Darbejiya itaciya ce wadda ake kira da neem a turance. A hausance ana kiran ta da darbejiya ko dalbejiya ko kuma bedi. Ana kuma kiran ta da suna azadirachta indica, sunan da masana suka gano cewa, ya samu ne daga harshen Persian da Sanskrit. Itaciya ce mai matuƙar amfani da tasiri ga rayuwar al’umma.

Asalin samuwar darbejiya
Asalinta ya samu ne daga ƙasar Indiya da yankunan kudu maso yammacin Asiya. An samo hujjar kasancewar ta a dazukan da ke tsakanin ƙasashen India, Myanmar (Burma), da Bangladesh tun shekaru aru-aru da suka wuce.
Yaɗuwar ta zuwa wasu ƙasashe
Bincike daga masana wajen gano amfaninta ya sanya ta soma yaɗuwa, musamman masu amfani da ita a ƙasar Indiya. Daga nan sai Turawan mulkin mallaka suka fara yaɗa ta zuwa Afirka da ƙasashen Larabawa a ƙarni na 19.
A lokacin mulkin mallaka, ‘yan kasuwa daga Indiya da masu aikin gona sun kawo iri ko ‘ya’yan darbejiya zuwa yankin Afrika ta Yamma, musamman Najeriya, Sudan, da kum Nijer.
Yaɗuwarta a Najeriya
A Najeriya, ta fara shahara ne a yankunan Arewa saboda yanayin ƙasa da zafi ya dace da ita. Daga cikin abin da ya sa bishiyar darbejiya ta yaɗu a Najeriya akwai: yanayin ƙasa da zafi:Darbejiya tana jure zafi sosai, tana girma a yankunan da ruwan sama bai yi yawa ba. Saboda haka ne aka fi ganin ta a Arewacin Najeriya musamman Kano, Katsina, Sokoto, da Borno inda aka saba kiran ta “darbejiya” ko “bedi”.
Sassan darbejiya
Darbejiya tana da sassa daban-daban waɗanda suka ƙunshi:
Ganyen darbejiya
Ganyen darbejiya wani muhimmin ɓangare ne na itaciyar. Ana ɗaukar ganyen ta a matsayin sashen da ya fi amfani wajen magunguna, tare da sarrafa kayayyakin amfanin gyaran fata da ma gida. Ganyen yana da nau’in ƙamshi mai ɗan ɗaci, kuma yana ɗauke da sinadarai masu ƙarfi waɗanda ke da tasiri ga lafiyar ɗan Adam da muhalli.
Ganyen darbejiya yana cikin tsarin compound pinnate, wato ganye ɗaya na iya ɗauke da ƙananan ganyaye 10 zuwa 15 da ke da siffa siririya. Launinsa koren ne mai ɗan kauri da santsi. Ana iya samun launin kore mai duhu ko kuma mai haske. Ganyen darbejiya yana ɗauke da sinadarai masu muhimmanci kamar:
- Azadirachtin: Yana taimakawa wajen kashe ƙwari da ƙwayoyin cuta.
- Nimbin: Yana da tasirin rage kumburi da zafi.
- Quercetin-antioxidant: Yana taka rawa wajen kare ƙwayoyin halittar jiki daga lalacewa.
- Sodium nimbinate: Wannan nau’in shi ne mai taimakawa wajen rage damuwa da zafin ciki.
Tsayin reshen ganyen darbejiya gabaɗaya yana kaiwa 20–40 cm, wani lokaci har 45 cm. Ganye guda ɗaya kuma yana ɗauke da 3-8 cm.
‘Ya’yan darbejiya
‘Ya’yan darbejiya suna daga cikin muhimman abubuwan dake tare da ita, domin su ne sassan itaciyar da ake amfani da su wajen samar da darbejiya bayan an shuka su. Ana ɗaukar su a matsayin ɗaya daga cikin muhimman kayayyakin da ake fitarwa daga wannan itaciya saboda yawan amfaninsu ga lafiya, aikin gona, da kuma masana’antu.

’Ya’yan Darbejiya suna cikin nau’in drupe, wato ‘ya’yan da ke da ɓawon waje mai laushi, sannan a ciki akwai ƙashi da ƙwayar ɗa guda ɗaya.
- Launinsu: A lokacin da suke sabbi suna kasancewa koraye masu duhu, amma yayin da suka nuna ma’ana suka ƙara girma suna zama launin rawaya mai haske wasu lokutan mai duhu.
