Skip to content

Budurci

Budurci wani tantani ne da yake cikin farjin mace, yana nan kamar jijiya kamar fata, ba shi da ƙwari, wanda ke nuna cewa budurwa ko mace ba ta taɓa yin jima’i ba. Yanayi ne na zamantakewa da al’adu wanda ke da alaƙa da dabi’u, fahimtar addini, da wasu abubuwa daban-daban na al’ada da rayuwa.

A mafi yawan al’adu, ana ganin budurci a matsayin kyakkyawan hali da kuma nagarta, alamar tsarki ce da kamewa ga mace. Kasancewa da budurci na da matuƙar daraja yayin neman aure. Sai dai masu tsokaci kan al’amuran rayuwa da dabi’u, sun soki wannan ra’ayi domin a cewarsu ya zama tsohon tunani.

Budurci wani lokaci ne ko zango a rayuwar mace wanda ke nuna cewa budurwa ko mace ba ta taɓa yin jima’i ba.

Yana da mahimmanci a gane cewa budurci wani ginshiki ne na zamantakewa, kuma mahimmancinsa da fahimtarsa na iya bambanta a tsakanin al’adu da ɗai-ɗaikun mutane. Kazalika, yana da matukar mahimmanci a yi taka-tsantsan game wannan batu, a yi amfani da ilmi da girmamawa da hangen nesa wajen fahimtar budurci a tare da mace, a ba da fifikon yarda da kuma ƙulla kyakkyawar alaƙa.

Dalilan tsare budurci

Abubuwa daban-daban da kan sa mace ta kiyaye ko kuma ta rasa  budurcinta, ga wasu daga cikin waɗannan abubuwa:

1. Al’adu da addini: Asalin al’adu da addini na iya tasiri sosai wajen kiyaye budurci da wasu al’amuran jima’i.

2. Dabi’u: Mutane na iya zaɓar su riƙe budurcinsu ko su rasa budurcinsu bisa ɗabi’u da tsarin rayuwar da suka taso a ciki.

3. Dangi da al’umma: Tsangwama daga wajen ‘yan’uwa da sauran al’umma na iya rinjayar mace har ta kai ga rasa budurcinta. Idan kuwa ta samu kulawa daga waɗannan to sai ta kiyaye budurcin.

4. Ilimi: Samun cikakken ilimin jima’i da cikakkun bayanai game da jima’i na iya yin tasiri wajen kiyaye budurci.

5. Tsangwamar ƙawaye:  ƙawaye da abokan zamanai na iya yin tasiri a kan ga kiyayewa ko akasin haka game da  budurci.

6. Ra’ayin ƙashin kai: Ra’ayin da sha’awar mace game da jima’i kan yi tasiri wajen tsare budurcinta.

7. Shekaru da balaga: Shekaru da balaga na iya yin tasiri ga budurcin yarinya, takan iya yanke shawarar kare budurcinta.

Alamomin budurci

Alamomin budurci wani batu ne mai sarƙaƙiya da ya bambanta ta fannoni daban-daban. A zamanin da, an yi amfani da hanyoyi daban-daban don tantance budurcin mace, amma galibin waɗannan hanyoyin ba su da inganci, yawanci ma bin hanyoyin tamkar cin zarafi da  muzantawa.

A da, wasu alamomin budurci da ake fahimta sun hada da:

1. Fatar Budurci: Ana yawan ganin kasantuwar fatar budurci a matsayin alamar budurcin mace. Duk da haka, wannan fata na iya samun matsala ta fashe a lokacin ayyuka daban-daban, kamar motsa jiki.

2. Ganin Jini a lokacin saduwar farko: Ana yawan ganin zubar jini a lokacin saduwar farko a matsayin alamar budurci. Sai dai, ba duka mata ne ke zubar da jini a lokacin jima’in farko ba, kuma zubar jini na iya faruwa saboda dalilai daban-daban.

3. Matsewa ko budewar farji: Wasu sun yi imanin cewa farjin budurwa zai fi wanda ya taba jima’i matsewa. Koyaya, matsewar farji ko sako-sako ya bambanta bisa ga al’ada a tsakanin ɗai-ɗaikun mutane kuma ba hakan tabbatacciyar ka’ida ba ce ta na gogewar jima’i.

