Bitget, babbar manhajar musayar cryptocurrency ce da kamfanin fasaha na Web3 ya kirkira, an bayyana ta a cikin jerin manyan amintattun manhajojin hada-hadar crypto 25 da kafar Forbes ta fitar. Tana matsayi na takwas a cikin jerin, kanfanin Bitget ya ba da rahoton kwararar masu amfani da manhajar a shekarar da ta gabata.

An samar da manhajar Bitget a cikin shekarar 2018, Bitget manhajar musaya da hada-hadar crypto ce ta duniya da ke masu amfani da ita har sama da miliyan 25 a dukkan faɗin duniya. Ana samun ta a cikin ƙasashe fiye da guda 100 in ban da Kanada da Amurka. Manhajar ta yi hadin gwiwa da fitattun mutane kamar ɗan wasan kwallon kafar nan mai suna Lionel Messi da kungiyoyi kamar kungiyar kwallon kafa ta Juventus domin bunƙasa tambarin kamfanin da kuma jawo sabbin mutane don yin rijista da ita. Bitget sananniya ce wajen samar da ƙaƙƙarfan bigiren kasuwanci mai sauƙi wanda ke ba da dama ga sabbi da ƙwararrun ‘yan kasuwa.
Ba da jimawa ba, kamfanin Bitget ya sami ƙaruwar kashi 400% a cikin masu amfani da manhajar wanda ya zarce adadin masu amfani da miliyan 100 a cikin Disamba kuma adadin ‘Spot trading’ ya karu daga dala biliyan 160 a Q1 zuwa dala biliyan 600 a Q4. Da ma dai tun bayan haɗa kai da ‘yan wasan kasar Turkiyya, zuwa gasar kwallon kafa ta LALIGA, har zuwa samun sabbin shugabannin kamfanin da kuma ba da lasisi da yawa, Bitget ya karfafa matsayinsa na jagora a duniya, ya zama na biyu mafi girma a fagen hada-hada da musayar crypto.
Ayyukan manhajar Bitget
Bitget spot trading
Manhajar tana tallafa wa tsarin spot treading don saye da sayar da cryptocurrencies nan take a farashi mai gudana. Wannan tsarin yana da fiye da nau’in kuɗaɗen dijital 750 domin cinikayya da kuma sama da 870 na nau’i-nau’in hada-hada. A halin yanzu, tsarin spot treading a Bitget yana samar da nau’ikan cinikayya iri uku:
• Stablecoin pair (USDT ko USDC)
A cikin wannan tsari, ana iya sayan cryptocurrencies da statscoins. Misali, za a samu nau’ikan BTC/USDT, ETH/USDC, da SOL/USDC.
• Cryptocurrency Pairing (BTC ko ETH)
Wannan nau’in cinikayya ya ƙunshi haɗa nau’ikan cryptocurrencies daban-daban, kamar Bitcoin (BTC) ko Ethereum (ETH) don musayar kai tsaye.’Yan kasuwar crypto za su iya sayan BTC tare da ETH ko akasin haka. Za a samu nau’ikan cinikayya daban-daban kamar BTC/ETH, SOL/BTC, ATOM/BTC, da sauran su.
• Fiat pairs (EUR, USD, da sauran su)
Wannan bangare shi ma yana ba wa masu amfani da manhajar Bitget damar yin cinikin cryptocurrencies kai tsaye tare da kuɗaɗen gargajiya kamar Yuro (EUR) da dalar Amurka (USD). Wannan yana kawo sauƙin shigarwa cikin kasuwar cryptocurrency ga mutane waɗanda suka fi son amfani da kuɗin asali na gida.
Bitget futures trading
Bitget tana ba da damar cinikin kadarori a lokaci mai zuwa, waɗanda ainihin yarjejeniya ce ta saye ko sayar da cryptocurrency a kan tabbataccen farashi a nan gaba. Wannan yana ba da damar yin hasashe kan ko farashin cryptocurrency zai hau ko zai sauka. Bitget tana ba da damar tsarin 125x don hada-hadar lokaci mai zuwa.
Wannan yana nufin za a iya ɗaukar matsayi mafi girma fiye da saka hannun jari na farko. Hakan na iya bunƙasa yuwuwar samun riba idan kasuwa ta motsa, za kuma a iya yin asara.
