Skip to content

Computer Vision

Computer Vision wani fanni ne na fasaha da nazari da ke mayar da hankali kan baiwa kwamfutoci damar fassarawa da fahimtar bayanai. Ya ƙunshi haɓaka fasaha da ƙirkira waɗanda za su iya sarrafawa da nazarin bayananai na gani da ido, kamar hotuna da bidiyo, domin samar da cikakken bayan mai amfani da aiwatar da ayyuka na musamman kamar:

Computer Vision na taimakawa wajen gano abu da rarraba shi da bin diddiginsa, da rarraba hotun da sabunta su da gane fuska haɗe da yin bincike da fahimtar yanayi har ma da gane ayyuka da tsinkaye a cikinsu.

Fasahar computer vision.

Computer Vision na aikace-aikace masu yawa a fannoni kamar:

– Motoci masu tuka kansu suna gane masu tafiya a ƙasa da kuma matsalolin hanya.

– Facebook yana ba da shawara ga abokanka a cikin hotunan da kuke wallafawa.

– Alexa na Amazon yana gane abubuwa da yin ayyuka daban-daban.

– Manhajar Likita na gano ciwake-ciwaken daji a cikin X-ray

Aikace-aikacen Computer Vision

Computer Vision ya ƙunshi dabaru da aikace-aikace iri-iri, gami da:

1.Gano Hoto: Gano abubuwa ko fannin da hotuna suke.

2. Gane Abu: Gano takamaiman abubuwa a cikin hotuna ko bidiyoyi.

3. Rarraba Hoto: Rarraba hotuna zuwa yankuna ko abubuwa.

4. Gane Fuska: Gano daidaikun mutane bisa yanayin fuska.

5. Gane Haruffa gani na (OCR): Ciro rubutu daga hotuna ko takardu.

6. Mayar da Hoto: Haɓakawa ko gyara hotunan da suka lalace.

7. Kimanta Zurfi: Ƙididdiga zurfi tsayin abu mai fuska uku 3D na al’amuran daga hotuna masu fuskoki biyu 2D.

8. Bibiya: Bin abubuwa ko ɗai-ɗaikun mutane a cikin a cikin bidiyo.

9. Gano Motsi: Gano motsi a cikin hotuna ko bidiyo.

10. Binciken Hoto na Likita: Yin nazarin hotunan likita don gano asalin bincike.

11. Sa ido: Kulawa da nazarin bidiyo don dalilai na tsaro.

12. Motoci masu sarrafa kansu: Ba da damar ababen hawa don kewayawa ta amfani da bayanan gani.

Muhimmancin computer vision

Computer Vision tana da mahimmanci mai yawa da aikace-aikace a fannoni daban-daban, ciki har da:

1. Kiwon Lafiya: Binciken hoto na likita, gano cututtuka, da gano magunguna.

2. Tsaro: Sa ido, gane fuska, da gano abu don samar tsaro.

3. Sufuri: Motoci masu cin gashin kansu, marasa direbobi a ciki na lura da zirga-zirga, da kewayawa.

4. Cinikayya: Ƙimanta samfurin kaya, sarrafa kayan, da ƙididdigar bayanan abokin ciniki.

5. Noma: Kula da amfanin gona, hasashen amfanin gona, da gano cututtukan da kan kama shuka ko lahanta amfanin gona.

6. Ilimi: ilmantarwa, sanin karimci, da kayan aikin koyo da koyarwa.

7. Nishaɗi: Gyaran hoto da bidiyo kan kawo nishaɗi, hakan kuma na da tasiri na musamman.

8. Kimiyya: Binciken hoto, duban bayanai, da binciken kimiyya.

Matsalolin computer vision

1. Matsayin Hoto: Rashin haske mara kyau, ko amo na iya rinjayar tasirin bincike.

2. Bambancin Abu: Abubuwa na iya bambanta a siffa, launi, da rubutu.

3. Rufewa: Abubuwan na iya zama ɓoyayyu ko toshe su.

4. Kamanceceniya tsakanin rukunai: Abubuwa daga rukunai daban-daban na iya bayyana kama.

5. Rashin Bayanan Horarwa: Ƙayyadaddun bayanai don wasu abubuwa ko yanayi.

6. Bias Data: Bayanan horo na son rai na iya haifar da sakamako mara kyau.

7. Bayyanawa: Wahalar fahimtar hanyoyin yanke shawara na AI.

8. Hare-hare: Ƙoƙarin ganganci da mutane kan don yaudarar fasahar AI.

9. Real-Time Processing: Gudanar da hotuna a cikin ainihin lokaci don aikace-aikace kamar motoci masu zaman kansu.

Magance waɗannan ƙalubalen yana da mahimmanci don bunƙasar fasahar computer vision da kuma tabbatar da amincin aikace-aikacenta a fagage daban-daban.

Don magance ƙalubalen computer vision , masu bincike da masu haɓakawa suna iya yin amfani da dabaru daban-daban, gami da:

1. Ƙara bayanai: Samar da ƙarin bayanan horo ta hanyar sauye-sauye.

2. Canja wurin koyo: Yin amfani da fasahar da aka riga aka horar da kuma daidaitawa don takamaiman ayyuka.

3. Haɗa fasahohi: Haɗa nau’ikan samfura da yawa don ingantaccen sakamako.

4. Koyon ayyuka da yawa: Samfuran horarwa don ayyuka da yawa a lokaci guda.

5. Hanyoyi masu nagarta: Mai da hankali kan yankuna ko fasali masu dacewa.

6. Dabarun daidaitawa: Rage wuce gona da iri da inganta fasaha.

7. Manyan ma’auni: Ƙirƙirar da kuma amfani da manyan bayanai.

8. Haɗin gwiwa tsakanin mutum da AI: Tsarin haɗin gwiwar haɗakar da ba damar yin aiki tsakanin mutum da kuma fasahar AI.

15. Ci gaba da ilmantarwa: Sabunta samfura tare da sabbin bayanai da daidaitawa ga yanayin canjin yanayi.

Ta hanyar bincike da haɗa waɗannan dabaru, za iya shawo kan ƙalubalen computer vision, kuma a samu cigaba.

Manazarta

Dobes, M. (2022, September 26). Computer Vision: learn about its applications and importance for digital transformation. CERTI Insights.

Microsoft Azure. (n.d.). What is Computer Vision?. Microsoft

Seo, H. (2023a, November 7).  Computer Vision: definition, importance, how it works, applications and example tasks Holistic SEO. Holistic SEO.

Was this article helpful?
YesNo

You cannot copy content of this page

×