Yana da mahimmanci a gane cewa yarda da waɗannan alamomi na da illa, kuma yana dawwamar da rashin yarda.  Domin gabaɗaya hanyoyin ba su da wata madogara ta ilimi, hasashen ne da kintace, wanda ba lallai ba ne ya yi aiki ga kowace mace ba. Maimakon mayar da hankali kan wadannan hanyoyin don tantance budurci, yana da mahimmanci a ba da fifiko ga yarda, yana da kyau a samu yarda tsakanin mutane. A tuna dai, budurci wani ɓangare ne na sirri da kuma ɓoyayye.

Dawo da budurci

Dawo da budurci abu ne mai matuƙar wahala da haɗari, akwai hanyoyi da dama da mutane ke bi don dawo budurcinsu. Wasu mutanen kan ni hanyoyin likitanci ko amfani da ƙwayoyin magani da ake da’awar suna mayar da budurci, amma yana da mahimmanci wadannan abubuwan:

1. Budurci abu ne na rayuwa da zamantakewa, ba yanayin jiki ba ne ake iya gani da ido ba.

2. Hanyoyin kiwon lafiya ko ƙwayoyi ba za su iya dawo da, ko goge abubuwan da suka faru na jima’i a baya ba.

3. Yunkurin dawowa da budurci na iya zama mai haɗari da cutarwa, kuma yana haifar da rashin gaskiya.

Wasu hanyoyi ko ƙwayoyin magani ake ikirarin suna dawo da  budurci sun haɗa da:

1. Hymenoplasty: Wannan fasaha ce ko hanyar tiyata da ake yi da nufin gyara ko sake gina fatar budurci (hymen).

2. Matse farji: Ana yin tiyata don matse farji, ko ma ba tiyatar ba, wasu dabaru ne dai da ake da’awar cewa suna matse farji.

3. Ƙwayoyin maganin budurci: Wasu ƙwayoyin magani da ba a tabbatar da su ba kuma galibi marasa inganci ne, ana amfani da su da nufin cewa suna mayar da budurci.

Waɗannan hanyoyin da ƙwayoyi galibi masu tsada ne, kuma kuma ba su da ingancin yin abin aka sha su domin shi. Hasali ma suna iya haifar da cutarwa ga jiki har ma da asarar rai.

Sakamakon rasa budurci

Hymen, wani abu a cikin farji mai kama da fata ko tantani da ke nuna budurci.

Sakamakon rasa budurci ba ta hanyar aure ba na iya bambanta dangane da yanayin mutum ɗaya, ko al’umma ko kuma al’ada. Abubuwan da mace za ta fuskanta idan ta rasa budurcinta sun haɗa da:

1. Laifi ne, kuma mutum zai kasance cikin jin kunya da nadama ko rashin jin daɗi.

2. Lalacewar dangantaka tsakanin budurwa da wanda take shirin aura har ma da abokai da dangi.

3. Haɗarin lafiya, yana ƙara haɗarin kamuwa da cututtukan jima’i (STIs), da ɗaukar cikin da ba shirya masa ba ko kuma samun lahani ga jiki.

4. Fuskantar izgilanci da tsegumi ko kuma ƙaurace wa ko yawan tsangwama.

5. Ɗaukar cikin da ba a yi niyya ko shirya masa ba, na zama ƙalubale wajen tsara iyali.

6. Hukuncin shari’a ko na al’ada: A wasu al’adu ko al’ummomi, yin jima’i ba tare da aure ba na iya zama haram ko kuma ya janyo hukuncin shari’a.

Manazarta

Amatulqahhar, U. (2024, July 8). Budurcin ’Ya mace. Amsoshi.

BBC News Hausa. (2020a, February 2). Ana neman a haramta tiyatar dawo da budurci.  BBC Hausa News

Flo.health (2020, September 8). What happens when you lose your virginity? Flo.health – #1 Mobile Product For Women’s Health.

HausaLoaded. (2018, September 26). Budurcin ‘Ya mace, ma’anarsa da Rabe-Rabensa. HausaLoaded.com

Planned Parenthood.  (n.d.).What is Virginity & the Hymen? | Losing your Virginity. Planned Parenthood.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×