An ƙirƙiro manhajar musanya da hada-hadar kuɗaɗen crypto ta kamfanin Bybit a watan Maris na shekarar 2018, wannan manhaja mallakar Ben Zhou ce. Bybit, manhajar musayar kuɗaɗen cryptocurrency ce ta gaba-gaba wadda aka fara amfani da ita a Singapore kafin ta koma Dubai a shekarar 2022. Tana aiki a ƙarƙashin babban kamfanin Bybit Fintech Limited, wanda ke da rajista da ofishi a British Virgin Islands. An ƙirƙiri Bybit bisa manufar yin aikace-aikace ga sabbin ‘yan kasuwa da ƙwararrun ‘yan kasuwa, tana samar da ba kawai hanyar sadarwa ta abokantaka ba har ma da tarin abubuwan da aka tsara don sauƙaƙe ciniki mai inganci a duniyar crypto.

Wani sanannen al’amari game da Bybit shi ne kasancewarta manhaja ta duniya. A halin yanzu, Bybit tana samar da sabis da aikace-aikacenta a cikin ƙasashe sama da 160. Tsarin fasaha mai ƙarfi na manhajar yana taimakawa ga rage ɓata lokaci da kuma saurin aiwatar da hada-hadar kasuwancin crypto, wanda zai iya yin babban tasiri lokacin da ake aiwatar da hada-hadar kasuwar crypto da sauri. Bybit tana da ɗimbin zaɓuɓɓukan ciniki da hada-hada masu yawa.
Nau’ikan kuɗaɗen da ake amfani da su a Bybit
Nau’ikan kuɗaɗen cryptocurrencies da aka amince da su a kan manhajar Bybit sun haɗa da na madaidaitan kamfanoni irin su Bitcoin (BTC), Ethereum (ETH), da Ripple (XRP). Baya ga samar da gurbin cinikayya, Bybit, tana ba da fifikon ilimi, tana samar da bayanai da darusa don taimaka wa masu amfani da manhajar su fahimci tsarin cinikayyar crypto. Bugu da ƙari, Bybit tana bambanta kanta ta hanyar sadaukar da kai ga tsaro da nuna kulawa ga abokan cinikayya, tana tabbatar da aminci da ƙwarewar kasuwanci ga masu amfani da ita.
Yadda manhajar Bybit take aiki
Bybit tana aiki makamancin ayyukan da sauran manhajojin musaya da cinikayyar hada-hadar cryptocurrency da yawa ke yi. Idan mutum yana da ilimin sarrafa irin waɗannan manhajoji, zai fahimci yadda Bybit ke aiki cikin sauƙi. Amma idan ya kasance mutum sabo ne a fagen amfani da ita, to ga wasu hanyoyi masu sauƙi da za su taimaka masa:
Yayin amfani da manhajar Bybit, ba kai tsaye ake cinikin cryptocurrencies a mafi yawan lokaci ba. A maimakon haka, ana saye da sayar da kadarorin da ke da alaƙa da waɗannan cryptocurrencies ne. Yayin da Bybit ke ba da izinin ciniki ta tsarin ‘spot trading’, babban abubuwan da ta fi mayar da hankali a kai koyaushe su ne ‘derivatives’ da ‘future trade’.
‘Derivatives’, samfuran kuɗaɗe ne waɗanda ƙimarsu ta samo asali daga kadara mai tushe, kamar Ethereum ko Bitcoin. ‘Future trade’ ya ƙunshi yin yarjejeniya don saye ko sayar da tabbatacciyar kadara a ƙayyadadden lokaci a nan gaba.
Bybit tana ba da damar cinikin lokaci na gaba ta dindindin, amma tana da ‘yar rikitarwa. Hada-hadar dindindin ta lokacin mai zuwa ba ta da ƙayyadadden kwanan watan yarjejeniya, ma’ana za a iya riƙe su har abada. Duk da haka, yana da mahimmanci a lura cewa hada-hada ta lokacin mai zuwa tana zuwa tare da wasu sharuɗɗa don tabbatar da cinikayyar. Bugu da ƙari, hada-hadar lokaci mai zuwa ta dindindin tana da ƙarin rikitarwa da haɗari. Bybit tana ba da damarmaki masu alfanubq bisa tsarin sau 100x, tana ba wa ‘yan kasuwa damar sarrafa matsayi fiye da ainihin matsayin asusunsu.
Shin Bybit tana da aminci?
