Ido gaɓa ce mai matuƙar muhimmanci a jikin halittu, masu hikimar zance suna cewa, ‘rashin ido mutuwar tsaye ce.’ Babu shakka wannan batu haka yake. Kimiyyar likitanci ta bayyana ɗaruruwan cututtukan ido, wasu daga cikin waɗannan cututtukan yanayi ne na yau da kullun ke haifar da su. Ana iya magance da yawa daga waɗannan cutukan, musamman idan an kula su da wuri. Cututtukan ido na iya afkuwa saboda abubuwan da dama.

Mene ne ciwon ido?
Ciwon ido yanayi ne da ke shafar kowane sashe na idanu, wannan na iya haɗawa da yanayin sauran sassan da ke kusa da idanu. Waɗannan cutuka na iya zama masu tsanani na ɗan lokaci, wato sukan ta’azzara na ɗan lokaci sannan su tafi, akwai kuma waɗanda za su ci gaba da ƙaruwa sannu a hankali kuma suna daɗewa ba su tafi ba.
Ƙwayar ido ita ce inda yawancin cututtukan ido ke faruwa, amma ba ita kaɗai ba ce. Ciwon ido na iya haɗawa da yanayin da ke shafar tsokokin idanu, ƙwayar ido, fatar ido, ko fata da tsokoki a kusa da idanu.
Cututtukan ido sun zama ruwan dare gama duniya. Wadanda suka yi tsayin rayuwa za su fuskanci aƙalla ciwon ido sau ɗaya yayin rayuwarsu. A duk duniya, aƙalla mutane biliyan 1 suna da nakasar ido ta kusa ko ta nesa da aka magance ko kuma har yanzu ba a magance ba. Idan ba a san takamaiman lokaci da aka kamu ba, cutar na iya yin tasiri na dogon lokaci da kan shafi har tattalin arziki. Rashin gani ko ciwon ido yana shafar mutane masu shekaru daban-daban, yawancin waɗanda suka haura shekaru 50. Yara ƙanana na iya fuskantar matsalolin ciwon ido.
Yawaitar ciwon ido
Ciwon ido da sauran matsalolin gani suna da yawa. Hukumar Lafiya ta Duniya ta kiyasta cewa sama da mutane biliyan 2.2 na da nau’in ciwo ko nakasar gani ko makanta.
Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa ciwon ido ya zama ruwan dare shi ne idanun ba su kasance a ware daga jiki ba. Yawancin matsalolin da suka shafi idanu suna faruwa ne saboda yanayin da ke shafar wasu tsarukan jiki. Shi ya sa akwai ɗaruruwan yanayi daban-daban waɗanda za su iya shafar idanu har su haifar da cututtuka.
Mafi yawan cututtukan ido a duniya su ne: cataracts, wato matsaloli kamar
astigmatism, hyperopia, myopia da presbyopia da glaucoma da cutar sankarau mai nasaba da ciwon sikari. Raunin ido shi ne babban dalilin matsalar gani da makanta. Masana kiwon lafiya na ci gaba bincike kan waɗannan cututtuka don nemo ingantattun hanyoyin riga-kafi da magancesu.
Kansar ido da wasu cututtukan, ba kasafai ba amma galibi ana iya gano su ta hanyar gwajin ido na yau da kullun. Yawancin cututtukan ido ba su da mummunan tasiri (wato ba su cika zama ciwon daji ba). Waɗannan cutuka ko matsaloli da ba su da tsanani ko mummunan tasiri na iya buƙatar cirewa ko magancewa don hana su shafar ƙwayoyi da tantanin halitta.
Nau’ikan cututtukan ido
Akwai nau’ikan cututtukan ido da yawa, kuma ana gane su ne ta wasu hanyoyi da kuma yanayin cutar:
- Tsarin idanu: Akwai ciwon ido wanda ke faruwa dalilin tsari ko siffar idon. Wato ciwon yakan kama wani sashe ne na ido, ba gabaɗaya.
- Dalilin wata cutar: Akwai kuma ciwon ido da kan afku a dalilin wani abu ko wata cuta a jiki. Ciwon ido na asali yana farawa a cikin ido. Haka nan kuma wani ciwon idon yana faruwa ne saboda wani yanayi a wani wuri a jiki wanda daga baya yake shafar ido.
Tsawon lokacin da ciwon ido ke ɗauka
Cututtukan idanu, kamar ciwon ido na yau da kullum yana da ɗan gajeren lokaci. Amma yanayin ido mai tsanani wanda yake a matakin chronic na iya ɗaukar watanni, shekaru ko ma ya zama har ƙarshen rayuwa. Idan ana batu game da cututtukan ido, yana da mahimmanci a fahimci bambanci tsakanin gani da hangen nesa.
