Ciwon sanyi (Infection)
Ciwon sanyi ko toilet infection ko vaginal infection duka suna nuni da abu ɗaya. Ciwon sanyi wasu ƙwayoyin cuta ne da ke addabar al’aurar mace har ma da maza .Wannan ƙwayoyin cutar suna hana sukuni ta hanyar janyo ƙaiƙayin gaba, warin gaba, fesowar kuraje, fitowar ruwa fari, ko ɗorawa ko kore, ko jin zafi yayin jima’i, jin zafi yayin fitsari da sauransu. Wannan fitar ruwan yana iya kasancewa na cuta a wasu lokuta.
Mata da yawa suna yawan samun kansu a wannan yanayi na fitar ruwa daga mafitsararsu fiye da maza. Domin yanayin yadda Allah (SWT) ya yi cikin al’aurar mace a jiƙe (mai danshi-danshi) a kowane lokaci. Ruwan da ke jiƙa gaban mace yana fitawo daga wasu ɓangarori daban-daban da suke cikin gabanta. Yawan ruwa yana iya ƙaruwa, ko raguwa ko kuma ya ɗauke gabaɗaya. Wannan zubar ruwa ana kiran shi “Vaginal Discharge” a likitance. Hausawa suna kiran shi da “Ciwon Sanyi”, wasu kuma su kiran shi da “toilet infection (ma’ana, cutar da ake ɗauka a banɗaki marar tsafta)”. Amma har yanzu, a likitance, ba a tabbatar da yin amfani da banɗaki marar tsafta yana ɗaya daga cikin hanyar da ake kamuwa da wannan cutar zubar da ruwan ba, amma dai ana zargin hakan, kuma ya kamata a yawaita tsaftace banɗaki.”
Zubar ruwa
Abubuwan da suke janyo zubar ruwa na cuta; shan magunguna barkatai, musamman waɗanda ake kira da antibiotics ko steroid da da ire-iren magunguna da ‘yan talla ke sayarwa don ƙarin ni’ima. Saboda suna haifar da cututtuka a jikin mutum kamar Diabetes (ciwon suga), HIV, Cancer da sauransu. Saduwa da wanda ke ɗauke da cutar; namiji zai iya ɗauka wurin mace, mace ma za ta iya ɗauka wurin namiji. Saboda gaban mace ba ya buƙatar kowane irin sabulun da za a wanke shi. Domin yadda Allah ya halicci wurin ya yi masa tsari mai kyau, ta yadda da kansa yake wanke kansa, ba ya buƙatar wani sabon sinadari. (vaginal douching). Masan tangaran (toilet seats) Musamman idan wacce take ɗauke da cutar ta yi amfani da shi kuma ba ta wanke masan ba. Idan mace tana da, ko kuma, tana aikata ɗaya daga cikin waɗanda ke aikata abin da aka ambata; za ta iya kamuwa da wannan cuta ta zubar da ruwa.
Rabe-raben infection.
• Akwai infection na reproductive organs: Shi wannan infection mai kama sassan da suke da alhakin haihuwa kamar vigenal infection overian yana rufe ko garƙame fallopian tubes.
• Akwai urinary tract infection (U.T.I): Shi kuma wannan yana kama hanyar mafitsara kai-tsaye. Shi kuma infection na reproductive organs ana daukar shi ne a toilet wanda babu tsafta, shi ya sa mafi yawanci wasu ke cewa toilet infection, wanda idan ma ba toilet ba to in dai za a tsuguna makewayi na kowa da kowa, to tabbas za a iya kamuwa da ire-iren infection. Sannan shi wannan infection wani zai iya ɗauka a jikin wani kamar yadda aka faɗa tun a farko, ta hanyar saduwa (jima’i).
Mata masu amfani da magungunan barkatai ko abubuwan da ake shafawa a gaba (matanci) su ma suna kamuwa da infection. Saboda mata da yawa masu amfani da magunguna barkatai ko abubuwan da ake shafawa a private sun sha kamuwa da infection.
Sai an je wurin likita sannan an yi gwaje-gwajen jini da fitsari, domin ta haka ne kaɗai za a iya tabbatar da cewa mutum yana da infection. Kuma wanne iri ne yake ɗauke da shi a jikinsa, saboda akwai bacterial infection da kuma parasitic infection da fungal infection sai kuma viral infection. Saboda kowannensu da akwai alamunsa, hakan ya sa wasu sukan yi kamanceceniya ta yadda za a yi wahalar bambance su ɗaya bayan ɗaya, don haka dole ne sai an yi gwaji tukunna ake gano wane iri ne kuma wane kalar magani za a yi amfani da shi.
Alamomin infection
Wasu daga cikin alamomin infection sun haɗa da;
- Fitar ruwa (discharge) indai ya canza kala tare da wari ko ƙarni
- Jin zafi lokacin jima’i
- Jin zafi bayan jima’i
- Jin zafi lokacin fitsari
- Jin zafi bayan gama fitsari
- Ɗaukewar ni’ima (vigenal dry)
- Ɗaukewar sha’awa
- Ciwon mara lokacin al’ada.
- Rikicewar al’ada.
Alamomin infection wanda fungal yake kawowa sun haɗa da;
- Ƙaiƙayin ciwon gaba
- Ƙaiƙayin ko bushewar vulva
- Fitar ruwa mai kauri tare da wari
- Farji kan sauya kala zuwa launin ja
- Farji kan kumbura
- Tsagewar farji
- Jin zafi lokacin fitsari.
Sai kuma alamomin infection wanda ƙwayar halittatar parasite yake kawowa.
- Fitar ruwa mai kala marar kauri, ko mai kumfa, ko kuma mai wari.
- Jin ƙaiƙayin gaba
- Ganin ƙuraje a gaba
- Rashin jin daɗi lokacin jima’i.
- Jin zafi lokacin fitsari.
Alamomin infection wanda ƙwayar cutar virus take kawowa kuma ita ce;
- Jin motsi a cikin gaba
- Bushewar gaba
- Jin zafi mai tsanani yayin fitsari
Hanyoyin kariya daga cutar infection
- Daina amfani da bayin kowa da kowa
- Daina amfani da banɗaki marar tsafta
- Daina cuɗanya da towel guda ɗaya
- Daina amfani da ra
- Daina jima’i babu kariya
- Daina cusa magunguna a matucci.
- Daina wanke matanci da sinadarin da ba a tabbatar da nagartarsa ba a likitance.
Hanyoyin magance infection.
Da farko dai idan mutum yana da ɗaya daga cikin alamomin infection ya je ya ga likita a kan lokaci. Domin gano a wani tsari likitan zai ɗora shi. Kuma likitan zai buƙaci gwajin jini, fitsari ko vaginal swab, domin ya tabbatar da wane kalar infection ne kuma wane magani za a ɗora mutum kansa.
Bacterial infection za a yi magani dangin antibiotics drugs.
- Fungal infection ne za a yi magani dangin antifungal drugs.
- Viral infection za a yi magani dangin antiviral drug.
- Parasitic infection to za a yi bincike da magani dangin antiparasitic drugs.