- Girmansu: Tsayin ’ya’yan darbejiya yawanci yana tsakanin 1.4 zuwa 2.8 cm, kuma suna da ɗan ɗaci sosai.
- Ƙwallo: A cikin ’ya’yan akwai ƙwaya mai tauri wadda ke ɗauke da iri, wadda ta kasance guda ɗaya, wannan iri ne ake sarrafawa domin samun man darbejiya.
Binciken masana ya tabbatar da cewa, ‘ya’yan darbejiya suna fitowa sau ɗaya a shekara, musamman bayan lokacin bazara (Mayu zuwa Agusta) a ƙasashen da ke da yanayin zafi.
’Ya’yanata na ɗauke da sinadarai da yawa masu amfani, musamman:
- Azadirachtin
- Nimbin
- Salanin & Meliantriol
- Fatty acids (oleic acid, stearic acid, palmitic acid).
Itacen darbejiya
Itacen darbejiya na ɗaya daga cikin muhimman itatuwa masu amfani sosai. Yana da jiki mai kauri da tsawo, tare da rassan da ke bazuwa a ko’ina. Jijiyoyinsa suna da ƙarfi ƙwarai, suna iya huda ƙasa sosai, su bazu domin neman hanyar samun ruwa da kuma gina tushensu. Itacen yana iya rayuwa tsawon shekaru da dama ba tare da ya bushe ba, ko da a wurare masu zafi da fari. Wannan yana sa shi ya zama ɗaya daga cikin itatuwan da suka fi jure yanayin fari a nahiyar Afirka.
Man darbejiya
Man darbejiya yana samuwa ne ta hanyar cire ƙwayar kwalon darbejiya.
- Launi: Man darbejiya yana da launi koren mai duhu ko kuma launin rawaya mai ƙasa-ƙasa.
- Ƙamshi: Yana da ƙamshi mai ƙarfi wanda bai yi kama da man shafawa na yau da kullum ba.
- Ɗanci: Mai ɗan ɗaci ne, yana da kauri kaɗan.
- Sinadarai: Yana ɗauke da azadirachtin, nimbin, salannin, gedunin, waɗanda suke da matuƙar amfani wajen magunguna da kashe ƙwari yadda ya kamata.
Amfanin darbejiya
Darbejiya na da amfani ta fuskoki da dama, amfaninta ya rabu zuwa kaso daban-daban waɗanda suka ƙunshi:
Fanin magunguna
Ana amfani da ita ta fuskar magunguna, waɗanda suka shafi na gargajiya har da ma Turawa suna amfani da ita wajen sarrafa wasu magunguna da yawa na fanin lafiya. Musamman abin da ya shafi ɓangaren ƙasar Indiya da kuma China. Ga wasu daga cikin magunguna da darbejiya take yi ga lafiyar ɗan Adam:
Tazarar haihuwa
Ana amfani da man darbejiya ga mace ko namiji domin samar da tazarar haihuwa ba tare da an sha wata ƙwaya ko wani abu da ya danganci haka ba. Ana amfani da man ne ta hanyar haɗa shi da zuma cokali ɗaya sai man rabin cokali ƙarami a sha bayan tarawa da iyali da kuma kafin. Sai dai wannan ba kimiyya ko likitanci ba ne ya tabbatar.
Maganin murɗawar ciki
Ana amfani da ganyen darbejiya wani adadi a tafasa a saka gishiri kaɗan tare da ganyen gwanda domin maganin ciwon ciki mai murɗawa.
Wankan jego
Ana mafani da ganyen darbejiya wajen yi wa mai jego wanka. Wanda bisa al’ada ta malam Bahaushe hakan yana taka muhimmiyar rawa wajen ƙara mata lafiya. Tare da saukar da kumburin sabon jinin da yau hau ga mai jego ba tare da ya sanyata jiri ba. Ana kuma amfani da ruwan wajen yi wa jarirai wanka bayan haihuwa.
Haɗin sirace
Ana amfani da darbejiya bayan an haɗa ta da wasu ganyayyaki domin yi wa mara lafiya sirace. Musamman idan zazzaɓi ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Kuma hakan yana taimakawa wajen warkar da zazzaɓin.