Tsaro yana da mahimmanci yayin zaɓar manhajar musayar kuɗaɗen cryptocurrency. Bybit sananniya ce kuma shahararriya cikin manhajojin hada-hadar crypto mafi aminci da tsaro. Ga yadda Bybit ke tabbatar da amincin kuɗaɗen masu amfani da ita:
Cold storagesolution
Bybit tana ba da fifikon tsaro ta hanyar amfani da ingantacciyar ma’ajiyar ‘cold storage solution’. Yawancin kuɗaɗen lalitar kamfanin da dukkan kuɗaɗen abokan cinikayya ana adana su a cikin jakar wallet ɗin da ba ta haɗe da yanar gizo, wannan tsari yana rage barazanar da masu satar bayanai ta yanar gizo ke yi. Hakan kuma yana nufin cewa ko da a yayin harin kutsen yanar gizo, yawancin kadarorin masu amfani da manhajar suna kasancewa cikin tsaro, ba sa isa ga ɓangarorin da ba su da izini.
Multi-signature addresses
Domin ƙara ƙarfafa tsaro, Bybit na amfani da tsarin adireshin sa hannu mai yawa. Wannan yana nufin cewa ana buƙatar maɓallai da yawa kafin ba da izinin hada-hada, rage haɗarin da ke tattare da mutum ɗaya mai sarrafa dukkan kuɗaɗen asusu.
SSL Encryption
Shafin yanar gizon Bybit yana amfani da rufaffen tsarin sadarwa na fasahar SSL domin kariya daga hare-hare da kutsen yanar gizo. Wannan fasaha tana tabbatar da cewa duk bayanan da aka watsa tsakanin na’urorin masu amfani da tirken sabar Bybit suna kasancewa masu sirri da tsaro. Masu amfani da manhajar Bybit za su iya gano wannan amintaccen tsari cikin sauƙi a tambari ko alamar kwaɗo da aka bayyana a cikin adireshin burauza ɗinsu.
Ƙarin wasu matakan tsaro
Baya ga ingantattun hanyoyin ajiya da ka’idojin tsarewa, Bybit tana ba da ƙarin ɓangarorin tsaro don kiyaye asusun masu amfani da kuɗaɗe. Waɗannan ɓangarori sun haɗa da:
Two-Factor Authentication (2FA)
Wannan yana ƙara nau’in tabbaci na biyu baya ga kalmar sirrin mai amfani da manhajar wato (user password). 2FA yana ƙara tsaro ga asusun masu amfani da manhajar Bybit, yana mayar da asusu mai matuƙar wahalar sarrafawa ga mutane marasa izini.
Fund password
BYBIT tana ba wa masu amfani da ita damar saita keɓantacciyar kalmar sirri musamman ga ayyukan da ke da alaƙa da asusu, suna ƙara tabbatar da kadarorinsu daga cirewa ko turawa zuwa wani wajen ba tare da izini ba.
Anti-Phishing codes
Wannan hanya tana taimakawa wajen daƙile kai harin ta hanyar tabbatar da sahihancin sadarwa daga Bybit. Ta hanyar tabbatar da kasancewar wannan lambar, masu amfani da manhajar Bybit za su iya tabbatar da cewa imel ɗin da ke sada su da Bybit ya halatta.
New address withdrawal lock
BYBIT tana ba da tsarin kullewa wanda ke buƙatar masu amfani da ita su tabbatar da duk wani sabon adireshin cirewa kafin a iya tura musu kuɗi.
Bybit authenticity check
Manhajar tana ba masu amfani da kayan aiki damar tabbatar da sahihancin sadarwa da tashoshi na hukuma, tana taimaka wa masu amfani da ita su gano da kuma guje wa yuwuwar faɗawa cikin zamba.
Siffofi da ayyukan manhajar Bybit
BYBIT tana samar da ɗimbin fasaloli da ayyuka waɗanda aka keɓance su don biyan buƙatu iri-iri na masu hada-hadar cryptocurrency. Ga wasu daga cikin manyan abubuwan da Bybit ta ƙunsa:
Spot treading
Yayin da Bybit da farko ta samu nasara a matsayin manhajar musayar kadodrin da suke haɓaka, ta faɗaɗa ayyukanta don tsarin hada-hadar cinikayya a cikin shekarar 2021. Ta hanyar amfani da Bybit, za a iya sayan cryptocurrencies a tsarin ‘spot trading’ kuma a yi kasuwanci da su ba tare da matsala ba. A halin yanzu, Bybit tana ba da damar hada-hadar nau’ikan crypto sama da 300, da suka haɗa da: BTC/USDT, ETH/USDT, da ETH/BTC.