Bitget margin trading
Har ila yau dai Bitget tana ba damar aiwatar da margin trading. Wannan tsarin cinikayya yana ba da damar hada-hadar kasuwancin cryptocurrencies ta amfani da kuɗin aro daga manhajar. Misali: mutum ya sanya adadin kuɗi kaɗan (wanda ake kira margin) a matsayin jingina, Bitget kuma ta ba shi rancen sauran don ya gudanar da kasuwancinsa. Akwai manyan nau’ikan cinikayyar margin guda biyu a kan manhajar Bitget: Isolated Margin da Cross Margin
Isolated margin
Wannan nau’i yana keɓance kuɗaɗen aro na kowace cinikayya. Don haka, idan farashin cryptocurrency ɗaya da aka yi tare ya ragu, ba zai shafi kuɗin da aka ara don wasu hada-hadar ba. Wannan na iya taimakawa wajen rage asara.
Cross margin
Wannan nau’i kuwa yana la’akari da dukkan kuɗaɗen asusu a matsayin babbar taska guda ɗaya. Duk wasu kuɗaɗen da aka karɓa za a iya amfani da su don aiwatar da kowace hada-hada. Wannan na iya zama mai amfani idan ana son baza hannaye a cikin hada-hadar cryptocurrencies daban-daban, amma sai an yi taka-tsantsan. Idan jimillar kuɗaɗen crypto ɗin mutum ta yi ƙasa da wani mataki, Bitget na iya tilasta masa sayar da wasu crypto ɗin domin ya biya lamunin.
Bitget convert
Bitget yana da wani fasali da ake kira “convert” wanda ke ba da damar yin musanyar wani nau’in cryptocurrency cikin sauƙi zuwa wani daban. Wannan ɓangare ko fasali yana da muhimmanci. Amfani da wannan ɓangare gabaɗaya kyauta ne. Babu wani ɓoyayyen caji ko ƙarin kuɗaɗen da za a damu da su. Bugu da ƙari, za a iya musanya duk wani adadin da ake so, muddin ya kai aƙalla cents goma na (USD) a darajar crypto.
Bitget P2P trading
Bitget tana samar da sashen cinikayyar P2P inda za a iya saye da sayar da cryptocurrencies kai tsaye tare da sauran masu amfani da manhajar. Ɗaya daga cikin manyan fa’idojin Bitget P2P shi ne babu wani caji don amfani da sashen, kyauta ne. Amma a lura cewa masu biyan kuɗi na iya yin caji.
Bitget a halin yanzu tana tallafa wa sama da kuɗaɗen gargajiya 140 (fiat) a kan kasuwar P2 tare da hanyoyin biyan kuɗi sama da 100. Haka nan tana ba da dama ga cryptocurrencies guda 6 don cinikayya a tsarin P2P.
- USDT
- USDC
- BTC
- ETH
- BGB
- DAI
Domin tabbatar da tsaro, Bitget tana amfani da tsarin ‘escrow’ don kare masu saye da masu sayarwa. Ga yadda yake aiki: Lokacin da aka ba da odar sayan crypto, Bitget a zahiri tana riƙe crypton mai sayarwa har sai mai saye ya tabbatar da cewa ya biya. Da zarar an tabbatar da biyan kuɗi, Bitget za ta saki crypto zuwa ga wanda ya saya. Ta wannan hanyar, za a iya tabbatar da cewa za a samu dukkan crypto ɗin da ake saya, kuma mai sayarwa zai iya tabbatar da cewa za a biya shi.
Bitget copy trading
Bitget ta shahara sosai a fagen “Copy Trading”. Kamar kwaikwayon sana’ar wasu gogaggun ‘yan kasuwa ne. Sashen kasuwanci na Bitget copy trading yana da tafki na ƙwararrun ‘yan kasuwa sama da 130,000, wanda ake kira ‘fitattun yan kasuwa’. Waɗannan
ƙwararrun ‘yan kasuwa suna da ingantaccen tarihi kuma ayyukan kasuwancinsu a bayyane suke. Mutum zai iya bincikawa cikin waɗannan ‘yan kasuwa ya zaɓi waɗanda aikinsu ya burge shi.
Bitget tana sauƙaƙa zaɓi ta hanyar bayyana yawan ayyuka a kan allon kasuwancinsu. Ana iya ganin riba ko asarar mai ciniki (PnL), dawowa kan saka hannun jari (ROI), AUM, masu kwafi PnL, da sauran ƙididdiga.
Akwai mabiya sama da 650,000 da ke amfani da sashen, Bitget ta sauƙaƙe jimullar riba da asara na sama da dalar Amurka $430,000,000. Wannan kuɗi ne mai yawa da mutane ke samu dalilin bibiyar tsarin kasuwancin gogaggun masu saka hannun jari.
