Skip to content

Dakin karatu

    Aika

    Ɗakin karatu wata matattara ce ta kayayyakin ilimi da bayanai musamman littattafai da aka tsara kuma aka sanya domin amfani ga jama’a ko wasu taƙamaiman rukunin al’umma. Waɗannan kayayyakin ilimi na iya kasancewa littattafai, mujallu, jaridu, rubuce-rubucen hannu, taswirori, abubuwan kallo da ji kamar faifan bidiyo da sauti, e-littattafai, bayanai na intanet (databases), da sauransu. Manufar ɗakin karatu ita ce samar wa mutane dama su samu ilimi, bayani, da kayan karatu; sawa’un ta tsarin rubutu ko kuma dijital, ba tare da la’akari da matsayi, ko sana’a ba.

    SCHOOL LIBRARY scaled 1
    Ɗakin karatu na ba da muhimmiyar gudummawa ga ci gaban ilimi.

    Littattafai da sauran kayayyaki ana shirya su ne ta hanyar masu ilimi da ƙwarewa, masu aikin ɗakin karatu, wato ‘librarians’ waɗanda ke da aikin hidima kamar tsara littattafai, daftarin ajiyar bayanai, kula da tsari, da taimaka wa masu amfani yadda za su samo abin da suke nema. A yau, ɗakunan karatu ba kawai wajen tara kayayyaki ba ne; sun zama cibiyoyin ilmantarwa masu matuƙar tasiri. Suna da muhimmanci wajen ƙarfafa ilimi, karatu mai zurfi, da ƙarfafa ɗabi’ar karance-karance a tsakanin al’umma. Walau a cikin manyan birane ne ko ƙauyuka, ɗakin karatu yana taka muhimmiyar rawa wajen bai wa kowa damar samun ilimi.

    Nau’ikan ɗakin karatu

    Akwai nau’o’i daban-daban na ɗakunan karatu waɗanda aka tsara su domin biyan buƙatu na wasu rukuni na mutane. Waɗannan sun haɗa da: ɗakunan karatu na jami’a (academic library) da na jama’a (public library) da na makaranta (school library).da na musamman (special library) da na ƙasa (national library), da kuma dijital ko virtual library.

    1. Ɗakunan karatu na jami’a

    Kamar ɗakunan karatun da ke jami’o’i, kwalejoji, da cibiyoyin bincike, suna taimakawa dalibai, malaman makaranta, da masu bincike wajen samun kayan karatun da suke taimaka musu. Misali, ɗakin karatun Jami’ar Bayero ta Kano, ya tattara littattafai da mujallu masu alfanu ga ɗalibai da masu bincike.

    2. Ɗakunan karatu na jama’a

    Waɗannan ɗakunan karatu suna buɗe ga kowa, kuma yawanci gwamnati ko ƙungiyoyi ke bunƙasa su. Waɗannan ɗakunan suna ba da dama ga karatun nishaɗi, cigaban ilimi ga kowa da kowa. A Najeriya, Hukumar ɗakunan karatu ta Jihar Legas (Lagos State Library Board) tana samar da littattafai, kwamfutoci, da shirye‑shirye na ilimi ga jama’a.

    3. Ɗakunan karatu na makaranta

    Waɗannan ɗakunan karatu suna cikin makarantu, na firamare da sakandare, suna tallafa wa manhajar karatun makaranta ta hanyar samar da littattafai, labarai, da wasannin ilimi waɗanda ke ƙarfafa ɗabi’ar karatu ga yara tun ƙuruciya.

    4. Ɗakunan karatu na musamman

    Waɗannan sun fi mayar da hankali ga biyan buƙatu na wasu fannonin masana’antu ko ayyuka na musamman misali na asibitoci, manyan lauyoyi, gidajen talabijin, da ma’aikatu. Misali, ɗakin karatu na Nigerian Institute of Medical Research (Cibiyar Bincike ta Kiwon Lafiya ta Najeriya) yana bayar da kayan karatu da bincike na likitanci da ƙirƙirar manufofi.