• Gani
Wannan yana farawa ne lokacin da haske ya shiga ta cikin wani sashe na ido mai suna cornea kuma yana ƙarewa lokacin da haske ya sauka a kan wani sashen daban wato retina.
• Hangen gani
Wannan ya ƙunshi kowane mataki wanda ke cikin ɓangaren gani da ke cikin ƙwaƙwalwa kuma ya haɗa da ganin kansa. Haka nan ya haɗa da yadda tsarin jijiyoyi ke sarrafa na’urar gani da juya su cikin abin da ake gani ɗin.
Yayin da mutane da yawa, har masana kan yi amfani da kalmar “hangen nesa” da “gani” akai-akai da nufin bayyana abu ɗaya, sai dai kuma a sani ba koyaushe suke zama abu ɗaya ba. Cututtukan da ke da alaƙa da gani sun keɓanta da idanu ne kawai, yayin da cututtukan da ke da alaƙa da hangen nesa na iya haɗawa da ƙwaƙwalwa da jijiyoyin gani. Abin da ya sa wasu cututtukan kan iya haifar da matsalolin hangen nesa koda kuwa idanu suna aiki daidai yadda ya kamata.
Alamomin ciwon ido
Akwai alamomin ciwon ido da yawa. Waɗannan alamomin yawanci suna faruwa ta wasu mahimman hanyoyi:
- Alamomin da za a iya ji. Misalai sun haɗa da ciwo, zafi ko gajiyawar ido ko damuwa.
- Canje-canje a ayyukan ido. Misalai sun haɗa da idanu masu ruwa (epiphora) da matsalar sarrafa yadda ake kifta idanu.
- Canje-canje a siffar idanu. Waɗannan canje-canjen sun haɗa da sauyawar farin ƙwayar ido zuwa launin rawaya (scleral icterus) ko jajayen idanu.
- Canje-canje a motsin ido ko daidaituwa. Misalai sun haɗa da exotropia ko esotropia.
- Canje-canje a yadda ake gani. Wasu misalan gama gari su ne hangen nesa nau’in (diplopia).
Abin da ke janyo ciwon ido
Cututtukan ido na iya faruwa saboda dalilai da yawa. Wasu dalilan na kai tsaye ne yayin da wasu ke ba da gudummawa wajen wanzuwar ciwon. Daga cikin dalilan akwai:
Genetics (gado)
Ƙwayoyin halittar DNA muhimmin ɓangare ne na yadda idanu suke girma da aiwatar da aiki, canjin DNA na iya haifar da matsalolin ido da yawa. Siffar ƙwayar halitta ta makanta misali ne na dalilan ciwon ido na gado.
Bambancin siffar ido
Akwai bambance-bambancen yadda siffofin ido suke da kuma yadda suke girma. Waɗannan bambance-bambancen za su iya farawa yayin da mutum yake girma a ciki, a matsayin ɗan tayi, ko kuma a wani zangon girma na ƙuruciya.
Abubuwan da ke muhalli
Wasu cutukan ido suna tasowa saboda abubuwan da ke faruwa ko a kusa da mutane. Fuskantar hasken ultraviolet (UV), yawaitar danshi a cikin iska da yayin zafin gari da ƙura ko ɓurɓushi abubuwa a cikin iska, da sauran abubuwa da yawa na iya zama wani ɓangare na wannan.
Cututtuka masu yaɗuwa
Yawancin nau’o’in ƙwayoyin cuta da ƙananan ƙwayoyin germs (pathogens) na iya haifar da ciwon ido. Wannan sun haɗa da ƙwayoyin cuta, kwayoyin bakteriya, fungi da farasayit (parasites). Waɗannan suna iya cutar da idanu kai tsaye ko kuma su yaɗu daga wani wuri a cikin jiki zuwa idanu.
Sauran matsaloli
Idanu suna da rauni ga yanayi da yawa waɗanda suka shafi dukkan jiki. Misalai sun haɗa da hawan jini, nau’in ciwon sukari na 2 da nau’ikan cututtukan thyroid.
Idiopathic
Idiopathic na nufin ciwon idon da ba a san takamaiman dalilin da ya haifar da shi ba. Wato wannan na nufin babu wani dalili ko hujja da masana za su iya ganewa. Sai dai kuma hakan na iya sauyawa bayan tsawon lokaci.
Gwaje-gwajen ciwon ido
Kwararrun masu kula da ido ko wasu ma’aikatan kiwon lafiya na iya gano cututtukan ido ta amfani da hanyoyin haɗaka da yawa. Abu na farko kuma mafi muhimmanci don gano waɗannan cututtuka shi ne gwajin ido. Duk da cewa yawancin mutane suna kallon yin gwajin ido a matsayin hanyar duba yadda ake gani kawai (wato hanyoyin gani), sai dai kuma ba koyaushe gwajin idon ke nufin haka ba.

