Skip to content

Bola Tinubu

An haifi Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Maris a shekarar 1952 a birnin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya. Bola Ahmed Tinubu, jajirtacce kuma fitaccen ɗan siyasa a Najeriya wanda ke da sarautar Asiwaju a ƙasar Yarabawa, kuma Jagaban a Borgu ta Jihar Neja, ya shahara a fagen siyasa da mulki a Najeriya.

Shugaba Tinubu da tsohon shugaban ƙasa Buhari, lokacin da ya karɓi shahadar lashe zaben 2023.

Iyayensa da iyalinsa

Ba kasafai ake magana a kan mahaifin Bola Tinubu ba, amma mahaifiyarsa sananniya ce, ita ce ma shugabar mata ‘yan kasuwa na birnin Legas da ke zaune a Unguwanr Tinubu, ana kiran ta da sunan Alhaja Mogajiya Habibat mai arzikin gaske.

Asiwaju Bola Tinubu yana da mata daya mai suna Oluremi Tinubu, wadda sanata ce mai wakiltar Jihar Legas ta tsakiya. Ta kasance mai fafutikar kare hakkin jama’a da kuma mai ilimi da ake mutuntawa. Tana kuma gudanar da ayyukan jin kai wadda aka karrama da lambar girmamawa ta kasa ta Officer of the Order of the Niger (OON).

Shugaba Tinubu da Maiɗakinsa, a wajen bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta.

Karatunsa

Shugaba Tinubu ya halarci makarantar firamare ta St. John’s da ke Aroloya da makarantar Children’s Home a Ibadan, da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Bayan nan sai ya wuce Kwalejin Richard Daley a Chicago da ke kasar Amurka, inda ya samun gurbin yin karatu a Kwalejin.

Daga baya ya zarce zuwa Jami’ar jihar Chicago, a Illinois inda ya kammala karatunsa ya kuma fito da Digiri a Harkokin Kasuwanci.

Tinubu ya kuma samu kyautar dalibin da ya fi ƙwazo a Jami’ar da kuma shaidar karramawa a ɓangaren Akanta da Hada-Hadar kudi.

Gwagwarmaya

A lokacin da yake Amurka a shekarar 1975 da taimakon mahaifiyarsa, kasancewar shi mai hazaka, da kuma ke da ƙudirin ganin ya cim ma burinsa, sai ya shiga yin ayyuka da za su kawo masa kuɗi kamar wanke-wanke a gidajen sayar da abinci da aikin gadi da kuma tuka motar-haya domin taimaka masa a ɓangaren karatunsa.

Jajircewar da yake da ita ce ta sa ya shiga jerin ɗalibai masu hazaka a Kwalejin Richard Daley da kuma ta kai har ya kammala karatu a Jami’ar jihar Chicago a 1979 inda ya fito da digiri a fannin Kasuwanci.

A shekararsa ta farko a Jami’ar Chicago, an karrama shi da mukamin malami mai taimakawa wato (tutor)ba turance, domin yana taimakon wasu ‘yan uwansa dalibai da ke ƙananan ajuzuwa. ‘Yan uwansa dalibai da dama sun yaba taimakonsa a ɓangaren karatunsu wanda har ta kai su ga samun sakamako mai kyau.

Shugaba Tinubu yayin da ake rera taken ƙasa Najeriya a wajen wani taro.

A tsawon shekarun da yayi a jami’a, Tinubu ya kasance dalibi mafi hazaƙa wanda ya yi ta samun kyautar dalibi mai ƙwazo da kuma shaidar karatu a ɓangaren Akanta da hada-hadar kuɗi, inda kuma ya ƙare digirinsa da sakamako mai daraja ta sama.

A matsayinsa na mai burin abubuwa masu kyau da za su zo, Tinubu ya tsaya tare da yin nasara a takarar shugaban ɗaliban nazarin Akanta da Hada-hadar kudi na jami’ar jihar Chicago a shekararsa ta karshe.

A matsayinsa na mutumin da ba ya manta mafararsa da kuma alakarsa da al’umma, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kasance mutumin da ya dauki hidimar al’umma da muhimmanci. Ko da a Mobil, ya jagoranci hidima daban-daban na tara-kudi domin tallafa wa shirye-shiryen ci-gaban al’umma a Jihar Legas.