    5. Ɗakin karatu na ƙasa

    Cibiyar ajiyar ƙasa ce, wadda ke tattara adabin da ake bugawa a ƙasar da na ƙasashen waje game da ƙasar. A Najeriya, National Library of Nigeria, yana da alhakin tattarawa, tsarawa, da kuma adana duk wani littafi da aka buga a ƙasar.

    6. Ɗakunan karatu na dijital

    Ana amfani da su ta hanyar intanet, waɗanda ke samar da damar karatu ga kayayyaki kamar e‑books, mujallu, da bayanai daga nesa. Wannan nau’in ɗakin karatu yana da matuƙar amfani wajen shawo kan tsaiko na lokaci da wuri. Misali, National Virtual Library of Nigeria, manufarsa ita ce faɗaɗa damar samun kayan karatu ta hanyar yanar gizo.

    Tarihin ɗakin karatu

    Tarihin ɗakunan karatu ya zama kusan daidai da tarihin ɗan’adam. Ɗakunan karatu na farko sun fara ne a Mesopotamia inda aka riƙe allunan laka (clay tablets) da ke ƙunshe da bayanai da adabi a mashaya da palasoni. Wasu daga waɗannan suna da shekaru tun abin da ya kai 2600 BCE. Library of Ashurbanipal, a Nineveh, wanda aka kafa kusan ƙarni na 7 BCE, shi ne ɗaya daga cikin tsoffin ɗakunan karatun da ke da ƙarin tarin adabi, ilimi, da addini.

    A zamanin da can, ɗakin karatu mafi shahara shi ne Library of Alexandria,  a ƙasar Masar, wanda aka kafa a ƙarni na 3 BCE. An ce yana da dubban rubutun da kuma tarihin da ya ja hankalin masana daga ko’ina cikin tsohon zamanin da ya shuɗe. Abin takaicin shi ne ƙonewar wannan ɗakin karatu ya jawo ɓacewar bayanan adabi masu daraja marasa adadi.

    A lokutan zamani, lokacin da aka ƙirƙiri injin buga littafi (printing press) a ƙarni na 15, ya sauƙaƙa yadda ake samun littattafai da kuma sa su yaɗu cikin sauƙi. Wannan ya haifar da haɓakar ɗakunan karatu na jama’a a ƙarni na 17 zuwa 18, wanda ya ba kowa dama samun ilimi.

    A Najeriya, ra’ayin ɗakin karatu na zamani ya faru ne yayin zamanin mulkin mallaka. Lokacin, ɗakunan karatu na farko ana samun su ne a cibiyoyi na mulkin mallaka da makarantu na mishinari. An kafa National Library of Nigeria a shekarar 1964 domin zama babban ɗakin karatu na ƙasa. Tun daga wannan lokacin, an buɗe ɗakunan karatu a jami’o’i, makarantu, da na jama’a a faɗin ƙasar, wanda suke fuskantar ƙalubale irin na kayan aiki, ilimin ma’aikata, da sauransu.

    Muhimmancin ɗakin karatu

    Muhimmancin ɗakunan karatu a kowace al’umma ba za a misalta shi ba. Ginshiƙi ne ga cigaban ilimi da bunƙasa tunani. Yana tallafa wa tsarin ilimi na makaranta da na neman ilimi kai-tsaye ta hanyar ba da damar samun littattafai, mujallu, da sauran kayan ilmantarwa. Ɗalibai sun dogara ga ɗakunan karatu wajen yin ayyukan gida, bincike, da shiri don jarabawa.

    Ɗakunan karatu suna taimaka wa masana kimiyya da bincike wajen samun mujallu da takardu na kimiyya waɗanda ke ba da bayanan da ke tallafa wa ayyukansu. Idan ba a samu ɗakunan karatu ba, to cibiyar bincike da ƙirƙira za ta yi matuƙar rauni.