Leverage trading /margin trading
Bybit tana ba da damar cinikayyar cryptocurrency ta hanyar hada-hada mai ƙarfi da inganci. Wannan yana nufin ‘yan kasuwa na iya kafa matsayi tare da ɗan ƙaramin adadin jari ta hanyar farawa da ƙaramin ɓangare. Misali, idan ɗan kasuwa yana son sayan Bitcoin guda ɗaya mai ƙimar da ta kai dalar Amurka $60,000 ta amfani da tsarin 100x, zai buƙaci saka dala $600 ne kawai a matsayin kafin alƙalami.
Perpetual trading
Wannan nau’in cinikayya yana ba ‘yan kasuwa damar buɗe matsayinsu ba tare da musayar kadara ba nan take. Muddin tsarin ya kasance daidai, ana iya dawwama a kan matsayin da ake har abada. Alal misali, idan mai ciniki ya bunkasa na dogon lokaci a farashin Bitcoin, zai iya buɗe matsayi na dindindin kuma ya riƙe shi har sai an cimma burin samun riba.
Futures Trading
Hada-hadar lokaci mai zuwa ta ƙunshi yarjejeniyoyin saya ko sayar da ƙayyadaddun kadarorin a ƙayyadaddun farashi da lokaci a gaba. Ba kamar cinikayyar dindindin ba, kadarori na gaba suna saita lokutan sasantawa da kwanakin ƙarewa. ‘Yan kasuwa na iya zaɓar hada-hada ta lokacin mai zuwa domin tabbatar da dabarun da suka ƙayyade lokaci ko don saka shinge da hauhawar farashin kayayyaki.
Zaɓin damarmaki
‘Yan kasuwa za su iya amfani da tsarin samar da damarmaki don haɓaka matsayinsu a harkar cinikayya, mai yuwuwa a samu bunƙasar riba idan hasashen farashin ya yi daidai. Sai dai, yin wannan hasashe yana haifar asara idan farashin ya yi juyawa marar kyau. Misali, idan ɗan kasuwa ya yi hasashen ƙaruwar kashi 15% a farashin Bitcoin kuma ya yi amfani da tsarin 2x, ribarsa za ta ninka idan hasashensa ya yi daidai. Saɓanin haka, idan farashin ya ragu, asarar kuma za ta karu.
Copy trading
Kwanan nan Bybit ta kaddamar da tsarin cinikayyar copy trading, tana ba wa masu amfani da ita damar aiwatar da wannan nau’in hada-hada ga ‘yan kasuwa masu nasara a cikin manhajar. Wannan ɓangare yana ba da dama ga ‘yan kasuwa masu ƙarancin ƙwarewa su bi dabarun ƙwararrun ‘yan kasuwa, domin inganta damar samun nasara a kasuwannin cryptocurrencies. Masu amfani da Bybit za su iya yin bincike cikin ƙwararrun ‘yan kasuwa, su duba dabarunsu da ayyukansu, kuma su kwaikwayi tsarin kasuwancinsu. Wannan ɓangare har ila yau yana ba da damar ƙaddamar da cinikayya da kuma samar wa masu amfani da Bybit damar yin amfani da dabarun hada-hada mai riba ba tare da buƙatar ilimin kasuwanci ko ƙwarewa ba.
Dabarun sarrafa haɗura da ƙalubale
BYBIT tana samar da kayan aikin sarrafa haɗura daban-daban domin taimaka wa ‘yan kasuwa su kare jarinsu. Waɗannan sun haɗa da karɓar-riba, tsaida-asara, da zaɓukan shinge (musamman a hada-hadar USDT). Haka nan akwai wasu keɓantattun hanyoyin da ke ba da ƙarin damar sarrafa yanayin haɗari da asara, wanda kan ba wa ‘yan kasuwa damar rage fuskantar shiga cikin haɗari. Misali, ‘yan kasuwa na iya saita odar tsaida-asara domin sayar da kadarorinsu kai tsaye idan farashin ya kai wani zango mai kyau, wannan na iyakance yiwuwar fuskantar asara.
Shin Bybit na aiki da tantancewar KYC?