Ciwon hanta
Duk da cewa ita hanta ba ta son abu mai ɗaci, haka kuma binciken masana ya tabbatae da cewa yawan amfani da kayan ɗaci na illata ta, amma in dai za a kiyaye da yanda ake sha to darbejiya na ɗaya daga cikin magungunan da ke kawar da ciwon. Ana samun ‘ya’yan darbejiya rabin gwangwanin tumatir a tafasa a sha da zuma da safe.
Ciwon haƙora
Binciken masana ya tabbatar da cewa yawan yin aswaki da itacen darbejiya, ban da sanya haƙora su yi fari, kuma yana ƙara ƙarfin dasashi, ya hana ciwon haƙori, ya kuma hana warin baki da ƙurajen baki. Bugu da ƙari yana rigakafin wasu cututtukan baki.
Fanin kwaliya
Darbejiya na taka muhimmiyar rawa wajen kwalliya musamman ga mata.
Gashi
Ana amfani da man darbejiya wajen gyaran gashi, yana taimakawa gashi wajen samar da tsayi da kuma laushi har ma da baƙi.
Fata
Ana amfani da man darbejiya wajen gyaran fata, musamman fatar da take fama da kaushi ko kuma matsalar tsattsagewa a lokacin sanyi.
Ana amfani da ganyenta wajen kwaɓawa bayan an busar da shi a haɗa da wasu sinadarai domin kawar da ƙurajen fuska tare da ƙarawa fatar laushi da santi.
Fanin masana’antu
- Ana amfani da darbejiya domin samar da takin zamani.
- Ana amfani da ita wajen haɗa sinadaren dake cikin sabulai da kuma mayuka, saboda tana ɗauke da sinadaren da ke hana samuwar kumburi a fata.
- Ana amfani da ita a sabulai saboda tana ɗauke da sinadaren da ke kashe ƙwayoyin cuttutukan fata.
- Ana amfani ta ita wajen samar da shampoo, domin tana ɗauke da sinadaren da suke kashe amosani da wasu kurajen kai kamar makero.
- Ana amfani da ita wajan samar da capsule da tablet na ciwon sugar a ma’aikatar lafiya.
- Ana amfani da ita ta hanyar samar da maganin ƙwari da kuma maganin sauro.
- Ana amfani ta ita wajen samar da abin wanke baki, saboda tana ɗauke da antimicrobial property.
Fanin amfanin gida
Ana amfani itacen darbejiya domin samar da kayan amfani na gida waɗanda suka haɗa da:
- Turmi
- Taɓarya
- Kujerar tsuguno ta zama
- Itace domin yin girki.
Matsalolin darbejiya
Darbejiya tana da illa a wurare da dama, musamman idan an yi amfani da ita ba bisa ƙa’ida ba, domin tana iya jawo matsalar ciwon ciki da ƙaiƙayi a fata, sannan tana iya haddasa samuwar ɗaci a bakin wanda ya sha ta, wasu lokutan ma har da amai.
Haka kuma tana da illa ga mata masu juna biyu saboda tana iya zubar da ciki idan an sha ta da yawa.
Darbejiya tana iya sauya aikin hanta ko ƙoda idan an sha mai yawa, sannan tana iya gurɓata jini ga yara ƙanana.
Haka kuma tana iya kashe ƙwayoyin halitta na ƙwari marasa cuta idan an yi amfani da man ta da yawa, sannan tana iya gurbata ruwa ko ƙasa idan aka zuba man darbejiya ba tare da kulawa da yanayin yadda aka zuba ba.
Manazarta
Braga, T.M., et al. 2021. Azadirachta indica A. Juss. In Vivo Toxicity—An Updated Review. Molecules, 26(2), 252.
Ishaq, M. (2019a, December 19). Amfanin ganyen dalbejiya guda 16 a jikin dan adam. Legit.ng – Nigeria News.
Wikimedia projects. (2024, July 31). ICen Dalbejiya (Azadirachta indica). Wikipedia.
Zee Darul Sunnah TV. 2023. Amfanin Ganyen Delbajiya (Neem Tree 16) – Dr. Abdulwahab Abubakar G/Bauchi YouTube.
Sharuɗɗan Editoci
Duk maƙalun da kuka karanta a wannan taska ta Bakandamiya, marubuta da editocinmu ne suka rubuta. Kuma kowace maƙala da aka buga ta bi muhimman matakai na tantancewa don ganin cewa bayanan dake cikinta sun inganta.
Idan kuma an ga wani kuskure a cikin kowace maƙalarmu, a sanar da mu. Za mu yi bincike sannan mu gyara gwargwadon fahimtarmu.
