Skip to content

Ciwon kai

Ciwon kai wani ciwo ne da mutane da yawa suke yawaita fama da shi, shi wannan ciwo bai taƙaita ga jinsi ko matsayin shekaru ba, ya haɗa kowa da kowa. Dalilai da dama kan iya kawo shi. Wato shi ciwon kai alama ce na rashin wani abu a jikin ɗan’adam, kuma kowa da irin yanayin nasa ciwon kan.

Wani binciken masana ya tabbatar da cewa; ciwon kai yana faruwa ta dalilin rashin isasshen ruwan jiki, yawan gajiya, rashin samun barci sosai, dumuwa, dalilin warkar da wani ciwon, matsalolin wasu ƙwayoyi maganin, ƙara ko hayaniya, mura, raunin kai, ciwon haƙori, matsalar da ta shafi hanci, ci ko shan abubuwa masu sanyi, da dai sauransu.

Ciwon kai na goshi yana faruwa ne sakamakon a jiye damuwa a cikin rai, kuma maganinsa shi ne mutum ya yi ƙoƙarin kauda damuwar.

Wani lokacin kuma ciwon kai na faruwa ne saboda gogayya ko cudanya tsakanin meningitis da jijiyoyin jini a cikin ƙwaƙwalwa, wani lokacin kuma tsokoki da ba su da signal wanda ƙwaƙwalwa ta rasa su ne suke jin rauni ko ciwo sai su haifar da ciwon kai, wani lokacin kuma cuɗanya ko in ce cakuɗar jijiyoyin jinin cikin kai, ko kuma kumburin tsokar da ke ba da signal ko infection ya same ta sai ciwon kai, sai kuma tsokar da ke aika signal zuwa ƙwaƙwalwa ta tura wa
ƙwaƙwalwa cewa wani wuri na ciwo.

Alamomin ciwon kai

Alamomin ciwon kai suna da yawa ga wasu kaɗan daga cikinsu:

  • Idanu sukan yi ja kamar an zuba musu wuta.
  • Jiri ko kuma jin ɗaurewar goshi ko kuma ƙeya.
  • Rashin son ganin hasken rana.
  • Ganin hazo-hazo cikin Idanu.

Abubuwan da suke kawo ciwon kai

Abubuwa da dama suna kawo ciwon kai kamar su,

  • Hawan jini
  • Tunani mai yawa
  • Rashin bacci
  • Rashin hutu

Rabe-raben ciwon kai

Binciken masana ya tabbatar da samuwar ciwon kai sama da guda 200 iri-iri wanda mutane ke fama da su, amma kuma binciken ya tabbatar da an fi fama da ciwon kai dalilin damuwa ko kuma wahala, wasu masu sauƙi, wasu masu tsanani, wasu kuma waɗanda za su iya kaiwa ga rasa rai, wasu ma sai an yi gwajin neurological kafin a gano su a wasu lokuta har da sauran gwaje-gwaje mabambanta.

A dunƙule ciwon kai ya kasu kaso biyu, primary da kuma secondary. Sai dai kuma a kasan su su ma akwai ire-iren ciwon kai da dama wanda suke ƙunshe da bayanai dalla-dalla game da musabbabansu da kuma abin da suka ƙunsa baki ɗaya.

Primary headeache

Wannan nau’in ciwon kai ne wanda yake samuwa a hankali, a wasu lokutan yakan yawaita zuwa kuma ya tafi. Yawanci ba wani ciwo ba ne babba yake kawo shi ba. Wani bincike ya tabbatar da kusan kashi 90% na ciwon kai primary headeache ne, kuma sun fi damun matasa ne daga shekaru 20-40 na rayuwarsu. Cikin waɗanda suka fi kama matasan ko waɗannan rukunan mutanen su ne damuwa ko wahala da kuma migraine watau na gefe wanda alamominsu na zuwa da tashin zuciya, ciwon kai, gani dishi-dishi, jiri, da kuma rashin son ƙara ko hayaniya.

Secondary headeache

Shi kuma nau’in ciwon kai ne da akasari yana faruwa ne dalili wani abu daya faru a cikin kai ko a cikin wuya yawancinsu ba masu cutarwa ba ne sosai misali kamar ciwon kai da zai fara daga jijiyar wuya zuwa kai, wani kuma yana faruwa ne saboda yawan amfani da magungungunnan rage raɗaɗin ciwo. A wani binciken kuma secondary headeach yana zuwa ne ta dalili wasu cututtuka kamar raunin kai, matsalar jijiyoyin kai, infection, bleeding ƙwalwa, kuma suna da haɗari sosai.