    Bugu da ƙari, ɗakunan karatu suna ƙarfafa ƙwarewar karatu da ƙarfafa ɗabi’ar karanta littafi. Wannan yana da matuƙar mahimmanci musamman a ƙasashe masu tasowa kamar Najeriya, inda littattafai a gida kaɗai kan iya yin ƙaranci saboda talauci. Ɗakunan karatu suna samar da mahalli ga yara da manya su haɓaka ɗabi’ar karatu, wanda hakan ke inganta musu fahimta da tunani mai zurfi.

    0c1c2d1a59a1a052ae35d016cf3f3ea9
    Kofar shiga shalkwatar Ɗakin Karatu na Ƙasa

    Haka kuma, ɗakunan karatu suna aiki a matsayin cibiyoyin al’umma. Ɗakunan karatu na jama’a sau da yawa suna shirya shirin karatun litattafai, bita na ƙwarewar sana’a, koyon amfani da kwamfuta, da sauran wasannin ilimi. Waɗannan shirye‑shirye na taimaka wajen haɗa kan al’umma.

    Bugu da ƙari, ɗakunan karatu suna adana al’adun ƙasa da tarihinta. Ɗakunan karatu na ƙasa da na musamman na adana jaridu, littattafai, hotuna, da rubuce‑rubuce waɗanda ke ajiye tarihin ƙasa. Wannan tabbas ana buƙatar hakan don al’ummu masu zuwa su samu hanyar sake komawa ga tarihin ƙasa.

    Matsalolin ɗakunan karatu a Najeriya

    Kodayake ɗakunan karatu suna da matuƙar muhimmanci, a Najeriya suna fuskantar matsaloli iri‑iri waɗanda ke rage ingancinsu. Daya daga cikin manyan matsaloli shi ne rashin isasshen kuɗi. Yawancin ɗakunan karatu, musamman na jama’a da makarantu, ba sa samun tallafi mai kyau daga gwamnati ko hukumomin da suka dace. Wannan na haifar da wahalar sarrafa tarin kayan karatu, sabunta kayan aiki, ko biyan ma’aikata yadda ya kamata.

    Matsalar gine‑gine ma ta kasance babbar ƙalubale. Wasu ɗakunan na aiki ne a cikin gine‑ginen da suka tsufa, ba su da haske mai kyau, iska, wuraren zama, ko tsaro. Wasu ma ba su da wutar lantarki ko haɗin intanet wanda ke da muhimmanci a zamanin dijital.

    Bugu da ƙari, yawancin kayan karatu da ake da tsaffi ne ko kuma ba su da alaƙa da cigaban kimiyya da fasaha. Ƙalubalen nan yana da matuƙar tasiri ga ɗalibai da masana da ke buƙatar bayanai na zamani.

    Akwai ƙarancin ma’aikata ƙwararru a fannoni kula da ɗakunan karatu. Wasu wurare suna ɗaukar ma’aikata marasa horo wanda kuma hakan ke haifar da tsaiko wajen tsara kayan karatu, jagoranci ga masu amfani, da kuma ingancin hidima.

    Matsalolin fasaha har ila yau suna kasancewa babbar matsala. Duk da cewa an mayar da hankali dangane da ɗakunan karatu na dijital a duniya, yawancin ɗakunan a Najeriya ba su da kayan aiki da tsari na samar da nau’ikan kayan dijital. Wannan na haifar da rashin damar samun e‑books, mujallu na kimiyya, da bayanai na intanet.

    Bugu da ƙari, ra’ayoyin jama’a game da ɗakunan karatu na da naƙasu. Mutane da dama, musamman a kauyuka, ba su sani ba cewa ɗakunan karatu na da amfani sosai, ko kuma ba su ɗauke su a matsayin muhimman wurare ba. Wannan ya samo asali ne daga rashin tsare‑tsare na gwamnatin da ke ƙarfafa amfani da ɗakunan karatu.

