Skip to content

Bramall Lane

Bramall Lane ɗaya ne daga cikin tsoffin filayen wasan ƙwallon ƙafa a duniya, tana da daɗɗen tarihi tun daga shekarun 1850. Asali, wurin ya kasance filin wasan cricket ne. An kafa filin wasan cricket na Bramall Lane a cikin shekarar 1855 da Sheffield Cricket Club. A cikin shekarar 1862, aka buga wasan ƙwallon ƙafa na farko a filin wasan Bramall Lane, wanda ke nuna farkon kyakkyawar dangantakar filin wasan da ƙwallon ƙafa.

A cikin shekarar 1889, Bramall Lane ya zama filin wasan mallakin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sheffield United Football Club, wadda aka ƙirƙira daga Sheffield United Cricket Club. Kulob ɗin ya yanke shawarar ɗaukar wasan ƙwallon ƙafa a cikin watannin hunturu don ci gaba da kasancewa tare da membobin ƙungiyar. An mayar da Bramall Lane a hukumance zuwa filin wasan ƙwallon ƙafa, kuma Blades sun buga wasansu na farko na ƙwallon ƙafa a ranar 29 ga watan Disambar 1889, karawa ce da Notts County, inda suka ci 5-1.

A cikin shekaru da yawa da suka shuɗe, Bramall Lane ya fuskanci gyare-gyare da yawa da ingantawa don ɗaukar yawan adadin magoya baya da kuma dacewa da ƙa’idojin zamani. Ɗaya daga cikin manyan canje-canjen ya faru ne a cikin shekarar 1975 lokacin da aka maye gurbin tsohon John Street Terrace da madaidaicin cantilever, wannan ya ƙara ƙarfin filin wasan. Babban gyare-gyare na baya-bayan nan ya faru a cikin shekarar 2006, wanda ya ƙara girman filin zuwa sama da mutane 32,000.

Tarihin ƙirƙirar filin wasan

Tarihin Bramall Lane ya fara ne a cikin shekarar 1855 lokacin da aka fara assasa shi a matsayin filin wasan kurket. An ba shi sunan Bramall saboda wani gidan tarihi a Sheffield. Filin wasan cricket ya kasance gidan cricket Club na Yorkshire County a tsawon shekaru da yawa.

Filin wasa na Bramall Lane yana cikin yankin Sharrow na Sheffield, Kudancin Yorkshire, a ƙasar Ingila. Adireshin filin wasan shi ne Bramall Lane, Sheffield S2 4SU. Kasancewar shi kusa da tsakiyar garin Sheffield, Bramall Lane yana samun sauƙin shiga ta hanyar jigilar jama’a, hakan ya mayar da shi kyakkyawar makoma ga magoya baya.

Bramall Lane shi ne mafi soyuwar filin wasan ƙungiyar Sheffield United Football Club, wanda aka sani da Blades. Kulob ɗin yana da tsohon tarihi, wanda ya kasance sananne a fagen wasan ƙwallon ƙafa na Ingila tun lokacin da aka kafa shi a shekarar 1889. Sheffield United ta sami nasarori masu yawa, ciki har da lashe gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta farko a shekarar 1898 da gasar cin kofin FA a shekarar 1899. Bramall Lane ya samu waɗannan nasarorin na tarihi kuma ya ci gaba da zama filin da ƙungiyar Blades take buga wasannin gida.

Baya ga ƙungiyar Sheffield United, filin wasan Bramall Lane kuma ya karɓi baƙuncin wasannin ƙasa da ƙasa daban-daban kuma wasu ƙungiyoyin cikin gida sun yi amfani da shi tsawon shekaru. Duk da haka, asalinsa ya kasance  mallakin ƙungiyar Sheffield United da kuma irin goyon bayan da suke samu daga magoya bayansu.

bramalllane1
Bramall Lane shi ne tsohon filin wasa mafi daɗewa a tarihin wasanni.

Kasancewar shi a tsakiya ya sa ya zama muhimmin ɓangare na asalin birnin, kuma filin wasan ya zama wurin da masu sha’awar ƙwallon ƙafa a Sheffield da kewaye ke dabdala.

Yayin da ƙungiyar Blades ke ci gaba da nuna muhimman batutuwa na Bramall Lane, filin wasan ya kasance wata alama ta al’ada, abin sha’awa, kuma ruhin ƙwallon ƙafa. Tare da ɗimbin tarihinsa da ci gaba da mahimmanci a wasan zamani, Bramall Lane babu shakka zai ci gaba da riƙe matsayi na musamman a cikin zukatan masu sha’awar ƙwallon ƙafa.

Sauyawa daga wasan cricket zuwa ƙwallon ƙafa

Sauya wannan filin wasa zuwa filin wasan ƙwallon ƙafa ya faru ne a cikin shekarar 1862 lokacin da filin ya karɓi baƙuncin wasan kwallon kafa na farko. Wannan ya nuna ƙyanƙyasar Bramall Lane a matsayin filin wasanni biyu, wanda ke nuna wasan cricket da ƙwallon ƙafa. A ƙarshen ƙarni na 19 ne aka kafa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sheffield United kuma ta mayar da Bramall Lane filinta.