Akwai ciwon kai kala-kala masu zafi da kuma sauƙaƙa. Wasu daga gundarin kai ko ƙwaƙwalwa suke faruwa wasu kuma ciwon wasu sassan jiki ke kawo su kamar zazzaɓi, wasu gadonsu ake yi, wasu kuma ciye-ciye da shaye-shaye da yawan aiki da gajiyar yau da kullum ce ke kawo su. Wasu suna da haɗari wasu kuma ba su da shi. Ciwon kai ya kasu kaso da dama ta fuskar rukunin mutanen da ke fama da shi, wanda suka haɗa da,

Ciwon kai na jarirai

Wani nau’in ciwon kai ne da ake haifar jarirai da shi, yana matuƙar wahalar da su, yaran sukan fita hayyacinsu ta yadda za su dinga addabar iyayensu da kuka. Akwai yawaitar kashi tare da yaran sai kuma amai. Yana saka yaro ya rame, yayin da idanunsa sukan fito su yi ƙwala-ƙwala.

Alamomin ciwon kan jarirai

  • Yawan kuka
  • Yawan kashi
  • Rama mai tsanani
  • Fitowar Idanu su yi manya
  • Yawan shan nono ba tare da nuna ƙoshi ba
  • Burmawar maɗigar kai

Ciwon kai na goshi

Ciwon kai na goshi nau’in ciwon kai ne da wasu masana suka yi hasashen damuwa ko gajiya na iya kawo shi. Shi ne ciwon kan da ya fi kowane ciwon kai addabar al’umma. Wato mutane da dama suna samun shi fiye da kowane irin ciwon kai. A wasu lokuta ba goshi kaɗai yake riƙewa ba, duk kan akan ji ya riƙe ya ɗaure kamar rawani. Sai dai shi magunguna irin su Panadol suna iya sa mutum ya ji dan sauƙi. Yana daga cikin ciwon kai wanda ba ya barin mutum har sai mutum ya canja yanayin abin da ke kawo masa damuwar.

Ciwon kai ɓari ɗaya

Nau’in ciwon kai ne da akasari ya fi kama mata musamman masu matsakaitan shekaru, su ba su yi shekaru da yawa ba kuma ba su yi ƙasa da samartaka ba. Masana da dama na ganin kamar ciwon ya fi shafar abin da ya danganci gado ne, wato dai kamar yadda ake gadon ciwon suga da sauran su. Masu irin wannan ciwon na shan matuƙar wahala. A lokuta mabanbanta ba sa son yawan haske ko hayaniya mai ƙarfi. Bisa shawarar likitoci yana da kyau mai ɗauke da irin wannan ciwo ya kasance cikin ziyartar likita da kuma asibiti akai-akai domin duba lafiyarsa. Akwai tabbacin na cewa idan ciwon ya yi ƙamari zai iya shafar ƙwaƙwalwa domin abu ne da ya shafi kai wanda a bayyane yake da kusanci da ita.

Bincike ya tabbatar gado shi ne babbar hanyar da ake iya kamuwa da ciwon sai kuma wasu hanyoyi kamar, shan magungunan hana ɗaukar ciki da cin wasu nau’ikan kayan abincin da jiki bai gamsu da su ba.

Ciwon kai na saman hanci

Shi ne wanda ake kira da sinus headache wanda ke kama masu murar sinusitis.

Ciwon kai na ƙeya

Nau’in ciwon kai ne da yake matuƙar wahalarwa. Yakan ɗaure ƙeya zuwa abin da ya shafi cikin idanu. A lokuta mabanbanta mutum kan ji ya kasa sarrafa dokin wuyansa ya juya zuwa wani sashe da yake so.

Ciwon kai dalilin sanyi

Ciwon kai ta dalilin sanyi, wanda aka fi sani da ciwon ƙanƙara ko daskarewar ƙwaƙwalwa, wani nau’i ne na matsakaicin ciwon kai wanda yake faruwa ta sanadin shan abin sha mai sanyi ko abinci, kamar ice cream, popsicles, da kuma dusar ƙanƙara. Yana faruwa ne ta hanyar wani abu mai sanyi da ke taɓa rufin baki, kuma an yi imanin cewa yana haifar da amsawar jijiyoyin kai wanda ke haifar da matsewa cikin sauri da kumburin jijiyoyin dasashi na jini.

Riga-kafin  ciwon kai

  • A daina tunani mai zurfi
  • A daina shan abu mai sanyi
  • A ƙaurace wa ƙin yin bacci wadatace wanda zai ba wa ƙwaƙwalwa damar samun hutu gamsasshe
  • A Guje wa yin aiki akai-akai da matsawa ƙwaƙwalwa wurin yin aikin da ya fi ƙarfinta.

Manazarta

Contributors to Wikimedia projects. (2023, July 18). Ciwon kai ta dalilin sanyi. Wikipedia.

Halifasabodantata, V. a. P. B. (2019, January 1). CIWON KAI NA BARI DAYA HSDantata Blog.

Hospitals, M. (n.d.-b). Ciwon kai ko Ciwon kai: Nau’o’i, Jiyya da shawarwarin Taimako. Best Hospitals in India | Medicover Hospitals.

Mustapha, O. (2018, May 26). Amsoshin tambayoyi da suka shafi ciwon kai.. Aminiya.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×