Bitget trading bots
Bitget tana samar da nau’ikan ‘bots’ na cinikayya waɗanda za su iya sarrafa dabarun kasuwancin cryptocurrency. Waɗannan ‘bots’ suna iya aiwatar da kasuwanci tsawon 24/7 ba tare da buƙatar saka idanu akai-akai game da kasuwancin ba. A nan akwai nau’ikan bots na Bitget daban-daban:
• Spot grid bot
Idan aka saita odar saye da sayarwa a kan wani takamaiman farashi, mai hawa da sauka. Wannan bot ɗin yana aiwatar da umarni ta tsarin atomatik, yana sayen coins idan farashin ya yi ƙasa kuma ya sayar a yayin da farashin ke hauhawa.
• Futures grid bot
Wannan bot ya yi kama da Spot Grid Bot, amma shi yana aiki ne a kan hada-hadar lokaci mai zuwa, waɗanda ke ba da damar haɓaka kasuwanci.
• Position grid bot
An ƙera wannan bot ne domin kasuwanni masu canjawa babu zato babu tsammani. Yana aiwatar da odar ta tsarin atomatik a tazarar lokaci iri ɗaya yayin da farashi ke raguwa, yana sqyan ƙarin coins a kan farashi kaɗan, sannan sayar da su lokacin da farashin ya tashi.
• Futures position grid bot
Wannan bot yana aiki daidai da Spot Position Grid Bot amma ga hada-hada ta lokaci mai zuwa.
• Spot auto-invest
Wannan bot yana da alfanu ga waɗanda ke son saka hannun jari a cikin crypto akai-akai amma ba sa son bincika farashin koyaushe. Idan aka saita adadin kuɗaɗen da ake son saka hannun jarin da su a ƙayyadaddiyar tazara (misali, $200 a kowace ranar Litinin), bot ɗin kula da hada-hadar.
• Spot martingale bot
Wannan bot yana bin dabarun sayan adadi kaɗan. Yana aiwatar da ƙananan odar sayayya yayin da farashin ke raguwa, yana daidaita farashin yadda ake sayen coins, tare da yin tsammanin farashin zai sake hawa daga baya.
• Spot CTA bot
Wannan bot yana amfani da dabarun ciniki na ɗan gajeren lokaci don sayarwa da samun riba daga kasuwa a cryptocurrencies daban-daban.
• Futures quant bot
Wannan bot shi ne wanda mafi yawan ‘yan kasuwa na fasaha ke amfani da shi. Yana ba da damar gina dabarun kasuwanci ta hanyar amfani da bayanan kasuwa da yawa.
• Futures signal bot
Wannan bot ɗin yana ba da damar haɗa asusun Bitget da TradingView, sananniyar manhajar tsara bayanai. Ana iya kwafin siginar cinikayya daga wasu ‘yan kasuwar crypto ko ƙirƙirar naku kuma ku sa bot ya zama mai aiwatar da su ta tsarin atomatik.
Lamunin crypto
Lamunin Bitget yana ba da damar aron cryptocurrency ta amfani da hannun jarin crypto a matsayin jingina. Akwai tsarin kuɗin ruwa na sa’a mai sauƙi. A halin yanzu, za a iya aron USDT a kan kuɗin ruwan da ya kai kashi 15% a tsawon kwanaki 30. Ga Bitcoin (BTC), yawan kuɗin ruwan shi ne kashi 1.9% kawai.
Launchpad da Lanchpool
Manhajar tana samar da hanyoyi uku domin shigar da sabbin kuɗaɗen cikin harkokin crypto:
- • Launchpad: Initial Exchange Offerings (IEOs), wannan na ba da dama domin sayan sabbin tokens da wuri, mai yuwuwa a farashin garaɓasa.
- Launchpool: Wannan yana riƙe crypto ɗin da aka mallaka kamar BGB don samun tukuici a sabbin tokens. Ya zuwa yanzu akwai jimullar crypto 67 da aka ƙaddamar da jimillar kudadensu suka kai dalar Amurka biliyan 2.1.
- PoolX: Wannan yana kama da Launchpool, amma za a ci nasara yayin raba airdrop.
Manazarta
BitGet: Exchange Ranking & trading Volume | CoinRanking. (n.d.-b). Coinranking.
McCracken, T. (2024b, November 27). BitGet Exchange Review 2025: Is it a good trading platform? Coin Bureau.
NFTevening, & NFTevening. (2025, February 22). BitGet Review 2025: Trading features, fees, and security. NFT Evening.
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.