Ya kuma jagoranci kungiyar Primrose, wata kungiyar siyasa da ke hankoron kawo canji a siyasar Jihar Lagos.

Haka nan, Bola Tinubu ya yanke shawarar shiga aikin hidimar al’umma gadan-gadan ta hanyar ajiye babban matsayi da yake da shi a kamfanin Mobil.

Shugaba Tinubu da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a wajen wani taro.

Kasuwanci da ayyukansa

Kafin kammala karatunsa na digiri, Bola Tinubu ya samu aiki da kamfanin harkar akantanci na Arthur Anderson.

Daga bisani kamfanin Deloitte Haskins (wanda ake kira da deloitte Haskins and Touche a yanzu) suka dauki hayarsa, bayan nan kuma sai ya yi aiki da GTE Service Corporation, wani babban kamfanin sadarwa a kasar Amurka.

A kamfanin Deloitte Haskins and sells, matashi kuma ƙwararre Bola ya fadada kwarewarsa ta hanyar shiga ayyukan dubawa da gudanarwa na General Motors da yin aiki a Babban Bankin Kasa na Chicago da kamfanin Procter and Gamble da International Harvester da General Electric da sauran kamfanoni na Fortune 500.

Bayan ganin kwarewarsa, kamfanin Deloitte sal da yawa ya kan dauki hayar Bola a matsayin jagoran mambobi da ke sa ido a kamfanin.

Bayan dawowarsa Najeriya da kuma samun gogewa a bangaren hada-hadar kudi, Tinubu ya fara aiki da Mobil a matsayin babban mai bincike wanda ta kai har ya zama ma’ajin kamfanin.

Siyasarsa

Bayan komowarsa gida ne kuma ya shiga harkokin siyasa, inda ya shiga kungiyar People Front ta marigayi Janar Shehu Musa Yaradua, kafin daga bisani su rikide zuwa jamiyar SDP, inda kuma a nan ne ya tsaya takarar Sanata mai wakiltar Legas ta Yamma, tare kuma da samun nasara.

A Majalisar Dattijan Najeriya, ya samu nasarar zama shugaban kwamitin da ke kula da bankuna, kuɗi da kasafi na Majalisar Dattawa – wanda babban kwamiti ne na Majalisar Dattawan Najeriya.

Bayan da sojoji suka soke zaben 12 ga watan Yuni da aka fi sani da zaben Abiola, Tinubu da wasu ‘yan siyasa, musanman daga kudancin kasar, sun tafi gudun hijirah tare kuma da kafa wata ƙungiya ta ‘yan adawa da mulkin soji mai suna NADECO. Sun tunkari gwamnatin mulkin soji na wancan lokaci wajen ganin an kikiro da tsarin dimokuradiyya a Najeriya.

Bola Tinubu ya sha barazana ga rayuwarsa da musgunawa wanda har ta kai ga kamawa tare da tsare shi wanda hakan ya sa ya gudu ya bar kasar. Duk da haka bai karaya ba a gwagwarmayarsu ta neman tsarin dimokradiyya inda ya zama shugaban kungiyar ta NADECO da ke gudun hijira, inda ya ci gaba da hankoron ganin mulkin dimokradiyya da tsarin shugabanci a Najeriya.

A yayin da sojoji suka kada gangan siyasa a 1998, Bola Tinubu ya dawo gida, ya tsaya takarar gwamna a karkashin jam’iyar AD ko Alliance for Democracy, inda ya mulki jihar Legas tsawon shekaru takwas.

A wannan lokaci ne dai Tinubu ya kafa abin da ake ganin jam’iyar siyasa da magoya baya da dama da suka zame masa jari a tafiyar siyasarsa ta neman shugabancin Najeriya a wannan lokaci.

Bola Tinubu ya kasance ginshiƙi wajen ci gaban jihar Legas ta fuskar tattalin arziki, siyasa da kuma abin koyi ga sauran jihohin kasar wajen dogaro da kai da samun kudaden shiga.

Shugaba Tinubu a wajen yaƙin neman zaben 2023.

