel.
    • Molecular genetics: Nazarin gado a matakin DNA da kwayoyin halitta.
    • Population genetics: Nazarin yadda halaye da ɗabi’u ke yaɗuwa a cikin al’umma.
    • Genetic engineering: Sauya halittar genes don samun halaye da ɗabi’un da ake bukata, kamar sabbin iri na hatsi masu jure yanayin fari.

    Alfanun fannin Genetics

    Gwajin DNA da magance cutukan da ake gadon su kamar sickle cell, hemophilia. Ana kuma amfani da ilimin wajen samar da magunguna masu daidaito ga tsarin gadon mutum

    Ecology

    Ecology na nazarin dangantakar da ke tsakanin halittu, kamar dabbobi da tsirrai da muhallan da suke rayuwa. Wannan fanni ya haɗa da nazarin yanayi, abinci, ruwa, iska da sauran halittu a wuri guda.

    Muhimman fannonin Ecology

    • Population Ecology: Nazarin yadda yawan halittu ke canjawa.
    • Community Ecology: Yadda halittu daban-daban ke rayuwa tare a wuri guda.
    • Ecosystem Ecology: Nazarin yadda makamashi da sinadarai ke zagayawa tsakanin halittu da muhalli.
    • Conservation Ecology: Kare halittu da wuraren da suke rayuwa misali; gandun daji.

    Alfanun fannin Ecology

    Ɗaya daga cikin alfanun wannan fanni shi ne kare nau’ikan dabbobi da tsirrai masu ɓacewa. Tsare muhalli daga gurɓacewa, tsara yadda kiwo a daji zai gudana tare da yin noma mai ɗorewa.

    Anatomy

    Anatomy shi ne nazarin tsarin sassa ko gaɓoɓin jikin halittu misali, ƙashi, tsoka, gabobi da jijiyoyi. Wannan fanni yana da nau’ika biyu:

    • Gross Anatomy: Su ne abubuwan da za a iya gani da ido.
    • Microscopic Anatomy (Histology): Wannan shi ne nazarin kwayoyin halitta (cells) da tsokoki ta hanyar amfani da microscope.

    Physiology

    Physiology na nazarin yadda sassa da gaɓoɓin jiki ke aiki, kamar yadda zuciya ke bugawa, yadda numfashi ke wanzuwa, aikin narkar da abinci da dai sauran su.

    Alfanun fannin Anatomy da Physiology

    Yadda magani ke amfani ga jiki da kuma aiwatar da ayyukan asibiti. Nazarin cutuka da ayyukan tsare-tsaren jiki da kuma gwaje-gwajen lafiyar jiki.

    Cell Biology

    Cell Biology shi ne fannin ilimin Biology da ke nazarin cells, ƙwayoyin halitta mafi ƙanƙanta da ke da cikakken tsarin rayuwa.

    Muhimman fannonin cell Biology

    • Structure of the Cell: Rabe-raben ƙwayoyin halitta ga dabbobi, tsirrai prokaryotic da eukaryotic.
    • Organelles: Nazarin sassan cikin ƙwayoyin halitta kamar nucleus, mitochondria, ribosome, da sauran su.
    • Cell Division: Yadda ƙwayoyin halitta ke raba kansu (mitosis da meiosis).
    • Cell Communication: Hanyoyin sadarwa tsakanin ƙwayoyin halitta da masu aika saƙonni (hormones, neurotransmitters).

    Alfanun fannin Cell Biology

    Amfanin wannan fanni sun haɗa da; nazarin cigaban ƙwayar cuta, fahimtar tushen cutukan cancer da nazarin sabbin ƙwayoyin halitta da haɓakar su.

    Matsalolin ilimin Biology a Najeriya

    1. Rashin kayayyakin gwaje-gwaje

    Yawancin makarantu, musamman na gwamnati, ba su da wadatattun kayan aiki a ɗakunan gwaji ko kuma suna da tsofaffi waɗanda suka lalace. Wannan na hana ɗalibai koyo ta fuskar gwaje-gwaje yadda ya kamata.

    2. Karancin littafai da manhaja na zamani

    Akwai matsalar amfani da tsoffin littafai da rashin sababbin manhajoji da suka dace da abubuwan da kimiyya ke ci gaba da haifarwa.

    3. Karancin ƙwararrun malamai

    Akwai yawan malamai da ba su da takamaiman ƙwarewa a fannin Biology, wasu kuma ba su da horo kan yadda za su koyar da ilimin Biology yadda ya dace.

    4. Tsarin koyarwa mara inganci

    Wannan matsala ce da ta shafi yadda ɗalibai ke dogaro da karanta littafi da haddacewa kawai, ba tare da fahimtar yadda ilimin Biology ke aiki ba.

    5. Rashin sha’awa daga dalibai

    Ɗalibai da dama ba sa jin daɗin Biology saboda ba sa ganewa ko kuma yadda ake koyar da shi yana musu nauyi.

    6. Matsin tattalin arziki da rashin tallafi

    Iyaye da makarantu da kansu ba sa iya biyan kuɗin littafai, kayan aiki da kuɗin gwaji.