A cikin shekarar 1867, Bramall Lane ya gudanar da gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta farko a lokacin da Hallam FC ta doke Norfolk don lashe Kofin Youdan. A cikin shekarar 1883, aka shirya ɗaya daga cikin wasannin farko na Ingila da Scotland a wajen London ko Glasgow, kuma a cikin shekarar 1889, Sheffield suka buga wasan farko na Semi Final a gasar kofin FA.

Bunƙasar Sheffield United

Ƙungiyar Sheffield United, wadda aka fi sani da Blades, an kafa ta a cikin shekarar 1889 kuma cikin sauri ta haskaka kanta a matsayin ƙungiya mai ƙarfin da za a iya lasafta ta a duniyar ƙwallon ƙafa ta Ingila. Ta zama ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a cikin shekarar 1888 kuma ta sami nasara a gasar farko a 1898.

Sababbin sauye-sauye a filin Bramall Lane

Filin wasan Bramall Lane ya kasance a sahun gaba ta fannin bijiro da sabbin hanyoyin cigaban ƙwallon ƙafa a ƙarshen ƙarni na 19. A cikin shekarar 1862, filin ya karɓi baƙuncin wasan ƙwallon ƙafa na farko a duniya, wanda jerin fitulu na zamani suka haskaka. Wannan sauyi na cigaba ya ci gaba da wanzuwa har shekarar 1911 lokacin da filin ya zama ɗaya daga cikin filayen ƙwallon ƙafa na farko aka kafa fitilun lantarki. Wadannan ci gaban sun ba da gudummawa ga martabar filin wasan a matsayin majagaba a fasahar ƙwallon ƙafa.

Muhimman lokutan tunawa

Filin Bramall Lane ya keto wasu lokuta da yawa a cikin tarihinsa wanda ba za a taɓa mantawa da su ba, kama daga gudanar da gasar cin kofuna masu ban sha’awa zuwa manyan nasarorin gasanni, filin wasan yana da matsayi na musamman a zukatan magoya bayan ƙungiyar Sheffield United. Ɗaya daga cikin muhimman lokuta shi ne a shekarar 1915 lokacin da ya karɓi baƙuncin wasan ƙasa da ƙasa tsakanin Ingila da Scotland a lokacin yaƙin duniya na ɗaya, wanda ke nuni da muhimmancin filin wasan.

Bramall Lane ya karɓi baƙuncin Lionesses yayin da suka doke Sweden da ci 4-0 a gasar mata ta Euro 2022.

Filin wasa na Bramall Lane, wanda aka buɗe a shekara ta 1855, shine filin wasan ƙwallon ƙafa mafi tsufa a duniya wanda har yanzu yake ɗaukar wasannin ƙwallon ƙafa. Asalin filin wasan cricket, ya koma wurin wasanni biyu a 1862 tare da wasan ƙwallon ƙafa na farko. Kungiyar Kwallon Ƙafa ta Sheffield United ta karɓe ta a matsayin gidansu a shekara ta 1889. Filin wasan kuma ya karɓi bakuncin wasu wasanni, da suka haɗa da rugby, keke, da wasannin motsa jiki.

Taƙaitattun bayanai game da filin wasan

  • A shekarar 1855: aka ƙirƙiro filin wasa na Bramall Lane a matsayin filin wasan Cricket mallakar kungiyar wasan cricket ta Sheffield Cricket Club.
  • A cikin shekarar 1862: Aka buga wasan ƙwallon ƙafa na farko a cikin Bramall Lane, wanda ke nuna alamar canjin filin zuwa filin wasan ƙwallon ƙafa.
  • A shekarar 1867: Aka gudanar da gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta farko a a filin wasan.
  • A shekarar 1878: Filin wasan ya karɓi baƙuncin wasan ƙwallon ƙafa na farko da aka taɓa haskakawa.
  • A cikin shekarar 1883: Wasanni na farko na Ingila a wajen birnin London da Glasgow ya faru a filin Bramall Lane.
  • A cikin shekarar 1889: Aka kafa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sheffield United kuma ta mayar da Bramall Lane filin wasanta na dindindin.
  • A shekarar 1936: Aka kafa na’urar tattara yawan mahalarta ‘yan kallo wanda ya 68,287 a wasan cin kofin FA tsakanin Sheffield United da Leeds United.
  • A cikin shekarar 2006: Aka gudanar da manyan gyare-gyare a filin wasan, wanda ya ƙara yawan kujerun zama zuwa sama da 32,000.
  • A cikin shekarar 2022: Bramall Lane ya karɓi baƙuncin wasanni a gasar cin kofin nahiyar Turai ta mata ta UEFA, wanda ya ƙunshi wasan kusa da na ƙarshe inda Ingila ta doke Sweden.

A halin yanzu dai filin wasa na Bramall Lane ya ci gaba da kasancewa mallakin ƙungiyar Sheffield United kuma ya kasance muhimmin wurin wasan ƙwallon ƙafa da sauran wasanni.

Manazarta

Sheffield United – Stadium – Bramall Lane. (n.d.). Transfermarkt.

Sheffield United FC. (n.d.). Bramall Lane. Bramall Lane.

Sheffield United, Info & Map | Premier League. (n.d.).

Tripadvisor. (n.d.). Bramall Lane Stadium (2025) – All You Need to Know BEFORE You Go (with Reviews). 

*****

Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

Maƙalar ta amfanar?
EAa

You cannot copy content of this page

×