Farin jininsa ya karu ne a siyasar Najeriya wajen sunan da ya yi wajen marawa ‘yan Arewa baya a siyasa, tun daga marigayi Janar Shehu Musa ‘Yaradua, zuwa Atiku Abubakar da Nuhu Ribado sai kuma Shugaban Muhammadu Buhari a karkashin jamiyar APC mai Mulki a yanzu.

Matsayinsa na gwamnan Legas

Bayan samun nasarar zama gwamnan Jihar Legas a zabukan 1999, Tinubu ya jagoranci jihar har na tsawon shekara 8.

Bayan shigar sa ofis a watan Mayun 1999, Bola Tinubu ya jawo hazikan mutane a cikin gwamnatinsa, wanda tare suka tsara kyakkyawan shiri na shugabancin Jihar lagos.

Ajanda 10 da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai sun kunshi bangaren ilimi da lafiya da samar da ayyukan yi da rage talauci, da samar da wutar lantarki da ruwan sha da tsarin zirga-zirga mai kyau da kula da muhalli da doka-da-oda da samar da abinci da kuma farfado da bangaren aikin gwamnati.

Gwamnatin Tinubu, ta inganta tare da gyara tsarin mulki ta hanyar kirkiro da sabbin ma’aikatu irinsu ma’aikatar gidaje da ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa da kuma ta harkokin mata da rage talauci.

A tsawon mulkinsa, Asiwaju Tinubu ya kawo hazikai da kuma kwararru a cikin gwamnatinsa a matsayin kwamishinoni da kuma masu ba shi shawara a bangarori da suka kware.

Ta hanyar tsare-tsare da aiwatarwa, gwamnatin Asiwaju Tinubu ta kara kasafin kudin Jihar Legas daga naira biliyan 14.200 a shekarar 1999 zuwa Naira biliyan 240.866 a shekarar 2007 domin Jihar ta samar da karin ababen more rayuwa ga al’ummarta.

Gwamnatin Tinubu ta ci gaba da kiyaye rabon kasafin kudi na shekara da akalla kashi 60-40 bisa dari a kan kudin da ake kashewa na manyan ayyuka don tabbatar da an samar da ababen more rayuwa ga al’umma.

Asiwaju Tinubu, ta hanyar kirkire-kirkire da sabbin tsare-tsare ya cire Jihar Lagos daga samun kudaden shiga na shekara-shekara na Naira biliyan 14.64 a shekarar 1999 zuwa Naira biliyan 60.31 a shekarar 2006. Ya zuwa watan Maris din 2007, jihar ta samu kudin haraji a wata da ya kai naira biliyan 8.2.

Ƙoƙarinsa wurin kafa APC

A zaɓen 2015, Asiwaju ya zama babban mai goyon bayan hadewar jam’iyyarsa da wasu jam’iyyun adawa biyu – Jam’iyyar CPC da kuma Jam’iyar ANPP domin kawo karshen mulkin Jam’iyar PDP.

Jam’iyyun guda uku sun hade daga baya inda suka samar da jam’iyar All Progressive Congress (APC). Duba da rawa da ya taka wajen kafa jam’iyyar, an bai wa Tinubu mukamin jagoran jam’iyyar na kasa. A nan ma, ya sadaukar da burinsa na siyasa, domin karfafa jam’iyyar da ba ta fifiko a kasa baki daya.

A 2015, jam’iyyar ta APC ta samu nasarar lashe zaben shugaban kasa na 2015, wanda karon farko da jam’iyyar adawa ta kada shugaba mai mulki a Najeriya. Tinubu ya taimaka wa Jam’iyyar ta APC wajen samun nasara.

A yau, APCn ita ke mulkin Najeriya bayan samun nasarar zaɓen shugaban kasa. Jam’iyar na kuma da mafi rinjayen mambobi a majalisar tarayyar kasar guda biyu da kuma gwamnoni a jihohi 22 na kasar.

Manazarta

BBC News Hausa. (2023, March 1). Bola Ahmed Tinubu: Tarihin zaɓaɓɓen Shugaban NajeriyaBBC News Hausa.

Voa. (2023, January 17). 2023: Tarihin Dan Takarar Shugaban Kasa, Bola Tinubu (APC). Voice of America.

McKenna, A. (2024, August 13). Bola Tinubu | Biography, Wife, Chicago, & Facts. Encyclopedia Britannica.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×