    7. Karancin bincike (research)

    Binciken kimiyya da sabbin abubuwa da ake ƙirƙira sun yi ƙasa sosai a Najeriya, musamman a jami’o’i.

    8. Matsalolin jarrabawa (WAEC/NECO)

    Ɗalibai da malamai na mayar da hankali ne kawai kan samun sakamako, ba fahimta ba. Hakan na haifar da maguɗi da rashin ƙwarewa.

    9. Bambancin koyarwa tsakanin makarantu

    Akwai bambanci sosai tsakanin makarantun birni da na ƙauye, masu zaman kansu da na gwamnati, wanda hakan ke haifar da rashin daidaito a fahimtar ilimin Biology.

    10. Rashin haɗin gwiwa tsakanin makarantu da hukumomi

    Akwai cikas na rashin kyakkyawar alaƙa tsakanin makarantu, cibiyoyin bincike da hukumomin kimiyya don tallafawa ilimin Biology.

    Hanyoyin magance matsalolin

    1. Gwamnati ta ware kuɗi na musamman domin gyarawa da samar da ɗakunan gwaji. Ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kamfanoni don ba da tallafin kayan aikin gwaji. A horar da malamai yadda za su iya ƙirƙirar wasu kayan gwaji da kayan gida masu sauƙin samu (improvised apparatus).
    2. A sabunta manhajar koyarwa bisa ga ci gaban da ake samu a fannin Biology. Kuma a samar da littafai na zamani a cikin dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu. Har ila yau akwai buƙatar a samar da e-books da online resources da ɗalibai za su iya amfani da su kai tsaye.
    3. A samar da tsarin horarwa da bita (training/workshops) na musamman ga malamai lokaci-lokaci. A gyara tsarin ɗaukar malamai, a tabbatar cewa dole sai Biology suka karanta ko fannin kimiyya da ya dace.
    4. Faɗaɗa tsarin koyarwa zuwa hanyoyin zamani kamar amfani da hotunan charts, models, videos, simulations da sauran su. A samar da lokaci na musamman don gudanar da practical sessions. A riƙa amfani da tsarin tambaya da amsa da ayyuka masu karfafa tunani (critical thinking).
    5. A inganta hanyoyin koyarwa domin su zama masu jan hankali da nishaɗi. A haɗa fannin da ayyukan rayuwa ta yau da kullum don su fahimci amfani da shi. A samar da gasar kimiyya da nune-nune (science fairs) don ƙara musu sha’awa.
    6. Gwamnati ta samar da tallafin ilimi na musamman ga Biology da sauran fannonin kimiyya. Kamfanoni da NGO su bayar da gudunmawa ta kayan aiki ko horar da malamai. Samar da kayan aikin gwaji masu sauƙi da rahusa.
    7. A samar da ɗakunan bincike a jami’o’i da tallafa wa bincike da kuɗi. A riƙa haɗa dalibai da masana don su koyi hanyoyin bincike tun suna makaranta. Haka nan a ƙarfafa wallafa sakamakon bincike da samar da haɗin gwiwa da ƙasashen waje.
    8. A inganta tsarin jarabawa domin ya ƙarfafi gwaji da kwarewa. A riƙa oyar da Biology ta hanyar bincike da ƙarfafa amfani da gwaji. A riƙa hukunta duk masu magudi da satar jarabawa.
    9. A daidaita rarraba kayan aiki da malamai a dukkan makarantu. A kuma samar da tsare-tsaren ɗakuna gwaje-gwaje na tafi-da-gidanka (mobile laboratories) da za su riƙa zagayawa makarantun ƙauyuka. Sannan a inganta amfani da na’urar kwamfuta da intanet don tallafa wa koyarwa.
    10. A samar da tsarin haɗin gwiwa tsakanin jami’o’i, makarantun sakandare da hukumomin kimiyya. A riƙa gayyato masana zuwa makarantu domin gabatar da jawabi da bita. A karfafa wa ɗalibai gwiwa su riƙa halartar nune-nune da tarukan kimiyya.
    11. Ilimin Biology yana da muhimmanci matuƙa wajen ci gaban ilimi da kimiyya a kowace ƙasa. Don haka, yakamata Najeriya ta mayar da hankali wajen magance waɗannan matsaloli ta hanyar tsara manufofi masu nagarta, samar da kayan aiki, horarwa, da haɗin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban.

    Manazarta

    STAN Biology Textbook for Senior Secondary Schools (NERDC)

    Bichi, A.H. (2008). Comprehensive Certificate Biology. Kano: Kalmax Publishers.

    Raven, P.H., Johnson, G.B. (2018). Biology, 12th Ed. McGraw-Hill Education.

    Solomon, E.P., et al. (2016). Biology, 10th Ed. Cengage Learning.

    *** Tarihin Wallafa Maƙalar ***

    An kuma sabunta ta 25 July, 2025

    *** Sharuɗɗan Editoci ***

    Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

    Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

    Maƙalar ta amfanar?
    EAa

    You cannot copy content of this page

    ×