Tantancewar KYC (Know Your Customer), wato (Sanin Abokin Cinikayya), wani muhimmin abin la’akari ne ga kowace manhajar hada-hadar cryptocurrency, kuma Bybit ma tana da tsarinta na KYC. Ga abin da ya kamata a sani game da wannan manhaja:
Bybit tana buƙatar tantancewa ta ainihi don ɗaga likkafar asusu da ba da damar hada-hadar sama da BTC 2 a kowace rana. Duk da haka, masu amfani da Bybit waɗanda suka gaza kammala tantancewar KYC, suna da damar yin amfani da dukkan abubuwa da tsare-tsaren manhajar. KYC daidaitaccen tsarin masana’antu ne da ake amfani da shi don tabbatar da asalin abokan ciniki da tabbatar da biyan buƙatu cikin tsari da aminci.
A matsayin wani ɓangare na tsarin tantancewar KYC, ana buƙatar masu amfani da Bybit su gabatar da wata tabbatacciyar shaida daga hukumomi, kamar fasfo ko lasisin tuƙi. Za a iya samun ƙarin bayani kan mahimman abubuwan da da ake buƙata a matsayin shaida daga hukumomi, ta hanyar komawa zuwa sharuɗɗa da ƙa’idojin Bybit da ake samu a shafin yanar gizon hukumar gudanarwar kamfanin Bybit ɗin.
Kuɗaɗen cajin hada-hada a Bybit
Dangane da cajin shigar kuɗi da cirewa, Bybit tana kula da tsarin caji mai cike da amana. Manhajar ba ta cajin kuɗaɗe idan aka shigar da kuɗi ko kuma aka cire, kamar yadda yake a kundin dokoki da ka’idojin kamfanin. Duk da haka, masu amfani da manhajar za su iya fuskantar cajin kuɗin yin mining ko kuma cajin kuɗin kamfanin sadarwa a yayin cire kuɗi ko kuma aiwatar da mining.
Har ila yau Bybit tana ba da damar cirewa da saka kudaden ‘fiat’ kyauta ba tare da wani caji ba. Duk da cewa wannan ɓangare kyauta ne kuma yana da fa’ida, amma yana da mahimmanci a lura cewa ba sabon abu ba ne a cikin manhajar. Masu amfani da Bybit ya kamata su nemi duk wasu caje-caje da suka dace kuma su bincika ɓangaren da ke ƙunshe da bayanin “Zero Fees” yayin gudanar da hada-hada don tabbatar da bayyanan gaskiya.
Tsarin kulawa da abokan cinikayya
Bybit ta fahimci mahimmancin kulawa da abokan cinikayya, musamman a yayin gudanar da babbar hada-hada. Don biyan buƙatun manyan ’yan kasuwa, manhajar ta wuce manufar musaya, tana samar da hanyoyin sadarwar sirri tsakanin membobin da waɗannan ’yan kasuwa, da tabbatar da inganta kwarewarsu, da kuma magance matsalolinsu cikin gaggawa.
Ga masu amfani da ita na yau da kullun, Bybit tana ba da kulawa cikin sauƙi ga amintattun abokan cinikayya ta tashoshi daban-daban. Tsarin yin hira a cikin manhajar a bayyane yake don amsa wa masu amfani da ita korafe-korafensun cikin ƙanƙanen lokaci, yawanci yana ɗaukar mintuna kaɗan kawai. Wannan babban cigaba ne idan aka kwatanta da wasu manhajojin. Bugu da ƙari, Bybit tana da tabbataccen sashen taimako, tana ba masu amfani da ita damar samun amsoshi cikin sauri ga tambayoyin gama-gari na yau da kullum tare da ba su damar magance matsalolin da kansu da ƙara bunƙasa ƙwarewar abokan cinikayya gabaɗaya.
Sadaukarwar Bybit wajen ba da kulawa da sauraron koken abokan cinikayya ta musamman tana tabbatar da kyakkyawan tsarin da ta samu tun daga tushe. Yawancin abokan cinikayya suna yaba wa ƙoƙarin Bybit na samar da ingantaccen sabis da ayyuka, wannan na nuna nasarar Bybit wajen biyan bukatun masu amfani da manhajar da kuma bunkasa ingantaccen yanayin hada-hadar cryptocurrency.
Manazarta
Carter, S. (2025, February 21). Latest on the Bybit record breaking 1.4 billion dollar crypto hack. Forbes.
Bybit (n.d). Bybit’s commitment to user protection and compliance. Bybit.com
Crypto Kid Blog. (2024, May 8). BYBIT Review: BYBIT exchange features, services, trading fees. Cryptokid.com
Streamflow Finance. (n.d.) What is Bybit exchange? Stresmflow
*****
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.