Gwajin ido na iya zama na yau da kullu, kuma zai iya kasancewa a duk bayan shekara ɗaya zuwa biyu kamar yadda ake duba lafiyar jiki gabaɗaya. Likitoci na iya yin gwaje-gwaje ta hanya ta musamman a yayin da ake duba alamomin ciwon ido. Ƙwararrun likitocin ido na iya ba da shawarar ƙarin tabbatattun gwaje-gwajen ido, waɗanda suka haɗa da:
- Fluorescein angiography
- Tonometry
- Retinal imaging
- Corneal topography
- Optical coherence tomography
Yawanci kuma akwai wasu gwaje-gwajen da ba na ido ba kai tsaye, amma suna iya taimakawa, su ma, sun hada da:
- Gwajin jini don tabbatar da alamomin sinadarai masu alaƙa da yanayin garkuwar jiki, cututtuka ko don gudanar da DNA da gwaje-gwajen kwayoyin halitta.
- Gwaje-gwajen daukar hoto kamar ultrasound da compute tomography (CT) da daukar hoton magnetic resonance imaging (MRI).
- Gwajin jijiya kamar, electroencephalogram (EEG), wanda ke bincika ayyukan ƙwaƙwalwa.
Kwararrun likitocin ido ko wasu masu kula da lafiya na iya yin ƙarin bayani game da duk wasu gwaje-gwajen da suke da muhimmanci don gano nau’in ciwon ido, tare da bayanin yadda waɗannan gwaje-gwajen ke aiki da kuma yadda za su iya taimakawa.
Yadda ake maganin ciwon ido
Magungunan cututtukan ido na iya bambanta ta fuskoki da dama dangane da nau’in ciwon da ake fama da shi. Wasu magungunan na iya taimakawa wajen magance cutuka da yawa. Wasu kuma suna aiki a kan takamaiman ciwo ne, ma’ana ba za su taimaka wajen magance wani nau’in ciwon idon ba sai dai wanda aka tsara su a kai.
Riga-kafin cututtukan ido
Wasu cututtukan ido ana iya daƙile su gabaɗaya, sannan kuma aƙalla za a iya rage haɗarin yawaitar wasu. Amma yawancin cututtukan ido suna faruwa ba tare da tsammani ba, wannan yana sawa ba zai yiwu a daƙile kamuwa da su ba ɗari bisa ɗari. Wasu manyan matakan da za a iya ɗauka don taimakawa kula da lafiyar ido sun haɗa da:
A riƙa gwajin ido akai-akai
Kowane mutum, har ma da mutanen da ba su sa ruwan tabarau masu gyara ba, ya kamata su yi gwajin ido aƙalla duk bayan shekara ɗaya zuwa biyu (ko fiye da haka idan ana da yanayin da ke ƙara haɗarin matsalolin ido).
A riƙa amfani da kariyar ido
Raunin idanu, fuska ko kai na iya haifar da matsalolin ido na dogon lokaci da lalacewa. Sanya kariyar ido musamman don wannan dalili na iya hana raunin ido ko rage matsaloli.
A guji amfani da nicotine
Shan taba, vaping da shan taba mara hayaki duk suna iya shafar tsarin jini. Wannan hakika yana da illa ga jijiyoyin jinin da ke ba wa idanu.
A kula da cututtuka
Idan mutum yana jin abu kamar ciwon ido har fiye da ‘yan kwanaki, to ya ziyarci ma’aikacin lafiya. Ciwon ido wanda ba a kula da shi na dogon lokaci zai iya zama babbar matsala kuma ya haifar da lalacewar ido ta dindindin ko kuma wasu matsaloli.
A guji watsi da alamomin ciwon ido
Canji a yanayin hangen nesa a hankali alama ce da ke nuna cewa ana buƙatar ganin likitan ido don yin gwaji. Haka nan canje-canjen hangen nesa da kan faru ba zato ba tsammani, musamman rashin hangen abu a nesa, su ne matsalolin ganin likita cikin gaggawa domin suna buƙatar kulawa ta gaggawa.
A ba abinci mai gina jiki fifiko
Idanu suna buƙatar tabbataccen sinadarin bitamin da minerals don yin ayyukansu yadda ya kamata da kuma kasancewa cikin kyakkyawan yanayi ingantuwar lafiyarsu.
Manazarta
Tasmanian Department of Health. (2021, November 28) Common eye disorders. Tasmanian Department of Health.
Vision and Eye Health. (2024, May 15). About common eye disorders and diseases. Vision and Eye Health.
WebMD. (2022, September 16). Top causes of eye problems. WebMD.