    Hanyoyin magance matsalolin ɗakunan karatu a Najeriya

    Domin shawo kan waɗannan ƙalubalen da aka ambata a sama, akwai matakai da dama da za a ɗauka domin inganta ɗakunan karatu a Najeriya.

    Na farko, akwai buƙatar ƙarin zuba jari daga gwamnati. Samar da kuɗi mai yawa zai taimaka wajen gina sabbin ɗakunan karatu, gyara tsofaffi, sayan sabbin kayayyaki, da kuma ɗaukar ma’aikata waɗanda suka kware.

    Tsarin haɗin gwiwa (Public‑Private Partnerships) zai taka rawa sosai. Kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyoyi da hukumomi na ƙasashen waje za su iya tallafa wa ayyukan ɗakunan karatu ta hanyar bayar da kayan aiki, horo, da gudummawar ICT.

    Ƙarin wani mataki shi ne haɓaka horo da ɗaukar ma’aikata ƙwararru. jami’o’i da ke koyar da ilimin ɗakin karatu (library science) ya kamata su zama masu ƙarfi; ta hanyar faɗaɗa karatu da samar da ƙwararru waɗanda za su shiga wannan fanni. Haka kuma, ya zama dole a samar da ƙarin horo ga ma’aikatan da ke aiki domin su cigaba da sanin tsarin zamani.

    Gine‑gine da kayan aiki su ma su zama masu inganci. Ya kamata ɗakunan karatu su samu wutar lantarki, kwamfutoci, intanet, da kuma yanayi mai kyau na karatu. Wannan zai jawo hankalin masu amfani da ɗakunan karatun, musamman matasa, domin sun ga ɗakin karatu a matsayin wuri mai kyau kuma mai amfani.

    Har ila yau, a yi ƙoƙarin zamanantar da tarin kayayyakin karatu da gina shafukan da manhajoji na yanar gizo domin samar da damar karatu daga nesa. Wannan zai taimaka sosai ga ɗalibai da ke kauyuka ko wuraren da ba za su iya zuwa ɗakin karatu ba, musamman a lokutan kama‑ciki ko annoba.

    Daga ƙarshe, ya zama wajibi a gudanar da gangamin wayar da kai game da amfani da ɗakunan karatu. Makarantu, kafafen watsa labarai, da shugabannin al’umma za su yi aiki tare wajen haska wa mutane muhimmancin ɗakunan karatu. Haka nan, ya kamata gwamnati ta ƙarfafa manufofi da dokoki da ke tabbatar da ɗaukar ɗakunan karatu cikin tsare‑tsaren cigaban ƙasa da ilimi.

    Manazarta

    Agboke, A. L., & Oladokun, B. D. (2025). Emerging technologies in academic libraries: prospects and challenges in Nigeria. Communicate: Journal of Library and Information Science, 26(2), 10–20.

    Governor, A. H., & Guobiazor, I. R. (2024). Challenges and prospects in the 21st century academic libraries in Delta State, Nigeria. Social Sciences Journal of Policy Review and Development Strategies, 6(1), 40–43.

    Umaru Musa Yar’adua University Library Staff. (2025). An appraisal of library infrastructure for effective service delivery by library staff in university libraries in North-West Nigeria. Global Scientific Journal, 13(5), May 2025.

    National Library of Nigeria. (n.d.). About the National Library. 

    Adebayo, O., & Oyewole, O. (2019). Public libraries in Nigeria: Challenges and prospects in the digital age. Library Philosophy and Practice, 1–14.

    *** Tarihin Wallafa Maƙalar ***

    An kuma sabunta ta 14 August, 2025

    *** Sharuɗɗan Editoci ***

    Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.

    Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.

    Maƙalar ta amfanar?
    EAa

    You cannot copy content of this page

    ×